Tag: yadda ake

  • Ni’imar Da Allah Ya Yi Wa Mutane Ba Tare Da Sun Fahimta Ba

    Ni’imar Da Allah Ya Yi Wa Mutane Ba Tare Da Sun Fahimta Ba

    Akwai takaici ka ga mutum koyaushe abinda ya rasa shi ya fi damunsa, da shi yake ƙorafi a rayuwa. Ba nazari, babu tunani akan me Allah ya ba shi. Shin ko kun san yayin wankin ƙoɗa (hemodialysis) manya-manyan kawunan allura ne masu zafin gaske da sanya hawaye ƙwaya biyu ake turawa mutum a jijiyar jininsa, wani ma saboda rashin kyawun jijiyoyin sai dai a saita masa a jijiyar jinin wuyansa kai tsaye. 

    Wannan wankin yana ɗaukar awoyi 4 ana yi mutum na kwance ba tare da ya motsa ba (immobilized) kafin a kammala, kuma mutum na buƙatar a maimaita hakan sau uku “3” dukkan satin duniya. Adadin sau goma sha biyu ’12’ a wata.

    Ga wahala, ga shi duk yi ana buƙatar sai wani ya ba ka gudummawar jini, ga zaman jira, wasu tun safe amma saboda layi da sarƙaƙiyar kayan aikin sai biyun dare za su bar asibiti zuwa gida, kuma a haka jibi za su dawo. Ga yawan mantuwa da zazzaɓi, kasala, tashin zuciya, ciwon kai da sauran side effects saboda chemical ɗin tace jinin.

    A ƙayyade dukkan wanki sai mutum ya biya kuɗin da suka kai dubu ashirin zuwa talatin N20,000 – N30,000. Wanda tunda sau uku ake a sati, wani ma sau huɗu za a yi, kuma huɗun shi ne ideal wanda jimilla zai kama dubu tamanin zuwa ɗari da ashirin duk satin duniya N80,000 – N120, 000.

    A wata zai kama dubu ɗari uku da arba’in zuwa dubu ɗari hudu N340,000 – N400,000. Ko yaushe sai ka shafe awa 4 a kwance ba ka motsi har a gama, adadin awa 48 a wata ba tare da motsi ba, kuma zagaye ne ɗaya. 

    AMMA ga kai wanda Allah ya yi masa baiwar lafiya, ya horewa ƙoda me lafiya kullum sai Allah ya wanke maka ita sau 36 free of charge, ba ka biya kowa ko sisi ba. Wanda in biya za ka yi dubu talatin sau 36 sai ka biya MILIYAN ƊAYA DA DUBU tamanin – N1,080,000 kullum na abinda Allah ke yi maka a wankin ƙoda kurum banda sauran ni’imomi.

    Amma don ka tashi ka ji ka lafiya sharr kai ta wulaƙanci da rashin mutunci, kana jin kai wata tsiya ne, ko kuwa don ba ka da ko sisi kana ganin kamar Allah bai ƙaunarka… Kai bayin Allah yaushe za mu hankalta ne? 

    Wannan tasa nake bamu shawarar yin check up, kana iya shekara 5 da ciwon ƙoda a hankali bai bayyana ba sai ta gama rikicewa baki ɗaya sannan ka fara jin alamomi, shi yasa ɗazu nace mu daure a je a yi awo ko da sau 1 ko 2 a shekara.

    Wallahi duk gatanka ka kiyayi wannan ciwon domin sai an gaji da kai, masu ba ka jini ma in za ai wankin wataran sai an rasa, komi yawan danginka, balle a ce ba ka da kirki dama. Dama a duniya ba abu me ƙaranci irin jini, duk mutum 10 za ka samu 9 a ciki ba wai ya wadace su ba ne.

    Kuma ba za a taɓa yi maka dashen ƙoda kai tsaye ba komai gatanka, dole sai ka biyo ta dialysis har ta jikinka ta ƙarasa lalacewa tukunna, domin inba haka ba ko an sa maka wata ba zama za tai ba. 

    A rage son kuɗi a dinga check up. In ka yi wasa za ka ga wasa. Mu cigaba da godewa Allah a kodayaushe.

    Danna nan don Karanta amfanin shan ruwa da safe kafin a ci komai

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Lokacin Sanyi

    Lokacin Sanyi

    Maganar gaskiya ana sanyi yau garin
    Tin a daren jiya na san yau za ai abin
    Iska ce kamar da rani ta game garin.

