Tag: yadda ake

  • Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Nau’ikan Sihiri

    a. Akwai kurciya

    b. Dan baka

    c. Sihirul firaƙ

    d. Sihirul muhabba

    e. Sihirul jini

    f. Sihirul tasrif

    g. Sihirul sariƙ

    Wannan su ne nau’i kaɗan daga cikin nau’ikan sihiri. Kowanne kuma da yadda ake yin sa. Ana yin sihiri mace ta saukar wa da ‘yar uwarta jini, ta rinƙa yin jini a duk lokacin da mijinta ke ɗakinta. Ana yin sihiri uba ya ji ya tsani ‘ya’yan wata sai na ɗaya. A na ma mutum sihiri ya ga duk abinda ya samu ya ruguje, ka ga kana samu amma kuma abun yana rushewa. Kuma ana iya yin sihiri a hana budurwa aure. Sannan ana iya yin sihiri mace ta rinƙa warin jaɓa, saurayi ya zo wajenta ya ji tana wari.

    Ana yi wa yaro sihiri dan a lalata rayuwarsa, ya zama ɓarawo, ɗan iska ko kuma ɗan shaye-shaye. Koma dai wane irin sihiri ne. Allah bai taɓa yin ciwo ba sai da maganinsa.

    Akwai matakai da ake bi domin a karya sihiri. Wani sihirin za a iya yi da an karya shi sai ya dawo, wani kuma da an karya shi yake tafiya. Sakamakon rashin kariya ne da tun farko ba a yi ba shi yasa da an karya zai iya dawowa.

    Da yawan waɗanda sihiri ke jikinsu ba su cika yadda da cewa sihirin ne ba. Gane sihiri aka yi maka, harka nemi maganin karya shi da na kariya shi ma arziki ne. Ga matakan da ya kamata ka ɗauka wajen maganin kariya yadda duk wani sihiri ba zai kamaka ba da kai da iyalanka, haka tsafin mai tsafi ba zai kamaka ba. Ko da mutum yana magana yana fitar da wuta a bakinsa saboda sihiri, to da yardar Allah ka fi ƙarfinsa. Sai dai a ganka ana faman duka amma ka kasa faɗuwa, ka zama shagwan mada. A kan yi amfani da ayoyi guda 33 a cikin Al-Ƙur’ani domin neman kariya daga sihiri.

    Ga ayoyin kamar haka;

    Za ka karanta su ne bayan fatiha Suratul baƙarah aya ta 1-5 Ayatul kursiyyu aya ta 255 Amanar rasul zuwa ƙarshen surar Suratul A’araf aya ta 54-56

    Sannan ka karanta;

    “ƙulid’ullaha awid’ur rahman, ayyam ma tad’u falahul asma’ul husna, wala tajhar bi salatika wala tukhafit biha wabtagi baina zalika sabila”

    Har zuwa ƙarshen suratul Isra’i

    Da kuma suratus safat aya ta 1-11 Da suratur rahman aya ta 33-35

    Sannan ka karanta;

    “lau anzalna hazal ƙur’ani ala jabalin lara’aitahu khashi’an mutasaddi’an min khashyatillah, wa tilka amthalu nadribuha linnasi la’allahum yata fakkarun”

    Zuwa ƙarshen suratul hashri

    Da surar jinn aya ta 3-9 Sannan suratul buruj aya ta 20-22

    Waɗannan ayoyin akan samu ruwan rijiya ko na zam-zam ko ruwan sama a karanta su kowacce ƙafa bakwai a tofa a cikin ruwan, a sa za’afaran ko na mai, ko na gari, ko kuma na ciyawa. Sai a rinƙa ɗiba kaɗan ana sha da safe da kuma in za a kwanta. Za kuma a iya karanta su a tofa a cikin man zaitun da man habba da man kwa-kwa ko na riɗi, a rinƙa shafawa a jiki. Mutum zai iya shafawa da iyalansa gaba ɗaya. Muddin kai da iyalanka za ku rinƙa shafa wannan addu’ar, ba wani tsafin mai tsafi ko sihirin mai sihiri da zai yi tasiri a jikinka insha Allah. Sannan wannan addu’ar ka karanta ta a gidanka kullum da safe, Ubangiji zai ba iyalanka da gidanka kariya daga dukkan sharrin mutum da aljan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Kariya Daga Hassada, Maita, Da Sharrin Aljanu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Maganin Damuwa danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa

    Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa

    Wannan addu’ar mutum yakan yi ta idan ya shiga cikin damuwa ko ya shiga cikin wani hali, ko tashin hankali; ya rasa yadda zai yi sai ya lazimci karanta wanan addu’ar. Allah zai fidda shi daga cikin wannan tashin hankalin da damuwa.

