Tag: yadda ake

  • Akwai Wata Alama Dake Tattare Da Jaririn Watan Ramadan?

    Akwai Wata Alama Dake Tattare Da Jaririn Watan Ramadan?

    Amsa: Babu wata alama da mutum zai gani; saidai kawai zai ga jaririn watan Ramadan ne kamar yadda ake ganin sabon kowanne wata idan ya kama.

    Hujja: “Mutane sunga jaririn wata, sai na bawa Shugaban halitta labarin cewa, nima na ganshi…..”

    Marawaici ibn Umar, littafi Al Abu Dawud, Haakim, Ibn Hibban.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Idan Naga Watan Ramadan, Zan Yi Shiru Nena Ɗauki Azumin Ni Kaɗai, Ko Yaya Zanyi? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Na Shaƙi Mantaleta Ko Rob Ko Na Saka Aleɓe, Shin Yaya Makomar Azumina? danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Mutum Nawa Ne Ake Buƙatar Suga Wata Kafin A Ɗauki Azumi?

    Mutum Nawa Ne Ake Buƙatar Suga Wata Kafin A Ɗauki Azumi?

    Amsa: Mutum ɗaya idan yaga watan azumi, ya wadartar ga mutanen wannan ƙasar, da mutum ɗayan nan ke ciki kowa ya ɗauki azumi.

    Hujja: “Wani Balaraben ƙauye yace: “Ya ga jaririn watan Ramadan”; Sai Manzo ya ce: “Ka shaida babu abin bauta da cancanta sai Allah, ka shaida Allah ne ya aiko ni? “Sannan Balaraben ya ce, “Na shaida”. Sai aka umarci Bilal ya faɗa wa mutane, su tashi da azumi gobe”.

    Marawaici Ibn Abbas, littafi Ahamad, Turmuzi, Nassa’i Ibnu Maajah, Abu Dawud.

    Domin karanta cikakken bayani akan Akwai Wata Alama Dake Tattare Da Jaririn Watan Ramadan? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Nayi Haɓo Da Azumi A Bakina, Yaya Azumina Zai Kasance? danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Wane Ne Azumin Ramadan Ya Wajaba Akansa?

    Wane Ne Azumin Ramadan Ya Wajaba Akansa?

    Amsa: Wanda azumin Ramadan ya wajaba akansa, shine wanda gashin mara ya fito masa, mace ko namiji.

    Hujja: “Shari’ar Musulunci bata aiki akan mutum uku, su ne: Ƙaramin yaro har sai ya balaga….”

    Marawaicin Aliyu ibn Abi Ɗaalib, Ummuna A’isha, littafi Musnadu Ahamada.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mutum Nawa Ne Ake Buƙatar Suga Wata Kafin A Ɗauki Azumi? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Waɗanne Abubuwa Ne Na Fili Dake Karya Azumi? danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Da Me Zan Dogara Wajen Ɗaukar Azumin Ramadan; Shin Sai Naga Watan Ramadan Da Idanuna Ƙuru-Ƙuru?

    Da Me Zan Dogara Wajen Ɗaukar Azumin Ramadan; Shin Sai Naga Watan Ramadan Da Idanuna Ƙuru-Ƙuru?

    Amsa: Mutum zai dogara ne da abin da shari’ar Musulunci ta umarce shi yayi; shi ne ya ɗauki azumi da zarar hukuma ta sanar daɗaukar azumin, ko kuma  ajiyeshi.

    Hujja: “Ku ɗauki azumin Ramadan da zarar kunga jaririn wata,ku ajiye azumi da zarar kunga jaririn watan Shawwal”

    Marawaiji Ibn Umar, littafin Bukhari & Muslim.

    Domin karanta cikakken bayani akan Wane ne azumin Ramadan ya wajaba akansa? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Niyyar Ɗaukan Azumi danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Abinda Ya Kamata A Sani Game Da Kabeji (Cabbage)

    Abinda Ya Kamata A Sani Game Da Kabeji (Cabbage)

    Kabeji: Ganyen Kabeji na daya daga cikin kayan lambu da mutane ke yawan amfani dashi.

    Dayawan mutane suna cin wannan ganyen kabejin ne don marmari ba tare da sun san tarin amfanin shi ba.

    Kabeji yana ɗauke da sinadarin:

    Calcium

    Potassium

    Magnesium

    Calories

    Protein

    Fiber

    Folate

    Manganese

    Vitamin K

    Vitamin C

    Vitamin B6

    Ga kaɗan daga cikin amfanin kabeji a jikin mutum:

    1- Yana karawa ƙwaƙwalwa kaifi.

    2- Yana taimaka wajen rage ƙiba.

    3- Yana ƙarawa fatan jiki kyau.

    4- Yana wanke dattin ciki.

    5- Yana ƙarawa garkuwan jiki ƙarfi.

    6- Yana yaƙi da cutar cancer ko wacce iri.

    7- Yana sauƙaƙa ciwon kai.

    8- Yana daidaita suga.

    9- Yana taimakawa masu gyambon ciki.

