Tag: yadda ake

  • Falalar Azumin Ranar Arfa

    Falalar Azumin Ranar Arfa

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce:

    “Azumin ranar Arfa ina nema da ga Allah ya kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta zo bayanta”. (Muslim 1162).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Kwana Uku A Kowanne Wata danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Ranar Arfa danna nan

    Don karanta cikakken bayani a kan Laccocin Ramadan Na Mumbarin Jawabi Daga Malamai danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Azumin Kwana Uku A Kowanne Wata

    Azumin Kwana Uku A Kowanne Wata

    Ana son a kowane wata mutum ya yi azumin kwana uku, kuma an fi so su kasance fararen kwanaki,, wato ranakun 13, 14, da 15 na kowane wata.

    Falalar Azumin Kwanaki Uku A Kowanne Wata

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce; da Abdullahi Ibn Amr “Ka yi azumin kwana uku a kowanne wata; saboda aikin lada ɗaya daidai yake da goma, sai ya kasance kamar mai yin azumi kullum”. (Bukhari 1976, Muslim 1159).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Litinin Da Alhamis da kuma Falalarsa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) Ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Azumin Litinin Da Alhamis

    Azumin Litinin Da Alhamis

    Kamar yadda ake son azumin ranakun Alhamis da Litinin.

    Falalarsa.

    An karɓo daga A’isha (Radiyallahu anha) ta ce: “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana yin azumin ranakun Litinin da Alhamis” (Tirmizi 7451 Nasa’i 2/86).

    Kuma Usama Ibn Zaid ya tambayi Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) kan azumin litinin da Alhamis da yake yi, sai ya ce: “Waɗannan ranaku ne biyu da ake bujirar da ayyuka ga Ubangijin Taliƙai a cikinsu, in an so a bujirar da aikina ina azumi”(Nisa’I 2357, Ahmad 5/201).

    Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam) da Falalarsa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal (Sitta Shawwal) danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam)

    Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam)

    Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam) shi ne, yau a yi, gobe a huta. Iya tsawon rayuwar mutum.

    Falalarsa.

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Sallar da Allah ya fi so,, ita ce sallar Annabi Dawud (Alaihis salam) Kuma azumin da Allah ya fi so, shi ne azumin Annabi Dawuud (Alaihis salam)”

    (Bukhari 1976. Muslim 1159).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Raya Daren Lailatul Ƙadari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Raya Daren Lailatul Ƙadari danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Falalar Dasa Bishiya danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Zikiri

    Falalar Zikiri

    Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:-

    “Fazkuruunii azkurkum washkuruu lii walaa takfuruunii

    { ku ambace ni, zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce min} (Baƙara, aya ta 152).

    Yaa ayyuhal – lazina amanuzkurul laaha zikran kasiiran wasabbihuuhu bukratan wa’asiilaa“.

    { Ya ku waɗanda suka yi Imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa } (Ahzab, aya ta 41).

    Wazzakiriinal – laaha kasiiran wazzaakiraati a’addallahu lahum magfiratan wa’ajran aziimaa

    { Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma }

    (Ahzab, aya ta 35).

    Wazkur Rabbaka fi nafsika tadharru’an wa khifatan wa duunal jahri minal ƙauli bil guduwwi wal’asaali walaa takun minal Gafiliina”.

    { Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai ƙasƙantar da kai da tsoro, ba da ɗaukaka murya ba (tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa), da safe da maraice, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu } (A’araf, aya ta 205).
    Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne”.

    Kuma yace: { Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakar ku, kuma mafi ɗaukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku da ku haɗu da abokan gabarku ku riƙa dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Maɗaukaki}.

    Kuma ya ce: { Allah Maɗaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin jama’a zan ambace shi a cikin jama’ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni taki ɗaya zan kusance shi kamu guda, in ya kusance ni kamu guda zan kusance shi tsawon gaɓa guda, in ya zo min ya na tafiya zan zo masa ina gaggawa }.
    Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce: Ya Ma’aikin Allah! Shari’o’in Musulunci sun yi yawa a gare ni; saboda haka ka nuna mini wani abu da zan yi riƙo da shi. Ya ce; { kar harshenka ya gushe face yana ɗanye daga ambaton Allah }.

    Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce; { wanda ya karanta harafi ɗaya daga Littafin Allah yana da (ladan) kyakkyawan aiki ɗaya saboda shi; kuma dukkan kyakkyawan aiki ɗaya yana da (ladan) misalinsa goma. Ba ina cewa Alif Lam Mim harafi ba ne a’a, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne}.

