Tag: yadda ake

  • Yadda ake Madi Rice

    Yadda ake Madi Rice

    1. shinkafa kofi ɗaya 

     2.kanunfari ƙwaya shida, star onise 

    1. kirfa sanda uku
    2. masoro da kakke cokali ɗaya/ 1 teaspoon
    3. sinadarin ɗanɗano
    4. man gyaɗa
    5. albasa
    YADDA AKE HAƊAWA
    1. Da farko za’a wanke shinkafa a tsane a kwalanda mai kyau.
    2. A zuba mai a cikin tukunya mai zurfi asa albasa idan ta fara soyuwa sai a zuba kanunfari ba kuma da star onise da kuma tafarnuwa  ayita juyawa kamar na minti ɗaya zuwa biyu
    3. A zuba shinkafa ayita juyawa har sai shinkafa ta soyu sai a zuba sinadarin ɗanɗano sannan a tsaida sanwar da zai dafa shinkafa.
    4. Idan ta dahu a kwashe a mazubi mai kyau Best eaten with peppered chicken.

    Domin karanta yadda ake Yadda ake Jollof Rice Danna nan 

  • Yadda ake Jollof Rice

    Yadda ake Jollof Rice

    ABUBUWAN BUƙATA:-

    1. shinkafa ½ cup
    2. Nama kilo 225 a yanka ƙanana
    3. Tumatir ɗin leda ko gwangwani (220g) T lpaste
    4. Tafarnuwa guda ɗaya babba
    5. Rabin kofin man gyaɗa ½ cup
    6. Nutmeg ½ tsp
    7. sinadarin ɗanɗano: Tumatir albasa, attaruhu da tattasai a markaɗa
    8. ¼ tsp chilli pepper
    9. Ruwa 2 cups
    YADDA AKE HAƊAWA
    Domibn sanin yadda ake miyar karkashi da kubewa danna nan
    1. Acikin tukunya mai zurfi a wanke nama a zuba aciki azuba ‘yar albasa, tafarnuwa da sinadarin ɗanɗano sai a barshi ya dahu acikin ruwan nama idan nama ya dahu ruwan ya ɗan ƙafe sai a zuba man- gyaɗa a soya naman ya soyu sai a kwashe 
    2. A zuba markaɗaɗɗen kayan miya a ɗan soya shi sama-sama sai a zuba tumatir ɗin gwangwani da kayan ƙamshi (tafarnuwa, kirfa, black pepper da kuma chilli powder) sai ayita juyawa har kayan miya su soyu.
    3. Idan kayan miya sun soyu sai a zuba nama da ruwa sannan a bar ruwan ya tafasa 
    4. A wanke shinkafa a zuba sai a saka  sinadarin ɗanɗano a juya a rufe

    NOTE:- A kula wajen juyawa don kar shinkafa ta caɓe

    1. A rage wutan shinkafa a bar shinkafar ta dahu har ta tsotse sai a sauke za’a iya cin shinkafar da salad idan ana buƙata ko da coslow.

    Domin karanta Yadda Ake Coconut Jollof Rice Danna nan

  • Yadda Ake Zaman Jiran Liman Bayan Nafila

    Yadda Ake Zaman Jiran Liman Bayan Nafila

    Bayan mutum yayi nafila,yana zaune yana jiran liman zai iya yin kowane zikiri kafin zuwan liman,misali istigifari ko tasbihi ko salati ko karatun Alqur’ani ko kuma ma yayi shuru,saboda shari’ah bata ce ga wani takamaiman zikiri da zaiyi tsakanin nafilar da ake yi kafin sallar farilla ba da kuma ita sallar farilla ba.

    shi yasa ma ( Ibnu taimayyah)idan yayi nafilar lokacin alfijir kafin liman yazo suyi sallar alfijir din yana yin wurudin (Ya Hayyu Ya Ƙayyumu Laa ILaaha illa anta bi ramatika astagis) sau 40,harma yake cewa wanda duk yake yin wannan wurudin zuciyar zata rayu bazata mutu ba.

    Domin karanta Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da BismillAh A Cikin Sallah Danna nan

    Idan liman yazo ana yin iƙama wato jan hankalin masallaci da cewa fa za a shiga ganawa da Allah, saboda akwai bambanci tsakanin kiran sallah da iƙama,shi kiran sallah nusantarwa ne ga duk wani musulmi na shigowar lokacin yin sallah,iƙama kuma kamar yadda bayani ya gabata.

    Idan ana iƙama mutum zai dinga maimaita abunda mai yin iƙama yake faɗa kalma bayan kalma tamkar yadda ake yi idan ana kiran sallah,iƙama kuma kowa na iya yinta misali liman ne ko mamu bawai sai lalle ladani ba,haka ma Kuma mai sallah shi kaɗai zaiyi wannan iƙamar mace ce ko namiji.

    Domin karanta Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su Danna nan 

  • Matsalar Rashin Ƙarfin Mazakuta Ko Rashin Tashin Gaba Gaba Ɗaya

    Matsalar Rashin Ƙarfin Mazakuta Ko Rashin Tashin Gaba Gaba Ɗaya

    Rashin ƙarfin gaba ko rashin taɓuka abun a zo a gani ko saurin kawowa lokacin jima’i duka matsalolin na da nasaba da waɗannan ababen.

