Jinjiri - Tana nufin jariri.
Misali; Jinjiri aka haifa masa shekaran jiya.
ENG; Infant (A turance tana nufin jinjiri)
Kishiyarta; Jinjinniya
Jinkiri - Tana nufin dakatawa ko ɗaukan lokaci.
Misali; An samu jinkiri wajen fitar da sakamakon jarrabawar saboda wasu ƙwararan dalilai.
ENG; Delay (A turance tana nufin jinkiri)
Jinya - Tana nufin kwanciya a dalilin rashin lafiya ko kula da mara lafiya.
Misali; Ya shekara guda yana jinya sakamakon haɗarin.
ENG; Nursing (A turance tana nufin jinya)
Jiri - Tana nufin juwa ko jin kai yana juyawa ko gani bibbiyu.
Misali; Naja'atu ta ce jiri take ji, gara ta je asibiti a duba ta.
ENG; Diziness (A turance tana nufin jiri)
Jita-jita - Tana nufin zancen da ba shi da tabbas.
Misali; Ya shahara wajen yaɗa jita-jita, sai dai mu yi masa fatan shiriya.
ENG; Rumour (A turance tana nufin jita-jita)
Jitu - Tana nufin shaƙuwa ko fahimtar juna.
Misali; Sun jitu da juna shi yasa ba sa faɗa.
ENG; Be on good terms with someone (A turance tana nufin jitu)
Jiya - Tana nufin ranar da ta gabata kafin yau.
Misali; Jiya ban je makaranta ba saboda babanmu ya aike ni.
ENG; Yesterday (A turance tana nufin jiya)
Jiɓi - Tana nufin gumi ko zufa.
Misali; Mara gaskiya ko a ruwa sai ya yi jiɓi.
ENG; Sweat (A turance tana nufin jiɓi)
Jiƙa - Tana nufin saka abu a cikin ruwa.
Misali; Ta jiƙa shinkafar tun safe saboda za ta yi wainar shinkafa.
ENG; Soak (A turance tana nufin jiƙa)
Joint Admission & Matriculation Board (JAMB) - Hukumar Jarabawar Shiga Jami'a