Rope - A turance tana nufin igiya.
Misali; Na gama wankin zan shanya a kan igiya yanzu.
HAU; Igiya (Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin shanyar kaya ko ɗaure abubuwa)
Rubber Research Institute of Nigeria (RRIN) - Cibiyar Binciken Noman Roba Ta Najeriya
Rule/Law - A turance tana nufin doka.
Misali; Duk wanda ya karya doka sai an masa hukunci.
HAU: Doka (Tana nufin ƙa'idoji ko tsare-tsare)
Rumour - A turance tana nufin jita-jita.
Misali; Ya shahara wajen yaɗa jita-jita, sai dai mu yi masa fatan shiriya.
HAU; Jita-jita (Tana nufin zancen da ba shi da tabbas)
Run - A turance tana nufin gudu.
Misali; Idan ka yi gudu zuciyarka na harbawa da sauri.
HAU;Gudu (Tana nufin tafiya da ƙololuwar sauri)
Running short of something - A turance tana nufin cankacakare.
Misali; Kayan marmarin sun zama cankacakare.
HAU; Cankakare (Tana nufin ƙarewar abu ƙarƙaf)
Rural Area - A turance tana nufin karkara.
Misali; Mutanen karkara suna da karamci matuƙa.
HAU; Karkara (Tana nufin ƙauye)
Rural Electrification Agency (REA) - Hukumar Raya Karkara da Wutar Lantarki
safiyo - Awo ne na zubin kasar da za a gina a matsayin gari ko mahalli.
Salary/Wage - A turance yana nufin albashi.
Misali; An biya ma'akata albashi yau da safe.
HAU; Albashi (Yana nufin kuɗi da ake biyan mutum sakamakon aikin da ya yi a wata ko sati)