    Daga jin fil-fifil na iska sai tausayin
    Kaina Auwalan ya zo mini tin Ajiyan
    Dan na san abin da zai faru da ni kurin.

    Yo ɗakin da anka ba ni gida dukkanin
    Bango nai ina zaton sanyi nan yakan
    Zauna yai watanda kafin ya game garin.

    Ga tagarsa babu ƙofa sai labulan
    Da idan nai fishi aradu ina cinye ɗan
    Malafar uba da bai kare sanyi ko kaɗan.

    Ga ƙofarsa ba ta rufuwa gam wai dukan
    Wanda ya ce fa zai rufe ta rubuk sai idan
    Zai ƙarawa kansa caji na rabin galon.

    Da ma can samansa lau ne to da da ɗan
    sauƙi dan kwa na yi imani zai ragen
    Sanyi tinda ai rufi da silin ba sa barin.

    To fauƙas-samawatin ma tin jiyan
    Na ji ta fara ba ni saƙon kar nai jiran
    Sai wani ya yi min bayani kan nai iyon.

    Ga bargon da ke yi min hidima ya yi min
    Ƙanƙanta dan kwa ƙwabrina ko kaɗan
    Bai samun shiga cikin halara ko kaɗan.

    In na sanya kai ƙafata ita ke wajen
    In kwa na sa ƙafar fa to kaina sai ya zan
    Ya bullo ta ɓangaren titin shonekan.

    An ce ba ku jin dukan sanyi wai hakan?
    Tattabaru da ku nake magana kun yi jim!
    Ko dan na mu lokacin muma is kwamin.

    Allah ga su Abba Yusuf nan na biɗan
    Canjin rayuwa da Bargo Ɗanlibiyan
    Da idan na shige ciki bai mai takuran.

    Danna nan don karanta waƙar halin da muke ciki

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Biyar

    Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Biyar

    Cinikin Bayi a Afrika ya ɗauki salo daban-daban kamar yadda na yi bayani a baya babu abin da ya kassara Afrika kamar wannan, ta hanyoyi daban-daban har da canja wa mutane da kuma canja yanayin zamantakewa. To kowanne sashe na Afrika akwai irin nau’in bautar da ake yi ta inda mutane tsakaninsu ma ko kuma su da maƙotansu wasu su je su sato wasu.

    Duk wannan abu yana faruwa, kafin masu waɗannan su zo su waɗannan mutanen Portugal, da bayan ma sun zo waɗanda su suka kawo cinikayyar Bayi gadan-gadan da kuma su mutanen Ingila Dens da Dutch su ma suka zo suka shiga cikin wannan ciniki.

    A ɓangaren abinda ya kama daga Senegal har zuwa Port Sudan da kuma Yammacin Tsakiyar Sudan (Western Central Sudan) wanda yawancin su duk musulmai ne nan ma an yi cinikin Bayi kuma an bautar da mutane, an yi yaƙe -yaƙe a tsakanin juna, an sayar da mutane, kafin ma zuwan Turawan Portugal da bayan zuwan su.

    Saboda su waɗannan da suke wannan sashe na Afrika yawanci idan sun kama Bayin suna amfani da su a tsakanin su wasu kuma su kai su su sayar a tafi da su ta Sahara. Tunda akwai ƙasashe manya a wannan nahiya, kama tun daga kan Ghana, Mali, Songhai da Borno idan aka zo Sokoto ƙasashe ne masu ƙarfi kuma suna da dawakai suna amfani da su akan maƙwabtan su, wannan abu ya ɗauki salo iri-iri da hanyoyi daban-daban, kuma bayan zuwan su da kuma kafin jihadi da kuma bayan jihadin Shehu Ɗan Fodio.

    Tunda a cikin tarihi ma wasu daga cikin malamai sun ce ɗaya daga dalilin da yasa su Shehu Ɗan Fodio suka yi jihadi saboda ana ɗiban musulmi ana sayar da su Bayi, wannan abu ya tayarwa da malamai da sauran mutane hankali, kuma da aka yi Daular Sokoto an yi ƙoƙari a hana wannan, waɗanda kawai suka yarda a dinga siyarwa su ne waɗanda ba musulmai ba.

