Prison - A turance tana nufin kurkuku.
Misali; Jami'an sun tafi da masu laifin kurkuku.
HAU; Kurkuku (Tana nufin inda ake ajiye masu laifi, waɗanda aka yankewa hukunci da masu jiran hukunci)
Private Discussion - A turance tana nufin ganawa.
Misali; Shugaban makarantar na ganawa da malamai a ofishinsa.
HAU; Ganawa (Tana nufin tattaunawar sirri ko ta musamman)
Program - Shiri, Gidauniya
Project - Gidauniya, Aiki
Project Development Institute (PDI) - Cibiyar Naƙaltar Bunƙasa Ayyuka
Property - A turance tana nufin kadara.
Misali; Sun buƙaci ya kawo takardun wata kadara kafin su ba shi rancen kuɗi.
HAU; Kadara (Tana nufin kaya masu daraja ko kayan kuɗi)
Prophet - A turance yana nufin wanda Allah ya aiko.
Misali; Shugaban annabawa shi ne annabi Muhammad (S.A.W)
HAU; Annabi (Wanda Allah ya aiko da saƙon addini)
Prostitute - A turance tana nufin karuwa.
Misali; Ku karanta ƙissar karuwa da karen da ta ba wa ruwa, akwai darasi.
HAU; Karuwa (Tana nufin mace mai zaman kanta)
Protection - A turance tana nufin kandagarki.
Misali; Ya yi wa kansa kandagarki don ya san zai daku.
HAU; Kandagarki (Tana nufin kariya)
Proverb - A turance tana nufin karin magana.
Misali; Darasin da malamin Hausa ya koyar yau shi ne karin magana.
HAU; Karin Magana (Tana nufin zance na hikima mai ƙunshe da nuni ko habaici wanda ake yi don azanci ko huce haushi)