    Matsalar na da dalilai da yawa waɗanda za su shigar da da namiji cikin wannan yanayin, idan an binciki wata hanyar ba a dace ba sai a yi nazarin wasu dalilan.

    Mafi yawan cutuka kan lalata 

    Nerves

    Arteries

    Muscles daga ƙarshe a samu wannan matsalar ta ERECTILE DYSFUNCTION ga DA Namiji.

    Sannan yana da kyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

    1- Hawan Jini

    2- Ciwon Sugar

    3- Chronic Kidney Diseases

    4- Heart Diseases

    5- Matsala ta Prostate cancer

    6- Injury ga Al’aura

    7- Unhealthily Lifestyle

    8- Smoking

    9- Yawan ƙiba ba tare da ana exercise ba

    10- Cutukan da kan addabi Nerves kamar Sclerosis

    11- Yawan Shan giya

    12- Matsalolin ƙwaƙwalwa 

    13- Haɗuwa da Accident ko yin Accident a baya a ɓangaren

    Al’aura, Spinal cord, Mafitsara

    A ɓangaren ƙwaƙwalwa matsalar za ta iya Haifar da wannan Yanayin ga mu mazaje musamman idan akwai 

    Ciwon Damuwa

    Fargaba a jima’i

    Jin Tsoro

    Worry

    Guilt

    Da dai sauran mihimman dalilai.

    Babbar matsalar da ke haifar da rashin ingancin magani shi ne rashin bincike a tabbatar da dalili. Zan cigaba ga maza wanda suke da tambaya ko neman ƙarin bayani ku yi join tambaya and answers.

    Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

  • Ciwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Maganc Shi

    Ciwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Maganc Shi

    Kowane mutum na da ciki, wanda a kusan kowane lokaci mutum kan samu ciwon ciki da ke da nau’i daban-daban. Akwai wasu nau’in ciwon ciki da idan mutum yana jin su to lallai ya hanzarta ganin likita, domin kuwa wannan suna nuni da cewar akwai matsala da kan iya haifar da matsalololi.

    Masana sun gudanar da wani bincike a kan jerin alamu na ciwon ciki da ke da matuƙar hatsari ga rayuwar ɗan Adam. Suka ce idan mutum yana yawan jin ƙunar zuciya, kamar zuciyar mutum daga tsakiya tana zafi, musamman idan mutum ya gama cin abinci, to lallai wannan idan ya ɗauki lokaci mutum na samun haka to ya garzaya asibiti mafi kusa da shi.

    Idan kuma cibiyar mutum na yawan ciwo, ko da kuwa mutum ya ci abinci ko kuwa, haka idan mutum yana samun ƙunar ciki idan yaci abinci mai zafi ko mai yaji to hakan kan iya zama wata cuta da shan wasu maguguna ba zai magance ba, akwai buƙatar mutum ya ga likita don ya duba ya ga abun da ke damun mutum.

    Haka ma idan mutum kan samu ciwon gefen ciki a kai-a kai to shi ma yana da buƙatar ganin likita, domin kuwa ana iya dace da hanjin mutum sun sauka daga kan layin da ya kamata, shi yasa mutum ke samun ciwon. Sai kuma wasu lokuta mutane kan zauna da cutar nan da ke kira dattin ciki, idan kuma ba a gaggauta aiki don cire ta ba, to tana iya haifar da wasu matsaloli da dama a cikin cikin mutum.

    Domin karanta Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction) shiga nan 

    Menene Ƙurajan Al’aura Da Yadda Za A Magance Su

    Ƙurajen al’aura wani irin cuta ko matsala da ke addabar fatar al’aurar ɗan Adam mace ko namiji. Kamar yadda kuka sani ne kalar ƙuraje ja ne, sannan wata sa’a ya kan haɗa da yi wa mutum zafi ko ka ƙaiƙayi tare da ɗan kumbura a daidai inda ya fitowa mutum. Idan mutum ya kamu da duk wani cutar ƙuraje wanda bai san da irinsa ba, ya yi ƙoƙari ya garzaya zuwa wurin likita domin ya duba lafiyarsa.

    Abubuwa Da Ke Janyo Kurajen Azzakari Ko Al’aura

    Abubuwa da dama kan janyowa mutum ƙurajen al’aura/azzakari daga cututtuka da ake kamuwa da su musamman a banɗaki, waɗannan cututtukan a kan kamu da su ta hanyar jima’i ko kuma ta matsalar rashin isasshen ƙarfin sinadarin kariya a jikin bil-adama wato autoimmune disorders. Ga kaɗan daga cikin Abubuwa Da Ke Janyo Kurajen Al’aura:

    Cutar Kaiƙayin Al’aurar mace (VAGINAL Yeast Infection):

    Irin wannan ƙurajen yakan addabi mata ne a al’aurar su musamman idan suna da wata matsalar infection, yana sa ƙaiƙayi, a kan fata ya yi ja, yakan sa fatar gaba ya kwaye sannan yakan sa mace ta rinƙa fitar da wani irin farin ruwa a gabanta.