    Kuma daga Uƙbata ibn Amir, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya fito alhali muna cikin rumfa, sai ya ce; A { wane ne daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ; ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna, ba tare da yin wani laifi ba, ko yanke zumunta? } muka ce; “Muna son haka” .

    Ya ce: { Ɗayanku ya je masallaci ya nemi sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin Littafin Allah; Mabuwayi mai ɗaukaka, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku; ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu, da kwatankwacin adadinsu na raƙuma }.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; {wanda ya zauna a wani waje bai ambaci Allah a wajen ba; wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. Wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajen ba; shi ma zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah}.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; { Babu wasu mutane da suka zauna a wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba; kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya; in Allah ya so ya yi musu azaba, in ya so ya gafarta musu }.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; { Babu wasu mutane da za su tashi daga wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan mushen jaki ne; kuma zai zamanto musu abin da- na- sani }.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’o’in Tashi Daga Barci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci

    Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci

    Allaahumma baarik lahum fimaa razaƙahum, wagfir lahum warhamhum”.

    {Ya Allah! Ka albarkance su a cikin abin da ka azurta su da shi, kuma ka gafarta musu, ka ji ƙansu}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Zikiri danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

    Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

    Alhamdu lil laahil lazii aɗ’amanii hazaa wa razaƙaniihi min gairi haulin minnii walaa ƙuwwatin”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da ni wannan (abincin); ya azurta ni da shi, ba tare da wata dabara ko ƙarfi daga gare ni ba}.

    Allamdu lil laahi hamdan kasiiran ɗayyiban mubaarakan fiihi gaira makfiyyi walaa muwadda’in walaa mustagnan anhu Rabbunaa“.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sanya albarka a cikin sa; (Allah) wanda ba a ɗauke masa azurta bayinsa, kuma ba a rabuwa da shi (a bar nema daga wurinsa), kuma ba a wadatuwa ga barinsa; shi ne Ubangijinmu}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Abincin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Shiekh Sa’id Ibn Ali Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane

    Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane

    Afɗara indakum saa’imuuna wa akala ɗa’aamakum abraaru; wasallat alaikumul mala’ikatu“.

    {Allah ya sa masu azumi su yi buɗa baki a wajenku; kuma Allah ya sa nagartattun bayi su ci abincinku; kuma Allah ya sa Mala’iku su yi muku addu’a}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyar Da Mai Azumi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Da Ga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

    Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

    Zahabaz zama’u wabtallatil uruƙu, wa sabatal ajru in sha’allaahu”.

    {Ƙishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah ya so}.

    Abdullah bin Amr bin Al- As ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “Mai azumi yana da addu’a da ba a mayar da ita idan ya zo buɗe baki”. Abdullahi bin Amr ya kasance idan ya zo buɗa baki sai ya ce:

    Allaahumma innii as’aluka bi rahmatikal latii wasi’atu kulla shai’in an tagfiralii“.

    {Ya Allah! Ina roƙon ka saboda rahamarka da ta yalwaci komai, ka gafarta mini}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Gaggauta Buɗa Baki danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Kasance A Cikin Zikiri Kowane Lokaci

    Kasance A Cikin Zikiri Kowane Lokaci

    Bari in kammala wannan babi da wasiyar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Basrin (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa wani mutum ya ce; da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Haƙiƙa shari’o’in Musulumci sun yi min yawa, ba ni labari ko da wani abu da zan yi riƙo da shi? Sai ya ce; “Kada harshenka ya bushe ba tare da ambaton Allah” (Tirmizi 3375).

    Wato koda yaushe mutum ya kasance cikin zikiri.

    Sannan kuma mu san cewa malamai sun kasa zikiri gida biyu: Akwai ƙayyadadden zikiri da kuma sakakken zikiri.

    Ƙayyadadden zikiri su ne zikirin da aka iyakance lokacin ko yanayin yin sa da kuma adadin sa, kamar zikirai da karatukan salla, zikirin safe da yamma da sauransu.

    Su kuwa sakakkun zikirai su ne waɗanda ba a yi musu iyaka ta lokaci ko adadi, ba sai dai ana so mutum ya shagala da shi a mafi yawancin lokutansa kamar hailala da tasbihi, salati ga Annabi da Istigfari da kuma karatun Alƙur’ani, waɗannan ana so mutum ya yawaita su a kowane lokaci.

    Ya Allah ka sanya mu a cikin masu yawan amabaton Allah maza da mata. Amin

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikirin Tashi Daga Majalisa Yake danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ɗabi’ar Lokaci, Saurin Wucewa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.