Tag: yadda ake

  • Yanayin Harshen Waƙar Baka

    Yanayin Harshen Waƙar Baka

    Mazubi na harshen waƙar baka yana ɗauke da ƙwayoyin sauti da gaɓoɓi da kalmomi da kuma jumloli; waɗanda suke ba makaɗa damar su iya aiwatarwa da sadarwa cikin rerawa a sauƙaƙe.

    A zubi na waƙoƙin baka, daɗa a wajen makaɗa masu shiri na baka ko masu shiri na ƙire ko haye ko masu shiri na rubuce; suna shirya kalmomi ne da kansu ko wasu su shirya musu, sannan su saka amo na murya da na kiɗa, su kuma rera.

    Waƙar Baka

    Shirya Kalmomi

    Shiri na Baka Shiri na Ƙire/Haye Shiri na Rubuce

    Kalmomi Kalmomi Kalmomi na kai
    na kai na kai
    Satar waƙar Kalmomi na wani
    Satar Waƙa

    Idan aka lura, dangane da harshe a zubin waƙar baka, makaɗa da mawaƙa suna tasirantuwa bisa wasu matakai na ginawa da shirya waƙa da suka haɗa da:

    3.1 Shirya Kalmomi

    Kamar yadda aka nuna a baya, waƙoƙin baka ana shirya su ta gaɓoɓin kalmomi bisa zaɓi na makaɗi. Kalmomi a harshe su suke yi wa makaɗi tsani ya saƙa saƙonni, manya da ƙanana, a waƙa.

    3.2 Daidaita Murya da Amon Kiɗa

    Makaɗi ko mawaƙi yana daidaitawa ne a tsakanin amon muryarsa, wadda take tafiya a saje da gaɓoɓi da kalmomi na zubinsa; da kuma amon kiɗa wanda yake wanzuwa daga kayan kiɗa waɗanda yake amfani da su. A lokacin da wannan yanayi ya daidaitu, sai rauji na waƙa ya wanzu; wanda yakan zama gajere ko dogo ko matsakaici, gwargwadon yanayin kalmoni da kuma amon kiɗan da aka ɗauka.

    3.3 Daidaita Tunani a Saɗaru

    A waƙar baka akan daidaita tunani da ma’ana, babba ko ƙarama ta waƙa ta gurabun kalmomin waƙa waɗanda ake rerawa ta hanyar tsayin rauji a saɗaru. Dole ne tunanin waƙa ya dinga tafiya tare da zubin kalmomi a saɗaru na waƙa.

    3.4 Kaucewa Dokokin Nahawu

    Harshen waƙa, musamman yadda wani bi yakan ƙunshi tarin kalmomi, sannan da yanayin rauji da rerawa; yakan wadatu da tsarinsa ne har ya dinga bauɗe wa wasu dokokin nahawu.

    Shi harshen waƙa yakan sanya masana nahawun harshe da jujjuyawar kalmomi da karin harshe da sauransu; su yi ta ƙoƙarin gwada ɗora kalmomi da jumloli na waƙa a kan daidaitaccen tsarin nahawu. A wajen waƙar baka ƙirƙirowa da baddala kalmomi ko tsarin jumla da sauransu wata hanya ce ta kamalar harshen waƙa.

    3.5 Jefa Dabarun jan Hankali

    Wasu daga cikin hikimomi na harshe wanda ake shirya waƙa da shi, sukan yi naso a waƙa. Makaɗi yakan yi amfani da dabaru na yi wa zubin waƙarsa kwalliya ya daɗa armasa waƙar; ya ƙara mata nagarta cikin dausayin harshe. Dabarun nan na jan hankali sukan iya sanya harshen waƙa ya ƙara tsada; ya zama mai nauyin fahimta, mai jefa sarƙadodo a wajen warware ma’ana.

    Akwai dabarun jan hankali da yawa waɗanda makaɗa da mawaƙa suke jejjefawa a waƙoƙinsu da suke bambanta a daraja da nauyi na kowace waƙa; ko kuwa a mabambantan waƙoƙi na makaɗi ko mawaƙi ɗaya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Makaɗi a Sarrafa Harshen Waƙa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Mu Yi Alhairi, Mu Guji Rowa

    Mu Yi Alhairi, Mu Guji Rowa

    An Karɓo daga Abu Hurairata (Radiyallahu anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Kullum da safe waɗansu Mala’iku biyu suna sakkowa, sai ɗayansu ya ce: “Ya Allah ka mayarwa da mai abin da ya bayar, ɗayan kuma sai ya ce; “Ya Allah kawo asara ga mai hanawa (Marowaci)” (Bukahri 1442, Muslim 1010).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Yin Sadaka A Asirce danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Koyi Da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayani an ciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Sadaƙa Tana Kawar Da Musiba

    Sadaƙa Tana Kawar Da Musiba

    An karɓo daga Mu’awiyya Ibn Haidah (Radiyallahu anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Haƙiƙa yin saƙaka a asirce tana gussar da fushin Ubangiji, Kuma haƙiƙa ayyukan alhairi suna kawar da mummanar faɗuwa”(Musibu da Asarori) Ɗabarani 951; Sahihul Jami’il Sagir (3759).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mu Yi Alhairi, Mu Guji Rowa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa. danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Sassauci Ga Wanda Ake Bi Bashi

