In’ina - Tana nufin yin magana da ƙyar ko ana yi ana tsittsitsinkawa.
Misali; An ce shan ruwan tattabaru na sauƙaƙa in'ina.
ENG; Stuttering/ Stammering (A turance tana nufin in'ina)
Inda - Tana nufin gurin da abu yake.
Misali; Mukullin yana inda nake ajiye kayana.
ENG; Where (A turance tana nufin inda)
Inda-inda - Tana nufin rashin ƙwaƙƙwaran ra'ayi ko kokwanto.
Misali; Tun ɗazu yake ta inda-inda saboda ba shi hujja a kan abinda ake tuhumarsa a kai.
ENG; Behaving or talking indecisively (A turance tana nufin inda-inda)
Indararo - Tana nufin hanyar da ruwa yake zubowa ta saman rufin kwano.
Misali; Mun cika gidan nan da ruwan da muka tara a indararo.
ENG; Metal Roof Drain (A turance tana nufin indararo)
Indecent talk - A turance tana nufin batsa.
Misali; Wasu daga cikin masu amfani da manhajar TikTok na yawan yin batsa a bidiyoyinsu.
HAU; Batsa (Tana nufin zantuttuka na rashin ɗa'a)
Independent Corrupt Practices Commission (ICPC) - Hukumar Hana Cin Hanci / Hukumar Yaki da Cin Hanci
Independent National Electoral Commission (INEC) - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa
Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) - Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Ta Najeriya
Indigineous Languages Writers Association of Nigeria (ILWAN) - Ƙungiyar Marubuta Ta Harsunan Najeriya
Indirect Reference - A turance tana nufin habaici.
Misali; Tun safe take yi wa kishiyarta habaici.
HAU; Habaici (Tana nufin magana a fakaice ba tare da ambaton suna ba, amma shi wanda ake da shi ya sani)