Terms Dictionary

Jarfa - Tana nufin tsagun fuska. Misali; Jarfa, gadon gidansu ne. ENG; Facial Markings (A turance tana nufin jarfa)
Jarida - Tana nufi takarda mai ƙunshe da rubutun labarai. Misali; Dattijai na son karanta jarida don jin halin da duniya take ciki. ENG; Newspaper (A turance tana nufin jarida)
Jarirai - Tana nufin jam'in jariri. Misali; Kayan da gwamnati ta kawo na tallafin jarirai ne. ENG; Infants (A turance tana nufin jarirai)
Jariri - Tana nufin wanda ba a daɗe da haifa ba. Misali; An tsinci jariri a unguwarmu. ENG; Infant (A turance tana nufin jariri)
Jarrabawa - Tana nufin gwaji. Misali; Suna gama jarrabawa za a ba su hutu. ENG; Examination (A turance tana nufin jarrabawa)
Jarumi - Tana nufin ƙaƙƙarfa ko jajirtacce. Misali; Shi kaɗai ne jarumi a cikin gidan. ENG; Brave (A turance tana nufin jarumi)
Jauje - Tana nufin abin kiɗa mai kama da kalangu. Misali; A cikin kayan da suke kaɗawa har da jauje. ENG; Drum similar to but larger than kalangu (A turance tana nufin jauje)
Jawabi - Tana nufin bayani a kan wani maudu'i. Misali; A halin yanzu mai girma gwamna ne yake jawabi a ɗakin taron. ENG; Speech (A turance tana nufin jawabi)
Jayayya - Tana nufin faɗi in faɗa. Misali; Tun safe suke jayayya a kan kuɗi. ENG; Controversy (A turance tana nufin jayayya)
Jaɓa - Tana nufin dabba mai kamar ɓera amma ta fi shi girma tana da dogon baki kuma tana wari. Misali; Akwai jaɓa a ɗakin nan don na ji warinta da na shigo. ENG; Stinking Shrew- Mouse (A turance tana nufin jaɓa)
1 165 166 167 168 169 300