    Cutar Molluscum Contagiosum:

    Wannan cutar yakan addabi fatar mutum, ƙurajen kan fito ƙananun zagayayyun kuraje a al’uarar ɗan Adam. Wani lokacin sukan yi ƙaiƙayi sannan kuma ta yi wa mutum zafi.

    Cutar Balantis:

    Wannan yakan fito a fatar al’aurar ɗan Adam ko a bisa kan alƙalamin azzakirin, Abun da yakan kawo irin wannan cutar shi ne rashin tsabta. Yana kawo ƙaiƙayi, yakan sa fatar wurin ya yi ja tare da saka al’aura ta fidda wani irin farin ruwa.

    Domin karanta Larurar Gaggautowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty) Danna nan

  • Addu’o’in Tashi Daga Barci

    Addu’o’in Tashi Daga Barci

    “Alhamdu lillaahil- lazii ahyaana ba’ada maa amaatanaa wa’ilaihin nushuuru”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya ɗauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi yake}.

    Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya farka da daddare yace:

    “Laa’ilaha illallahu wahdahu la shariikalahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa alaa kulli shai’in ƙadiirun. Subhanallahi wal hamdu lillaahi walaa ilaaha illallahu Allahu akbaru walaa haula walaa ƙuwwata illaa bil laahil aliiyil aziimi, Rabbigfirlii”.

    {Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne, kuma shi Mai iko ne a bisa komai, Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah shi ne mafi girma, kuma babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, Maɗaukaki, mai girma Ya Ubangijina! Ka gafarta mini}.

    Wanda ya faɗi wannan za a gafarta masa, idan kuma ya yi addu’a za a amsa masa, idan kuma ya tashi ya yi alwala, ya yi sallah za a karɓi sallarsa.

    “Alhamdu lillaahil lazii afaani fii jasadii waradda alayya ruuhi wa’azina lii bi zikrihi”

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ba ni lafiya a jikina, kuma ya dawo min da raina, kuma ya ba ni izinin ambatonsa}.

    “Inna fii khalƙis- saamaawati wal ardhi wakhtilaafil laili wannahari la ayaatil li ulil albaab allaziina yazkurunallaaha ƙiyaaman waƙu’udan wa alaa junuubihim wayata fakkaruuna fii khalƙis- samaawati wal ardhi rabbanaa maa khalaƙta hazaa baaɗilan subhaanaka faƙinaa azaban naari rabbanaa innaka man tudkhilun nara faƙad akhzaitahu wamaa liz zaalimiina min ansaari rabbanaa innanaa sami’ina munaadiyan yunadii lil imani an aminuu bi rabbikum fa’amanna rabbanaa fagfirlanaa zunuubanaa wa kaffir annaa sayyi’ atinaa watawaffanaa ma’al abraar rabbanaa wa atinaa maa wa’adtanaa alaa rusulika walaa tukhzina yaumal ƙiyaamati innaka laa tukliful mii’ada fastajaaba lahum rabbuhum annii laa udhi’u amala amilin minkum min zakarin au ansaa ba’adhukum min ba’adhin fallaziina haajaruu wa ukhrijuu min diyaarihim wa uzuu fii sabiili waƙaataluu wa ƙutiluu la’ukaffiranna anhum sayyi’ atihim wala udkhilannahum jannatin tajrii min tahtihal anhaaru laziina kafaruu fil bilaadi mataa’un ƙaliilun summa ma’awaahum jahannamu wa bi’isal mihaadu laakinil laziina taƙau rabbahum lahum jannatun tajrii min tahtihal anhaaru khaalidiina fiihaa nuzulan min indil laahi khairun lil abraar wa’inna min ahlil kitaabi laman yu’uminu bil laahi wamaa unzila ilaikum wamaa unzila ilaihim khaashi’ina lillaahi laa yashtaruuna bi ayaatil laahi samanan ƙaliilan ulaa’ika lahum ajruhum inda rabbihim innal laaha sari’ul hisaabi yaa ayyuhal laziina aamanuus biruu wa saabiruu wa raabuɗuu Wattaƙullaaha la’allakum tuflihuuna”.

    (Ali imrana, aya ta 190 zuwa ƙarshen surar)

    {Haƙiƙa a cikin halittar sammai da ƙassai, da saɓawar dare da rana, lallai akwai ayoyi ga ma’abota hankula. (su ne) waɗanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma a zaune da kuma a kishingiɗe, suke kuma tunani a kan halittar sammai da ƙassai (suna cewa):

    “Ya Ubangijinmu! Ba ka halicci wannan abu a banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta. Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa kai, duk wanda ka shigar da shi wuta, babu shakka ka kunyata shi. Azzalumai kuwa ba su da wasu mataimaka. Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa mu, mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, cewa; ku yi imani da Ubangijinku. Sai muka yi imani.

    To ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, ka kuma kankare mana miyagun ayyukanmu, ka kuma karɓi rayukanmu tare da mutane nagari. Ya Ubangijinmu! Ka ba mu abin da ka yi mana alƙawari da shi a kan harshen manzanninka, kada kuma ka kunyata mu ranar alƙiyama. Haƙiƙa, kai ba ka saɓa alƙawari.