    Sun mayar da mutanen da suke ƙananan ƙabilu da suke a tsakiya su aka rinƙa farauta a na sayar da su, wannan abin ya jawo musu baƙin jini a wajen sauran mutane bayan zuwan Mishan, wanda Mishan sun yi amfani da wannan don su ƙarfafi ko su dasa ƙiyayya tsakanin musulmin Arewa da waɗanda ba musulmi ba, cewa dama can iyayen su, idan mutum ya karanta littattafan su zai ga duk irin waɗannan abubuwa da irin abin da suka nuna sai suka mayar da abin cewa, gaba ɗaya a wannan nahiya ba abin da aka yi sai dai kashe su da mayar da su Bayi.

    Wannan abu ya shiga zukatan waɗanda ba musulmi ba, wanda daga baya suka zo suka karɓi addinin kirista. Mun san irin waɗannan cewar wancan zamanin da yanzu ba ɗaya ba ne, to amma wannan abin ya yi tasiri gare su da mutanen su ya kuma cunkusa ƙiyayya daban-daban.

    A irin wannan yanayi na yadda ake kama Bayi a wannan nahiya ta Sudan, an yi rubuce rubuce daban-daban musamman Turawan da suka zo a da can kafin su yi mulkin mallaka, har da wanda ya ba da labarin irin abubuwan da suka faru a Borno, tunda babbar  ƙasa ce kuma suna da ƙarfi a lokacin da suke kai hari wurin irin waɗannan ƙananan ƙabilu, kuma in ba su bayar da kai ba za a ɗebo su da matan su da yaran su, manya-manyan mazan duk a karkashe su. Yara da mata a ɗebo su a sayar da su, waɗanda suke sha’awarsu su mayar da su ƙwarƙwarori ko su bayar da su duk wannann ya faru.

    Daga cikin irin waɗannan mutanen da suka ga abin da ya faru akwai Harith Barth, ya faɗi abin da ya gani da Borno ta kai hari Mandara wurin mil 300 daga ƙasar Borno (Kukawa) da irin abubuwan da suka faru aka dinga ɗebo mutanen. Duk wannan sun rubuta su kuma sun bayar da bayanai a kansu a irin wannan yanayi, mun ga shi ma kansa Luggard da sauran su abin da suke ta cewa su Turawan Ingila cewa su sun zo ne don su kawar da cinikin Bayi.

    Bayan an yi jihadin Shehu Ɗan Fodio an ci nasara waɗanda aka kama aka mayar da su Bayi, wasu a faɗace-faɗace inda wasu har ma an sayar da su an tafi da su wata ƙasa kamar irin su Nicolas wanda aka sayar da shi har ya kai Rasha, wanda Sir Nicolas ya yi Baptising ɗin sa daga nan ya tafi Spain bayan ya ‘yantar da shi, inda daga nan ya tafi America aka yi yaƙi da shi.

    Duk irin wannan ya sa a zagi Shehu Dan Fodio da cewa jihadi ne da irin wannan bautar ta sa aka kama shi ya tafi, duk mun san irin wannan idan ma ƙasashen an samu waɗanda suke son Shehun kuma suka yi amfani da wannan abin da aka yi na jihadi su ma suka tayar da rigima kamar Ab-bahiya a ƙasar Brazil. Wannan duk ya nuna mana irin yadda wannan ƙasa ta Afrika take da yanayin zamantakewa na rigingimu da faɗace-faɗace da abubuwan da suka jawo.

    A wannan nahiyar ƙasashen musulmi kenan wanda yawancin Bayin su suna sayar da su ne a Sahara wasu suna shiga Europe ɗin wasu suna shiga nan iyakar Magrib da Misra, yawancin irin waɗannan Bayin nan ake kai su, mun san cewa a irin bauta ta ƙasashen musulmi daban take da ta sauran ƙasashe tun da akwai ƙa’idoji na shari’a waɗanda aka gindaya ba za ka iya yi wa Bawanka ba da sauran su, kuma a can ƙasashen musulmi su na da tsarin cewa, mutum zai iya nemo ‘yancin sa.

    Duk da dai a nan nahiyar Sudan abin bai fiye tabbata ba, kuma da su kan su Bayi a nan waɗanda aka haife su a cikin bauta ba a sayar da su saboda sun musulunta sun zama Bayi na gida, wanda a hankali suna shiga gida har ma ya zama su mata a mayar da su ƙwarƙwarori, ko wasu da suke fara mulki suna samun ‘yanci su ma su zama wasu abu kamar yadda muke ganin Bayi a Fada. Wannan yana daga cikin abubuwan da suke faruwa a irin bautar ƙasashen musulmi da kuma nan ƙasar Sudan daban suke da sauran wurare.

    Ana ɗiban su su ma ana kai su can ƙasashen Larabawa, wasu su mutu a hanya, wasu kuma su tsira da wahala dai iri-iri. A irin ƙasashensu su ma ana samun bauta da kuma yaƙe-yaƙe a wurare irin su Upper Volta ɗin nan wanda aka ce ita ce ta zama Burkina Faso, wanda waɗannan ƙasashen ma yawanci ba ɓarin musulmi ba ne, har ma aka ga cewa a ƙididdigar da aka yi kashi 17 bisa ɗari na ƙasar gaba ɗaya an bautar da su, kafin Turawa su zo lokacin da aka hana waɗannan abubuwan.

    Kowacce nahiya da irin nata, saboda idan ka tafi can ɓangaren su Ethopia nan ma da take babbar ƙasa ce ta kirista su ma sun bautar da mutane wasu an kama su wasu kuma an sayar da su wasu an mayar da su Bayi. Akwai ƙasashen da suke na musulmi su ma suna ɗiban Bayi. Kiristocin Ethopia bayan da suke ɗiba ma suna bautar da su wasu, sun kashe wasu kuma su sayar da su tunda su ba tsarin su ɗaya da musulmi ba.

    Su ma musulmin da suke wannan nahiya ta Gabashin Afrika, Bayi ana tafiya da su can Gulf da kuma sauran ƙasashen Asia ma duk ana ɗiban ‘yan Afrika. Waɗannan abubuwa ne da suke dama kafin zuwan Portugees ɗin su fara wannan cinikayya tasu kuma har su canja yanayin yadda ma bautar da ɗiban zai kasance a wannan nahiya ta Afrika.

    Kamar yadda na faɗa su ma ƙasashen kurmi yadda suke ɗiban nasu Bayin ya sha bamban da irin namu na Savannah, saboda su ƙasashen kurmin nan yawancin su ba su da dauloli masu ƙarfi in banda irin su Benin da Oyo da France. Waɗannan manyan dauloli kuma da sauran waɗanda suke kusa da su da ‘yan Uyo su idan sun ɗiba sayar wa da Turawa suke, kuma a irin wannan wurare irin su Oyo Bayin ana yayyanka su a ba wa ababen bautar su, tunda duk sun yarda da sadaukarwa saɓanin irin  ƙasashen musulmi ko na kirista na gabashin Afrika inda ba a yanka mutum a sadaukar da shi da irin shirka da suka saba.

    Wannan yana daga cikin abubuwan da suka sha bamban da bautar musulmi da waɗanda ba musulmi ba, ta inda su musulmi idan sun ɗiba Sahara suke kaiwa su kuma waɗannan suna ɗiba ne su kai Atlantic. Duk wannan kafin zuwan Turawan Potugal waɗanda lokacin da suka zo kurmi suka yi da kuma inda yake suna da ruwa suka dinga ɗiba su da ƙabilun da suke a waɗannan wurare da mutane masu ƙarfi, amma duk kusan abin da ya faru shi ne, su waɗannan ƙasashe da na Arewacin Sudan da na Kudu na can bakin teku suna shigowa tsakiya ne suna ɗiban ƙananan ƙabilu su suke sayarwa.

    Saboda haka suka ragargaji wurin da ake cewa Middle Belt ba ma kaɗai a Nijeriya ba, inda ita kanta Middle Belt ɗin an canja mata suna kuma mun san cewa ita Nijeriya ita ta fi kowacce ƙasa yawa da yadda su waɗannan mutanen aka dinga ɗiba, waɗanda suke a bakin teku cikin ƙasa suka dinga shigowa shi yasa za ka ga yawanci su ƙabilar Igbo su aka fi yi wa wannan farmaki tunda su ne suke kusa da Ijo kuma ba su da ƙarfi ba su da tsarin gwamnati irin na waɗannan ƙasashe.

    Yawancin waɗanda aka fi kai wa farmaki ana ce musu Stateless ko kuma non-State, waɗanda ba su da tsarin hukuma irin na waɗannan ƙasashe su aka dinga ɗiba ana sayarwa a ko ina a Afrika, su suka shiga wannan tsari na ɗiban Bayi da rashin albarka na cutar da su tun ma dai kafin su Turawan Portugal ɗin su zo, tunda dama mutane suna faɗa a tsakanin su, wannan ya ɗebi wannan wancan ya ɗebi wannan, zuwan Turawa sai ya zama ya canja wannan abin gaba ɗaya yanda za mu gani su kuma wane irin tasiri abin su ya yi wa al’ummar Afrika.

