Pipelines & Products Marketing Company (PPMC) - Kamfanin Bututu da Jigilar Tataccen Mai
Place - A turance tana nufin bigire.
Misali; Idan mutum yana sallah ana so ya kalli bigiren sujjadar sa.
HAU; Bigire (Tana nufin guri ko gurbi)
Plaiting Of Hair - A turance tana nufin kitso.
Misali; Mata su ne ke yin ado da kitso da ƙunshi.
HAU; Kitso (Tana nufin salon tufke gashi don ado da kwalliya)
Plants growing in farm from seeds unintentionally dropped on the ground - A turance tana nufin gyauro.
Misali; Mangwaron gyauro ne, kawai fitowa ya yi aƙofar gida.
HAU: Gyauro (Tana shukar da take fitowa a gona ko wani guri bayan an yar da ƙwallo ko iri)
Plate - A turance tana nufin faranti.
Misali; Ki zuba abincin a faranti don ya huce da wuri.
HAU; Faranti (Tana nufin mazubin abinci)
Plentiful - A turance tana nufin jingim.
Misali; Ya tara kayan wanki jingim a ɗaki, da ƙyar zai iya wankewa shi kaɗai.
HAU; Jingim (Tana nufin adadi mai yawa)
Pluck (hair, feathers) - A turance tana nufin fige.
Misali; Na biya kuɗi an fige min kajin da na siya.
HAU; Fige (Tana nufin cire gashi)
Poison - A turance tana nufin guba.
Misali; Na sa wa ɓeraye guba jiya da yamma.
HAU; Guba (Tana nufin duk wani abin da zai iya kisa)
Poison - A turance tana nufin dafi.
Misali; Dabbobin da suke da dafi suna da hatsari matuƙa.
HAU; Dafi (Tana nufin abin da ke iya kisa, zai iya kasancewa daga dabbobi ko wani abu daban)
Police Service Commission (PSC) - Hukumar Aikin 'Yansanda