Tag: yadda ake

  • Dabarun Noman Zamani

    Dabarun Noman Zamani

    Noma babbar sana’a ce a ƙasar Hausa (Madauci, Isa da Daura, 1968). Ana ma kallon cewa, ita ce sana’ar da ta fi kowace sana’a muhimmanci, wacce idan babu ita, rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwu ba (Yakasai,1989). Sana’a ce da kowane gida ake yin ta, musamman a karkara. Sana’a ce da ta girmi kowace irin sana’a a ƙasar Hausa, da ma duniya baki ɗaya, saboda wannan dalilin ne ma ya sa, masu iya magana suke yi wa sana’ar noma kirari da “Na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya taras“, ko kuma “Bawan damina, attajirin rani”.

    Asalin wannan sana’a yana komawa ne ga tun farkon samun halitta a doron wannan duniyar. Wato ke nan, ana iya cewa, tun saukowar Adamu da Hauwa cikin duniya (Durumin Iya, 2006). Noma zamani shi ne noman da ake yi da kayan zamani, don haɓɓaka bunƙasuwar kayan abinci gami da samun riba mai yawa.

    Hanyoyin bunƙasa noma

    Akwai hanyoyi da dama, wanda manoma za su bunƙasa harkar noma a ƙasar Hausa kamar su;

    1. Iri (Shuka).

    2. Maganin feshin ciyawa.

    3. Bayar da tazara tsakanin shuka zuwa shuka (ƙafa ɗaya ko 25 cm).

    4. Maganin feshin ƙwari.

    5. Kayan aiki na zamani kamar injin huɗa, injin shuka da sauransu.

    6. Hanyoyin samar da takin gargajiya mai inganci.

    7. Halartar taron ƙarawa juna sani (workshop ko seminar).

    8. Haɗin gwuiwar kanfanoni da manoma.

    9. Canza abin da aka shuka a gona lokaci zuwa lokaci.

    10. Karɓan sabbin dabarun noma daga masana.

    11. Tuntuɓar malaman gona akai-akai, don inganta harkar noma.

    Don karanta yadda ake noman wake danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

     

  • Sunayen Annabi Muhammad (S.A.W)

    Sunayen Annabi Muhammad (S.A.W)

    Annabi Muhammad (S.A.W) yana da wasu sunaye har guda ɗari biyu da ɗaya (kamar yadda mai dala’ilu ya kawo su), sannan kuma wasu malamai sun ce sun kai dubu uku, saboda dalilai da halaye ne suka iya sa a kira mutum da sunaye da yawa. Ga sunayen nan kamar haka:

    1. Muhammad

    2. Ahmad

    3. Hamid

    4. Mahmud

    5. Ahid

    6. Wahid

    7. Mahi

    8. Hashirun

    9. Aƙibun

    10 Ɗaha

    11. Mansur

    12. Ɗahirun

    13. Muɗaihirun

    14. Ɗayyabun

    15. Sayyadun

    16 Rasulun

    17. Nabiyun

    18 Rasulur Rahmati

    19. Ƙayyimun

    20. Jami’un

    21 Muƙtafi

    22. Muƙaffa

    23. Rasulul malahimi

    24. Rasulur rahati

    25.  Kamilun

    26. Ikililun

    27.  Mudassirun

    28.  Muzammilun

    29.  Abdullahi

    30.  Habibullah

    31.  Safiyyullah

    32. Najiyullah

    33.  Kalimullah

    34.  Katimul Anbiya

    35. Khatimur Ruslu

    36.  Muhyi

    37.  Munji

    38. Muzakkirun

    39. Nasirun

    40. Yaasin

    41. Nabiyyur rahmati

    42. Nabiyun taubati

    43. Harisun alaikun

    44. Mu’alumun

    45. Shahidun

    4. Shahirun

    47. Shaahidun

    49. Mashhudun

    50. Bashirun

    51. Nazirun

    52. Munzirun

    53. Nurun

    54. Sirajun

    55. Misbahun

    56. Hudah

    57. Mahdiyyun

    58. Munirun

    59. Ɗa’in

    60. Mad’uwun

    61. Mujibu

    62. Mujabun

    63. Hafiyyun

    64. Afuwan

    65.Waliyyun

    66. Haƙƙun

    67. Ƙawiyyun

    68. Aminu

    69. Ma’amunun

    70.Karimun

    71.Mukarramun

    72. Makinun

    73. Matinun

    74. Mubinun

    75. Mu’ammalun

    76. Zu-ƙuwatin

    77. Zu-hurmatin

    78. Zu-izzin

    79.Zu-fadlin

    80. Muɗa’un

    81. Muɗi’un

    82. Ƙadamus-sidqin

    83. Rahmatun

    84. Bushra

    85. Gausun

    86. Gaisun

    87. Giyasun

    88. Hadiyatullah

    89. Urwatu wusƙa

    90. Siraɗallahi

    91. Siraɗun Mustaƙim

    92. Zikirullahi

    93. Saifullahi

    94. Hizbullahi

    95. Najimus saƙib

    96. Musɗafa

    97. Mujtaba

    98. Muntaƙa

    99. Ummiyun

    100. Muktarun

    101. Ajirun

    102. Jabbarun

    103. Abul-ƙasim

    104. Siraɗul mustaƙeem

    105. Kanzullah

    106. Zikirullah

    107. Mushaffa’un

    108. Shafi’un

    109. Salihun

    110. Muslihun

    111. Muhaiminun

    112. Sadiƙun

    113. Musadduƙun

    114. Sidƙun

    115. Sayyadul Mursalina

    116. Imamul Muttaƙin

    117. Ƙa’idul Gurril Muhajjalin

    118. Kalilur Rahman

    119. Barrun

    120. Mubarrun

    121. Wajihun

    123. Nasihun

    124. Na’sihun

    125. Wakilun

    126. Mutawakkilun

    127. Kafi

    128. Shafi’u

    129. Muƙimus Sunnati

    130. Muƙaddasun

    131.  Ruhul ƙudusi

    132. Ruhul Haƙƙi

    133.:Ruhul ƙisɗi

    134. Kaafi

    135. Muƙtafi

    136. Baligun

    137. Muballigun

    138. Shafi

    139. Wasilun

    140. Mausulun

    141. Sabiƙun

    142. Sa’iƙun

    143. Hadi

    144. Muhdi

    145. Muƙaddamun

    146. Azizun

    146. Fadilun

    147. Mufaddalun

    148. Fatihun

    149. Miftahun

    150. Miftahur Rahmati

    Domin Karanta Haihuwar manzon Allah SAW danna nan

    151. Miftahul Jannati

    152. Alamul Imani

    153. Dalilul Khairati

    154. Musahhihul Hasanati

    155. Muƙilul Asarati

    156. Safahu Anil-zallati

    157. Sahibus Shafa’ati

    158. Sahibul Maƙami

    159. Sahibul ƙadami

    160. Makhsusu Bil Izzu

    161. Makhsusu Bil Majdi

    162. Makhsusu Bish Sharafi

    163. Sahibul Wasilati

    164. Sahibus Saifi

    165. Sahibul Fadilati

    166. Sahibul Izari

    167. Sahibul Hujjati

    168. Sahibul Sulɗani

    169. Sahibur Rida’i

    170. Sahibud Darajati Rafi’ati

    171. Sahibut Taaji

    172. Sahibul Migfar

    173. Sahibul Liwa’i

    174. Sahibul Mi’iraji

    175. Sahibul ƙadibi

    176. Sahibul Buraƙ

    177. Sahibul Alamati

    178. Sahibul Khattimi

    179. Sahibul Burhani

    180. Sahibul Bayani

    181. Fasihul Lisani

    182. Ra’ufun

    183. Rahimun

    184. Azinul Khairi

    185. Sahibul Islami

    186. Sayyadil Kaunaini

    187. Ainun na’imi

    188. Ainul Gurri

    189. Sa’adullahi

    190Sa’adul Khalƙi

    191. Khaɗibul Umami

    192. Kashiful kurabi

    193. Rafi’ur ratbi

    194. Izzul arabi

    195. Sahibul bayan

    196. Sahibul faraji

    197. Sahibul alami

    198. Zu-mukanatin.

    199.Zu-izzin.

    200.Fadhilun.

    201.Mufaddhilun.

