Industrial Training Fund (ITF) - Asusun Horon Ɗalibai na Masana'antu
Infant - A turance tana nufin jariri.
Misali; An tsinci jariri a unguwarmu.
HAU; Jariri (Tana nufin wanda ba a daɗe da haifa ba)
Infant - A turance tana nufin jinjiri.
Misali; Jinjiri aka haifa masa shekaran jiya.
HAU; Jinjiri (Tana nufin jariri)
Kishiyarta; Jinjinniya
Infants - A turance tana nufin jarirai.
Misali; Kayan da gwamnati ta kawo na tallafin jarirai ne.
HAU; Jarirai (Tana nufin jam'in jariri)
Information Technology Association OF Nigeria (ITAN) - Ƙungiyar Masana Fasahar Bayanai Ta Najeriya
Infrastructure Concession Regulatory Commission (ICRC) - Hukumar Kyautata Samuwar Ababen More Rayuwa
Ingarma - Tana nufin babban doki ko gabjejen mutum.
Misali; Dokin yarima ingarma ne.
ENG; Large Stallion (A turance tana nufin ingarma)
Inheritance - A turance tana nufin gado.
Misali; Iyalan na rikici akan rabon gado.
HAU; Gado (Tana nufin kuɗi da kadarorin da mamaci ke bar wa iyalansa, ma'ana duk abin da mutum ya mallaka idan ya mutu ya zama gado)
Inibi - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari.
Misali; Inibi yana da tsada sosai don kawo shi ake daga ƙasashen ƙetare.
ENG; Grapes (A turance tana nufin inibi)
Inna - Tana nufin mahaifiya.
Misali; Kande ƙanwar inna ce.
ENG; Mother (A turance tana nufin inna)