Terms Dictionary

Republic - A turance tana nufin jamhuriya. Misali; Jamhuriyar Niger ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za a yi amfani da shi a ƙasar. HAU; Jamhuriya (Tana nufin ƙasar da ke da tsarin mulki na musamman)
Rest/Holiday - A turance tana nufin hutu. Misali; Yara ba sa zuwa makaranta saboda an ba su hutu. HAU; Hutu (Tana nufin zama guri ɗaya ba tare da aikin komai ba ko rashin zuwa gurin aiki ko makaranta ko gyurin sana'a na wani lokaci don a tsahirta kafin a ɗora)
Reticence - A turance tana nufin kawaici. Misali; Laure tana da kawaici shi yasa suke mata abinda suka ga dama. HAU; Kawaici (Tana nufin ɗauke kai ko yin shiru a kan abinda ya kama mutum ya yi magana amma sai ya yi shiru)
Revenue Mobilization, Allocation & Fiscal Commission (RMAFC) - HukumarTattarowa da Kasafta Haraji Ta Ƙasa
Rhinoceros - A turance tana nufin karkanda. Misali; Ba a ganin karkanda sai a ƙungurmin daji. HAU; Karkanda (Tana nufin ɗaya daga cikin dabbobin daji mai matuƙar ƙarfi)
Rib - A turance tana nufin haƙarƙari. Misali; Sanyi ya sa min ciwon haƙarƙari. HAU; Haƙarƙari (Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jikin ɗan Adam, gefen hagu da daman ƙirji)
Ridge-row on farm - A turance tana nufin kunya. Misali; Iro ya noma kunya bakwai yau a gona. HAU; Kunya (Tana nufin dogwayen tudu-tudun da ke gona)
Rinse - A turance tana nufin ɗauraye. Misali; Na ɗauraye kwanon kafin in zuba abinci. HAU; Ɗauraye (Tana nufin sa ruwa a sake wanke abu)
Rinse (Mouth) - A turance tana nufin kurkure. Misali; Idan za a yi alwala ana kurkure baki sau uku ne. HAU; Kurkure (Tana nufin zuba ruwa a jujjuya shi a cikin baki da zimmar ɗurayewa)
Risk - A turance tana nufin kasada. Misali; Bin hanyar nan kasada ne saboda akwai 'yan ta'adda a wajen. HAU; Kasada (Tana nufin yin abu mai hatsari ko ganganci)
1 258 259 260 261 262 300