    Don karanta yanayin duniya kafin aiko da Manzon Allah SAW danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu

  • Dalilan Da Ke Sa Kaurin Bangon Mahaifa Da Hanyoyin Magance Su

    Dalilan Da Ke Sa Kaurin Bangon Mahaifa Da Hanyoyin Magance Su

    Endometrial hyperplasia yanayi ne wanda yake faruwa ga mace ta hanyar sanya bangon mahaifarta (endometrium) ya yi kauri fiye da kima. Abinda yake haddasa shi shi ne yawan hayayyafar ƙwayoyin halittar bangon mahaifa (overgrowth of endometrial lining cells). Endometrial hyperplasia ba cutar cancer ba ne. Amma wani lokacin idan ya yi tsanani, kuma ba a ɗauki matakin magance shi ba, zai iya rikiɗewa ya zamo cancer.

    Babban abinda yake haddasa endometrial hyperplasia shi ne rashin daidaiton zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin mace (estrogen and progesterone imbalance). Waɗannan sinadaran su ne suke sarrafa yanayin zubar jinin al’ada da kuma girma ko kaurin bangon mahaifa. Ma’ana, abubuwan da suke haddasa endometrial hyperplasia su ne:

    1. Rashin daidaito tsakanin sinadaran estrogen da progesterone (imbalance of estrogen and progesterone): idan sinadarin estrogen ya fi sinadarin progesterone yawa a jikin mace, to, hakan zai sanya cells ɗin bangon mahaifarta su yi ta hayayyafa fiye da kima. Daga nan sai bangon mahaifar ya yi kauri sosai, kuma a sami matsalar endometrial hyperplasia. Abubuwan da suke sanya rashin daidaiton zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone ɗin su ne ƙibar jiki (obesity), kamuwa da cutar polycystic ovarian syndrome – PCOS, ko kuma ɗora mace akan magunguna masu haɓaka zubar ruwan sinadarai a cikin jikinta domin wata matsalar rashin lafiya da ta yi fama da ita.
    2. Gabatowar ɗaukewar al’ada (menopause): macen da ɗaukewar al’adarta ya gabato, za ta iya samun sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinta. Hakan zai iya haifar da zubar sinadarin estrogen fiye da progesterone.
    3. Matsalar rashin saka ƙwan haihuwa na lokaci mai tsawo (chronic anovulation): idan wani dalili ya sanya mace ba ta saka ƙwan haihuwa kuma ta daɗe a cikin wannan yanayin, to, za ta samu ƙarancin sinadarin progesterone a jikinta. Ma’ana ba ta da progesterone amma tana da estrogen. Hakan zai sanya cells ɗin bangon mahaifarta su yi ta hayayyafa fiye da kima kuma su sanya bangon mahaifar ya yi kauri.
    4. Teɓa ko ƙiba (obesity): kamar yadda na faɗa a sama, ƙibar jiki ga mace tana da alaƙa da hauhawar sinadarin estrogen, wanda shi kuma zai iya haifar da endometrial hyperplasia. Da wannan ne muke ganin beken matan da suke haukacewa wajen ganin cewa sun yi ƙibar karfi-da-yaji ta hanyar shaye-shayen magunguna.

    Idan mace ta sami matsalar endometrial hyperplasia, to, matakan da za a iya ɗauka domin magance shi sun danganta ne da tsananinsa (severity) da kuma wanzuwar cancer cells a cikinsa (atypical cells). Saboda haka, za a iya magance endometrial hyperplasia ta hanyoyi kamar haka:

    1. Ɗora mace akan magungunan haɓaka zubar ruwan sinadarin progesterone a jikinta (progesterone therapy): tunda bayanan da suka gabata sun tabbatar da cewa samuwar sinadarin estrogen fiye da progesterone ne yake haddasa endometrial hyperplasia, to, za a iya ɗora mace akan maganin progestin mai haɓaka progesterone. An fi yin amfani da magungunan progestin ne idan endometrial hyperplasia ɗin ba a ga cancer cells a cikinsa ba (non-atypical hyperplasia).
    1. Yin tiyatar yayyanke tsiron bangon mahaifar (dilation and curettage – D&C procedure): ita ma wannan hanyar ana yin amfani da ita idan ba a ga cancer cells a cikinsa ba.
    1. Cire mahaifa gaba-ɗaya (hysterectomy): wannan hanyar ana yin amfani da ita ne ga macen da ta wuce shekarun haihuwa, sa’annan kuma aka ga akwai cancer cells a cikin endometrial hyperplasia ɗin. Likita yana bayar da shawarar yin wannan tiyatar ne domin mace ta kauce ma hatsarin kamuwa da cutar cancer ta mahaifa (uterine cancer).
    1. Canza tsarin rayuwa (lifestyle changes): idan endometrial hyperplasia bai yi tsanani ba, to, mace za ta iya magance shi ta hanyar canza tsarin rayuwarta. Ma’ana ta ɗauki matakin rage ƙiba ta hanyar daina ci da shan duk abubuwan da suke haddasa ƙiba, tare da yin ayyukan motsa jiki (physical exercises).
    1. Zuwa asibiti akai-akai domin a duba lafiyarta (regular medical check ups): yin wannan zai taimaka ƙwarai wajen gane cewa endometrial hyperplasia ɗin zai zamo mai hatsari ga lafiyarta ko kuwa a a.

        Domin karanta bayani akan sankarar bakin mahaifa danna nan

    Edita: Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)

    Haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)

    Shugabanmu Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) shi manzon Allah ne, zuwa ga mutane baki ɗaya, cikamakin Annabawa, shugaban Manzonnin Allah ne.

    1. Ya zo da addinin musulunci, wanda Allah ba ya karɓa (amsa) wanin addininsa ranar lahira.

    2. Yana daga cikin dangin ƙuraishawa, mafificiyar ƙabila, a cikin Makkah abar girmamawa.

    3. Dangantakarsa tana haɗuwa da Annabi Isma’il ɗan Annabi Ibrahim (Alaihis-salam).

    Sharihi; Annabi: shi ne wanda Allah (Subhanahu wata’ala) ya umarce shi da ya aikata wasu ayyuka akan kansa kuma wanda ya  kuɓuta daga dukkanin wani  aibu, sannan ɗa ne ba bawa ba, kuma namiji ba mace ba, lafiyayye ba mara lafiya ba. Sannan adadin Annabawa an samu saɓani; amma ruwaya mafi shahara ita ce, dubu dari da ashirin da hudu (124,000).

    Sai adadin sahabban annabi su guda dubu ɗari da ashirin da huɗu (124,000). Haka ma adadin taurarin da ke sama guda dubu ɗari da ashirin da huɗu (124,000) da adadin gashin da ake jinkin mutum guda dubu ɗari da ashirin da huɗu (124,00) da adadin numfashin da mutum yake yi a kowa ce rana guda dubu ɗari da ashirin da huɗu (124,000) ko kuma dubu ɗari da  uku da ɗari shida da tamanin (103,680). Sai adadin lomar da SA na layya yake yi a kowace rana idan an bar shi .

    Mazon: Shi ne wanda ya cika dukkanin sharaɗai na Annabta, sai Allah (Subhanahu wata’ala)  ya zaɓe shi mayar da shi a matsayin ɗan aiken Sa (Mazon) ma’ana , wanda zai dinga ba shi saƙo zuwa ga wasu mutane, umarni ne ko hani ne ta hanyar mala’ika zuwa gare shi ko shi (Manzon Allah) wasu sun ce ɗari da uku da goma sha uku (103) ko ɗari uku da goma sha uku (313). Bugu da ƙari kuma, daga cikinsu Al-ƙur’ani mai girma ya faɗi sunayen annabawa guda ashirin da biyar (25) daga cikinsu kamar haka:-

    Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam)

    Annabi Dauwuda (Sallallahu alaihi wasallam)

    Annabi Ibrahim (Sallallahu alaihi wasallam)

    Annabi Zakriyya (Alaihis-salam)

    Annabi Musa (Alaihis-salam)

    Annabi Ayuba (Alaihis-salam)

    Annabi Nuhu (Alaihis-salam)

    Annabi Sulaiman (Alaihis-salam)

    Annabi Isah (Alaihis-salam)

    Annabi Zulƙifil (Alaihis-salam)

    Annabi Yusuf (Alaihis-salam)

    Annabi Haruna (Alaihis-salam)

    Annbi Yunus (Alaihis-salam)

    Annabi Isma’il (Alaihis-salam)

    Annabi Yaƙub (Alaihis-salam)

