Tag: yadda ake

  • Abin Da Zai Faru Gobe

    Abin Da Zai Faru Gobe

    Ban san gaibu ba, amma tabbas na san abin da zai faru da ni gobe, domin kuwa yau ɗina yayar gobe ce tunda ni ne a yau ɗin kuma ni ne zan je goben.

    In ban canza a yanda nake ba yau to gobe ma haka zan kasance, domin babban dalilin da ya sa aka samar da Yau da Gobe shi ne canjawar aiki da matsaya, lokaci da matafiya, dan gujewa kwan-gaba kwan-baya.

    Idan ba a buƙatar a canja to babu hikimar saka lokaci, na sallah ne ko kwa na cin abinci, to bare a gane lokacin zuwa Masallaci ko kuma Coci.

    Idan ba ka canza daga yanda kake ba har gobe ta yi to malam har yanzu a jiya kake, kasancewar ka a yau shi ne canjawar aikinka, ɗabi’arka, mahangarka da yanda kake tunaninka.

    Dan haka akwai buƙatar in gobe ta yi na ji a jikina na shiga gobe, in kuwa ta wuce to cikin biyu ɗaya nake yi. Ko dai na bar jiya a taho da ni yau ko kuma na tsaya a jiya kafin na ƙaraso, wanda kuma bai cika yiyuwa ba, abin da ya fi kawai shi ne na dage na kyautata abubuwan da nake yi yau na kuma gama da su ba tare da na bar kwantai ba.

    Sabo da haka kar ka yaudari kanka da cewa gobe ta Allah ce, domin ba a taɓa samun jahili a yarinta kuma ya zama malami sanda ya girma ba, musammam a ce bai canja jiyansa da yau ɗinsa ba.

    Yanzu tunda kake ka taɓa ganin yaran banza bai zama babban banza ba? Ko ka taɓa ganin mummunar yau, ba ta haifar da wulaƙantacciyar gobe ba?

    Abban Marke

    Don karanta waƙar Yaushe Tura Za Ta Kai Bango danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Me Za Ka Yi Idan Ka Ga Ɗan Uwanka Zai Mutu?

    Me Za Ka Yi Idan Ka Ga Ɗan Uwanka Zai Mutu?

    Manzon Allah S.A.W Yayi Mana Wasu Bayanai Dangane Da Mutuwa: Da farko babbar alama da za a gane kusantowar mutuwa ga mutum mai matsananciyar jinya ta rashin lafiya shi ne, lokacin da ka ga bayan tsananin ciwo sai ka ga an samu ɗan sauki, zufa wato gumi ya fara fita daga goshin shi mara lafiyan. To wannan in dai ba a yi Sa’a  ba to alamar mutuwa kenan.

    IDAN KA GA WAƊANNAN ALAMU SUN BAYYANA MENENE ZA KA YI WA ƊAN UWANKA

    Abinda akeso a daidai wannan lokaci shi ne, kalmar shahada wato LA’ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADURRASULULLAH. A sigar karantawa tare da maimaitawa. Ba za ka ce wane ka ce LA’ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADURRASULULLAH ba, ba za ka ce haka ba, za a yi ta maimaitawa a gabansa har shi ma ya kama faɗa, ko kuma ya faɗi a zuciyarsa, saboda ya mutu akan sunnar annabi Muhammad S..A.W.

    Abu na gaba shi ne, idan kai makaranci ne, an so ka karanta masa Suratul-Yaseen. Bayan ka tabbatar ya rabu da duniya, wato bayan ran ya fita. Abinda za ka yi na gaba shi ne za ka rufe idanunsa da kuma bakinsa, shi mamacin.

    Sa’annan kuma a wannan lokacin ne za ka ba da labarin mutuwarsa ga makusantansa, kafin sanarwa ga sauran jama’a. Daga wannan lokaci ne za a fara shirya shi izuwa ga masaukinsa, ba tare da jinkiri ba.

    Bayan shirya shi, abinda ke biye shi ne yi masa wanka tare da sutura wato likkafani kenan, daga nan kuma sai yi masa rakiya zuwa makwancinsa, wato kabarinsa tare da sanya shi a ciki da rufewa, wato binnewa.

