Rat/Mouse - A turance tana nufin kusu.
Misali; Na ga kusu a cikin ɗakin ajiya, dole sai mun sa magani.
HAU; Kusu (Tana nufin ɓera)
Raw Materials Research & Development Council (RMRDC) - Hukumar Bunƙasa Binciken Ɗanyen Kaya
Reach Limit - A turance tana nufin intaha.
Misali; Darasin ya zo intaha, sai mun haɗu wani lokaci sai mu ɗora.
HAU; Intaha (Tana nufin ƙarshe)
Reading - A turance tana nufin karatu.
Misali; Tun safe ɗaliban suke karatu ba ƙaƙƙautawa.
HAU; Karatu (Tana nufin ambaton abinda aka rubuta)
Real Estate Developers Association of Nigeria (REDAN) - Ƙungiyar Masu Sana'ar Gina Mahalli Ta Najeriya
Reap - A turance tana nufin girbi.
Misali; Manoman na cikin farin ciki sakamakon lokacin girbi ya yi.
HAU; Girbi (Tana nufin kwashe amfanin gona bayan ya gama nuna)
Reason - A turance tana nufin hujja.
Misali; Sun yi rashin nasara saboda ba su da ƙwaƙƙwarar hujja a shari'ar.
HAU; Hujja (Tana nufin dalili)
Reckoning up the good and bad deeds of a person on judgement day - A turance tana nufin hisabi.
Misali; Muna fatan samun dace a ranar hisabi.
HAU; Hisabi (Tana nufin lissafa ayyukan mutum masu kyau da marasa kyau a ranar lahira)
Red - A turance tana nufin ja.
Misali; Akwai launin ja a jikin kayan da ya saka.
HAU; Ja (Tana nufin launin ja)
Reform - A turance tana nufin jaddada.
Misali; Shugaban makarantarmu ya jaddada mana muhimmancin taron iyayen yara da za a yi gobe.
HAU; Jaddada (Tana nufin tabbatarwa)