Husks of Rice - A turance tana nufin ɓuntu.
Misali; Shinkafar da muka siyo cike take da ɓuntu, sai an gyara ta ƙwarai.
HAU; Ɓuntu (Tana nufin kwanson da shinkafa ke ciki)
Hut - A turance tana nufin bukka.
Misali; Fulani na gina bukka a rugagensu domin su zauna.
HAU; Bukka (Tana nufin ƙaramin ɗakin da ake ginawa da busasshiyar ciyawar da ake kira da zana)
Hutu - Tana nufin zama guri ɗaya ba tare da aikin komai ba ko rashin zuwa gurin aiki ko makaranta ko gyurin sana'a na wani lokaci don a tsahirta kafin a ɗora.
Misali; Yara ba sa zuwa makaranta saboda an ba su hutu.
ENG; Rest/Holiday (A turance tana nufin hutu)
Huɗu - Tana nufin lambar da ke bin bayan uku.
Misali; Musulunci ya ba wa maza damar auren mata guda huɗu.
ENG; Four (A turance tana nufin huɗu)
Huɗuba - Tana nufin jawabai na hikima da jan hankali don faɗakarwa ko kwaɗaitarwa a kan binn Allah da kuma gujewa saɓa masa.
Misali; Muna sauraron huɗuba daga masallaci mai alfarma a rediyo.
ENG; Sermon (A turance tana nufin huɗuba)
Hyena - A turance tana nufin kura.
Misali; Mafarautan sun kamo kura.
HAU; Kura (Tana nufin wata dabbar daji mai cin ɗanyen nama)
Ibada - Tana nufin bautawa Allah.
Misali; Idan mutum ya kasance mai ibada rayuwarsa tana albaraka.
ENG; Serving God (A turance tana nufin ibada)
Iblis - Tana nufin sheɗan.
Misali; Allah ya raba mu da sharrin sheɗan.
ENG; Satan (A turance tana nufin sheɗan)
Iburo - Tana nufin hatsi mai kama da acca.
Misali; Na auno iburo a kasuwa.
ENG; Cereal like acca (A turance tana nufin iburo)
Icce - Tana nufin reshe ko gangar jikin bishiya da ake amfani da shi wajen hura wuta a yi girki.
Misali; Idan aka samu icce busasshe wuta tana saurin kamawa.
ENG; Wood (A turance tana nufin icce)