    Daga wannan lokaci da aka binne mamaci, shari’a ta hana ake ambatarsa da mummunan aiki da ya aikata ko kuma wasu munanan kalamai ko suna. Domin duk abinda ya aikata ya koma tsakaninsa da Ubangijinsa.

    Domin daga wannan lokacin dukkan lamuransa sun koma ga mahalicci Ubangijinsa.

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Yaushe Tura Za Ta Kai Bango?

    Yaushe Tura Za Ta Kai Bango?

    Jama’a wai kwa du kuna iya ji na
    Na ga kamar fa ba ku saurare na
    Ya na gane ku ne a zaune a rana
    An ya ma kwa za ku so waƙe na.

    Da dai na mayar wuƙar ƙuguna
    Na ajiye dukka al-ƙalumana
    Domin ni fa ko? Akwai hange na
    Shi nassa gidan ga ba waƙe na.

    Yanzu hakan ga za ku zauna ni kam?
    Wasu gommai suna zuba muku poison
    Ko sai sun fara dangana ku da prison
    Ƙarni CENTURY decade kuma season.

    Ba ni da arzuƙin zama a gidana
    Ba ni abin da zani bai ‘ƴa’ƴana
    Balle ma na kai gidan surukaina
    Haka kullum nake barin matana.

    Yanzu ƙasar ga babu canji kenan
    Ba mai tausayin da zai ce uffin
    Sai wahala ake ta sha ni wai kam
    Ko sararin ga mun fi kowa more than.

    Sai an ambata ku ce watarana
    In komai ya kai mahudar rana
    Akuya in ta dangana bangona
    Cizo za ta dunga yi ɗan Chana.

    An zo an kashe iyayen wancan
    An ɗau wane sai kace Al-kakin
    Wane kwa an kashe hi can ba haƙƙin
    Matar wane ko gabansa ka haiken!!

    An sace ɗiyar mutum fa da rana
    Ni kuma an kashe ɗiyata gidana
    Haka an sace wance du a idona
    Dan Allah ku kai kuɗin fansana.

    Na kai shekara rabon a gidana
    Da Tukunya ta doshi kan murhuna
    Kuma wallahi babu ko son raina
    Tsabar an ci ne da haƙƙoƙina.

    Na je Hospital a ban haƙƙina
    Ba komai cikinsa duk sai yana
    Ba daktas da sunka kai saba’una
    Kuma adadin garinmu ya fi a auna.

    Ba mai faruwa a bayan wannan
    Akuyar ta shige ta bayan bangon
    Ta ma tsallake ginin har zauren
    Ta manta ashe fa an zo bangon.

    To ko dai mu tashi ko kwa mu zauna
    Ko kwa mu dunga shan bugun fir’auna
    Ba baƙon da za ya zo shi gidana
    Ya yi aikin da ban iya ba ku auna!!

    Sai gyara ake a wassu ƙasashen
    Amma mun yi shu kamar ba ma nan
    Kuma mun fi su ma karmar mu yi wannan
    Dan kwa da mai kama ake yin ƙotan.

    Abban Marke.

    Edita: Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Duka A Murɗe

    Duka A Murɗe

    Afwan yau jikin kamar wani mai laulayi

    Haka na yini ta har daren Allah haka na yi

    Ban aika ba babu wanda kuma nace ya yi

    Shi ai so fa ba abin dama ba ya yi.

     

    Ita waccen tana faɗin ni ce taka ɗai

    ‘Ƴar dangi na faɗin ba mai min kwaɗai

    Abba fa nawa ne ki jini na ni ni kaɗai

    Gogan naku ko yana kwance kishingiɗe

     

    Babu fa wanda za ya ce bai son nasa kam

    Sai dai in ya zam yana ɓoyewa kurum

    Ba a makara idan handset kwai alarm

    Babu ruwansa sai ya yo ma ƙara daram.

     

    Maganar gaskiya fa waccen na riƙa sila

    Tun da kamar muna ƙanana fa ya ‘ƴan shila

    Ba ko hantara bare zancen matsala

    Tun ma kan tsayinta ɗinnan fa ya kammala

     

    Haka siddan ki zo ki ce sai min banƙara

    Daga haddar izawaƙa kika nufi baƙƙara

    Kika bar nan kika wuce ƙarshen saɗɗara

    Fazuƙu falan-nazidkum ki yi hattara.