    An ruwaito daga Imam Ali Hassan Shazah, yana koyawa almajirinsa wannan addu’ar. Ga ta kamar haka;

    “Ya wasi’u ya Aleem, ya zal fadlul azeem, wa in tamsasni bi durrin fala kashifa lahu illa anta, wa’in turidni bi khairin fala raadda bi fadlik, tusibu man tasha’u min ibadak wa antal gafurur rahim”

    Akan so duk lokacin da ka yi salla ko ka yi wani aikin alkhairi ka karanta wannan addu’ar, Ubangiji Allah zai yaye maka damuwarka In Sha Allah. Ansamo wannan addu’ar daga littafin MAFATIHUL FARAJ shafi na 110. Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Kyautata Tsakanin Ka Da Ubangiji Da Neman Gafara dannna koren rubutu. Don karanta Addu’a Gatan Mumini danna koren rubutu. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Yadda ake Rice Chocolate Cookies

    Yadda ake Rice Chocolate Cookies

    ABUBUWAN DA’AKE BUƘATA

    1. Fulawar shinkafa    1    cup
    2. cocoa powder    ½ cup 
    3. chocolate flavour ( Filabon chakulet )
    4. Bicarbonate soda ½ ƙaramin cokali 
    5. Kirfa (cinnamon) ½ ƙaramin cokali
    6. Gyaɗar miya (nutmeg) ½ ƙaramin cokali
    7. Butter 2 manyan cokali
    8. Egg 2
    9. sigar  1 cup
    Yadda Ake Haɗawa

    Domin karanta Yadda Ake Rice Cocktail Bites Cikin Sauki Danna nan

    1. za’a haɗa fulawa, cocoa powder, bicarbonate soda, baking powder, kirfa, gyaɗar miya a waje ɗaya a juya sai a ajiye gefe
    2. A cikin roba mai kyau a zuba bota ayita juyawa har sai botar ta canza kala, sannan a saka kwai a buga komai ya haɗe jikinshi. 
    3. A ɗauko haɗin fulawa a zuba cikin bota a juya da kyau ta haɗe.
    4. sai a sami  

    Domin karanta Yadda Ake Rice Butter Cookies Danna nan 

  • Yadda Ake Rice Butter Cookies

    Yadda Ake Rice Butter Cookies

    Abubuwan da ake bukata domin hada Rice Butter Cookies cikin sauki.

    1. fulawar shinkafa     1 cup
    2. Butter   4 tablespoon
    3. Baking powder     ½ teaspoon
    4. Bi- carbonate soda     ½ teaspoon 
    5. Natmeg da cinnamon  ½ teaspoon each
    6. ƙwai guda  1
    7. strawberry ko cherry idan ana buƙata.
    Domibn sanin yadda ake miyar karkashi da kubewa danna nan
    Yadda Ake Haɗawa
    1. A haɗa komai cikin roba a murzashi da kyau.
    2. sai a sami rolling pin da board a murza a yanka zuwa shape ɗin da ake so za’a iya yi mishi ado da cherry yankakku ko kuma strawberry a ɗora sa sama bayan an yanka zuwa shape ɗin da akeso .
    3. A ɗora akan farantin gashi a gasa na minti 10 – 15 a temperature 110c – 115c.

