Terms Dictionary

Sallah - Sallah wata nau'in ibace da mutane musulmai suke gabatar da ita a matsayin bauta ga Allah da yayi halitta. Jam'i ; Salloli
Salt - A turance tana nufin gishiri. Misali; Kirarinsa shi ne: Gishiri in ba kai ba miya. HAU: Gishiri (Tana nufin sinadarin da ke ba wa abinci ɗanɗano)
Saluting a superior - A turance tana nufin jinjina. Misali; Shugaban sojojin yana shigowa ɗakin taron aka yi masa jinjina. HAU; Jinjina (Tana nufin gaisuwar ban-girma)
Sand Lice - A turance tana nufin kurkudu. Misali; Yaran sun kamo kurkudu a lokacin da suke wasa. HAU; Kurkudu (Tana nufin wani ƙwaro da yake fitowa a cikin rairayi)
Sarcasm - A turance tana nufin gatse. Misali; Ta yi musu gatse tace su faɗa wuta. HAU; Gatse (Tana nufin a faɗi abu saɓanin abinda ake nufi)
Satan - A turance tana nufin sheɗan. Misali; Allah ya raba mu da sharrin sheɗan. HAU; Sheɗan (Tana nufin sheɗan)
Satchel - A turance tana nufin gafaka. Misali; Malamin ya saka Al'ƙur'ani a gafaka. HAU; Gafaka (Tana nufin jakar fata da ake yi musamman don saka littattafai)
Satumba - Wata ne na tara a shekara.  Misali; Sabon zangon karatuna farawa ne a watan Satumba. ENG; September (A turance yana nufin wata na tara a shekara)  
Saturday - A turance tana nufin rana ta shida a mako.  Misali; Ranar Asabar ne bikin. HAU; Asabar (Rana ce ta shida a ranakun mako)
Sayings of prophet Muhammad SAW - A turance tana nufin Hadisi. Misali;Malam Ado yana karanta mana hadisi kullum a makaranta. HAU: Hadisi (Tana nufin maganganun manzon Allah SAW)
1 261 262 263 264 265 300