    Annbi Adamu (Alaihis-salam)

    Annbi Ishaƙ (Alaihis-salam )

    Annabi Alyasa’u (Alaihis-salam)

    Annabi Iliyasu (Alaihis-salam)

    Annabi Salihu (Alaihis-salam)

    Annabi Idris (Alaihis-salam)

    Annabi Shu’aibu (Alaihis-salam)

    Annbi Yahaya (Alaihis-salam)

    Annabi Hud (Alaihis-salam)

    Annabi Luɗ (Alaihis-salam)

    Sannan kuma daga cikin su ne Allah (Subhanahu wata’ala) ya fitar guda biyar (5) ba su lamba ta Manzanni a ruwaya mafi, amma akwai ruwaya da ta nuna cewa guda goma (10) kamar haka:-

    Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam)

    Annabi Yusuf (Alaihis-salam)

    Annabi Ibrahim (Alaihis-salam)

    Annabi Yunus (Alaihis-salam)

    Annabi Musa (Alaihis-salam)

    Annabi Ishaƙ (Alaihis-salam)

    Annabi Nuhu (Alaihis-salam)

    Annabi Isma’il (Alaihis-salam)

    Annabi Isah (Alaihis-salam)

    Annabi Yakubu (Alaihis-salam)

    Sannan kuma ruwaya wacce ta nuna cewa ulul-azmi guda biyar ne su ne kamar haka;

    Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam)

    Annabi Ibrahim (Alaihis-salam)

    Annabi Nuhu (Alaihis-salam)

    Annabi Musa (Alaihis-salam)

    Annabi Isah (Alaihis-salam)

    Sannan alama ta uku (3) Yace: Yana daga cikin dangin ƙuraishawa kuma cikin garin Makkah abar girmamawa’’. Saboda guda goma sha biyu (12) kamar: Banu-Adnan Banu-Hashim, Banu-Abdulmudamllab, Kuraishawa Banu-Sa’ad Banu-Zuhra, Banu Ka’abu, da dai sauransa amma duk cikin waɗannan ƙabilu.

    Babu kamar ƙuraishawa a cikin garin  makkah, sannan asalin sunan garin makkah shi ne Bakka saboda zuwan annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya koma Makkah kamar yadda Alƙur’ani ya yi mana bayani a cikin Suratul Ali-Imrana aya casa’in da biyar (95). Haka ma garin Madinah kafin zuwan Annabi suna garin Yasrib, Saboda zuwan annabi ne ta koma Madinah, kamar yadda Alƙur’ani mai girma ya yi mana bayani a cikin Suratul Ahzab aya ta goma sha biyu (12).

    Don karanta kakannin manzon Allah SAW danna nan

    Haka kuma, a lambar ta huɗu (4), Yana cewa Dangantakar sa tana haɗuwa da (Annabi) Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ne sai dai guda goma daga cikinsu. Sannan kuma a lamba ta uku yace “yana daga cikin dangin ƙuraishawa, a Makka abar girmamawa”. Saboda haka, Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yana daga cikin mutanan garin Makka bakuraishe ne, haka kuma a cikin garin Makka akwai manyan-manyan ƙabilu har guda goma sha biyu (12)  a cikin garin kamar haka;

    Banu-Adnan

    Banu-Hashim

    Banu-Abdulmuɗallib

    Banu-Sa’ad

    Ƙuraishawa

    Banu-Zuhra

    Banu-Ka’ab

    Banu-Fahra

    Banu-Galib

    Banu Mudrakata

    Banu-Tamim

    Banu-Nadhir

    Haka kuma haihuwar Annabi ne ya sa garin Makka ta koma Makka wanda da can sunan garin Bakka kamar yadda ya zo a cikin Alƙu’ani mai girma a cikin suratul Ali-Imran aya ta casa’in da biyar (95), sannan kuma garin Madina kafin haihuwar Annabi sunan garin Yasriba, saboda zuwan Annabi ne ya sa garin ya zama Madina kamar yadda ya zo a cikin suratul Ahzab aya ta goma sha biyu.

    Bugu da ƙari kuma, dukkanin Annabawa larabawa ne in banda guda huɗu  daga cikin su su ne: Annabi Hud da annabi Yunus da annabi Salihu. Haka kuma wata rayuwar an ce daga kan Annabi Isma’il (Alaihis-salam) zuwa Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) akwai mutane guda Ashirin (20).

    Haka ma daga kan Annabi Adamu (Alaihis-salam) zuwa Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) akwai mutane Talatin (30), amma saninsu da rashinsu babu abbin da zai ƙara mana, saboda kawai kissa ta Israliyat ko Banu-Isra’il.

    Domin Karanta halayen annabi Muhammad danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Uku

    Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Uku

    Yawancin cinikin Bayin da aka yi a wannan ƙarni na 16 ana ɗiban su ne ana kai su Satomi inda suke noman rake da sigari  tobacco taba kenan, sai kuma waɗanda ake kai su Elmina  ƙasar Ghana inda suke haƙo gwal, a wannan lokacin dai Bayin da aka dinga ɗiba wannan abin suka dinga yi abin bai kankama ba sosai, kuma a sauran shekaru da suka biyo baya.

    Abin ya yi tsamari dalili kuwa shi ne, na farko su Spain da Portugal sun kafa sansanin su wato Colonies ɗin su a Brazil da kuma wasu ƙasashe na ƙasar Amerika, wannan ya sa sun fara neman mutane da yawa don su je su yi wannan aikin noma saboda su mutanen ƙasar Brazil ba su da ƙarfi kamar mutanen Afrika a ɗauke su su yi aikin wahala, saboda haka  wannan ya sa cinikin ya bunƙasa ana ta ɗiban mutanen Afrika ta Yamma ana kai su. 

    Dalili na biyu kuma shi ne, su waɗannan Turawa masu cinikin bayi sun ta kawo kayayyakin su suna sayarwa da sarakuna na wannan ƙasashe, su kuma waɗannan sarakunan wannan dukiya da suka samu ta ƙara musu ƙarfi da kuma bindigogi da suka dinga sayar musu musamman da sarkin Dahome da Oba na Lagos da Oba na Benin da kuma Sarakunan Ifik na can kusa da Calabar.

    Suna ba wa mutane suna shiga suna ɗebo musu bayi  daga  sauran ƙasashe, wannan kayan yaƙi da Turawa suka kawo ya sake ragargaza mutanen Afrika, saboda ƙarfin da suka ba wa waɗannan sarakuna su kuma suna yin amfani da shi su na ɗebo mutane, inda har ta kai aka ɗebi mutum miliyan ashirin (20 million)  a wannan lokaci. 

    Waɗannan shekaru ƙarni na 17 da 18 da na 19 fiye da ƙarni na 16 inda  kawai mutum miliyan ɗaya ne (1million) aka ɗiba. Kuma su Turawan Ingila ba su shiga ba, to shigar Turawan Ingila ma shi kenan magana ta canja, saboda a wannan lokaci sun samu Amerika sun fara ɗiban mutane suna kai su Amerika suna yi mu su noma.

    Sai Ingila ta zo ta wuce ma Spain da Portugal a harkar sayen bayi, saboda ita ta samu Amerika kuma wannan ya taimaka ya ƙara ƙarfin Ingila, saboda cinikin bayi shi ne tabbatar Ingila da suka yi amfani da shi suka samu ƙarfi a Amerika suka samu dukiya har suka zo suka caccanja abubuwan suka samu sauyin arzikin masana’antu (Industrial Revolution).

    Kuma an ce daga Liverpool ma kawai bayin da aka ɗauka a shekara goma 1783-1793 sun kai dubu ɗari uku aka ɗiba daga gaɓarta. Dalilin cinikin bayi ma har ta zama cewa ta samu ɗaukaka a duniya, kuma su kansu Turawan nan su suka yi rubutu suka dinga ba da labarin yadda ake yin cinikayyar Bayin nan da yadda ake yi wa mutane azaba da sauran su.

    Har ma akwai wani Kaftin John Adams shi ma ya rubuta littafin sa mai suna Scaches taken 10…. Of Africa between 1786 and 1800, ya yi maganar irin abubuwan da ya gani a Lagos da cewa mutane an yi faɗa ko ana yaƙi, an ɗebo Bayi waɗanda suka yi faɗa an sossoke kawunan su a kan bishiya ga shi nan kana ganin kawunan mutane, kuma ga wasu irin ɓera su ma saboda mushen mutane da suke ci sun bunƙasa sun yi yawa.

