Terms Dictionary

Jido - Tana nufin ɗebo kaya daga wani guri zuwa wani gurin. Misali; Mun jido kayan daga tsohon gida zuwa sabo. ENG; Removal of things to another location (A turance tana nufin jido)
Jigida - Tana nufin dutsinan ado da mata ke ɗaurawa a ƙugu. Misali; Tana da jigida mai hawa goma. ENG; Ornamental beads worn around hips by women (A turance tana nufin jigida)
Jigila - Tana nufin kai wa da komowa (kai-komo). Misali; Kamfanonin jiragen sama na ta jigilar alhazai daga ƙasashe daban-daban. ENG; Going back and forth (A turance tana nufin jigila)
Jiha - Tana nufin wani yanki daga cikin ƙasa. Misali; An ƙirƙiri sabuwar jiha a ƙasar Najeriya. ENG; State (A turance tana nufin jiha)
Jihadi - Tana nufin yaƙi don ɗaukaka addinin musulunci. Misali; Sahabbai sun yi jihadi don ɗaukaka addinin musulunci. ENG; Holy war to spread Islam (A turance tana nufin jihadi)
Jijiya - Tana nufin hanyar jini a jikin mutum ko dabba. Misali; Allurar jijiya aka yi masa saboda zafin zazzaɓin. ENG; Vein (A turance tana nufin jijiya)
Jijjiga - Tana nufin girgizawa. Misali; Sai an jijjiga maganin sannan ake sha. ENG; Shake (A turance tana nufin jijjiga)
Jika - Tana nufin yaro ko yarinyar da ɗa ko 'ya suka haifa. Misali; Maƙoci na ya yi jika, jiya 'yarsa ta haihu. ENG; Grandchild (A turance tana nufin jika)
Jiki - Tana nufin sassa gaba ɗaya daga kai zuwa ƙafa. Misali; Ya sha maganin ciwon jiki ya kwanta. ENG; Body (A turance tana nufin jiki)
Jima’i - Tana nufin saduwa tsakanin mace da namiji. Misali; Cututtukan sanyi na da nasaba da jima'i a lokuta da dama. ENG; Sexual Intercourse (A turance tana nufin jima'i)
1 167 168 169 170 171 300