    Sai Ubangijinsu ya amsa musu (cewa); Haƙiƙa, Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinku, namiji ko mace sashinku daga sashi yake.

    To, waɗanda suka yi hijira, aka kuma fitar da su daga gidajensu, aka cuce su saboda Ni, suka kuma yi yaƙi, kuma aka kashe su, lallai zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar da su aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu; (wannan) sakamako ne daga Allah.

    Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai- koman waɗanda suka kafirta a cikin garuruwa ta ruɗe ka. Jin daɗi ne ɗan ƙanƙani; sannan sakamakonsu wutar jahannama ce, tir da wannan makwanta.

    Amma, waɗanda suka ji tsoron Ubangijinsu, suna da aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, masu dawwama a cikinsu; wannan liyafa ce daga Allah; abin da kuwa ya zo daga wajen Allah shi ya fi ga managarta, kuma haƙiƙa akwai daga ma’abota Littafi wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abin da aka saukar.

    Zuwa gare su, suna masu ƙanƙan da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da ɗan tamanni ƙanƙani. Waɗancan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Haƙiƙa Allah mai hanzarta hisabi ne. Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi haƙuri, kuma ku rinjayi kafirai a cikin haƙuri, kuma ku yi zaman dako, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta}.

    (Ali Imran, 190 zuwa ƙarshen surar).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Jagoran Noman Waken Soya

    Jagoran Noman Waken Soya

    Gabatarwa

    Waken soya yana daga cikin amfanin gonar da aka ɗauka a matsayin abinci; wanda ake shukawa kuma ake sarrafawa a kowace nahiya. Ana samun nasarar shuka waken soya a jihohi masu yawa na Nijeriya ta hanyar amfani da iri ɗan kaɗan ko kuma kayan aiki.

    Danna nan domin dauko cikakken littafin

    Noman waken soya ya bunƙasa sakamakon amfani da yake da shi ga jikin ɗan Adam, da kuma amfani ga tattalin arziƙi, da yawan sarrafa shi a gidaje. Shi ginshiƙi ne wajen samun man girki, ana samun kashi 18 zuwa 22 na man girki a cikin ƙasa. Yana kuma ƙunshe da shi 40 zuwa 42 na sinadarin gina jiki.

    Hoto Na farko: Waken Soya

    Yanayi Da Ake Buƙata Wajen Noman Waken Soya

    • Yanayi da nau’in ƙasa yana da tasiri wajen haɓakar waken soya. Waken soya yana yi sosai a Arewacin Nijeriya, inda yawan ruwan sama ya wuce mili-mita ɗari bakwai (700mm) zuwa dubu ɗaya (1000mm).
    • Waken soya tsiro ne mai son gajeren yini sannan furensa yana buƙatar gajeren yini. Ana iya shuka shi a gona wadda ma’aunin PH ɗin ƙasar ya fara daga 4.5 zuwa 5.5. Ba a shuka waken soya a ƙasa mai tsakuwa ko gona mara nagarta domin zai sa shukar ta tsiro cikin rauni.
    • Yana buƙatar yanayi mai zafi, tsakanin yanayin zafi 22 oc zuwa 35 oc.

    Aikace-aikacen Da Ake Buƙata Domin Noman Waken Soya

    Gyaran Gona

    • Sharar gona; Za a cire dukkan ciyawa a filin, sannan a shirya gadon-shuka da hannu ta hanyar amfani da fatanya ko wani kayan aiki da aka maƙalawa shanu ko kuma motar gona (tarakta).
    • Kasar da aka gyara da kyau na sanya shukar fita da kyau da rage haɗarin ciyawa. Za a iya shuka a kan kunya ko a gyararren fili.
    Hoto Na Biyu: Gyaran Gona Da Tantan

    Zaɓar Irin Shuka

    Danna nan domin dauko cikekken littafin

    Zaɓaɓɓun irin shuka

    • Ka zaɓi irin da ya dace da yankin da kake noma.
    • Zaɓen irin waken soya ya danganta ne ta wajen lura da lokacin nunar sa, da jure fari da cututtuka.
    • Lokaci shi ma abin lura ne wajen zaɓen irin da ya dace da yankuna, a lura da iri mai zuwa da wuri ba mara saurin zuwa ba a guraren da suke da ƙarancin ruwa.
    Hoto Na Uku: Wanke Iri da Gyaran sa
    • A wanke iri da sinadarin (Fungiside kamar Captain, Apron plus) a yi amfani da fakiti ɗaya ga kilo takwas (8kg) na iri kafin a shuka domin kariya daga ƙwayoyin cututtuka dake cikin ƙasa.
    • A yi amfani da irin shuka mai inganci na kalar da aka zaɓa. A guji irin da ya tsage ko wanda ya samu illa, a yi amfani da iri wanda bai wuce watanni 12, ba domin samun tsirao mai kyau.
    Hoto Na Hudu: Iri Mara Kyau
    • Zaɓi iri mai kyau don shuka sannan a tabbatar da babu ƙwari a cikin sa. Kada a sayi irin shuka a gama-garin kasuwa, domin babu tabbacin kyawun sa ko tsirar sa.