    Ya ce wani lokacin ma idan Turawa sun zauna in dai ba ka ɗaga kaya ba za ka dinga ganin ɓerayen su na shigowa ta ƙarƙashin su. Akwai wani shi ma William Bossman shi ma ya rubuta littafi mai su na New and accurate description of the coast of Guinea aka buga shi a Landon a shekarar 1805.

    Inda yake faɗar yadda ake yi wa Bayin nan cewa a ƙirjin su ake yi musu lamba, kuma mata ba su fi kwata ko kashi ashirin tsadar namji ba yadda ake sayar da su, idan kuma aka shiga da su ruwan ma duk kwashe musu kayan su ake yi a tafi da su tsirara, kuma jirgin ya kan ɗauki mutum 600 zuwa 700. 

    Micheal Crowder ya yi lissafin irin mutanen da aka ɗiba daga nan Yammacin Afrika (West Afrika) da Angola ya ce, a ƙarni na 16 an ɗebi mutum miliyan 1, a ƙarni na 17 an ɗebi mutum miliyan 3, a ƙarni na 18 an ɗebi mutum miliyan 7. To yana maganar cewa a duk shekara a kan ɗauki mutum dubu ashirin da biyu daga ƙasar Najeriya, duk da yake cewa a ƙarni na 19 ma an hana cinikin Bayin, amma an ɗebi a ƙalla mutum miliyan 4. 

    A cikin irin bayanin da wani mai suna Rossel Warren Horray ya rubuta,  ya ba da labarin yadda ake cinikin Bayi da yadda cewa mutum ɗaya daga cikin mutum bakwai ko wane zai iya zama Bawa a cikin ‘yan Afrika saboda bala’i, kuma namiji ɗaya daga cikin ko wanne maza biyar zai iya zama, mace ɗaya daga cikin kowacce goma za ta iya zama Baiwa, saboda wannan masifar da aka yi ta cinikin Bayin nan.

    To cinikin Bayi ya kawo wa mutane rashin kwanciyar hankali da zaman lafiya, mutane ko yaushe su na cikin tashin hankali na cewa za a iya zuwa a kame ka a tafi da kai, wannan abu ya daɗe ya shiga ƙwaƙwalwar mutane an ragargaje su, gaba ɗaya aka rusa tunanin al’umma saboda harkar Bayin nan.

    Wani abu da ya faru a shekara ta 1835 inda wasu daga cikin Bayin da aka kai su Brazil suka yi tawaye, saboda sun samu wasu daga cikin su sun kasance mutanen da suka san Shehu Ɗanfodiyo ne da kuma Jihadin da ya yi, saboda haka wannan ya ba su ƙwarin gwiwa suka yi tawaye.

    Don haka mutanen Brazil suka koro su suka dawo da su Lagos, wasu daga cikin su musulmi suka zo suka kafa sansanin su na musulmi, wasu ma da ba musulmin ba suka biyo su da suka ga abin da musulmi suka yi. Wannan ya kawo canji a Lagos da samun abubuwa na ci gaba inda har suka yi Unguwar ‘yan Brazil (Brazillian quarters) a Lagos, har yanzu za ka ga cewa wasu daga cikin mutanen Lagos ɗin za ka ji sunayen su irin su Codoso, Perrara su Sanchez duk wannan sun same su ne a dangantaka da irin mutanen Brazil da suka zauna a can. 

    Haka kuma suka zo Lagos suka samu ɗaukaka suka shiga harkokin rayuwa da kasuwanci da harkokin ilimi har suka yi babban masallaci a Lagos, duk wannan su na daga cikin ɓurɓushin waɗanda suka taho daga Brazil da kuma samun wani abu na ci gaba a wannan lokaci. 

    Don karanta tarihin Afrika danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Lokacin Da Ya Dace Mace Ta Yi Amfani Da Dabarun Tazarar Haihuwa

    Lokacin Da Ya Dace Mace Ta Yi Amfani Da Dabarun Tazarar Haihuwa

    Mace zata iya fara yin amfani da magungunan tazarar haihuwa kafin ta fara yin al’adarta, ko lokacin da take yin al’adarta, ko bayan ta gama yin al’adarta. Tasirin magungunan wajen hanata daukar juna biyu, ya danganta ne da nau’in maganin. Amma magana ta gama-gari ita ce anfi bayarda shawarar fara yin amfani da magungunan a cikin kwanakin farkon fara yin al’adarta. Ga bayanin yadda rabe-raben yake:

    ƘWAYOYIN MAGANIN TAZARAR HAIHUWA MASU ƘUNSHE DA HAƊAKAR SINADARAN ESTROGEN DA PROGESTERONE (COMBINED ORAL CONTRACEPTIVE PILLS – COCs)

    Ƙwayoyin maganin tazarar haihuwa masu haɗuwar hormones kamar Microgynon, Yasmin, ko Nordette, suna daga cikin magungunan hana ɗaukar ciki waɗanda mata suka fi yin amfani da su. Waɗannan ƙwayoyin suna ɗauke da sinadaran estrogen da progestins. Idan mace ta fara shan waɗannan ƙwayoyi a cikin kwanaki biyar na farkon jinin al’adarta (rana ta ɗaya da fara jinin al’adarta), za ta sami kariya daga ɗaukar ciki nan-take.

    Wannan yana faruwa ne saboda sinadaran da suke cikin ƙwayoyin suna fara yin aiki nan-take wajen hana fitar ƙwan haihuwa (ovulation). Amma idan ta fara shan ƙwayoyin bayan kwanaki biyar da fara jinin al’adarta, to, riga-kafin ba zai yi aiki nan-take ba, kuma dole ne sai ta ƙara da yin amfani da wata hanyar kariya kamar kwaroron roba (condom) har tsawon kwanaki bakwai, domin ƙwayar maganin tana ɗaukar lokaci kafin ta fara aiki.

    ƘWAYOYIN MAGANIN TAZARAR HAIHUWA MASU ƘUNSHE DA SINADARIN PROGESTIN KAƊAI (MINI PILLS)

    Ƙwayoyin tazarar haihuwa masu progestin kaɗai, kamar Cerazette, Micronor, da Noriday, suna da bambancin fara yin aiki idan aka kwatanta su da ƙwayoyi masu haɗakar sinadaran estrogen da progestin, saboda progestin kawai suka ƙunsa. Idan mace ta fara shan waɗannan ƙwayoyi a ranar farko da ta fara jinin al’adarta, to, za ta sami kariya nan-take.

    Amma idan ta fara shan su bayan ‘yan kwanaki da fara al’adarta, to, dole ne ta yi amfani da ƙarin wata hanyar kariya idan za ta yi jima’i har sai bayan tsawon awoyi 48 (kwanaki biyu) don tabbatar da samun kariya daga ɗaukar juna biyu, saboda ƙwayoyin suna buƙatar lokaci kafin su fara yin tasirin hana mace samun juna biyu ta hanyar hana ta saka ƙwan haihuwa (ovulation) da kuma sanya kaurin bangon mahaifa.

    MAGUNGUNAN TAZARAR HAIHUWA NA NA’URA (HORMONAL INTRAUTERINE DEVICES – IUDs)

    IUDs waɗanda suke ƙunshe da sinadaran estrogen da progesterone, su ne kamar Mirena da Skyla. Wannan na’ura ce da ake sanyawa a cikin mahaifa don samar da kariya daga ɗaukar juna biyu na dogon lokaci, kamar shekaru uku zuwa biyar. Idan mace ta sanya IUD a lokacin da take yin jinin al’adarta, musamman a cikin kwanaki bakwai na farkon al’adar, za ta samu kariya daga ɗaukar ciki nan-take.

    Amma idan an sanya mata IUD a wani lokaci daban ba wannan ba, a zangon jinin al’adarta (menstrual cycle), dole ne sai ta yi amfani da wani ƙarin hanyar kariya kamar kwaroron riba (condom), har na tsawon kwanaki bakwai kafin na’urar ta fara aiki.