    Domin karanta Yadda Ake Rice Cocktail Bites Cikin Sauki Danna nan

  • Yadda Ake  Rice Cocktail Bites Cikin Sauƙi

    Yadda Ake Rice Cocktail Bites Cikin Sauƙi

    Abubuwan da ake buƙata domin haɗa Rice Cocktail Bites Cikin Sauƙi su ne:

    1. Rice fulawa 2 cups
    2. Garin wake 1 cup
    3. curry powder  ½ teaspoon 
    4. Baking powder 1 ½ teaspoon
    5. Barkono dakakke idan akwai yaji a saka dai dai yadda akeso.
    6. sinadarin ɗanɗano dunƙule 2
    7. Tafarnuwa garin  1 teaspoon
    8. bota ko mai cokali uku.
    9. mai na suya.
    Yadda Ake Haɗawa
    1. A haɗa komai cikin roba mai kyau sai a zuba ruwan ɗumi a kwaɓa ya yi kauri
    2. A samu extnuder ko injin taliya a fitar da shape a soya acikin mai me zafi.
    Domin sanin yadda ake miyar karkashi da kuɓewa danna nan
  • Yadda ake Rice Biscuits (COCONUT)

    Yadda ake Rice Biscuits (COCONUT)

    Abubuwan da ake bukata domin yin rice bsicuit cikin sauki

    1. Rice fulawa    1 cup
    2. Butter     2 tablespoon 
    3. siga      ¼ cup
    4. Bi – carbonate  soda   1 teaspoon
    5. Baking powder     1 teaspoon 
    6. Flavour nil
    7. Egg   2
    8. Milk  1
    9. Desiccated coconut   4 tablespoon
    10. Cinnamon   ½ teaspoon
    11. Nutmeg    ½ teaspoon

    Domin karanta Yadda Ake Coconut Jollof Rice Danna nan

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A sa butter da siga a buga har sai bota ta canza kala
    2. A zuba ƙwai a sake bugawa.
    3. A zuba sauran kayan haɗin sannan a kwaɓa da kyau a murza
    4. A sami chopping board a murza a kai sannan a yanka da cookies cutter zuwa shape ɗin da akeso.
    5. A yi baking a temperature na 115c na minti 10 – 15 ko kuma idan ya fara ƙamshi.
    Domibn sanin yadda ake miyar karkashi da kubewa danna nan
  • Yadda Ake Rice Bread Cikin Sauki

    Yadda Ake Rice Bread Cikin Sauki

    Idan za’a yi biredin ana buƙatar a niƙa fulawar tayi laushi sannan a haɗa da fulawar alkama domin a sami good end product mai kyau, tayaya zamu sami good end products zamu iya 50

    50 na alkama da kuma shinkafa ko kuma zamuyi 70% alkama da kuma 30% shinkafa domin kamar yadda muka faɗa a baya itama shikafa bata da sinadarin protien wanda yake fitar da (Gliadin da kuma Gluten) in da su wannan sinadaren ke bawa fulawa danƙo idan ana sarrafata. Idan muka ce zamuyi breadin fulawar shinkafa zalla tun daga murji bazamu sami abunda mukeso ba sai bincike ya nuna cewa proportion of 70 : 30 wheat rice is the best when it’s comes to bread making in da shi breadi na neman wannan danƙo domin ya tashi kuma yayi laushi sannan bazai  farfashe ba idan an gama gasa bread ɗin.

    Haɗa  fulawar alkama ya tasar da wannan biredi daga gluten – free bread idan za’a iya yi na shinkafa 100% fulawa.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.

    Idan zamuyi biredi mai kyau na shinkafa da farko muna buƙatar shinkafa mai kyau da kuma tsafta.

    ABUBUWAN DA AKE BUƘATA 
    1. fulawar shinkafa   30g
    2. fulawar alkama (normal wheat fulawa) 70g
    3. ruwan ɗomi
    4. milk (madara)
    5. yeast
    6. butter 1 tablespoon cokali ɗaya babba.
    YADDA AKE HAƊAWA
    1. A haɗa yeast da ruwan madara mai ɗumi a ajiye a gefe.
    2. A zuba fulawar shinkafar data alkama acikin kwano mai zurfi sai a zuba bota cokali ɗaya a chakuɗa da ɗan gishiri da siga.
    3. sai a kawo ruwan yeast da madara a haɗa a kwaɓa.
    4. A shafawa roba mai kyau mai a sami  roba a mulmula a saka aciki. A rufe da tsumma mai kyau a rufe ya kai wuri mai ɗumi ko kuma akai rana a barshi ya tashi kamar na minti 50 zuwa awa ɗaya.
    5. Idan ya tashi sai a barbaɗa a tebur ɗin kichin (tebur ɗin aiki) sannan a sake murza fulawar na minti 3 – 4 a yanka yadda ake son girman
    6. A sami abun gashin biredi mai kyau a shafa bota sannan a barbaɗa fulawar a ciki. A ɗauko fulawar a saka aciki a rufe abarshi ya sake tashi na minti 30 kafin a saka acikin oven a gasa.
    Doughnut:- 13
    1. Da wannan kwaɓin zamu iya yin doughnut ɗinmu sai dai shi donut zamu murza a yanka da roba mai round sannan a saka robar lemo a cire tsakiya idan kuma akwai abun yankan donut sai a fidda shape ɗin da shi.
    2. A soya har sai yayi golden brown