     

    Maganar gaskiya kamata fa ki hanƙura

    Tinda gidanku na sani ba mai takura

    Ba mai ji kama da kamun da ta kumbura

    Ko mai na ci ya beban da ya ke bara.

     

    Kin ga fa ni gidanmu ni ne ɗai salimi

    Kar fa ki sa mutan gidajenmu a zullumi

    Kar ki bari na dinga jin zafi ba gumi

    Sai dai in jikin ga nau to da akwai shimi

     

    Kin ga idan akwai rabo wataƙil za ya zo

    Ko duk duniya su taru su yo dandazo

    In dai Rabbi ya hana to dai ba ya zo

    Ba na son kira a ce min to je ka zo.

     

    Tabbas na sani kina so na Mahira

    Kuma ni ma fa da hakan take ya Ɗahira

    Amma yanzu kam a ƙyale ni na tsahira

    Ɗandagus da shi da Ɗanbello Jira! Jira!!

     

    Afwan ni fa ba na yin ƙusƙus duk dare

    In ka ganni kan icen kuka maza ɗare

    Ba akuya kana sannan kuma ba kare

    Sai ‘ƴa’ƴan fire a mota fal maƙare.

     

    Afwan duk da na sani ba kya jin bari

    Mai suna Karima ce aka cewa Kari

    Mai son shi a kai shi police bai jin bari

    Sai ya je shi dole wata ƙila da ma mari.

     

    Allah ya sani fa ba so ne ba na yi

    Da harawa da garera a haɗa da ƙamayi

    Duk akuyar da tai ta kushe haka so ta yi

    Tattauna shi gunta ko ba ranar ta yi.

     

    Domin ni fa ɗan titis nake sam ba nawi

    Ba Li’irab bare a ce mini annahawi

    Shi farce yana da aiki ran ƙaiƙayi

    Allah dai ya sa abin da ake so na yi.

     

    Abban Marke

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Har Yanzu Akwai Matsala Fa

    Har Yanzu Akwai Matsala Fa

    Daga Lokacin da ya zamto mace na goyon ciki amma kullum tana cikin ƙunci da kuka lokaci zuwa lokaci, wannan na shafar yanayin bugun zuciyar abinda take ɗauke da shi (heart rate) wanda yakan iya developing ɗin heart problems tun a ciki (jaririn) Sannan ita kanta ba za ta dinga saurin warkewa ba akan lokaci in rashin lafiya ta same ta. Don haka wajibi ne mazaje ku gane matanku fa abokanku ne, ƙannenku ne, ƙawayenku ne, jikinku ne baki ɗaya don haka ku yi duk yadda za ku yi ku kyautata musu.

    GA INDA BAYANIN NAWA YAKE

    Akwai babbar matsala tabbas a yanzu mata sun duƙufa suna zuwa Awo (ANC)  amma ba sa zuwa asibiti haihuwa.

    A gaskiya muna asarar rayukan mata masu ɗsmbin yawa Sakamakon matsalolin da ke biyo baya bayan an haihu. Kamar yadda nake faɗa muku ba fa a gane an haihu lafiya sai an sami kwana 40 da haihuwa. Wallahi mu muka san irin ƙididdigar da muke samu a ƙauyuka, garuruwa da birane.

    Lallai muna buƙatar ku  ringa zuwa asibiti haihuwa, saboda jijjiga, da zubar jinin da komai. Wallahi dole mu kau da tunanin babu da zancen talauci. Daga Sanda ka ga iyalinka da ciki ya kamata a tanadin da za ka fara ya zamto har da na kaita asibiti ta sami kulawar jami’an lafiya wajen haihuwa don girman Allah.

    Musamman jihohin Jigawa, Kano, Yobe, Maiduguri suna daga gaba-gaba cikin jihohin da ake rasa mata. Yanzu  an yi tsari a duk yadda mace ta saba haihuwa za a bar ta ta haihu a haka; walau a ruwa, a tsugune, a tsaye, a kwance ko a dire.

