Terms Dictionary

Refuse - A turance tana nufin bola. Misali; Motar ɗiban shara ta kwashe bolar bakin kasuwa. HAU; Bola (Tana nufin shara ko kayan da aka gama amfani da su waɗanda za a zubar)
Relationship - A turance tana nufin dangantaka.  Misali;Akwai dangantaka tsakanin angon da amaryar. HAU; Dangantaka (Tana nufin alaƙa)
Relax, Enjoy - A turance tana nufin hole. Misali; Yau za mu hole mu sha shagali saboda an ɗaura auren ƙawarmu. HAU; Hole (Tana nufin hutu da jin daɗi)
Religious Impurity - A turance tana nufin janaba. Misali; idan mutum na da janaba, ba zai yi sallah ba dole sai ya yi tsarki. HAU; Janaba (Tana nufin rashin tsarki a addinin musulunci sakamakon biƙi, haila, kusantar iyali da sauransu) Kishiyarta; Tsarki
Remaining particles - A turance tana nufin diddiga. Misali; Naman ya ƙare saura diddiga. HAU; Diddiga (Tana nufin sauran abu ko ɓirɓishinsa)
Removal of things to another location - A turance tana nufin jido. Misali; Mun jido kayan daga tsohon gida zuwa sabo. HAU; Jido (Tana nufin ɗebo kaya daga wani guri zuwa wani gurin)
Repair - A turance tana nufin gyara. Misali; An gyara mana titin garinmu. HAU; Gyara (Tana nufin daidaita abu ko mayar da abu yanda ya kamata) Kishiyarta; Ɓatawa
Repeat - A turance tana nufin kuma. Misali; Yanzu zazzaɓi ba ya jin magani ko kin sha sai kin kuma sha. HAU; Kuma (Tana nufin sake yi ko maimaitawa)
Repeatedly - A turance tana  nufin bini-bini. Misali; Abokina bini-bini ya zo gidanmu, hakan ya sa mun shaƙu. HAU; Bini-bini (Tana nufin akai-akai)
Reporters Without Borders - Tawagar Manema Labarai/'Ƴanjarida Marasa Shamaki
1 257 258 259 260 261 300