Vein - A turance tana nufin jijiya.
Misali; Allurar jijiya aka yi masa saboda zafin zazzaɓin.
HAU; Jijiya (Tana nufin hanyar jini a jikin mutum ko dabba)
Verdict - A turance tana nufin hukunci.
Misali; Duk wanda ya aikata laifi, za a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata.
HAU; Hukunci (Tana nufin matsayi ko sakamakon abin da aka aikata ko za a aikata)
Very Short - A turance tana nufin ɗigil.
Misali; Na ga wani ɗan ɗigil a kasuwa yau.
HAU; Ɗigil (Tana nufin ɗan gajere ko ƙanƙani)
Very Sweet - A turance tana nufin carkwai.
Misali; Raken yana da zaƙi carkwai.
HAU; Carkwai (Tana nufin zaƙi sosai)
Very Wet - A turance tana nufin jagab.
Misali; Ruwa ya jiƙa su jagab saboda ba su daɗe da fita ba ya sakko.
HAU; Jagab (Tana nufin tsananin jiƙewa)
Veterinary Conucil of Nigeria (VCN) - Majalisar Likitocin Dabbobi Ta Najeriya
Vigilante Group of Nigeria (VGN) - Hukumar Jami'an Banga Ta Najeriya
Village Head - A turance tana nufin dagaci.
Misali; An naɗa shi dagaci a ƙauyensu.
HAU; Dagaci (Tana nufin shugaban ƙauye)
Voice Of America (VOA) - Muryar Amurka
Voice of Nigeria (VON) - Muryar Najeriya