    Shuka

    Lokacin shuka waken soya: Waken soya yana yi sosai a lokaci mai faɗi, idan gurin yana da danshi; kwanakin shukar da aka amince da su domin shuka waken suya a yankuna daban-daban na Nijeriya su ne aka gabatar a Tebur na Ɗaya (1).

    Tebur na Ɗaya: Lokutan da aka amince don shuka waken soya a Nijeriya

    S/N YANKI Lokuntan da aka tabbatar don shika
    1. Arewa ta Tsakiya Farko kan Yuni zuwa farkon Yuli
    2. Arewa maso Yamma Tsakiya Yuni zuwa farkon  Yuli
    3. Sudan savanna/Arewacin-Arewa Satin farko da na biyu na Yuli (1-2) weeks)
    • Kada a yi shukar wuri, saboda tsoron fari kan iya jawo yankwanewar shukar da kuma buƙatar sake shuka (kofi).

    Yawan Irin Shuka

    • Kimanin kilo 50-70 (Tiya 20-28) ake buƙata domin samun yawan tushe da ya kai (444,444) a cikin kadaɗa ɗaya na waken soya.

    Tazara Tsakanin Shuka

    • A shuka waken soya da hannu ko da injin shuka sannan a shuka kwaya 3 zuwa 4 a rami; a tazara sentimeta saba’in da biyar (75cm) tsakanin kunya da kunya, sannan sentimeta goma (10cm) tsakanin tushe da tushe.
    Hoto Na Biyar: Yadda Ake Shukan Waken Soya

    Sa Takin Zamani

    Taki da ake saka wa Waken Soya.

    • Ya danganta ne daga gwajin ƙasa. Waken soya a matsayin sa na amfanin mai gululai a sauyarsa zai iya samar wa kansa sinadarin nitrogen ta hanyar jawowa daga sararin sama.
    • Sinadarin phosphorus ne wanda waken soya ya rasa sosai. Don haka, sai a zuba takin phosphorus daidai don haɓakar yabanya. A zuba takin (SUPA) (3 x 50 kg bags) haɗe da ƙarin 2 x 50 bags na takin kamfa NPK (15:15:15).
    • Yawan takin da aka aminta a zuba wa gonar waken soya:

     Tebur na biyu: Yawan taki da za a saka wa Waken Soya

    S/n Yawan Taki (Kg/Ha)
    1 Buhu biyu da rabi na (NPK(15:15:15)
    2 Buhu uku na SSP (SUPA)

    Noma

    Feshin Maganin Ciyawa:

    Noman farko zai fara ne a sati na biyu (2) bayan shuka; sannan noma na biyu a sati na biyar zuwa na shida (5-6).

    Danna nan domin dauko cikekken littafin

    Feshin Maganin Ciyawa:

    Magungunan kashe ciyawa in an yi amfani da su da kyau, suna aiki sosai wajen magance ciyawa. Akwai maganin ciyawa na waken soya da za a iya fesawa kafin tsirowar shi da kuma bayan tsirowar shuka. Idan an yi amfani da maganin kashe ciyawar, to noma ɗaya ake buƙata bayan sati biyar zuwa shida (5 -6); a goran magani a yi amfani da maganin kashe ciyawa kamar yadda aka yi bayani.

    Ƙwari da Hanyoyin Magance su;

    Za a iya magance kwarin waken soya ta hanyer feshi ɗaya na (CYPERMETRIN) Di-mechecate 10EC; a adadin 100ml a cikin lita goma sha biyar (15) na ruwa.

    Tuge Waken Soya:

    Waken soya yana isa tugewa ne a watanni uku zuwa huɗu bayan shuka; sannan yana buƙatar girbi da wuri domin kaucewa asarar yawan amfani.

    Za a iya girbe waken soya a lokacin da ya kai matakin da ƙwari ba za su addabe shi ba; sanda danshi (yawan ruwa) dake cikinsa ya kai tsakanin kashi 14-16%.

    Ayyukan da ake yi bayan tuge waken soya

    Bugu da Shiƙa:-

    • A buge waken soya da hannu ko da injin da zarar ya bushe sosai, ba tare da ɓata lokaci ba.
    • An yarda a yi bugu da hannu a ƙananan gonaki. Wannan ya ƙunshi sanya waken soya a buhu da kuma bugun shi da sanda. Sannan za a sheƙe shi don a fitar da kwayar daga raugar.
    • Ana iya amfani da inji wanda zai buge ya kuma cire datti cikin sauƙi.
    Hoto Na Shida: Bugu Da Shiƙa Da Hannu
    Hoto Na Bakwai: Amfani Da Injin Casa

    Ajiya

    • Ana ajiye waken soya ne a lokacin da ruwan da ya kai cikin ƙwayar yake kashi goma 10% ko ƙasa da haka.
    • Ana iya gane bushewar ƙwayar waken soya ne sanda aka kasa gatsa shi da haƙora ko fasa shi da ‘yan yatsu, don ajiya daga wata 6 zuwa 12 sannan kuma domin dogon ajiya fiye da shekara.
    • Kada a ajiye waken soya a ƙasa, a sa itace ko katako idan za a ajiye shi a cikin suto ko rumbu.
    • Kada a jingina shi da bango wajen ajiya.