    Fatan wannan sakon ya shiga kunnuwan mu, musamman ku maza wannan matsalar daga ku ne, wani azzalumin yana da hali amma in an magana sai Yace za a jawo masa wahala ko kuma wani ma da niyya, amma ‘yan uwansa su hana, to ka sani iyalinka haƙƙin ka ne kuma kai Allah zai kama da laifi ba ‘yan uwanka ba. 

    Domin in ta mutu hidimar abincin da za ka yi da sauran ɗawainiya ai ka kashe ninkin kuɗin asibitin, wani dama ba ya gane Allah ya yi masa baiwa sai ran da ya rasa abinda yake ganin a da ba komai ba ne.

    In kana son matarka da gaske to mu gani a asibiti. Allah yasa mu dace.

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Sanya Contact Lenses Domin Ado Na Birgewa

    Sanya Contact Lenses Domin Ado Na Birgewa

    Muna cikin wani zamani da koyaushe sababbin abubuwa ƙara ɓullowa suke domin ƙayatar da jiki. Musamman mu mata. Contact lenses glass ne da ke da designing na kalolin ƙwayar ido daban-daban wanda ke tattare da jan hankali tare da maida mace so sexy. 

    Akwai kalar baƙi, ruwan toka, ja, blue da sauransu. Babbar matsalar shi ne yadda abin ya fantsama cikin kasuwanni har wasu ke sai da shi tamkar yadda za ka je ka sayi alewa me tsinke alhalin abu ne da a ƙa’ida ba a sa shi da ka, sai an je ga likitocin ido sun ba mutum shawarar wanda ya dace da shi bayan sun auna ƙarfin ganinsa.

    Sannan uwa uba wasu da ka suke amfani da shi. Ba kuma su san sharruɗan komai a kai ba. Wanda haƙiƙa amfani da wannan abu yana ba ƙwayoyin bacteria damar shigewa idon mutum 100% domin tamkar mayen ƙarfe haka yake a wajen ƙwayoyin cuta, wannan ta sa yana jawo ciwon idanu, hawan jinin idanu, apolo, gyambon idanu, da makanta baki ɗaya sakamakon irin waɗancan kura-kurai.

    Don haka abinda nake so mu sani duk da ƙila bai yawaita ba to idan ma za ki ko za ka yi, tunda har Maza ma na sa wa ku sani:

    1.Wajibi ne ya zamto bisa umarnin likitan idanu.

    1. Ba a bacci da shi.
    1. Duk wanda aka sa sau ɗaya ko minti 30 ya yi ba a kuma mai da shi.
    1. Ba a alwala da shi a ido
    1. Ba a wanka ko shower da shi.
    1. Ba a shiga swimming pool da shi.
    1. Ba a wanke fuska da shi.
    1. Ba a yadda a sayo a kasuwa ba domin ba ka san da me aka yi irin wannan ba. 

    Wannan su ne matakan kiyayewa, in ba haka ba to fa akwai damar makancewa ɗari bisa ɗari a gareka. 

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Yadda Alamomin Ciwon Sanyi Yake

    Yadda Alamomin Ciwon Sanyi Yake

    Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin ciwon sanyi, kamar haka;

    • Ƙurajen gaba
    • Ƙaiƙayin gaba
    • Fitar da farin ruwa mai kauri
    • Jin zafi idan za a sadu
    • Jin zafi idan za a yi fitsari
    • Ɗaukewar sha’awa
    • Kunburin mara ko ciwon mara
    • Ƙanƙancewar azzakari ga namiji
    Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin ciwon sanyi. Duk da yake fitar da farin ruwa a gaba yana daga cikin babbar alamar ciwon sanyi, amma shi kansa farin ruwa ba kowanne yake da matsala ba. Akwai mara matsala. Shi kansa farin ruwan da yake fita ya kai kala huɗu, ga su kamar haka;
    • Akwai mai fita fari tas, kamar koko mai kauri mara yauƙi ko kamar madara;
    • Akwai mai fita kamar gasara ko kuma in ce kamar kitse, wata ma sai ta sa hannu a ciki tana zaro shi;
    • Kuma akwai mai fitowa kamar zare a rinƙa zaro shi kamar zare, da ya taɓa jiki sai ya bushe;
    • Sannan akwai mai fita kamar majina mai haske mai ƙyalli mai yauƙi.
    Duk a cikinsu guda uku na ciwo ne wanda ba a sonsu a jikin mace. Wanda ake so shi ne mai fitar kamar majina, mai yauƙi, wannan shi ne ruwan ni’ima. Idan mace ta rasa shi a jikinta to akwai matsala. Samuwar ɗaya daga cikin ukun nan a jikin mace yakan hana wannan zuwa, daga nan sai ka ga mace ta shiga cikin damuwa. Domin karanta cikakken bayani akan Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi danna nan Domin karanta cikakken bayani akan Maganin Damuwa danna nan Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Hanyar Korar Aljanu Da Kariya Daga Dawowar Su

