Terms Dictionary

Scalp Disease - A turance tana nufin kora. Misali; Yana da kora, idan ka sa hularsa za ka iya ɗauka kuma lalura ce mai wuyar sha'ani. HAU; Kora (Tana nufin nau'in cutar fata da yake fitowa a kai)
Scheme - Shiri, Tsari
Science Teachers Association of Nigeria (STAN) - Ƙungiyar Malaman Kimiyya Ta Najeriya
Scorpion - A turance tana nufin kunama. Misali; Kunama ce ta harbi Lado a ƙafa. HAU; Kunama (Tana nufin ƙwaro mai cizo kuma mai dafi)
Scratch - A turance tana nufin kuje. Misali; Amir ya faɗi ya kuje a gwuiwa. HAU; Kuje (Tana nufin jin ciwo a saman fata)
Seal - A turance tana nufin hatimi. Misali; Wasiƙar tana ɗauke da hatimin sarki. HAU; Hatimi (Tana nufin wata shaida ko alama)
Search - A turance tana nufin caje. Misali; Na caje yaran duka ban ga wanda ya ɗauki littafin ba. HAU; Caje (Tana nufin duba ko ina)
Search - A turance yana nufin biɗa. Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi. HAU; Biɗa (Tana nufin nema ko lalube)
Second (of time) - A turance tana nufin daƙiƙa. Misali; Na samu faɗuwar gaba na tsawon daƙiƙa ashirin saboda firgicin da na shiga. HAU; Daƙiƙa (Tana nufin motsawar da ƙaramin hannun agogo yake yi)
Secret - A turance tana nufin asiri.  Misali; An tonawa mutumin asiri, dama ya daɗe yana  satar kayan mutane. HAU; Asiri (Tana nufin abinda yake a ɓoye)
1 262 263 264 265 266 300