    ALLURAI NA TAZARAR HAIHUWA (CONTRACEPTIVE INJECTIONS)

    Allurai na tazarar haihuwa kamar Depo-Provera ko Sayana Press wasu hanyoyin tazarar haihuwa ne masu ƙunshe da sinadaran estrogen da progesterone da ake bayarwa ga mace a duk bayan watanni uku. Idan aka yi wa mace allurar a cikin kwanaki biyar na farkon zangon jinin al’adarta (menstrual cycle), to, za ta sami kariya daga ɗaukar juna biyu nan-take. Amma idan aka yi mata allurar a wani lokaci na daban, to, dole ne sai ta yi amfani da wata hanyar samun kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai domin allurar ta fara aiki.

    DAN-MAƘALE NA TAZARAR HAIHUWA (CONTRACEPTIVE PATCH)

    Ɗan-maƙale, wato faski, na hana ɗaukar ciki, kamar Ortho Evra ko Xulane, wani ƙaramin abu ne da ake manna shi a fatar jiki wanda yake sakin sinadaran estrogen da progesterone zuwa cikin jiki. Idan mace ta manna wannan faski, a rana ta farko na jinin al’adarta, za ta sami kariya nan-take. Amma idan ta manna faski bayan jinin al’adarta ya yi kwanaki da farawa, to, dole ne sai ta yi amfani da wata hanyar kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai kafin faski ɗin ya fara aiki da kyau.

    Don karanta dalilan da ke kawo rashin haihuwa danna nan

    ZOBEN FARJI (VAGINAL RING)

    NuvaRing wani sassauƙan zobe ne da ake sakawa  mace a cikin farjinta don sakin sinadaran estrogen da progesterone a cikinsa. Idan mace ta saka zoben nan a rana ta farko na jinin al’adarta, to, za ta sami kariya nan-take daga ɗaukar ciki. Amma idan ta saka shi a wani lokaci daban a cikin zangon jinin al’adarta, to, dole ne sai ta yi amfani da wata hanyar kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai kafin zoben ya fara aiki da kyau.

    ASHANAR HANNU (CONTRACEPTIVE IMPLANT)

    Ashanar hannu, kamar Nexplanon, dabarar tazarar haihuwa ce, mai kama da ƙaramar sanda wacce ake saka ta a ƙarƙashin fatar hannun mace ta sama. Tana sakin sinadarin progestin ne domin hana ɗaukar ciki na tsawon shekaru 3 ko fiye. Tana hana saka ƙwan haihuwa, kaurara majinar bakin  mahaifa don hana ‘ya’yan maniyyi shiga, sa’annan tana ƙara kaurin bangon mahaifa don hana ƙyanƙyasasshen ƙwan haihuwa maƙalewa a jikin bangon mahaifa.

    Idan aka saka ashanar hannu a cikin kwanaki biyar na farkon jinin al’ada (Rana ta 1 ita ce ranar da jinin al’ada ya fara), tana bada kariya nan-take daga ɗaukar ciki. Idan kuwa aka saka ta bayan kwanaki biyar da fara al’adar, to, dole ne sai mace ta yi amfani da wata hanyar kariya, kamar kwaroron roba, na tsawon kwanaki bakwai, har sai allurar ta fara aiki sosai.

    ME YA SA LOKACIN FARA AMFANI DA MAGUNGUNAN YAKE DA MUHIMMANCI?

    Lokacin da ake fara amfani da magungunan tazarar haihuwa yana da matuƙar muhimmanci don samun cikakkiyar kariya nan-take daga ɗaukar ciki. Fara amfani da su a lokacin ko bayan mace ta fara yin jinin al’adarta yana taimakawa wajen daidaita tsarin jikin mace na halitta, yana rage haɗarin fara amfani da su yayin da ba a san tana ɗauke da ciki ba, kuma yana bayar da kariya da wuri. Idan an fara amfani da su bayan jinin al’adarta, yawanci za a buƙaci yin amfani da wata kariya (na kwanaki bakwai) don jikinta ya daidaita da hormones.

    Domin karanta bayani akan ciwon ciki da mara lokacin al’ada danna nan

     Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu   

  • Matsalolin Mace-Macen Aure

    Matsalolin Mace-Macen Aure

    Wannan muƙalar za ta yi duba ne akan matsalolin auratayya, saboda idan mutum ya yi duba na tsanaki sosai akan sha’anin aure, zai ga ana ta samun mace-macen aure a wannan yanayin da muke ciki. Saboda haka, aure shi ne jigo na rayuwar mutum, sannan aure shi ne yake samar da nutsuwa da kwanciyar hankali a tsakanin mutane, shi ne abin da yake  ƙulla alaƙa mai ɗorewa a tsakanin mutane.

    GABATARWA

    Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah (Subhanahu wata’ala), wanda ya yi sama da ƙasa ba tare da an yi musu tokara ba, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugabanmu annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam).

    Bayan haka, abubuwan da suke kawo matsaloli akan mace-macen aure suna da alaƙa da sauka daga kan tafarkin tsarin addinin musulunci da kuma abubuwan da al’adar mu take kai, wanda addininmu ya amince mana da sauran su.

    MUTUWAR AURE 

    Bismillah rahmanin rahim, akwai abubuwa da yawa, waɗanda suke kawo akan mutuwar aure a tsakanin ma’aurata da yawa kamar su, auran ƙarya, aikin gwamnati, rashin iya girki, rashin iya kwanciya, auran dole, rashin iya kulawa, rashin iya gina alaƙar soyayya, rashin iya kalaman soyayyya, rashin iya kwalliya da tsafta, rashin wasa da juna, rashin shawara ga juna, sai wasu cututtuka wanda suke faru a tsakanin ma’aurata, wasa da abokan miji, wasa da ƙannan miji da buri kamar yadda ya zo a cikin littafi na biyar (Kambun Ma’aurata 5). Haka kuma, a cikin litttafi mun kawo ƙarin wasu daga ciki, kamar haka:-

    1. Auran ƙarya:  Yana kawo mutuwar aure, saboda gina aure akan ƙarya da facaka da dukiya, sannan da nuna mata mutum ɗan wajan wani ne ko nuna mata motoci har da gidaje masu alfarma, bugu da ƙari ma har da ‘yan uwa masu alfarma. Sannan da yi mata hidima ta kece alfarma, ta kayayyaki ko anko na bukukuwa na alfarma, musamman a watan ramadan da sallar idin ƙaramar sallah da babbar sallah ko yawan turo mata kati a waya da dai sauransu.

    2. Aikin gwamnati:– yana ɗaya daga cikin abin da ke kawo mutuwar aure ga wasu mazajan, saboda yana iya samun rashin iya kulawa da fahimtar junansu, sannan ana iya mu’amala da wasu mazajan a wajen aiki har ma da wasa da dariya har da goya ta a motarsa ko mashin ɗinsa wanda haka yana kawo zargi a tsakanin ma’aurata da dai sauransu.

    3. Rashin iya girki:- rashin iya abinci yana ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo rabuwar aure, saboda yana ɗaya daga cikin abubuwan da maza suka fi so a wajen matayensu, domin macen da ta iya abinci daban take a wajan mijinta, saboda haka ya zama tilas ga wacce take so ta mallake mijinta ta iya girki, girkin ma ta yi da hannunta, saboda idan girki ya yi zai yaba mata sosai sannan  za su yi so da shaƙuwar junansu.

    4. Auren dole:- auren dole yana kawo rabuwar aure da raba kan al’umma ta kowanne irin hali, saboda an gina auran ne akan dole, ba a a kan soyayya ba. Saboda wata alfarma da yake da ita a wajen iyayenta ko ‘yan uwanta. Haka kuma ‘ya’yaye yana da matuƙar kyau sosai idan sun samu kan su a cikin hali, kada su yi gaggawar rabuwa, su fahimci dalilan da yasa aka yi musu wannan aure, saboda idan ma sun bi zaɓin zuciyar su, to su iya haɗuwa da waɗansu matsaloli na rayuwa, saboda kaucewa umarnin iyayensu.

    5. Rashin iya kulawa:- rashin iya kulawa da suna yana  iya kawo mutuwar aure, saboda wasu mata suna barin mazajensu a wulaƙance ko maza su ma suna barin matarsu a wulaƙance, yin hakan bai dace ba ga addinin musulunci, saboda haka barin mace ko miji babu wata kulawa mai kyau yana kawo mutuwar aure, musammamma a karkara, za ka ga miji ya bar matarsa da wankau har da sirfau don ta nemi abin da za ta sa a baka da rana. Saboda shi mijinta abin da wai  ya sani a kansa shi ne ciyarwan safe da yamma, yin hakan bai dace ga musulmi ba sannan bidi’a ce kai tsaye. Ya Allah ka ba mu yadda za mu yi mu sahayar da matayanmu har da ‘ya’yanmu.