    Danna nan domin dauko cikekken littafin

    Domin karatna cikakken bayani a kan Jagoran Noman Masara danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tuwon Masara danna nan.

  • Yadda Ake Noman Wake

    Yadda Ake Noman Wake

    Wake muhimmin abinci ne wanda yake da matuƙar amfani a jikin mutane da dabbobi. Akwai manyan kasuwanni da ake sayar da wake, kuma manoma suna sarrafa harawar wake don sayarwa a lokacin rani don samun kuɗin shiga da kimanin kashi ashirin da biyar cikin ɗari (25%).  

    Danna na domin dauko cikekken littafin

    Wake na taka muhimmiyar rawa wajen samar da sinadarin takin Nitrogen ga amfanin gona (kamar masara, gero da dawa); idan ana sauya abin da aka shuka bayan damina uku zuwa huɗu da wake ko waken soya, musamman a sauran wurare. Wake baya buƙatar a yawaita masa takin zamani, sabo da sauyi na inganta ƙasar gona. Wannan ƙasida na bayyana mana dabarun noman fari da jan wake da nufin taimakawa masu noman waken don riba.

    Hoto na farko: Gonar wake

    Gyaran Gona

    • Ka yi sassabe da sharar gona kafin damina, sannan in damina ta faɗi, ka yi feshin maganin ciyawa glyphosate (round-up) wanda aka fi sani da Randon adadin lita huɗu (4) a faɗin hecta ɗaya.
    • Bayan sati biyu, sai a yi kaftu, ko kuma haro ko a yi huɗa, daga bisani sai a yi shuka.

    Gonar da ta dace a Noma Wake

    • Lokacin damina, ana iya noman wake a nau’o’in ƙasa masu yawa, amma zai fi kyau a gonakin tudu, wuri mai yashi-yashi kuma mai tsanewa da wuri.
    • In kuma da rani ne, za a noma waken, sai a sami gona a kusa da wurin da za a sami isasshen ruwa. (Wato korama ko dam ko rijiya mai ruwa).

    Yanayin da Wake yake Buƙata

    • Ana iya noman wake a lokacin damina da lokacin rani, muddin akwai yanayin zafi kimanin awa 28-30 a dare da rana a lokacin noman wake.
    • Wake yana yabannya mai kyau a wuraren da ake samun ruwan sama da ya kai kamar kimanin ma’aunin 500-1200mm a shekara.
    • Amma saboda sabbin irin wake da aka samu, yanzu ana noma wake a wurare masu samun ƙarancin ruwan sama kamar ƙasa da ma’auni 500mm a shekara.      
    • Wake yana jure fari, kuma ana iya noma shi a gona mai yashi ko kuma saimon gona

    Zaɓen Irin Wake don Shuka                                                                  

    • Ka zaɓi irin waken da ya fi dacewa da yanayin gonarka, ana zaɓen irin waken ne bisa la’akari da yawan kwanakin da yake ɗauka a gona kafin ya nuna da kuma yawan buhunan da yake bayarwa a hecta ɗaya, da jure ƙarancin ruwa, da jure wa ƙwari da cututtuka.
    • Kuma a yi lakari wajen zaɓen irin wake ta lura da launinsa da kuma girman ƙwayarsa.

    Adadin Irin da Ake Buƙata

    • Ka yi amfani da kilo (12-25) sha biyu zuwa ashirin da biyar na irin wake a hecta ɗaya.
    • Wannan ya danganta ga kalar irin waken, girman ƙwayar waken da tsarin noman shi
    • Ana buƙatar irin wake mai yawa idan waken mai yaɗo ne?
    • Ba a buƙatar iri da yawa indai waken mai yaɗo ne.

    Wanki da Gyaran Iri don Shuka

    • A wanke irin wake kafin shuka, gyara irinka, kafin shuka kuma a yi amfani da maganin wanke iri mai inganci saboda cututtukan dake cikin irin ko cikin ƙasa. Cututtuka da tsuntsaye suna kai hari ga wake kafin ya tsira da bayan ya tsiro.
    • Maganin wanke irin ya haɗa da MASHAL 2 percent APRON STAR, ALL STAR, DRESS FORCE SEED PLUS e.t.c. yi amfani da gram 10 domin wanke kilo 2-5 na iri.
    • Ka wanke hannunka da kyau da sabulu da ruwa bayan wankin iri da shuka.

    Danna na domin dauko cikekken littafin

    Shukar Wake:

    • A lokacin damina, kada ka yi gaggawar shuka wake don kada ya nuna a tsakiyar damina, kuma kada ka yi jinkiri sosai don gujema matsalar ɗaukewar ruwan sama da wuri.
    • Abu mai muhimmanci wadda za ka yi la’akari da shi, shi ne, ka gane lokacin da ruwan saman ya fara da kuma tsawon lokacin da yake ɗaukewa da kuma tsawon lokacin da waken yake ɗauka kafin ya nuna.
    • Mafi yawan waken da yake yaɗo da mai girma a tsugune suna lura da faɗuwar rana kafin su fara fure.