    Hanyar Korar Aljanu Da Kariya Daga Dawowar Su

    Kamar yadda muka sani aljani wata halitta ce da Allah ya yi ta ya kuma ɓoye ta ba za mu ganta ba; amma ita Allah ya hore mata za ta ganmu. Kamar yadda Allah (Subhanahu Wata’ala) ya faɗa a cikin Alƙur’ani mai girma a suratul A’araf aya ta ashirin da takwas (28).

    Sannan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace aljanu sukan shiga jikinmu kamar yadda jini ke gudana a cikin jikinmu; da haka muke sanin cewa aljanu suna ma da haƙuri dan sun fi mu haƙuri. Don da mu ke ganinsu, su ba sa ganinmu, kuma mu shiga cikin jikinsu kamar yadda Allah ya hore musu su shiga cikin namu, da mun cutar da su fiye da yadda suke cutar da mu. Da haka ne za ka gane lallai aljanu suna da haƙuri fiye da mu mutane. Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Nau’ikan Aljanu Suke danna koren rubutun nan. Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Za A Gane Matsalolin Aljanu Tare Da Magance Su danna koren rubutun nan. Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu
  • Dalilan Wajabcin Azumin Ramadan

    Dalilan Wajabcin Azumin Ramadan

    Allah Maɗaukakin Sarki, ya wajabta Azumin Ramadana; a inda ya ce, “Ya ku waɗanda suka yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga waɗanda suka gabace ku, wala-alla kwa sami taƙawa”. 

    Sanannen hadisin nan wanda Imam Muslim ya fitar cikin littafinsa, daga Umar Bin Khaɗɗab (Radiyallahu Anhu), da kuma hadisin da aka yi tarayya wajen fitarwa tsakanin Imamul Bukhari da Muslim daga Abu Abdulrahman Abdullahi Bn Umar Bn Khaɗɗab (Radiyallahu Anhu) duk sun bayyana wajibcin yin azumin watan Ramadana. 

    SHARUƊAN WAJABCIN AZUMIN WATAN RAMADAN. 

    Azumin watan Ramadan yana sauka a kan wasu, sakamakon waɗansu dalilai da shari’a ta aminta da su, shi ya sa wajen ci gaba da ayar da ta gabata, malamai suka bayyana ire-iren waɗannan mutane, tare da dalilan. 

    Domin karanta bayani a kan Falalar Kuka Ranar Ashura Danna nan 

    Ci gaba da bayani, sai Allah ya ce; “Waɗansu kwanaki ne ababan ƙidayawa. To wanda ya kasance mara lafiya a cikinku, ko a kan wata tafiya, to (idan ya sha ruwa) sai ya rama a waɗansu kwanakin na daban, har ma waɗanda za su iya yin azumin, su ba da fansa ta ciyar da abinci ga miskini guda ɗaya, to dukkan wanda ya ƙara (a kan abincin miskini), to wannan ya ƙara wa kansa alheri”.

