Terms Dictionary

Sense - A turance tana nufin hankali. Misali; Idris yana da hankali da sanin ya kamata. HAU; Hankali (Tana nufin sanin ya kamata) Kishiyarta: Rashin Hankali
September - A turance yana nufin wata na tara a shekara.  Misali; Sabon zangon karatuna farawa ne a watan Satumba. HAU; Satumba (Wata ne na tara a shekara)  
Sermon - A turance tana nufin huɗuba. Misali; Muna sauraron huɗuba daga masallaci mai alfarma a rediyo. HAU; Huɗuba (Tana nufin jawabai na hikima da jan hankali don faɗakarwa ko kwaɗaitarwa a kan binn Allah da kuma gujewa saɓa masa)
Servant - A turance tana nufin bara. Misali; Idris bara ne a gidan Alhaji Sani. HAU; Bara (Tana nufin mai yin hidima a cikin gida)
Service - Hukuma, Ma'aikata
Serving God - A turance tana nufin ibada. Misali; Idan mutum ya kasance mai ibada rayuwarsa tana albaraka. HAU; Ibada (Tana nufin bautawa Allah)
Set Aside - A turance tana nufin keɓe. Misali; Sun keɓe suna tattaunawa saboda batun yana da muhimmanci. HAU; Keɓe (Tana nufin warewa gefe)
Setting one person against another through gossip - A turance tana nufin gulma. Misali; Musulunci ya haramta gulma. HAU; Gulma (Tana nan nufin ɗaukar zancen wani a kai wa wani da zimmar haɗa su faɗa)
Sexual Intercourse - A turance tana nufin jima'i. Misali; Cututtukan sanyi na da nasaba da jima'i a lokuta da dama. HAU; Jima'i (Tana nufin saduwa tsakanin mace da namiji)
Shake - A turance tana nufin jijjiga. Misali; Sai an jijjiga maganin sannan ake sha. HAU; Jijjiga (Tana nufin girgizawa)
1 264 265 266 267 268 300