Innanaha - Tana nufin ƙololuwa.
Misali; Ai munafiki ne na innanaha.
ENG; Extreme Degree (A turance tana nufin innanaha)
Innovation in religious practices - A turance tana nufin bidi'a.
Misali; Wannan zamanin cike yake da bidi'a.
HAU; Bidi'a (Tana nufin sabon al'amari musamman a cikin addini)
Inquisitiveness - A turance tana nufin kazallaha.
Misali; Kazallaha ake ce masa saboda yana da shiga sharo ba shanu.
HAU; Kazallaha (Tana nufin shisshigi ko katsalandan da shiga abinda be shafi mutum ba)
Institute - Cibiya, Mahaɗa
Institute for Peace & Conflict Resolution (IPCR) - Cibiyar Sasantawa da Ɗorewar Zaman Lafiya
Institute of Advanced Medical Research & Training (LAMRT) - Babbar cibiyar Horarwa da Binciken lafiya
Institute of Agricultural Reserch & Training (IAR&T) - Cibiyar Horarwa da Nazarin Aikin Gona
Institute of Public Analysts of Nigeria (IPAN) - Cibiyar Manaƙalta Lafiyar Jama'a Ta Najeriya
Institute of Registered Administrative Managers of Nigeria (IRAMN) - Cibiyar Manajojin Gudanarwa Ta Najeriya
Institute of Strategic Management, Nigeria (ISMN) - Cibiyar Tsara Dabarun Gudanarwa Ta Najeriya