    Tazarar Shukar Wake

    • Ana shuka wake mai yi a tsugune a tazarar kimanin 50cm a tsakanin kunya da kunya da kuma tazarar kimanin 20cm a tsakanin shuka da shuka. Wake mai yaɗo ana shuka shi a tazarar 75cm tsakanin kunya da kunya, 50cm tsakanin tushen wake zuwa wani tushen.

    Zurfin Shukar Wake

    • Ana shuka wake a adadin zurfi na 2.5cm zuwa 5cm. Shukar farin wake fiye da zurfi na 5cm zai haifar da jinkiri wajen tsirar sa.
    • Idan ya yi zurfi sosai yana iya ruɓewa ko ya tsiro ɗaiɗai.

    Adadin Takin da Wake Yake Buƙata

    • Noman wake ba ya buƙatar taki mai yawa.
    • Ya kamata a yi amfani da takin NPK 15;15;15, kowace hecta ɗaya a sa mata buhun taki biyu a lokacin huɗan gonan ko takin SUPA SSP 30kg bayan shuka.

    Magance Ciyawa da Wuta-Wuta

    • A nome ciyawa aƙalla sau biyu. Noma na farko makonni biyu bayan shuka, sannan noma na biyu makonni huɗu zuwa biyar bayan shuka.
    • A iya amfani da maganin ciyawa wajen magance ciyawa a gonar farin wake
    • Wuta-wuta tana kawo illa sosai a gonar wake, takan fita a tushen waken ta dankwafe shi, ta hana shi fitowa ko girma, ganyensa ya rinƙa bushewa, kuma ya daina ‘ya’ya.
    • Saboda haka, ya kamata a cire wuta-wuta tun tana ’yar ƙaramar yabanya, kafin ta yi fure kuma yana da kyau a shuka wake mai jure wa wuta-wuta.
    Hoto na biyar: Wuta-wuta a gonar wake

    Kwarin Wake da Maganinsu

    • Matsalar ƙwarin wake su ne babban ƙalubale a kan harkar noman wake a Nijeriya. Ƙwarin sun kasu kashi uku:
    Hoton na shida: Tsutsar wake

    1. Ƙwari masu lalata ganyen wake kafin fure/huda.

    2. Ƙwari masu lalata wake a lokacin fure/huɗa.

    3. Ƙwari masu lalata wake bayan ya saki ‘ya’ya.

    Dabarun Magance Kwari a Gonar Wake

    • Wake yana buƙatar feshi sau biyu ko sau uku ya danganta ga yanayin ɓarnar ƙwari a gonar.

    Feshin farko: Ka yi feshin farko a tsakanin kwana talatin (30); ko talatin da biyar (35) bayan shuka lokacin da wake zai fara fure.

    Feshi na biyu: Ka yi feshi na biyu kwana goma bayan feshin farko a lokacin da waken yake fure.

    Feshi na uku: Ka yi feshi na uku idan ya zama dole, kwana goma da yin feshi; na biyu idan akwai mummunan farmaki daga ƙwarin wake MAIKOT (MARUCA) da kuma ƙwaro mai tsotse kalaben wake.

    Roron Wake

    • Ka yi roron waken a lokacin da ‘ya’yan waken suka bushe.
    • Wake mai zuwa da wuri da kuma wanda baya yaɗo, ana roro sau ɗaya.
    • Wake mai yaɗo kamar kanannaɗo a kan yi roro sau biyu ko sau uku.
    Hoto na bakwai: Roron Wake

    Ajiyar Wake

    • Ka ajiye wake a mazubin da iska bata shiga kamar duro ko buhun leda ko jarka
    • Ka ajiye tsabar waken ta hanyar jera su a buhu mai leda a ciki ko kuma ta hanyan ninka buhuna uku.

    Ajiyar Wake Na Lokaci Mai Tsawo

    • Ka yi amfani da maganin ƙwari mai suna samanda gari (Phostoxine). Ka lulluɓe maganin da tsumma ko takarda mai laushi wato (Toilet paper) ƙwaya ɗaya ko biyu sannan ka saka a cikin buhun wake mai nauyin kilo ɗari (100kg).
    • Kada ka yi amfani da, ko ka sayar da tsabar waken da aka cuɗanya shi da maganin ajiya har sai bayan wata shida.
    • Ka tabbata da tsaftar ma’ajiya, kuma duk sati biyu ka duba ko za a sami wani canji a yanayin ajiyar waken.

    Danna na domin dauko cikekken littafin

    Domin karanta cikakken bayani a kan Jagoran Noman Shinkafa A Najeriya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Noma A Najeriya danna nan.

  • Lokuta Da Yanayi Da Kuma Wuraren Da Ake Karɓar Addu’a

    Lokuta Da Yanayi Da Kuma Wuraren Da Ake Karɓar Addu’a

    Yana cikin kamala da girman karamci da rahamar Allah ya sanya a kowanne lokaci dare da rana bawa ya fuskanci Allah yayi addu’a za’a amsa masa.

