Risk Managers Association of Nigeria (RIMAN) - Ƙungiyar Manajojin Tsagaita Asara Ta Najeriya
Risk, Accident - A turance tana nufin haɗari.
Misali; 1. Shaƙar hayaƙin taba na da haɗari ga lafiya.
2. Ya samu karaya sakamakon haɗarin mota.
HAU; Haɗari (Tana nufin abin da zai iya cutarwa, ko tsautsayin da ke faruwa a kan titi)
Rivalry/Opponent - A turance tana nufin hamayya.
Misali; Abokan hamayya ne su a siyasa shi yasa ba sa ga maciji.
HAU; Hamayya (Tana nufin kishi ko takun saƙa)
River - A turance tana nufin kogi.
Misali; An tsinci jariri a bakin kogi ranar Asabar.
HAU; Kogi (Tana nufin ruwa mai gudana)
River - A turance tana nufin gulbi.
Misali; Indo da ƙawayenta sun tafi gulbi yin wanki.
HAU; Gulbi (Tana nufin kwari da ruwa yake taruwa)
Road Transport Employers’ Association of Nigeria (RTEAN) - Ƙungiyar Direbobi Ta Najeriya
Road/ Path - A turance tana nufin hanya.
Misali; Gwamnati ta gina hanya a tsakanin ƙauyukan guda biyu.
HAU; Hanya (Tana nufin guri ko inda ake wucewa)
Roaming about leading a loose, carefree life - A turance tana nufin dandi.
Misali; Ta dawo daga yawon dandi ɗauke da cuta mai tsanani.
HAU: Dandi (Tana nufin yawo da rayuwa ta rashin mafaɗi)
Rolling on the ground - A turance yana nufin birgima.
Misali; Yaron yana ta birgima don an hana shi fita wasa.
HAU; Birgima (Tana nufin a yi ta juyi a ƙasa)
Roof Of The Mouth - A turance tana nufin ganɗa.
Misali; Ƙuraje sunm fito masa a saman ganɗa, sun hana shi cin abinci.
HAU; Ganɗa (Tana nufin saman bakin mutum)