Permission - A turance tana nufin izini.
Misali; An ba shi izini ya fito neman auren Binta.
HAU; Izini (Tana nufin dama ko yarda ko amincewa)
Person of great energy - A turance tana nufin gwarzo.
Misali; Abdulhamid shi ne gwarzon wannan shekarar.
HAU; Gwarzo (Tana nufin mai ƙwazo)
Person of weak physical constitution - A turance tana nufin kumama.
Misali; Sadiq kumama ne, ko yaya aka yi ruwa sai ya sa rigar sanyi.
HAU; Kumama (Tana nufin mutum mai saurin jin sanyi)
Person with extra ordinary ability - A turance tana nufin hatsabibi.
Misali; Jauro hatsabibi ne, jiya ya shiga dajin da ba kowa ne yake shiga ya fito lafiya ba.
HAU; Hatsabibi (Tana nufin mutum mai ɗabi'un ban mamaki ko wanda yake abubuwan tsautsayin da ba kowa ne zai iya ba)
Person with sixth finger - A turance tana nufin cindo.
Misali; Jaririn da Latana ta haifa yana da cindo.
HAU; Cindo (Tana nufin wanda aka haifa da yatsu shida)
Petrol - A turance tana nufin fetur.
Misali; Fetur ya yi matuƙar tsada a Najeriya.
HAU; Fetur (Tana nufin man da ake zubawa a mota ko wani abin hawa don ya yi tafiya)
Petroleum & Natural Gas Senior Staff Association of Nigeria (PENGASSAN) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Kamfanin Fetur da Gas Ta Najeriya
Petroleum Equalizing Fund (management) Bord - Hukumar Daidaita Farashin Man Metur
Petroleum Products Pricing Regulatory Agency (PPPR) - Hukumar Ƙayyade Farashin Albarkatun Fetur
Petroleum Technology Development Trust Fund (PTDF) - Asusun Bunƙasa Fasahar Fetur