Pour much water - A turance tana nufin kuza.
Misali; Hindatu ta kuza ruwa a cikin shinkafar shi yasa ta yi luguf.
HAU; Kuza (Tana nufin zuba ruwa da yawa)
Powder - A turance tana nufin hoda.
Misali; An zubo hoda kala-kala a kayan lefen Tsahare.
HAU; Hoda (Tana nufin gari mai laushi da mata ke shafawa a fuska don yin ado, akwai ja akwai fara da sauransu)
Power/Authority - A turance tana nufin iko.
Misali; Shugabanni su ke da iko a kan mabiyansu.
HAU; Iko (Tana nufin ƙarfi ko isa)
Praise - A turance tana nufin kirari.
Misali; A kodayaushe akan yi wa mafarauta kirari kafin su tafi farauta.
HAU; Kirari (Tana nufin maganganun da ake yi wa mutum ko mutane don kwarzantawa ko kambamawa)
Presents of foodstuffs given by parents of bride to parent of groom - A turance tana nufin gara.
Misali; An yi wa amaryar gara ta ban mamaki.
HAU; Gara (Tana nufin kayan masarufi da iyayen mace ke haɗota da su bayan aure)
Press - A turance tana nufin danna.
Misali; Ina ta danna ƙofar amma ta ƙi buɗuwa.
HAU; Danna (Tana nufin amfani da hannu a ba da ƙarfi akan abu)
Prevent - A turance tana nufin hana.
Misali; An hana zuwa makaranta a makare.
HAU; Hana (Tana nufin ƙin ba da dama)
Price - A turance tana nufin farashi.
Misali; Ana ta ƙarawa kaya farashi a kasuwa saboda karyewar tattalin arziƙi.
HAU; Farashi (Tana nufin kuɗin abu)
Pride - A turance yana nufin alfahari.
Misali; Mata suna da yawan alfahari.
HAU; Alfahari (Jin isa ko fifiko akan wasu)
Primary School - A turance tana nufin firamare.
Misali; Farida ta shiga firamare.
HAU; Firamare (Tana nufin matakin farko na karatun boko)