Terms Dictionary

Putting a pot on the fire - A turance tana nufin girka. Misali; Ta girka tukunya, ba za mu tafi ba sai ta sauke. HAU; Girka (Tana nufin ɗora tukunya a kan wuta)
Quantity Surveyors Registration Board Of Nigeria (QSRBN) - Hukumar Maƙiyasta Kayan Gini Ta Najeriya
Quarrel - A turance tana nufin faɗa. Misali; Ɗaliban faɗa suke bayan an tashi daga makaranta. HAU;Faɗa (Tana nufin ɗaga murya da faɗin maganaganu marasa daɗi saboda ɓacin rai)
Quick Action/ Haste - A turance tana nufin garaje. Misali; Indo tana da garaje, shi yasa ta zubar da niƙan. HAU; Garaje (Tana nufin hanzari ko sauri ko zafin nama)
Quick-Tempered - A turance tana nufin ƙufula. Misali; Ƙufula ya yi har ta kai ga ya mare shi. HAU; Ƙufula (Tana nufin saurin fushi)
Radio, Television & Theatre Workers Union (RATTAWU) - Ƙungiyar Ma'aikatan Gidan Radiyo da Talabijin da Wasannin Daɓe
Rain-Cloud - A turance tana nufin girgije. Misali; Girgije ya lulluɓe sararin samaniya. HAU; Gajimare (Tana nufin gajimaren da yake ɗauke da ruwa)  
Rainy Season - A turance tana nufin damina. Misali; Lokacin damina ni'ima na sauka kuma ana samun iska sassanya. HAU; Damina (Tana nufin lokacin ruwan sama)
Raised Doorstep - A turance tana nufin dandali. Misali; Inna tana zaune a kan dandamali. HAU; Dandamali (Tana nufin ɗan tudu da ake yi kofar ɗaki)
Rape - A turance tana nufin fyaɗe. Misali; Ƙungiyar tana yaƙi da masu fyaɗe a jihar baki ɗaya. HAU; Fyaɗe (Tana nufin yin tarayya da mace ta ƙarfi ba da son ranta ba)
1 255 256 257 258 259 300