Kasance A Cikin Zikiri Kowane Lokaci

0
380

Bari in kammala wannan babi da wasiyar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)

An karɓo daga Abdullahi Ibn Basrin (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa wani mutum ya ce; da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Haƙiƙa shari’o’in Musulumci sun yi min yawa, ba ni labari ko da wani abu da zan yi riƙo da shi? Sai ya ce; “Kada harshenka ya bushe ba tare da ambaton Allah” (Tirmizi 3375).

Wato koda yaushe mutum ya kasance cikin zikiri.

Sannan kuma mu san cewa malamai sun kasa zikiri gida biyu: Akwai ƙayyadadden zikiri da kuma sakakken zikiri.

Ƙayyadadden zikiri su ne zikirin da aka iyakance lokacin ko yanayin yin sa da kuma adadin sa, kamar zikirai da karatukan salla, zikirin safe da yamma da sauransu.

Su kuwa sakakkun zikirai su ne waɗanda ba a yi musu iyaka ta lokaci ko adadi, ba sai dai ana so mutum ya shagala da shi a mafi yawancin lokutansa kamar hailala da tasbihi, salati ga Annabi da Istigfari da kuma karatun Alƙur’ani, waɗannan ana so mutum ya yawaita su a kowane lokaci.

Ya Allah ka sanya mu a cikin masu yawan amabaton Allah maza da mata. Amin

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikirin Tashi Daga Majalisa Yake danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Ɗabi’ar Lokaci, Saurin Wucewa danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceYadda Falalar Zikirin Tashi Daga Majalisa Yake
Labarin na GabaAddu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki