Short - A turance tana nufin guntu.
Misali; Da wani guntun itace na ƙarasa girkin.
HAU; Guntu (Tana nufin mara tsayi)
Kishiyarta; Dogo/ Mai tsayi
Shoulder - A turance tana nufin kafaɗa.
Misali; 'Yan mata na rawar girgiza kafaɗa a dandali.
HAU; Kafaɗa (Tana nufin sashen jiki da ke saman hannu)
Shoulder of Meat - A turance tana nufin karfata.
Misali; Karfata na samu a rabon naman da aka yi.
HAU; Karfata (Tana nufin kafaɗar naman rago ko sa ko raƙumi da sauransu)
Shouting - A turance tana nufin kuwwa.
Misali; Yara na waje suna kuwwa saboda saukar ruwan sama na farko.
HAU; Kuwwa (Tana nufin ƙara)
Shouting - A turance tana nufin kururuwa.
Misali; Sadiƙ yana da rowa idan aka ɗauki abinsa kururuwa yake.
HAU; Kururuwa (Tana nufin ihu da ƙarfi)
Showing eagerness - A turance tana nufin hanƙoro.
Misali; Tun safe yake hanƙoro, saboda za su buga ƙwallon ƙafa da abokansa.
HAU; Hanƙoro (Tana nufin nuna zaƙuwa)
Showing Energy - A turance tana nufin kuzari.
Misali; Jaririn yana da cikakken kuzari masha Allah.
HAU; Kuzari (Tana nufin ƙarfi da lafiya)
Shrilling done by women to express joy - A turance tana nufin guɗa.
Misali; Matan sun kaure da guɗa a lokacin da aka shigo da amaryar.
HAU; Guɗa (Tana nufin wani salo na sarrafa ihu da mata ke yi musamman a lokutan farin ciki)
Side - A turance tana nufin gefe.
Misali; Na ajiye kayan a gefen rijiya.
HAU; Gefe (Tana nufin wani sashe)
Sign/Indication - A turance tana nufin ishara.
Misali; Duk wanda ya yi mugunta sai ya ga ishara kafin ya mutu.
HAU; Ishara (Tana nufin nuni ko alama)