Terms Dictionary

Ja - Tana nufin launin ja. Misali; Akwai launin ja a jikin kayan da ya saka. ENG; Red (A turance tana nufin ja)
Ja - Tana nufin janyowa. Misali; Ya ja igiyar da ƙarfi shi yasa ta tsinke. ENG; Pull/Drag (A turance tana nufin ja)
Ja’iba - Tana nufin masifa ko rashin sa'a ko ibtila'i. Misali; Ya ga ja'iba, bayan ya rasa ɗansa shagonsa ya kama da wuta. ENG; Misfortune/Calamity (A turance tana nufin ja'iba)
Ja’iri - Tana nufin mara kunya. Misali; Babu mai yin rawar Gala sai ja'iri. ENG; Shameless/Disrespectful Person (A turance tana nufin ja'iri)
Ja-gaba - Tana nufin shugaba ko jagora. Misali; Annabi SAW shi ne ja-gaban dukkan halitta. ENG; Leader/Guide (A turance tana nufin ja-gaba)
Jabu - Tana nufin abin da ba shi da inganci. Misali; Madarar jabu ce, idan aka sha tana sa ciwon ciki. ENG; Fake (A turance tana nufin jabu)
Jackal - A turance tana nufin dila.  Misali; Akwai dila a cikin dabbobin da na gani a gidan ajiye namun daji. HAU; Dila (Tana nufin wata dabba mai kama da akuya amma ta fi akuya siranta)
Jaddada - Tana nufin tabbatarwa. Misali; Shugaban makarantarmu ya jaddada mana muhimmancin taron iyayen yara da za a yi gobe. ENG; Reform (A turance tana nufin jaddada)
Jagab - Tana nufin tsananin jiƙewa. Misali; Ruwa ya jiƙa su jagab saboda ba su daɗe da fita ba ya sakko. ENG; Very Wet (A turance tana nufin jagab)
Jahili - Tana nufin wanda ba shi da ilimi. Misali; Rashin zuwa makaranta ne ke mai da mutum jahili. ENG; Illiterate Person (A turance tana nufin jahili)
1 2 3 10