    6. Rashin iya gina aure a kan soyayya:- yana kawo mutuwar aure, saboda duk abin da aka gina shi akan soyayya komai daren daɗewa yana nan, misali kalli uwa da ‘yarta, kalli mahaifi da ‘ya’yansa, saboda duk irin yanayin da ma’aurata suka tsinci kansu a ciki za su iya haƙuri da junansu  su zauna lafiya komai tsanani ko talauci ba za su iya rabuwa ba, ya Allah ka haɗa mu da masu so da ƙaunar mu don Allah, ameen summa ameen.

    7. Rashin iya kalamai na soyayya:- rashin iya kalamai masu tafiyar da zukatan mijinki shi ma yana iya kawo rabuwar aure, saboda rashin magana mai daɗi, amma fa ku lura idan sun je siyan sarƙa da awarwaro da kayan kwalliya iri-iri, za ka gan su suna raunar da muryarsu, haka ma ida za su yi magana da abokannan miji ko ƙannan miji, a cikin sassanyar murya za ka ji su suna yi.

    Amma wata macen idan za ta kira ka ko magana da mijinta sai ka ji tana cewa, Salman, Salman, Salman, ko Farisi, Farisi, Farisi, babu wasu kalamai masu daɗin sauraro kamar su , “ya angona, ya mijina, ya maigidana , ya abin taƙamata, ya shugabana, ya yayana, ya dalin-ɗina, ya jinin jikina, ya rayuwata, ya ranka shi dade, ya honarable, ya honi je, ya habibina, ya sahibina, ya hasken rayuwata, ya abban ameer, ya jigon rayuwata, ya annurin zuciyata, ya farin cikin rayuwata, my dear, ya abban ameerah, ya abin alfaharina, ya abban dadi, ya baban Salman ko Salma ko Yasir da dai sauransu.

     Mene ne so?

    So wata tsoka ce ko jijiya ce a cikin zuciya, wanda Allah yake halittar bayinsa ko ɗan Adam da ita, don haka so wata ƙaramar tsoka ce, wadda kowane ɗan-Adam yake da ita, sa’annnan shi so ba a ganinsa, saboda sirri ne wanda Allah ya ɓoye a zuciyar kowane mutum, sai dai kawai alamoninsa ne za ka iya ganewa da zarar wani ko wata ta kamu da son wani. Saboda haka, shi so daga ƙarami yake farawa sai ya cigaba da girma da faɗaɗa, saboda yawan tunanin abin da kake so ko kike so.

    Saboda haka, a lokacin da mutun ya shiga cikin soyayyar abokinsa, sai kuma ya kasance suna ƙaunar juna, to idan hakan ta faru, so ya haɗu a nan, sannan sai su fahimci abubuwan da ke dauwamar da ƙauna guda goma sha biyu (12) kamar su:-

    a. Tausayawa juna: Idan wani abu ya samu ɗayansu na musiba da dai sauransu, sai a nuna damuwa akan haka.

    b. Kulawa da juna: Kamar yadda muka yi bayaninsa a darasin da ya wuce.

    c. Yarda da juna: Yana ga samari da ‘yan mata har da ma’aurata, su yarda da junansu, ma’ana su fahimci abin da kowannansu zai iya aikatawa saboda mahassada.

    d. Amincewa juna: Yana ga samari da yan mata har da ma’aurata su amincewa junansu, saboda zargi yana iya kawo matsala a tsakanin masoya.

    e. Fahimtar juna: Ya zama wajibi akan masoya su fahimci junansu, saboda munafikai ko magulmata.

    f. Haƙuri da juna: Yin haƙuri da juna, idan wani ya yi laifi, sai a danne a zuciya, yana ƙara ƙauna a cikin zukatan masoya mai ɗorewa.

    g. Kau da kai da juna: Kau da kai ga juna, yana ƙara soyayya a cikin zukatan masoya, saboda yawan zargi ko sa ido yana kawo rashin fahimtar juna.

    h. Kyauta: Yawan yin kyauta, yana ƙara danƙon soyayya da ƙauna a cikin zukatan masoya.

    i. Shawara da juna: Yawan shawara ga juna, yana kawo shaƙuwa da juna.

    j. Danne zuciya: Kamar haƙuri ne, idan wani ya yi laifi ko ya ɓata muku rai ko fushi, sai a danne abin a cikin zuciya, ka yi kamar ba ka damu ba.

    k. Rangwame ga juna: Yin afuwa ko uzuri, yana ƙara so da soyayya mai danƙo.

    9. Kwalliya da tsafta: Suna ɗaya daga cikin abubuwan dake dauwamar da ƙauna, saboda ita tsafta ko kwalliya tana fito da ɗan Adam. Sannan ya zama dole a kansu, su guji baza sirrinsu da ɗaukar  jita-jita har da zargin junansu. Sannan su guji zargi a cikin soyayyarsu, bugu da ƙari ma su lura da maƙiyansu har da mahassadansu da dai sauransu.

    10. Rashin iya kwalliya da tsafta: Na iya kawo rabuwar ma’aurata, saboda ita tsafta cikon addinin musulunci ce, sannan ku san su ne abin da mai gida yake lura da shi ga matarsa har ma ‘yan uwansa. Saboda haka, ya zama wajibi akan matan aure su iya kwalliya da tsafta, saboda Allah (subhanahu wata’ala) yana san masu tsarki, ma’ana masu tsafta.

    Har ila yau, kada matan aure su zauna  ba tare da tsafta ba, musamman a dai-dai lokacin da miji yake dawowa gida, wata mace za ka ji hammatarta tana wari har da jikinta baki ɗaya, saboda ta bar hammatarta da gashi ba ta cisgewa (ko askewa), wata ma ɗakinta za ka ji yana wari kamar mai sayar da daddawa ko wacce ɓera ya mutu a cikin ɗakinta.

    11. Rashin wasa da juna: Shi ma yana iya kawo rabuwar ma’aurata, saboda rashin zolaya da juna yana iya kawo rashin shaƙuwa da juna, babu laifi wata rana mai gida zai iya shan kwalliyarsa mai kyau ya fesa turaransa mai kamshi, ya fito bakin ƙofar ɗakin matarsa ya tsaya ya aika ko ya yi sallama ya kira ta, idan ta tambaya wane ne? Sai ya ce, “da ita honije ɗinki ne ke kira, bayan ta fito, sai ku tayin zantukanku na soyayya. Sannan babu laifi ku yi tseran gudu har da langa, amma idan babu kowa a gidan, sai ku kaɗai da dai sauransu.

    12. Rashin shawara da juna: Yana iya kawo mutuwar aure, saboda yin wani abu ba tare da shawara ba, yana iya kawo saɓanin fahimta a tsakanin ma’aurata.

    13. Rashin iya magana: Yana raba aure, saboda wata macen idan mijinta ya yi mata magana, sai ka ji tana cewa gani ko mene ne, wata ma macen idan mijinta yai kiranta tana ji sai ta yi shiru. Saboda haka, dole ne akan ma’aurata su iya kalaman da za su samar da nishaɗi, kamar su “idanuwana sun kasa rufewa, saboda rashin ganinka ko jin muryarka ya angona na wasu ɗan lokuta, kunnuwa sun kasa toshewa, saboda maraicin jin lallausar sautin muryarka na wasu ɗan lokuta, bacci ya ƙauracewa idanuwana, saboda rashin kallon fuskarka ya sahibina, a yanzu haka, babu komai a cikin zuciyata sai tunanin ganinka ya jigon rayuwata” haka shi ma mijinta zai yi mata, idan yana so ya ƙara samun so da shaƙuwa a wajan matarsa, kusha shagalin ku lafiya.

    14. Rashin iya ado: Yana iya kawo rabuwar aure ko kishiya, saboda haka da zarar mijinta ya fita waje ya ga wata santaleliyar zugegiyar yarinya, sai ya ji yana sha’awar auranta, saboda ita kwalliya ko ado tana ƙarawa mutane kyau sosai.

    Saboda duk mutanen da ka gani duk ma’abota kyau ne, sai dai rashin ado ya gusar da kyawunsu, ka duba ka gani ranar sallar idi ƙarama da babbar salla yaya? Saboda haka, ya zama wajibi akan ma’aurata su iya kwalliya da neman magunguna da za su iya gyara jikinsu, don neman ƙarin bayani ko magani za a iya nemana, Allah yasa mu dace.