    10- Yana kare mutum daga kamuwa da cutar zuciya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mene Ne Abinci A Lafiyance? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.

  • Jan Hankali Game Da Sallar Asuba

    Jan Hankali Game Da Sallar Asuba

    Sallar Asuba itace mafi Alheri fiye da barci, mu rage barci don mu ribanta da goben mu.

    Barci amsawar zuciya ne; ita kuwa sallah amsawar kiran Ubangiji ne.

    Barci mutuwa ne; ita kuwa sallah rayuwa ce.

    Shi barci hutu ne na gangar jiki; sallah kuwa hutu ne na ruhi.

    Shi baci, da mumini da kafiri duk suna yinsa ita kuwa sallah mumini ne kaɗai yake yinta.

    Masu tashi lokacin futowar Alfijir sun rabauta, fuskarsu kuma ta haskaka; goshinsu kuma yayi haske da ƙyalli, lokacin su kuma yayi Albarka. Idan kana cikinsu toh ka godewa ALLAH daya fifita ka, idan kuwa baka cikinsu toh ka roƙi ALLAH Ya saka ka cikin su.

    Amma menene yafi Alfijir kyau?

    Farillarsa (Sallar Asuba) zata saka ka acikin kulawar Ubangiji

    Sunnarsa (Rak’ataanil fajr) ta fi Duniya da abinda ke cikinta (Hadeeth)

    Ita Sallah Asuba da Mala’iku masu dutyn dare; da Mala’iku masu dutyn safe duka suna Halartar ta. Ya kai ɗan’uwa, ya ke yar’uwa, kisani fa kaima kasani duk wanda ya rayu akan wani toh akansa zai mutu, wanda ya mutu kan wani aiki kuma akansa za’a tashe shi.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Raka’atil Fajr danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Nafilolin Sallah danna nan.

  • Islamiya Daɗi

    Islamiya Daɗi

    Ko ka san wanda ya fara harba kibiya a tafarkin Allah shine Sa’ad Bin Abi Waqqas..

    Amintaccen Al’ummar Annabi (SAW) shine Abu Ubaidatu bn Jarrah.

    Annabi (SAW) Yace: wanda yake so yaga ɗan aljannah yana yawo a bayan ƙasa ya kalli Dalha bn Ubaidullah.

    Wanda yafi kowa tausayi a alummar Annabi (SAW) shine Sayyadina Abubakar.

    Wanda yafi kowa tsananin kishin addinin musulinci shine Sayyadina Umar.

    Wanda yafi kowa tsananin kunya a alummar Annabi (SAW) shine Sayyadina Usman.

    Wanda yafi kowa sanin hukunci a alummar Annabi (SAW) shine Sayyadina  Aliyu.

    Wanda yafi kowa sanin halal da haram shine Mu’azu bn Jabal.

    Wanda yafi kowa iya karatun Ƙur’ani shine Ubayyu bn Ka’ab.

    Wanda yafi kowa sanin ilimin rabon gado shine Zaidu bn Thabit

    Wanda yafi kowa sanin ma’anar ALƘUR’ANI shine: ABDULLAHI BN ABBAS.

    Ya Allah Kayi tsira da rahama ga Annabinmu Muhammad, da iyalansa, da sahabbansa, da duk wanda yayi aiki da saƙonsa har zuwa ranar tashin ƙiyama. AMEEN.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Sahabbai Suka Yi Koyi Da Annabi Muhammad (S.A.W) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sahabban Da Suka Fi Kowa Rawaito Hadisai danna nan.

  • Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

    Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

    Halayen mai Azumi – Akwai waɗansu muhimman halaye da ya kamata mai azumi ya siffanta da su; a gan su da gaske a tattare da shi. Cikin halayen akwai:

    1. Haƙuri, wato mai azumi ya siffantu da haƙuri wanda shi zai zama jagaba a cikin lamuransa; ya hana shi bin son zuciya da saɓa wa Allah. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce “Idan ɗayan ku yana azumi, kada ya yi maganganun fasiƙanci. Idan wani ya zage shi, ya ce Ni mai azumi ne” (Sahihul Bukhari 1894, Sahih Muslim 1151).

    2. Riƙon amana, yana da kyau mai azumi ya zama mai riƙon amana; domin tana daga cikin abar da za ta taimaka masa wajen kiyaye azuminsa.

    3. Rahama, ana son mai azumi ya siffantu da rahama, da sakin hannu da karamci, da kuma yalwar zuciya. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatankwacin ladan wanda ya ciyar ba tare da an rage ladan wanda aka ciyar ɗin ba” (Sunan al-Tirmizi 647, Sunan Ibn Majah 17).

    4. Nasiha, yana da kyau mai azumi ya kasance mai yin nasiha da kuma umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

    5. Sulhu, mai azumi yana da kyau ya kasance mai yin sulhu da sasanta mutane; musamman la’akari da cewa ƙiyayya da gaba na kawo tsaiko wajen karɓar ibada da addu’a.

    6. Kame harshe, ya kamata mai azumi ya kame harshensa daga maganganu na shirme da shashanci, sannan ya nesanci giba, zagin mutane da yi musu ƙage ko sharri da ƙarya ko musu marar dalili; musamman abin da ya shafi siyasa ko wasan ƙwallo ko wanin waɗannan.