    “ Amma ku riƙa yin azumin shi ne ya fi alheri a gare ku, in har kun kasance kuna sani. Watan Ramadan shi ne wanda aka sauƙar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane, kuma ayoyi bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa tsakanin ƙarya da gaskiya’ 

    “ Don haka dukkan wanda ya halarci watan cikin ku, to ya azumce shi. Kuma wanda ya kasance marar lafiya, ko a kan tafiya, (to idan ya sha ruwa) sai ya rama a waɗansu kwanaki na daban. Allah yana nufin sauƙi a gare ku, kuma ba ya nufin tsanani a gare ku” 

    “ Don haka ku cika adadin (kwanakin Ramadan), kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da ya yi, kuma ku zamo masu godiya gare Shi. Kuma idan bayi Na suka tambaye Ka game da ni, to Ni kusa nake (da su), ina amsa kiran mai kira, da zarar ya kiraye Ni” 

    “To su nemi amsawa ta, kuma su yi imani da Ni, domin su shiryu. An halatta muku saduwa da matayenku a daren watan Azumi, su sutura ne gare ku, ku ma suturu ne gare su. Allah ya san ku kun kasance kuna ha’intar kawunanku, sai ya dawo da ku, kuma ya yi muku afuwa|” 

    Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

    “To a yanzu ɗin ku sadu da su (da daddare), kuma ku nemi abin da Allah ya rubuta muku, kuma ku ci, kuma ku sha har farin zare ya bayyana daga baƙin zare na alfijir, sannan ku cika azumi zuwa dare, kuma kar ku sadu da su alhali kuna i’itikafi a masallaci. Waɗannan iyakoki ne na Allah, kada ku kusance su! Kamar haka ne Allah yake bayyana ayoyinSa ga mutane, don su zamo masu taƙawa” (Baƙara: 184 – 187)”.

    Waɗannan ayoyi a dunƙule sun yi bayanin waɗanda shari’a ta dauƙe musu azumin watan Ramadan; sakamakon wasu dalilai da karɓaɓɓu ne a Shari’a da sharaɗin bayan waraka daga waɗannan al’amura, sawa’un rashin lafiyar da za ta hana yin azumin ne, ko mace mai shayarwa ko juna biyu (kamar yadda wasu malamai irin su Ibn Taimiyya da almajiransa, Auza’i, Hasanul Basri da Ibrahimul Nakha’i suka tafi a kan su ma marasa lafiya ne), ko matafiya ne, to za su rama waɗannan azumi da suka sha bayan kwanakin azumin, ma’ana bayan Ramadan. 

    Sannan a cikinsu akwai bayanin waɗanda za su ciyar da miskinai abinci sakamakon rashin lafiya, ko tsufa da mai ciki ko shayarwa bisa fatawar Abdullahi Ibn Umar, Abdullahi Ibn Abbas da Ishaq Ibn Rahawaihi, kamar yadda Sheikh Nasiruddeen Albani ya fitar a cikin littafinsa Irwa’ Alghalil 4/18 – 24). 

    Shahid dai, waɗannan ayoyi ƙunshe suke da cikakkun bayanai game da wajabcin azumin Ramadana, da kuma nuni a kan waɗanda azumin ya wajaba a kansu, misali dukkanin musulmi, baligi, mai hankali, kuma wanda yake da ikon yi, mazaunin gida. 

    Sannan an bayyana matakan da aka bi wajen shar’anta shi, da kuma waɗanda azumin ya zama wajibi a kansu. Domin neman cikakken bayani, sai a tuntuɓi malamai a majalisunsu domin jin yadda abin yake. 

    A gefe guda kuma, akwai waɗanda azumin Ramadana ya sauka a kan su, ma’ana su azumin Ramadana bai wajaba a kan su ba. Cikin irin waɗannan akwai:

    i. Kafiri. 

    ii. Yaro, amma za a iya umartarsa da yin azumin domin ya saba. 

    iii. Mahaukaci, wannan kuwa ko da balagagge ne, domin ba ya cikin hankalinsa. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce “An ɗauke alƙalami a kan mutum uku: mai barci har sai ya farka, yaro har sai ya balaga, da mahaukaci har sai ya warke”. (Sahihul Jami’ al-Saghir (3513). 

    Domin Karanta Cikakken Littafin Danna nan

    1. Tsoho, amma zai bayar da Mudun-Nabi guda biyu ko ya ciyar da miskini dafaffen abinci a madadin kowacce rana. 
    2. Mara lafiya, sai dai akwai ramuwa a kansa bayan ya warke, wannan kuwa ko da bayan shekara nawa ne. Amma cutar da ƙwararrun likitoci suka tabbatar ba za a warke ba, sai dai kawai a ciyar a madadin kowacce rana. 
    3. Matafiyi, zai yi ramako bayan Ramadana.

    vii. Mai jini haila ko jinin biƙi, amma ita ma akwai ramuwa a kanta. 

    viii. Mace mai ciki ko shayarwa, ita ma za ta iya ajiye azumi idan tana tsoron cutuwarta ko cutuwar abin dake cikinta, ko abin da take shayarwa idan ta ci gaba da azumin. 