    15. Rashin iya tafiya: Tana iya kawo matsalar aure ga wasu mazan, saboda wasu mazan tafiyar mace suke fara kalla, da zarar matarsa ba ta iya tafiya ba, sai ya ji ta fara fita daga zuciyarsa, da zarar ya fita waje ya samu macen da ta iya tafiya ya aura. Saboda haka, mace ta iya tafiya sosai kamar yadda mu yi bayani a babin mallakar miji.

    Haka kuma, lallai yana da matuƙar kyau sosai akan ma’aurata, su yi hattara sosai,saboda su sani fa shi aure ana gina shi akan ibada, domin samun dacewa a wajen Allah ranar lahira.

    Har ila yau, duk wanda ya yi aure, sai ya yi haƙuri sosai a cikin rayuwarsu da matar sa, saboda sai ya samu wajen shekara ashirin ko kuma sama da haka, sa’annan zai fara jin daɗin zaman aurar su da ita.

    Saboda daga kan shekara ɗaya zuwa huɗu(1-4), za su kwashi soyayyar su ne ,saboda babu wani nauyi sosai akan su mai yawa(`ya`ya), haka kuma daga kuma shekara huɗu zuwa takwas(4-8), wata rana zai iya samu cikin gidan kaca-kaca, idan ya yi mata magana akan haka, sai ta yi haƙuri ta gyara ko da ko abin ya ɓata mata rai.

    Har ila yau, daga kan shekara takwas zuwa goma sha biyu (8-12) idan matar sa ta yi masa wani abu mara kyau ko kuma ya samu cikin gidan kaca-kaca, sai ya tambaye ta meye dalilin da yasa ta bar gidan kaca-kaca, to a wannan lokaci za ta iya mayar masa da saƙo kamar haka” toh! ka ba ni kuɗn da za’a siyo sabulun da za’a wanken kayan ne”?

    Sa’annan kuma, daga kan shekara goma sha biyu zuwa goma sha shida(12-16), a wannan lokacin sun tara ‘ya’ya da yawa, haka kuma ba su da wani lokaci da za su zauna su yi wa kan su kwalliya, domin su ji daɗin tattaunawarsu, saboda neman abin da yaran su za su ci haɗi da abin da za a dafa musu har izuwa shekara ashirin da biyar da bakwai, to a wannan lokacin ne suke damar jin daɗin auran su, saboda ‘ya’yan su girma, sa’annan kuma matar sa ta kusa daina haihuwa.

    Akwai abubuwa da dama, waɗanda su ke kawo mutuwar aure da yawa wanda In Sha Allah a littafin mun na uku za mu ji bayanin su da yardar Allah.

    Don karanta fa’idojin da suke cikin yin aure danna nan

    Domin karanta fa’idojin wadatar zuci danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Hakimin Kudan Marigayi Alhaji Ishaƙ Muhd Ashir Kudan

    Tarihin Hakimin Kudan Marigayi Alhaji Ishaƙ Muhd Ashir Kudan

    An haifi mai girma Ishaƙ Muhammad Ashiru a garin Kudan a ranar 15/03/1944, shi ne ɗa na farko ga sarkin Kudan Muhammad Ashiru, Alhaji Ishaƙ ya yi makarantar allo tun yana ƙarami a garin Kudan. Tun yana ƙarami ne kuma aka kai shi makarantar elementare a shekara ta 1954-1958.

    Da ya gama ya wuce babbar makarantar firamare da ke Giwa a shekara ta 1958-1960. Daga nan sai ya zarce kwalejin gwamnati ta fasaha da ke Kano (Govt Tech Training School Kano) a 1964-1967. Ya wuce Kwalejin Horon Sojojin sama da ke Ingila (School of Tech Training Royal Airforce Newto England) a 1970. A inda ya samu takardar shaidar Diploma a kan gyaran injin jirgin sama.

    Bayan ya dawo gida, sai ya shiga aikin sojan sama, inda ya kai har W.O II (warrant officer II) a 1968. Ya yi ritaya a shekara ta 1977, bayan rasuwar mahaifin sa, Sarkin Kudan Ashiru. A shekara ta 1977, ya samu aikin ƙaramar hukumar Ikara. A shekara ta 1991 ya zama Sarkin Nassarawa, A shekara ta 2001 (30/06/2001) ya zama Sarkin Kudan a sakamakon zamowa Hakimi da ƙanin mahaifinsa Alhaji Haladu Yakubu ya yi, haka kuma Alhaji Ishaƙ Ashiru ya zama Hakimin Kudan Ciritawan Zazzau.

    Abubuwan ci gaba da aka samu a zamaninsa

    1. Shimfiɗa kwalta da ta ratsa garin Kudan gabas da yamma, kudu da arewa.

    2. Shimfiɗa kwalta daga Kudan zuwa Sundu.

    3. Kafa Asibitin ƙorama.

    4. Kafa makarantar firamare guda biyu a kudu da arewacin Kudan.

    5. Ƙarin fanfunan burtsatsai a garin Kudan.

    6. Ƙarin rumfunan kwano a kasuwar Kudan.

    7. Kafa barikin ‘yan Sanda.

    8. Kafa kamfanin buga bulo na farko.

    9. Kafa makaranta mai zaman kanta (Private School).

    Bugu da ƙari kuma, yana ɗaya daga cikin manya-manyan sarakunan Kudan waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya haɗi da kula da tarbiyar mutanan da yake shugabanta a lokacin sa. Sannan kuma yana sasanta ma’aurata haɗi da ba su shawara akan zamantakewar auratayya, sannan kuma mutum ne mara girman kai, saboda idan wani abu ya faru na addinin wanda mas’alar ta zo gaban sa, to yana ɗaukar wayar sa ya tuntuɓi masana na wannan ɓangaran, kamar yadda marigayi malam Surajo Yunusa Kudan ya shaida mana a lokacin da yake raye.

    “Mai girma hakimin Kudan yana kiran sa a waya idan wani abu ya taso na addinin domin neman fatawa”, bugu da ƙari kuma ni ma kai na shaida ne, saboda a shekarata 2014 akwai wata mas’ala da ta taso wanda wani ya auri wata mace watan su biyar dai-dai sai ta haihu. Wanda aka kawo wannan mas’alar gaban sa, kuma ya yi hukunci akan haka, ni kuma ina gefe ɗaya a zaune, sai ya tambaye ni akan hukuncin da ya yanke, yaya addini ya tsara, nan take na duba abinda na ga hakan ya yi daidai.

    Sannan sai ya yi wa mutanan wajen jawabi cewa “kada ku ga na tambayi wannan yaron wani abu akan wannan mas’alar, saboda akwai wani littafi ne wanda ya rubuta akan irin wannan mas’alar, ya kuma turawa mai martaba sarkin Zazzau Dr. Shehu Idris har ma ya ɗauki nauyin buga littafin”.

    Sanna kuma dukkanin wanda ya ga ya yi shigar banza ko kuma ya yi askin banza ko kuma ya zo ya wuce ta gabansa ba tare da ya yi musu sallama ba ko gaisuwa ba, sai ya kira shi ya yi masa faɗa akan haka.

    Sannan kuma a shekara ta dubu biyu da ɗaya ne (2001) aka naɗa shi a matsayin sarkin Kudan, bayan sarkin Haladu Yaƙubu ya tafi, wanda ya yi mulki na tsawon shekara ashirin da shida, wato daga 1975-2001, Sannan kuma a shekara ta 2008 ne a sake naɗa shi a matsayin Ciritawan Zazzau kuma Hakimin Kudan.

    Mai girma Ishaƙ Muhammad Ashir ya samar da ci gaba a garin Kudan sosai tare da nuna ƙaunarsa ga mutanan garin, saboda haka tun daga rasuwar Mahaifin sa da kuma sarkin Kudan Haladu Yakubu da mutanan Kudan, mutanan Kudan suke raɗaɗin rabuwa da mai kishin su, har sai da Allah ya kawo musu mai girma Ishaƙ Muhammad Ashir, wanda ko yanzu mutum ya shiga garin zai tabbatar haka, wanda waɗan su suke ganin tunda aka mai da shi Ciritawan Zazzau kuma Hakimin Kudan, suka rasa sarkin mai kishin su haɗi da kula da al’amuran su tare da zama da su haɗi da zuwa gidan rasuwa ko suna.