    Danna nan don karanta cinkin bayi a tarihin Afrika kashi na huɗu

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Mata Ku Ba Ni Kunnenku

    Mata Ku Ba Ni Kunnenku

    A yayin da aka yunwatar da jiki wato ‘Starvation’ jikin a karan kansa yakan fara nemo hanyar da zai cigaba da bai wa mutum kuzari domin kar ya ya shiga mawuyacin hali, wanda daga cikin hanyar da yake bi shi ne narka kitsen da ke jikin mu wanda asalin sa sugar ne da aka samar daga rarar abinci me ba da kuzari wato carbohydrate.

    Don haka jiki zai ta zaizayo wannan kitsen yana narka shi zuwa sinadarin sugar don ba mu kuzari…. Wanda shi ne sai a fara gani ƙarara mutum na ramewa domin ɗan kitsen da ke ƙasan fatar duk ya zaizaye… 

    Idan aka cigaba da samun rashin cin abinci akai-akai ƙarshe in rarar kitsen ta ƙare sai jiki ya fara ƙone sinadaran da suka gina shi wato protein, kamar irin lakar simintin da ake sa wa tsakanin bulo da bulo yayin gini don ya haɗe to kamar haka sai wannan simintin ya zaizaye ya zamto sai bulo kurum wato tsoka ba tare da inganci ba.

    Toh kamar haka ga macen da ta dage wajen gyaran nono ita dole sai ya ciko tai ta shaye-shayen abubuwa da shafe-shafe…. Alhalin ba ta wani cin ingantaccen abinci’ ta ya nono zai girma? Hala kun mance nono kusan 95% duk kitse ne, shi ke ba shi shape da laushi… Don haka yadda kike ba kya son cin abinci wannan kitsen na jikinsa jikinki zai ta ƙonawa yana ba ki kuzari, shi yasa duk sanda mace ta rame nonuwan ma kwanciya suke.

    Haka duk yadda kika dage da gyaran su idan babu abinci me kyau ba za ki ga yadda kike so ba, ƙarshe ki ta shaye-shayen abubuwa ana wance ai iri kaza ta sha kuma ya yi mata… Amma ni ga shi na yi babu wani canji? Sai ki kalli yanayin cin abinci ki.

    Wanda kuma suka matsa suka haikewa abubuwa masu estrogen to su kuma ko nonon ya yi girma ƙarshe in an haihu sai ka ga mace ga nono da girmansu amma babu ruwan nono saboda ta hura ba ta shiga ba ne, tudu ne amma babu isassun glandular tissues.

    Don haka abinci FIRST!!!

    Domin karanta sakaran nono danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

     

  • Babban Kundi

    Babban Kundi

    Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah (Subhanahu wata’ala), wanda ya halitta sammai da ƙassai guda bakwai, haka kuma ya halicci mutum daga farin ruwa, sai ya sanya masa ji da gani tare da tunani da hankali, domin ya bi umarninsa. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam).

    Sanin irin mu’ujizojin da suke cikin Alƙur’ani kamar su haɗa magun-guna da Alƙur’ani, sai dalilin da Allah ya faɗi lahira da duniya sau ɗari da goma sha biyar (115), shiriya da rahma sau saba’in da tara(79), shaiɗan da mala’iku sau tamanin da takwas(88) duk a cikin Alƙur’ani mai girma da dai sauran su.

    Sa’annan kuma da sanin yadda Alƙur’ani mai girma ya tsara mana rayuwar mu, domin hawa kan gadan tsira tare da sanin yadda Allah (Subhanahu wata’ala) yake halittar mutane a cikin iyayen su (embryology da genetic) da yadda suke shaƙan numfashi (physiology) .

    Bugu da ƙari kuma, da sanin adadin ƙira’o’i haɗi da ruwayoyin da muke da su, domin ƙarawa ɗaliban Ilimi himma wajen karatu tare da kaucewa kura-kurai a wajen karatu, saboda muna da ruwayoyi guda ko goma ko sha huɗu, haka kuma ana iya samun banbancin rubutu da karatu a tsakanin waɗancan ruwayoyi haɗi da tarihin malaman ruwayoyi, amma kuma a taƙaice da dai sauran su .

