Jealousy - A turance tana nufin kishi.
Misali; Matan wannan zamani na da matuƙar kishi wanda ya saɓawa shari'a.
HAU; Kishi (Tana nufin sosuwar zuciya da ɓacin ran da suke jawo fushi, a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani, a kan abin da wanin ya keɓanta da son sa koma mallakarsa)
Jefi-jefi - Tana nufin ba kodayaushe ba.
Misali; Yana zuwa gaishe da kakarsa jefi-jefi.
ENG; Often (A turance tana nufin jefi-jefi)
Kishiyarta; A kai-a kai
Jego - Tana nufin shayar da jariri.
Misali; Indo jego take shi yasa ba za ta bi mu ba.
ENG; Suckling of Infant (A turance tana nufin jego)
Jela - Tana nufin bindi.
Misali; Jakin yana da doguwar jela.
ENG; Tail (A turance tana nufin jela)
Jemage - Tana nufin dabba mai tashi sama wadda ba ta taɓa ƙasa.
Misali; Akwai jemage a kan bishiyar ƙofar gida.
ENG; Bat (A turance tana nufin jemage)
Jewa - Tana nufin je-ka-ka-dawo.
Misali; Na gan shi yana ta jewa saboda tashin hankali.
ENG; Going to and fro (A turance tana nufin jewa)
Jibga - Tana nufin ɗora kaya da yawa.
Misali; Na ga Habu ya jibga kaya a jikinsa wai sanyi yake ji.
ENG; Pile loads on top of one another (A turance tana nufin jibga)
Jibi - Tana nufin ranar da ke bin gobe.
Misali; Jibi za a fara bikin kuma sai an jera sati ana yi.
ENG; Day After Tomorrow (A turance tana nufin jibi)
Jidali - Tana nufin rikici ko ɗawainiya.
Misali; Ya janyo wa kansa jidali tunda ya auri yarinyar nan.
ENG; Struggle/Trouble (A turance tana nufin jidali)
Jiddin - Tana nufin kodayaushe.
Misali; Ai Jiddin yana masallaci tunda Allah ya shirye shi.
ENG; Always (A turance tana nufin jiddin)