    Mutanan garin Kudan ba su taɓa mantawa da irin alherin da mai girma Ishaƙ Muhammad Ashir ya yi musu ba, saboda an samu cigaba da yawa a garin, wanda furtawa a yanzu ƙauyanci ne, kawai mutum ya shiga garin zai gani ko kuma ya tambayi mutanan garin manyan zai ji ruwan amsoshi. Sannan kuma ya yi aure yana da mataye guda uku kamar haka;

    1. Halima

    2. Mariya

    3. Hindatu

    Sai kuma sunayen ‘ya’yan sa kamar haka;

    1. Usman (Ɗanladi).      10. Nafi’u

    2. Balarabe.                  11. Isma’il

    3. Mas’ud                     12. Gaddafi

    4. Nasiru                      13.   Imrana

    5. Abdulshahid             14. Umar

    6. Abubakar                 15. Yunusa

    7. Muzammil                16. Sha’awanatu

    8. Furaira(Hajiyayye)    17. Karimatu

    9. Aisha                       18. Shamsiyya

    10. Raliya                     19. Aliyu (Ɗan Asabe)

    (more…)

  • Fa’idojin Da Suke Cikin Yin Aure

    Fa’idojin Da Suke Cikin Yin Aure

    Fa’idojin da suke cikin aure ba za su ƙididdigu ba. Amma ga wasu kaɗan daga ciki  za mu lissafo kamar haka:- 

    1. Yin aure biyayya ne ga Umarnin Allah da Manzonsa. 
    2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) farin ciki a ranar  lahira. Yace : “Ku yi aure ku hayayyafa. Domin ni zan yi ma sauran al’ummomi  alfahari da ku a ranar Alkiyama”. 
    3. Ta dalilin aure za a samu wanda zai fito ya furta kalmar Shahada!! “la ilaha illal  lahu Muhammadur rasulullahi”
    4. Ta dalilin aure ne za ka samu zuriyar da za su yi maka addu’a bayan rasuwarka.  Wannan yana daga cikin ayyukan da ladansu ba zai yanke ba har abada. 
    5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun mutum daga kale-kallen haramun,  sannan ya kare masa al’aurarsa daga zina. 
    6. Ta dalilin aure ne za ka samu damar taimaka ma ‘yar uwarka musulma, ka aure ta, ku kiyaye kan ku daga zina. 
    7. Ta dalilin aure ne za ka samu cikar addininka, da ninkawar ladanka fiye da wanda  ba su da aure. 
    8. Ta dalilin aure ne za ka samu ladan ciyar da matarka, da ɗaukar nauyinta, da ladan  samar mata da mazaunin da za ta rayu.
    9. Ta dalilin aure ne za ka samu damar ƙara yawan musulman duniya ta hanyar  haihuwar da za ka samu. 
    10. Ta dalilin aure ne za ka samu damar karkatar da himmarka daga kan neman biyan  buƙatarka ta hanyar haram izuwa ga hanyar halal. Da kuma samun ladan saduwa da  iyalanka. 
    11. Za ka samu lada mai girma sosai idan har Allah ya azurtaka da ‘ya’ya mata guda  biyu, kuma ka yi haƙuri da su ka kyautata musu, ka kyautata tarbiyyarsu, su za su  zama garkuwarka daga shiga wuta. 
    12. Idan har ‘ya’yanka guda biyu suka rasu, kuma ka yi hakuri, to Allah zai shigar  da kai Aljanna saboda wannan. 
    13. Ta dalilin aure za ka samu karuwar mutuncinka da darajarka a cikin al’umma. Ka shiga sahun mutanen da za su iya jagorantar lamuran rayuwar al’umma.
    14. 14. Ta dalilin aure ne za ka samu taimakon Allah cikin lamarinka. Kamar yadda  Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: “Mutum Uku, hakki ne akan Allah ya  taimakesu. Wanda zai yi aure don nufin kame mutuncinsa da bawa wanda yake  neman ‘yancinsa saboda ya samu daidaituwa (A cikin Addini) da kuma Mujahidi  (mai yaƙin ɗaukaka addinin Allah)

    Danna nan domin karanta alamomin shigar so 3

    Domin karanta falalar yin aure danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Falalar Yin Aure

    Falalar Yin Aure

    Aure shi ne ginshinƙin rayuwar mutane haɗi da yaɗuwar jinsin mutane, sannan  kuma dukkanin mutanan da basa yin aure ko gari ko jiha ko ƙasa za ka same su da  raunin tunani da hankali haɗi da rashin sanin ingantacciyar rayuwa. Aure yana da falaloli  masu girma ga waɗanda suka yi shi a matsayin sunnar ma’aiki (Sallallahu alaihi  wasallam) kuma suka kiyaye dokokin shi, ga kadan daga cikin su: 

    Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) ya ce “Wanda ya yi aure, haƙiƙa ya  kammala rabin addininsa, to ya ji tsoron Allah a sauran rabin” Wato ibadar  da aka halicce ka don ka yi ta, idan ka yi aure, Allah SWT ya ba ka rabin ta kyauta.

    Mu’azu bn Jabalin (R.A)wani Sahabin Manzo (Sallallahu alaihi wasallam)  yace; “Sallar mai aure ta fi sallar marar aure sau arba’in”. Wato sai marar  aure ya yi sallah sau arba’in sannan za ya yi daidai da sallar mai aure guda ɗaya.

    Ibn Abbas (R.A) sahabin Annabi SAW, yace; “Ku yi aure, domin kwana guda  da aure shi ne mafi alheri daga ibadar shekara dubu”. Waɗannan hadisan  akwai su cikin Buguyatul Muslimina. Waɗanda ba su da aure, su yi ƙoƙari su yi  aure kafin duniyar ta tashi.

    Bukhari da Muslim su fitar da hadisi daga Ibn Mas’ud (R.A) ya ce: Manzon  Allah s.a.w ya ce “Ya ku taron samari! Duk wanda ya sami iko daga cikinku;  to ya yi aure, domin shi ya fi taimakawa wajen rintse gani, kuma shi ya fi  taimakawa wajen kare farji. Wanda bai sami iko ba, to ya yi Azumi, domin  Azumi garkuwa ne”.

    Muslim ya fitar da wani hadisin daban daga Abu-Huraira (R.A) ya ce: Manzo  s.a.w ya ce “Idan ɗayanku ya ga wani abin da ya burge shi a jikin wata mace,  to ya koma zuwa ga iyalinsa, yin hakan zai mayar da abin da ke ransa na  sha’awa”. Waɗannan hadisai biyu sun nuna zahirin falalar da ke cikin aure da  kuma amfaninsa. Babbar falalar da ke cikin aure ita ce kare mutum daga  faɗawa cikin saɓon Allah ta hanyar kallon haramun ko aikata laifin zina.  Haka nan yana daga falalar yin aure akwai lada da Allah zai bai wa ma’aurata  a duk lokacin da suka biya buƙatarsu ta saduwa.

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) yana faɗa a cikin wani hadisi  cewa “A cikin tsokar ɗayarku (wato, saduwa) akwai ladan sadaka”, sai wani  Sahabi ya ce “Yanzu ɗayanmu ya biya sha’awarsa, sannan ya samu lada” sai  Manzon Allah s.a.w ya ce “Shin idan ya sanya ta a haramun zai samu zunubi? (wato idan ya yi zina)? Sai ya ce “Ƙwarai!” Sai Manzon Allah s.a.w “To haka  idan ya sanya ta a halal zai samu lada”.

    Na daga cikin falalar yin aure; samun ladan ciyarwa, Manzon Allah  (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce “Ciyarwar ɗayanku ga iyalinsa ladan  sadaka ne”. To kun ga waɗannan falaloli ba wanda zai samu sai wanda ya yi  aure. Don haka na ke jan hankali samari da ‘yan mata da a zage damtse wajen  yin aure domin riskar waɗannan falaloli.

    Ubangiji ka bai wa gwauraye cikin maza da mata damar yin aure. Ya kuma  sanya albarka cikin aurarrakin da aka yi da waɗanda za a yi. Ya Allah ka sa mu auri masu taƙawa da kwantar mana da hankali a duk lokacin da  muke cikin wani hali sannan su zamto hanyar shigarmu aljanna ameen. 

    Don karanta alamomin  shigar so danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu