Terms Dictionary

Iko - Tana nufin ƙarfi ko isa. Misali; Shugabanni su ke da iko a kan mabiyansu. ENG; Power/Authority (A turance tana nufin iko)
Ilahiri - Tana nufin duka ko gaba ɗaya ko bai ɗaya. Misali; Ya shafe ilahirin jikinsa da maganin. ENG; Whole (A turance tana nufin ilahiri)
Ilimi - Tana nufin sani. Misali; Allah ya yi masa baiwar ilimi ƙwarai da gaske. ENG; Knowledge (A turance tana nufin ilimi)
Illiterate Person - A turance tana nufin jahili. Misali; Rashin zuwa makaranta ne ke mai da mutum jahili. HAU; Jahili (Tana nufin wanda ba shi da ilimi)
Illness - A turance tana nufin cuta. Misali; Wata sabuwar cuta ta ɓullo mai suna korona. HAU; Cuta(Tana nufin rashin lafiya)
Imani - Tana nufin yarda, amincewa ko ba da amanna ɗari bisa ɗari. Misali; Yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin rukunan imani. ENG; Faith (A turance tana nufin imani)
Imitate - A turance tana nufin kwaikwaya. Misali; Habu kukan doki yake kwaikwaya da na mage. HAU; Kwaikwaya (Tana nufin yin abu kamar yanda na asali yake)
Imitate - A turance tana nufin koyi. Misali; Koyi da annabawa kyakkyawar ɗabi'a ce. HAU; Koyi (Tana nufin kwaikwaya ko yin abinda wani ya yi)
Imma - Tana nufin ko. Misali; Ka zaɓi ɗaya, imma makarantar kwana ko ta je-ka-ka-dawo. ENG; Either/Or (A turance tana nufin imma)
Impress - A turance tana nufin burge. Misali; Samarin na ƙoƙarin yin komai don burge 'yan matan su. HAU; Burge (Tana nufin ƙoƙarin janyo ra'ayi ko yardar wani)
1 152 153 154 155 156 300