    Falalar Sassauci Ga Wanda Ake Bi Bashi

    An karɓo daga Abul Yasar (Radiyallahu anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Wanda ya yi jinkiri ga wanda yake cikin ƙunci ko ya yafe masa abin da yake bin sa, Allah zai sanya shi a cikin inuwarsa”

    (Muslim: 3014).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sadaƙa Tana Kawar Da Musiba danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za A Ci Jarabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauki danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa

    Falalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa

    An karɓo da ga Salman ɗan Amr (Radiyallahu anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Bai wa miskinin sadaƙa lada ɗaya ne, bai wa ɗan uwa saƙaka lada biyu ne” (Ladan sadaƙa da ladan sada zumunta)

    (Tirmizi 658).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Sassauci Ga Wanda Ake Bi Bashi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Zikiri danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Yin Sadaka A Asirce

    Falalar Yin Sadaka A Asirce

    An karɓo daga Abu Harairata (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce: “Mutane bakwai Allah zai sanya su a cikin inuwarsa a yinin da babu wata inuwa sai inuwarsa:

    1) Shugaba mai adalci.

    2) Matashi da ya taso kan bautar Allah.

    3) Mutumin da zuciyarsa take a rataye a masallaci.

    4) Da mutanen da suke ƙaunar juna saboda Allah, suka haɗu a haka, suka rabu a haka.

    5) Da mutumin da kyakkyawar mace mai matsayi ta neme shi, sai ya ce: Ni ina tsoron Allah.

    6) Da mutumin da ya yi sadaka a ɓoye ta yadda hagunsa ba ta san abinda damansa ta bayar ba.

    7) Da mutumin da ya tuna Allah yana shi kaɗai, har ya yi ƙwalla. (Bukhari 1423, Muslim 1031).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Dasa Bishiya

    Falalar Dasa Bishiya

    An karɓo daga Jabir (Radiyallahu anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Duk musulmin da ya dasa bishiya, za a rubuta masa lada duk lokacin da aka ci wannan dashe. Ko aka sata, ko namana dawa ya ci ko tsuntsu ya ci, ko aka ragi dashen.”(Bukhari 2320, Muslim 1552).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Yin Sadaka A Asirce danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Ake Springrolls

    Yadda Ake Springrolls

    A yau za mu koya muku yadda ake haɗa springrolls na mussaman. Springrolls abin taɓawa ne na mussamman, mai sauƙin narkewa a ciki wanda yake da saukin haɗawa. Ku biyo ni domin koyon yadda ake haɗa shi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    1.Fulawa kofi 4.

    2.Mai cokali 6.

    3.Abin ɗanɗano (yadda kake so).

    4.Kayan ƙamshi.

    5.Man suya.

    6.Cabbage da carrots.

    Yadda Za a Haɗa

    A kwaɓa fulawa da mai cokal 6, kisa ruwa kaɗan, yayi kamar kwaɓin cincin. Ki murza da abin murji ya yi fale-fale. Ki shafa musu mai ki ɗora ɗaya kan daya, kamar hawa hudu.

    Sai kisa mu murfin tukunya ki kifa shi a kan wuta ki shafa mai a jiki, ki gasa kowanne ɓari minti 2. Ki raba su a hankali ba tare da ya yage ba. Ki gama gaba ɗaya, ki ajiye su a gefe.

    Mu dawo kan nama mu zuba mai kaɗan a kasko, ya ɗan fara zafi sai musa naman a ciki muna juyawa. Idan ya kusa mu saka abin ɗanɗano da kayan kamshi.

    Mu kara juyawa a kawo kabeji da aka yanka sirisiri da gogaggen karas a zuba. A cigaba da juyawa su yi laushi kaɗan, sai a sauke.

    A ɗauko fulawa falle ɗaya a zuba kayan haɗi daga sama a naɗo daga farko, a sake naɗo gefe da gefe a naɗa kamar tabarma a liƙe da ruwan fulawa da haka har a gama da sauran fulawa. Sai a sa mai a kaskon suya mai yawa ya fara zafi sannan a zuba ana soyawa kamar guda 10, idan ya yi a kwashe asa wani har a gama.

    Wannan shi ne Spring rolls.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls. da Yadda Ake Biskit Cikin Sauƙi danna koren rubutun nan.

  • Azumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja

    Azumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja

    Watan Zul-Hajji wata ne mai tarin falala da ɗimbin daraja, cike yake da alhairai masu yawa.

    Kuma a cikinsa ake yin aikin hajji, kwanaki goma na farkonsa, kwanaki ne masu daraja, saboda haka ake son yin azumi a cikinsu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Azumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja

    Falalar Azumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja

    An karɓo daga Ibn Abbas (Radiyallahu anhu) “Babu waɗansu kwanaki da Allah ya fi son aikin alhairi a cikinsu irin waɗannnan kwanaki goma; sai suka ce:

    “Ya Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) har jihadi? Sai ya ce,”Har jihadi, sai dai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa; sannan bai dawo da komai ba”. (Bukhari, Muslim).

    Ma’anar wannan hadisi shi ne; Mujahidin wanda ya yi shahada shi ne kaɗai ya fi wanda ya yi ayyukan alhairi a waɗannan kwanaki goma lada.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Ranar Arfa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Ranar Arfa danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Azumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.