    BABBAN KUNDI

    Alqur’ani mai girma shi ne littafin da ya fi dukkanin litittafai (104) waɗanda Allah (Subhanahu wata’ala) ya saukarwa da Annabawa da manzonnin sa masu daraja.

    Babban Kundi shi ne littafin da Allah (Subhanahu wata’ala) ya saukarwa da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) da larabci wanda ya ƙunshi dukkanin abubuwan da suka faru haɗi da waɗanda za su faru a nan gaba.

    Alqur’ani littafi ne wanda aka saukar da shi da larabci wanda yake nufin abin karantawa. Saboda haka ne ma yasa Allah (Subhanahu wata’ala) yake yi wa waɗansu mutane baiwar haddace Alƙur’ani mai girma .

    Alƙur’ani mai girma maganar Allah ne, kuma litafinsa ne mai girma, shi ba kamar sauran gama-garin maganganu ba ne, domin saukakke ne daga mai hikima abin godiya. Don haka ne Allah maɗaukakin sarki ya shara’anta mana waɗansu ladubba da ya wajaba mu lura da su wajen karatun Alƙur`ani, don girmama sha’aninsa, da ɗaukaka matsayinsa. Ya shara’antawa wanda zai karanta shi ya kasance mai tsarki, kuma ya kasance mai ƙanƙan da kai, tare da lura da tadabburinsa, da dai sauransu.

    Danna nan don karanta falalar karatun Ƙur’ani

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

     

  • So Da Shaƙuwa

    So Da Shaƙuwa

    Akwai hanyoyi da dama, waɗanda miji zai iya samun so da shaƙuwa mai tsanani a wajen matarsa, kamar su kyauta, kulawa, yabo, kwalliya, zantawa da sauransu.

    1. Kyauta: Tana ɗaya daga cikin abubuwan da miji zai iya samun so da shaƙuwa a gurin matarsa. Saboda yawan kyauta tana ƙara danƙon ƙaunar shiga cikin fagen zandagaryar soyayya a cikin zukatan ma’aurata har da samari da ‘yan mata.

    2. Kulawa: Tana ɗaya daga cikin abin da miji zai iya samun so da shaƙuwa mai tsanani a gurin matarsa. Saboda shi kan shi aure an gina shi ne akan kulawa da juna da dai sauransu. Har ila yau,idan miji yana kulawa da matarsa a kowane lokaci, zai iya samun so da shaƙuwa mara adadi, misali kamar su yawan zolaya da wasanni, sannan da bibiyar halin da take ciki da zarar ka ga yanayinta ya canza, sai ka binciko mai ke damunta, don yi mata maganin abin da ke damunta.

    Yana daga cikin kulawa idan miji zai fita daga gidansa, ya zauna da matarsa su yi hira kafin ya fita wajan aikinsa, sai ya faɗa mata yana sonta yana ƙaunarta. Bugu da ƙari kuma, idan ya fita wajan aikinsa ko sana’arsa sai ya kira ta ya faɗa mata yana matuƙar ƙaunarta da kalamai masu nishaɗi, sannan ya sanar da ita halin da yake ciki a wajan aikinsa.

    Haka miji zai aikata duk bayan rabin awa ko awa ɗaya ko lokaci bayan lokaci, sannan za ka iya kiranta a waya ko tura saƙo akan  waya ko takarda, idan gidan na ka a kusa yake, haka ma su mata za su aikata idan suna so su mallake mijinsu.

    3. Yabo: Yana ɗaya daga cikin abin da miji zai iya samun so da shaƙuwa a gurin matarsa, saboda duk abin da mace ta aikata ko ta yi,to tana buƙatar yabawa, misali idan matarka ta yi abinci mai daɗi, sa’annan kuma  kai ka ji daɗin abinci, sai ka yabe ta sosai da irin abincin da tayi.

    Bugu da ƙari ma idan ta yi kwalliya, wadda ta haɗu sosai, sai ka zuga ta ko ka yabe ta sosai, haka nan miji zai yi a duk irin abin da matarsa ta yi, haka ita za ta aikata idan tana so ta mallake mijinta.

    Misali “ya zankaɗeɗiyar santaleliyar zuƙeƙiyar hamshaƙiyar tauraruwar ‘yar santimantiliyar kyakkyawar zabgegiyar gimbiyar jarumar zaƙaƙurar amaryata” Wannan kwaliyar taki ta yi kyau ko abinci ko dai waɗansu abubuwan.