    Tare da akwai wasu lokuta da gurare waɗanda Allah jalla wa’alaa ya albarkacesu da daraja ta musamman, wanda addu’a acikinsu keda tasiri na musamman. Ga wasu daga ciki:

    1. Addu’a ranar Arafah.

    2. Addu’a a Lailatul ƙadr.

    3. Addu’a akashi daya cikin ukun karshen dare.

    4. Addu’a bayan tahiyar karshe.

    5. Addu’a a cikin sujjadah.

    6. Addu’a tsakanin kiran Sallah da Iƙama.

    7. Addu’a yayin saukar ruwan sama.

    8. Addu’a ranar juma’a.

    9. Addu’a yayin shan ruwan zam-zam.

    10. Addu’a yayin da ake kiran sallah

    11. Addu’a yayin tashi daga bacci.

    12. Addu’a a kwanaki goman farko na Dhul-hijjah.

    13 .Addu’a a cikin ka’abah.

    14. Addu’a yayin gama karatu ko karantarwa.

    15. Addu’a yayin da mayaƙa sukayi sahu.

    16. Addu’a a majalissan da ake ambaton Allah.

    17. Addu’a yayin da imani ya ƙaru a zuciya.

    18. Addu’a bayan zare ran mamaci.

    19. Addu’a yayin jifan jamraat.

    20. Addu’a akan dutsen safa.

    21. Addu’a akan dutsen marwa

    22. Addu’a a mash’aril haram.

    23. Addu’a yayin ziyarar marar lafiya.

    24. Addu’a gabannin sallar azzahar.

    25. Addu’a a watan Ramadhan.

    26. Addu’a yayin sahur ga mai azumi.

    27. Addu’a yayin buɗa-baki ga mai azumi.

    28. Addu’a yayin shiga tsanani, matsi da ƙunci.

    29. Addu’a da addu’ar zun-nun Alaihis salaam.

    30. Addu’a da Istirja’i.

    31. Addu’a a multazam.

    32. Addu’a a Makam Ibrahim.

    33. Addu’a yayin karatun suratul fatiha.

    34. Addu’a yayin ƙarfafuwar Mahabbah da Ikhlasi a zuciya.

    35. Addu’a yayin carar zakara.

    Duba:

    1. Du’aa na Dr. Yassir Qadhi

    2. Addu’a wa Manzilatahu Minal Aqidatil Islamiyyah na Dr. Jilan Alarusiy wanda rubuntunsa ne, na Masters Degree kulliyatud da’awah, Qismul Aqidah a Jami’atul Islamiyyah Madinatul Munawwarah a shekarar 1410A.H.

    3. Ahmiyyatud Du’a wa Kaifiyyatahu fis Sunnatin Nabawiyyah na Dr.Ibrahim al-Hamd.

    Domin karanta cikakken bayani akan Alkunyar Da Ake Wa Manzon Allah (S.A.W) danna koren rubutun nan.

  • Addu’a A Yayin Sujjada

    Addu’a A Yayin Sujjada

    “Subhaana Rabbiyal a’alaa”.

    {Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi ɗaukaka}. Sau uku (3).

    “Subhaanakal laahumma rabbanaa wa bihamdika Allaahummagfir lii”.

    {Tsarki ya tabbata gare ka, ya Allah! Ya Ubangijinmu! Tare da godiya gare ka. Ya Allah! Ka gafarta mini }.

    “Subbuhun ƙuddusuun Rabbul Mala’ikati war ruuhi”.

    {(Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kuɓuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala’iku da Jabrilu}.

    “Allaahumma laka sajadtu wa bika aamantu, walaka aslamtu sajada wajhii lillazii khalahu wa sauwarahu wa shaƙƙa sam’ahu wa basarahu tabaarakal laahu ahsanul khaaliƙiina”.

    {Ya Allah! Gare ka na yi sujada, kuma da kai na yi imani, kuma gare ka na miƙa wuya. Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta. Kuma ya yi mata sutura, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta. Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita}.

    “Subhaana zil jabaruuti, wal malakuuti, wal kibriyaa’i, wal azamati”.

    {Tsarki ya tabbata ga (Allah) Mai dole, da mulki, da ƙasaitar ɗaukaka da girma}.

    “Allaahummagfil lii zanbii kullahu, diƙƙahu wa jillahu, wa auwalahu wa akhirahu wa alaaniyatahu wa sirrahu”.

    {Ya Allah! Ka gafarta min zunubaina dukkanninsu, ƙanananansu da manyansu, na farkonsu da na ƙarshensu, bayyanannunsu da ɓoyayyunsu}.

    “Allaahumma inni a’uzu bi ridhaaka min sakhaɗika, wabi mu’aafaatika min uƙuubatika wa a’uzu bika minka, laa uhsii sanaa’an alaika anta kamaa asnaita alaa nafsika”.

    {Ya Allah! Ina neman tsari da yardarka daga fushinka, da kuma rangwamanka daga uƙubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gare ka. Ban isa na tuƙe ga yabo mai cancanta gare ka ba; kai dai kamar yadda ka yabi kanka ne}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tahiyya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Ruku’u danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.