    Domin karanta Abinda Ya Kamata A Sani Game Da Kabeji (Cabbage) Danna nan 

  • Yadda Ake Rice Waffies

    Yadda Ake Rice Waffies

    ABUBUWAN DA AKE BUƘATA

    1. fulawa  1 ½ cup
    2. Baking powder 1 teaspoon 
    3. Egg kwai 2
    4. Bota 
    5. Madara 
    6. Abin gashin waffce (waffce maker).
    Yadda Ake Haɗawa
    1. A haɗa dry ingredients waje ɗaya
    2. A haɗa wet ingredients waje ɗaya
    3. A haɗa wet da dry ingredients a kwaɓa da mixer
    4. A zuba butter waffces a cikin abun gashin waffce a gasa

    Domin karanta Yadda Ake Rice Cake Danna nan 

  • Yadda Ake Rice Cake

    Yadda Ake Rice Cake

    ABUBUWAN DA AKE BUƘATA

    1. Flour shinkafa 1 ½ cup
    2. baƙin hoda 1 teaspoon
    3. kwai guda biyu
    4. bota ¼ cup 
    5. filebo (vanilla flavour)
    6. madara ½ cup
    Yadda Ake Haɗawa

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.

    1. A sami roba mai kyau a tankaɗe fulawa da bakin hoda.
    2. A zuba bota da siga a cikin wata roba ayita juyawa har sai yayi haske, sai a zuba kwa, filebo da madara a juya.
    3. A ɗauko fulawa a zuba a juya da kyau.
    4. A samu abun gashi mai kyau a shafa bota aciki sannan a barbaɗa fulawa.
    5. A zuba botter a cikin gasarar cake/ ƙullin cake ɗin.
    6. in a pre- heated open of 180c a saka kek na minti 15 ko kuma idan an saka tsinke ya fito babu ƙullin kek.

    Domin karanta Abinda Ya Kamata A Sani Game Da Kabeji (Cabbage) Danna nan 

  • Yadda Ake Pancake Cikin Sauki

    Yadda Ake Pancake Cikin Sauki

    Pancake abinci mai sauƙin sarrafawa kuma na karin kummalo ko kuma domin yara ‘yan makaranta ana iya cin pancake da lemo ko madara ko shayi.

    ABUBUWAN BUƘATA
    1. fulawar shinkafa 1 ½  kofi ɗaya da rabi
    2. Madarar ruwa rabin kofi 1 ½ cup
    3. kwai 2
    4. Baking powder (baƙin hoda) ½ teaspoon
    5. sugar ½ kofi
    6. flavour (vanilla flavour) 1 teaspoon.
    7. Bota (butter) ¼ cup
    8. Dafaffiyar shinkafa kofi ɗaya 1 cup.
    Yadda Ake Haɗawa

    Domin karanta cikakken bayani akan Mene Ne Abinci A Lafiyance? danna nan.

    1. A haɗa dry ingridients cikin roba mai tsafta (fulawa, baƙin hoda).
    2. A cikin wata roba mai zurfi a sa bota da siga ayita juyawa har sai yayi fari.
    3. A fasa kwai a zuba ana juyawa.
    4. Bayan nan sai a zuba madara, filabo a juya.
    5. A ɗauko fulawa mai baƙin hoda a zuba a juya da kyau sannan a zuba dahon shinkafa.
    6. A sami abun gashi mara kamu (non- sticky frying pan) A shafa mai sai a zuba gasarar pancake idan ya gasu sai a juya ɗayan ɓarin shima ya gasu.
    7. Haka za’a yi tayi har a gama da gasarar.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Farfesun Kayan Ciki A Sauƙaƙe danna nan.