Idan - Tana nufin in har.
Misali; Idan an tashi daga taron za mu je ta'aziyya.
ENG; If (A turance tana nufin idan)
Idda - Tana nufin kwanakin da mace take yi bayan mijinta ya sake ta kafin ta yi wani auren.
Misali;Ta kammala idda gobe ma za a sake ɗaura mata aure.
ENG; Period during which a woman may not remarry (A turance tana nufin idda)
Idi - Tana nufin biki.
Misali; Yara na matuƙar son idi musamman na sallah babba da ƙarama.
ENG; Any major muslim festival (A turance tana nufin idi)
Ido - Tana nufin gaɓar da ake gani da ita.
Misali; Ido na ɗaya daga cikin sashen jiki mafi muhimmanci.
ENG; Eye (A turance tana nufin ido)
Idol - A turance tana nufin gunki.
Misali; Indiyawa na da gunki a gidajensu, don sun yarda shi ne abin bautarsu.
HAU; Gunki (Tana nufin sassaƙaƙƙen abu musamman wanda ake bautawa, zai iya kasancewa mai siffar mutum ko dabba da sauransu)
If - A turance tana nufin idan.
Misali; Idan an tashi daga taron za mu je ta'aziyya.
HAU; Idan (Tana nufin in har)
Igiya - Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin shanyar kaya ko ɗaure abubuwa.
Misali; Na gama wankin zan shanya a kan igiya yanzu.
ENG; Rope (A turance tana nufin igiya)
Ignore - A turance tana nufin biris.
Misali; Duk da yana cikin mawuyacin hali amma matarsa ta yi biris da shi saboda rashin kirkinsa.
HAU; Biris (Tana nufin nuna halin ko-in-kula da abu ko yin watsi da shi)
Ihu - Tana nufin ƙara ko fitar da sauti da ƙarfi.
Misali; Matasan na ihu ne don sun ci ƙwalo.
ENG: Yelling (A turance tana nufin ihu)
Ijaba - Tana nufin cikar buri.
Misali; Allah ya yi mana ijaba, yau ruwa ya sauka.
ENG; Fulfilment Of Wish (A turance tana nufin ijaba)