    4. Kwalliya: Tana  ɗaya daga cikin abin da ɗa namiji yake so, kuma zai iya janyo so da shaƙuwa a wajan matarsa, saboda ita kwalliya tana ƙarawa mutum kyau da fito da mutum sosai kamar yadda muka yi bayani a babin mutuwar aure.

    6. Zantawa: Tattaunawa  tana ɗaya daga cikin abin da ke kawo so da shaƙuwa a tsakanin ma’aurata, saboda idan kana yawan magana da mutum yakan sa ku fahimci juna da samun shaƙuwa da juna, haka nan ma ma’aurata idan suna zantawa da junansu yakan sa su fahimci junansu da ƙara samun so da shaƙuwa, sannan za su fahimci abubuwan da kowannensu ya fi so a rayuwarsa da dai sauransu, Allah yasa mu dace.

    Don karanta abubuwan da ke sa wa miji ya zama mafi soyuwa a wajen matarsa danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Dabarun Bunƙasa Noman Masara

    Dabarun Bunƙasa Noman Masara

    1. Wajen shuka

    Dukkanin wanda zai noma irin wannan masara, don samun masara mai inganci, to ya kamata ya yi la’akari da;

    a. Ƙasar wajen da zai yi shuka ta kasance ba ta ajiye ruwa sosai, kuma wajen bai da alaƙa da kan hanyar ruwa mai ƙarfi, kamar kogi ko dam.

    b. Ƙasar wajen ta kasance tana da kyau sosai, wato tana ɗauke da takin gargajiya.

    c. Rage wajen ƙona ciyayi a cikin gonar.

    d. Yin huɗa da garma mai kyau.

    2. Iri (abin da za a shuka)

    a. A tabbatar da irin da za a shuka mai kyau ne kuma mai inganci.

    b. Bayar da tazara tsakanin shuka da shuka da takun ƙafa ɗaya (25 cm) da kuma tazarar ƙafa uku a tsakanin kunya zuwa kunya (75 cm).

    c. Idan kuma mutum zai shuka wani abu a cikin masarar, to ana buƙatar ya bayar da tazarar ƙafa ɗaya da rabi zuwa biyu (40cm-50cm) kamar wake, dawa, gero da sauransu.

    d. A tabbatar an tona rami sosai, ta yadda shukar za ta zauna a cikin ƙasa sosai.

    e. Za a iya sanya irin a cikin ruwan ɗumi, don kashe ƙwarukan da suke cikin irin.

    3. Taki

    a. A tabbatar takin da za a sanya ma shukar, yana da inganci sosai.

    b. A binne takin a jikin jijiyoyin shukar, maimakon watsawa da ake yi gona.

    c. A tabbatar an yi amfani da wadataccen taki a gona, misali a yi amfani da takin kamfa 15-15-15 ko 20-10-10 buhuna biyar da kuma buhuna uku na yuriya (Urea) ga shukar da ta kai hekta ɗaya.

    d. Ana fara amfani da takin kamfa ne a shuka, bayan an samu kamar sati biyu da shuka, sai kuma bayan sati huɗu, sai a yi amfani da takin yuriya.

    4. Hanyoyin magance ciyawa da ƙwari

    a. Manomi, ya tabbatar ya nome ko feshe dukkanin wata ciyawa da take cikin gonarsa.

    b. A yanzu ana amfani da maganin ƙone ciyawa a gona, wanda shi ne ma ya fi sauƙi ga manomi, sai dai ana buƙatar manomi ya nemi shawarar malamin gona, kafin ya yi amfani da maganin ƙone ciyawa, don kaucewa asarar abin da ya shuka a gonarsa.

    c. Manomi, ya dinga ziyartar gonarsa akai-akai, don lura da halin da shukarsa take ciki, idan ya ga wani abu a gonarsa kamar ƙwari ko shukarsa ta canza launinta, to ya tuntuɓi malamin gona.

    5. Dabarun girbin masara

    a. Manomi, ya tabbatar masararsa ta bushe sosai, tun kafin ya girbe ta.

    b. A yi amfani da waje mai tsabta, don casa abin da aka noma kamar buhu, tanfal da sauran su.

    c. A samu mazubi mai kyau, don adana abin da aka casa, idan kuma ajiye ta za a yi zuwa wani lokaci mai tsawo, to a sanya mata maganin ƙwari a ciki, don kaucewa asara.

    d. A tabbatar an raba masarar da kan ƙasa, wato a samu wani abu a ɗora buhuna masarar a kai.