    An rawaito hadisi daga Anas Ibn Malik Al-Ka’abi (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Haƙiƙa Allah ya ɗauke wa matafiyi rabin sallah, kuma ya ɗauke azumi ga matafiyi da mai ciki da mai shayarwa”. (Sunan Ibn Majah, (1667). 

    A nan malamai suka yi bayanin cewa, idan matuƙar dai matafiyi da mara lafiya za su rama azumi, to babu abin da zai sa a ce mai ciki ba za ta rama ba. 

    Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

    TSAYUWAR WATAN RAMADAN. 

    Azumin Ramadana yana tsayuwa ne da ganin jinjirin watan Ramadana, wato ba a amfani da ƙirge na kalanda ko lissafin taurari ba, a a Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya alaƙanta yin azumin ne da ganin watan na Ramadana. 

    Hadisi ya tabbata daga Abu Hurairata (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Ku yi azumi domin ganinsa (wato Ramadan), kuma ku sha ruwa domin ganinsa (wato Shawwal). Idan watan ya faku a gare ku (ba ku gan shi ba), to ku cika Sha’aban kwana talatin”. (Sahihul Bukhari (1909), Sahihuul Muslim (1081). 

    Wani abu muhimmi shi ne, ba sai kowa ya ga watan Ramadan ba sannan ya ɗauki azumi, ana iyar ɗaukar azumi ko da mutum ɗaya ne ya ga watan. Domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Umar (Radiyallahu Anhu) cewa, “Mutane sun yi ƙoƙarin ganin jinjirin wata, sai na gaya wa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewar ni na ga wata, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ɗauki azumi, kuma Ya umarci al’umma da su ɗauka”. 

    (Sunan Abu Dawud, 2342. Hakim, 423, da Ibn Hibban 3438). 

    FAƊAKARWA: Son zuciya da jahilci kan hana wasu tashi da Azumi da hujjar cewa shugabanni ba adalai ba ne, alhali Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba da dama a bi su hatta sallah, ballantana azumi. Bisa haka, idan adali ya shaida ya ga wata, kuma shugaba ya aminta da ganinsa, to wajibi ne a tashi da azumi.

    Dangane da sauƙe azumin kuwa, sai mutane biyu sun shaida cewar sun ga watan Shawwal, sannan a ajiye kamar yadda aka rawaito daga Abdulrahman Ibn Zaid Ibn Khaɗɗab yayin da ya yi wa mutane huɗuba a ranar shakku (wato ranar da ake kokwanton ko Ramadan ne ko ba Ramadan ba ne.

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

  • Yadda ake haɗa Kufta

    Yadda ake haɗa Kufta

    KAYAN HAƊI 

    • Niƙaƙƙen nama 
    • Abin ɗanɗano 
    • Tafarnuwa 
    • Shammar 
    • Masoro 

    Yadda za a haɗ

    Za a niƙa nama dai-dai yadda ake so, sai a sa masa abin ɗanɗano daidai gwargwado, a sa shammar, tafarnuwa,da masoro, sai a haɗa da mai kaɗan a cakuɗa, ya haɗa jikinsa a shafa a faranti . Sai a riƙa cirar naman ana dundunƙulawa, dogo-dogo sai a soya a ruwan mai me zafi.

    Domin karanta yadda ake Fish – Cakes Danna nan 

    Miyar da suke ci da Ita. 

    Za a iya yi masa miya a ci da ita, a sami markaɗe na tumatur mai yawa, tattasai kaɗan, sai ki zuba a tukunya, ki sa masa ƴar kanwa, ki sa mai, a sa masa tafarnuwa (dakakkiya), a sa abin ɗanɗano, a bar ta ta yi kauri kamar faten doya sai a sa naman a ciki, ya yi minti 1 ko 2 , sai a sauke za a iya ci da dogon biredi.

    Domin karanta cikekken littafin Girke Girke  Danna nan