Jimada Awwal - Tana nufin wata na biyar a watannin musulunci.
Misali; A watan Jimada Awwal za a yaye ɗaliban.
ENG; Fifth month of Islamic calendar (A turance tana nufin jimada awwal)
Jimilla - Tana nufin sakamako na bai ɗaya.
Misali; Idan an haɗa kudina da naka za a samu jimillar dubu goma sha biyu.
ENG; Sum Total (A turance tana nufin jimilla)
Jimina - Tana nufin nau'in tsutsuwa mai dogon wuya wadda ke yin ƙwai.
Misali; Akwai jimina a gidan adana namun dajin da ke garinmu.
ENG; Ostrich (A turance tana nufin jimina)
Jimiri - Tana nufin haƙuri da juriya.
Misali; Duk wanda ya yi jimirin yin aiki zai samu kyakkyawan sakamako.
ENG; Endurance/Patience (A turance tana nufin jimiri)
Jinga - Tana nufin yarjejeniyar biyan kuɗi.
Misali; Mun yi jinga da shi zai biya ni da zarar na kammala aikin.
ENG; Wages (A turance tana nufin jinga)
Jingim - Tana nufin adadi mai yawa.
Misali; Ya tara kayan wanki jingim a ɗaki, da ƙyar zai iya wankewa shi kaɗai.
ENG; Plentiful (A turance tana nufin jingim)
Jingina - Tana nufin bayar da ajiyar wata kadara domin rancen kuɗi da zimmar idan aka biya kuɗin sai a karɓa.
Misali; Gidansa ya bayar jingina a banki ya karɓo bashin.
ENG; Deposit given as a pledge for money borrowed (A turance tana nufin jingina)
Jini - Tana nufin sinadarin ruwa mai launin ja wanda zuciya take harbawa sassan jiki, yana ƙunshe da abubuwan da jiki ke buƙata domin rayuwa.
Misali; Likita ya ce sai an ƙara masa jini leda ɗaya.
ENG; Blood (A turance tana nufin jini)
Jiniya - Tana nufin ƙarar da motar asibiti ko ta 'yan kwana-kwana ko 'yan siyasa ke ɗauke da ita. Ƙarar na nuni da cewa abu ne na gaggawa ya faru, ko gobara, ko an ɗauko mara lafiya da sauransu.
Misali; Na jiyo jiniya, da alama 'yan kwana-kwana sun zo gurin gobarar.
ENG: Siren (A turance tana nufin jiniya)
Jinjina - Tana nufin gaisuwar ban-girma.
Misali; Shugaban sojojin yana shigowa ɗakin taron aka yi masa jinjina.
ENG; Saluting a superior (A turance tana nufin jinjina)