    An karbo hadisi daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Wanda duk bai bar faɗin magana ta zur da aiki da ita ba; to Allah ba shi da buƙatar ya bar cinsa da shansa”. (Bukhari 4/99).

    Haka nan wani hadisin dai daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) dake cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ba azumi ba ne barin ci da sha, shi azumi shi ne na yasasshen zance da batsa; ko da wani ya zage ka, ko ya yi maka wauta, to ka ce; “Ni mai azumi ne”. (Ibn Khuzaima 1996). Ibnu Majah ya fitar da hadisi mai ɗauke da razani ga mai yin maganganun banza a yayin da yake azumi, ya ce; “Sau da yawa wani mai azumin ladansa shi ne yunwa da ƙishirwa”.

    7. Rintse ido da kame farji, yana da kyau mai azumi ya rintse idanuwansa daga kallon haramun; ya kuma kare farjinsa daga dukkanin haramtattun abubuwa. A nan muna jan hankalin waɗanda ke ganin kallon fina-finai ko tashoshi na gusar musu da yunwa; haƙiƙa wannan kuskure ne babba da kuma munana zato ga Allah, da kuma keta iyakokin Sa. Su ma masu sanya fina-finai a tashoshi wajibi su ji tsoron Allah; su sani ribar rayuwa da albarkar abin da suke so shi ne ginawa bisa tafarkin Musulunci.

    8. Iklasi, ya kamata mai azumi ya ƙudurce cewa lalle yana yin wannan azumin ne saboda Allah; kuma domin neman yardar Allah, ba domin mutane su yabe shi ba. A nan, ana jan hankalin yan’uwa masu yin sadaka ko ciyar da masu azumi da masu tafsirin Alkur’ani; da limamai masu rera tilawa, da masu zuwa Umarah, da sauran aiyuka nagari; wajibi su sanya iklasi kada shaiɗan ya lalata musu ayyukansu.

    9. Bin sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam); wajibi ne mai azumi ya nesanci bidi’o’i, ya tsaya kan sunna ka’in da na’in; domin kyakkyawan aiki yana cikin koyi da Fiyayyen Halitta (Sallallahu Alaihi Wasalam).

    10. Tarbiyya, wajibi ne mai azumi ya tsaya wajen ƙoƙarin tarbiyyantar da kansa da ‘ya’yansa; ko ‘yan’uwansa ko waɗanda yake da iko a kansu. Kuma iyaye su ɗauki wannan wata a matsayin lokacin roƙarwa ‘ya’yansu shiriya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Aiyukan Mai Azumi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Niyyar Ɗaukan Azumi

    Niyyar Ɗaukan Azumi

    Ana ɗaukar niyyar azumi ne kafin fitowar alfijir; saboda hadisin da Nana Hafsat (R.A) ta rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa: “Wanda bai ɗauki niyyar azumi da dare ba (kafin fitowar alfijir) ba shi da azumi”.

    (Sheikh Nasiruddeen Albani ya yi tahƙiƙinsa a cikin Sahih Jami’ al-Saghir, 6536).

    Sannan a yayin niyya, ba a ƙulla ta da lafazin cewa, na yi niyyar yin azumi, a’a ana ƙulla ta ne a zuci, da zimmar gobe zan tashi da azumi idan Allah ya kai mu rai da lafiya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Ayyukan Mai Azumi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Rashin Yin Sallah A Cikin Jama’a Na Lalata Azumi? danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Watan Ramadan (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarbiyar Yaro

    Tarbiyar Yaro

    Cikin shekara 21 farkon Rayuwar yaro ake ba shi tarbiya.

    Duk wanda ya kiyaye wannan ya huta.

    Ka raba 21÷3= 7

    7 na 1 dinga wasa da shi,

    7 na 2 dinga ladabtar da shi,

    7 na 3 dinga sa mi shi ido.

    Daga lokacin da ya kai shekara 21, to sakan masa Mara.

    Allahu Akbar:

    Idan ka lura da kyau za ka ga yanda Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama Yake wasa da ƙananan yara; ‘yan ƙasa da shekara 7, har yakai suna sukuwa a Gadon bayan sa Yana sujjada,

    7 na 2, Manzo yayi Umurni da ladabtar da su, idan basuyi Sallah ba, ai musu bulala,

    7 na 3, ba wasa ba duka sai sai sa ido.

    Da Manzo ya aiki Anas Ɗan Malik se ya bi shi a bata, kaga wannan sa ido kenan da lura.

    Duk wanda ya kiyaye wannan jadalin cikin ikon Allah tarbiyar ‘ya’yan sa zatayi kyau.

    Ya Allah ka sauƙaƙa mana tarbiyar ‘ya’yanmu baki ɗaya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Abin Lura Idan ‘Ɗan Ka Ko ‘Yar Ka Sun Kai Shekarun Farko Na Tashen Balaga danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Kura-kuran Masu Bayar Da Tarbiyya. danna nan.