Terms Dictionary

Polite - A turance tana nufin kintsattse. Misali; Ai da ganinsa an ga kintsattse, don kamanninsa sun nuna haka. HAU; Kintsattse (Tana nufin mutum mai kamala da nutsuwa)
Political Party - A turance tana nufin jam'iyya. Misali; Dukkansu 'yan jam'iyya ɗaya ne. HAU; Jam'iyya (Tana nufin zauren siyasa)
Poor, Destitute - A turance tana nufin faƙiri. Misali; Idan za ka yi sadaka ka nemi faƙiri ka ba shi. HAU; Faƙiri (Tana nufin talaka wanda ba shi da komai)
Portfolio & Debt Management Institute of Nigeria (PDMIN) - Cibiyar Naƙaltar Juya Dukiya da Bashi Ta Najeriya
Potash - A turance tana nufin kanwa. Misali; Ki ɗan jefa kanwa a waken don ya yi laushi da wuri. HAU; Kanwa (Tana nufin wani nau'in gishirin tabki mai ƙunshe da sinadarin sodium a ciki)
Potatoes - A turance tana nufin dankali. Misali; Ina son dankali musamman soyayye. HAU; Dankali (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci)
Poultry Association of Nigeria (PAN) - Ƙungiyar Makiwata Tsuntsaye Ta Najeriya
Pound - A turance tana nufin kirɓa. Misali; Za mu kirɓa sakwara a ranar bikin da yardar Allah. HAU; Kirɓa (Tana nufin daka abu sosai a cikin turmi)
Pound and Crush something - A turance tana nufin dandaƙa. Misali; Za mu dandaƙa geron kafin mu yi kunu da shi. HAU: Dandaƙa (Tana nufin daka abu har ya zama gari)
Pounding corn for pay - A turance tana nufin dakau. Misali; Matar Ado dakau take yi a unguwarsu. HAU: Dakau (Tana nufin yin daka a matsayin sana'a)
1 251 252 253 254 255 300