Terms Dictionary

Peace Corps of Nigeria (PCN) - Rundunar Zaman Lafiya Ta Najeriya
Pediatric Association of Nigeria (PAN) - Kungiyar Likitocin Yara Ta Najeriya
Penalty to atone for breaking certain islamic law - A turance tana nufin kaffara. Misali; Azumi uku ake yi a kaffarar rantsuwa. HAU; Kaffara (Tana nufin abin da mutum zai yi don karya rantsuwa ko sakamakon kisa da sauransu. Akan yi kaffara da azumi ko ciyarwa da sauransu)
Pencil - A turance tana nufin fensir. Misali; 'Yan aji ɗaya da fensir suke rubutu. HAU; Fensir (Tana nufin abin rubutu)
Penny - A turance tana nufin kwabo. Misali; Kwabo ɗaya ake ba wa su Baba idan za su je makaranta da suna yara. HAU; Kwabo (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in kuɗin Najeriya da ake amfani da shi a da)
Pension - A turance tana nufin fansho. Misali; Ma'aikata da dama da fansho suke siyan gida. HAU; Fansho (Tana nufin kuɗin da ake ba wa mutum bayan ya kammala shekarun aikinsa)
Pepper - A turance yana nufin barkono. Misali; Inna ta siyo barkono za ta daka yajin daddawa. HAU; Barkono (Yana nufin tsiro daga cikin kayan lambu, yana kama da tattasai amma shi dogo ne)
Pepper Soup - A turance tana nufin farfesu. Misali; Tunda ya fara zazzaɓi yake sha'awar farfesu. HAU; Farfesu (Tana nufin dafa abu da romo-romo, kamar kaza ko kifi da sauransu)
Performing Musicians Association of Nigeria (PMAN) - Ƙungiyar Mawaƙa Ta Najeriya
Period during which a woman may not remarry - A turance tana nufin idda. Misali;Ta kammala idda gobe ma za a sake ɗaura mata aure. HAU; Idda (Tana nufin kwanakin da mace take yi bayan mijinta ya sake ta kafin ta yi wani auren)
1 247 248 249 250 251 300