    Danna nan don karanta dabarun noman zamani

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Mallakar Miji

    Mallakar Miji

    Ya zama dole akan waɗanda suke so su mallake mai gidansu, su iya waɗannan abubuwan, kamar yadda sheikh Halliru Maraya Kaduna, Shiekh Aminu Daurawa Kano da Malam Suraj Yunus Kudan suka faɗa kamar haka:

    1. Girki: Girki yana ɗaya daga cikin abin da mace takan iya mallake mijinta da kuma kammala abinci akan lokaci, saboda dukkanin mutumin da yake rayuwa a doran ƙasa, to yana buƙatar abinci, kamar yadda Allah (subhanahu wata`ala) yace acikin alƙur`ani mai girma

    ”ku ci ku sha” a kuma cikin wata ayar yace ”ku ci daga cikin tsarkaka”. Sannan kuma da iya abinci kala-kala daban-daban da kayan abinci guda ɗaya. Misali dawa, ta iya yin ɗan-wake, tubani, tuwo, gauɗa,’yarsalo (waina) da kunu.

    2. Tsabta: Tsabta cikon addini kamar yadda Hausawa suke faɗa, haka kuma annabi Muhammad (sallallahu alaihi wasallam) yace “tsabta tana daga cikin yankin imani”. Saboda haka, tsabta tana ɗaya daga cikin abubuwan da mace kan iya mallake mijinta fiye da yadda take tunani, kodayaushe gidan mijinta a cikin tsafta, sannan kuma ke ma kanki a cikin tsabtar har ma da ‘ya’yanki.

    3. Kwalliya: Kwalliya tana ɗaya daga cikin abubuwan da mace za ta iya mallake mijinta a kowanne lokaci, musamman ta iya fari da ido da murmushi mai sace zuciyar mijinki, wanda zai ɗauke hankalin mijinki da kawar masa da duk irin abin da yake damunsa cikin zuciyarsa.

    4. Tafiya: Iya tafiya ita ma na ɗaya daga abubuwan da mace za ta iya ɗauke hankalin mijinta musamman lamɓo, rangwaɗa, kina tafiya kina rangwaɗe-rangwaɗe.

    5. Magana: Iya furuci ko magana ita ma na ɗaya daga cikin abubuwan da mace za ta iya mallake mijinta, idan ya yi mata magana ko ya tambayeta wani abu sai ta mayar masa a cikin tausasawar zukata da lanƙwasa harshe, sannan ta iya gunna da ƙalƙala sugura haɗi da kubra.

    Sannan kuma iƙlabi a cikin magana har ma idgami, duk a cikin magana tsakanin mata da mijinta. Bugu da ƙari ma har ikfai da izhari duk a cikin magana da dai sauran su, duk a cikin kalamai tsakanin ango da amarya.

    Danna nan don karanta yadda ake yi wa maigida a lokacin fushi

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Huɗu

    Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Huɗu

    Great Britain, Ingila ke nan duk da yake ita ta zama ta fi kowacce cin ribar cinikin Bayi, ba ta soke bauta ba da wuri, sai bayan an ɗauki lokaci, inda sauran ƙasashen Turai suka ce sun haramta cinikin Bayi. 

    Ƙasar da ta fara yin doka ita ce, Denmark a shekara ta 1804, Ingila ta yi a shekara ta 1807, sai Amerika ta yi a shekara ta 1808, sai Sweden a shekara ta 1817, sai Holand a shekara  ta 1814, an ba da dalilin da yasa su Turawa ba su damu da cinikin Bayi ba da azabar bautar da mutane da ake yi saboda su ma a ƙasar su ana azabtar da mutane da suka yi ɗan laifi kaɗan, sai ka ga mutum ana bin sa kuma a ƙarshe an zo an kashe shi, ko an tsire shi, ko an ɗauke shi an jefar da shi a wata ƙasa.

    Duk wannan zaluncin su ma ya dame su sai ya zamanto ma ba sa ganin zaluntar da ake yi wa Bayin, sai da abubuwa suka fara kankama tukunna, aka fara sanin cewa lallai fa Bayi suna shan wuya, wani lauya ana ce masa Grandba Shap  ne ya fara ƙoqarin maganar ‘yantar da Bayi, ya taimakawa wani Bawa da ya gudu ana ce masa Somaset.

    Wannan Bawan ya gudu aka je aka kamo shi za a dawo da shi, sa ya shigar da ƙara a gaban alƙali wato Lord…. inda aka yi wani abu da ake ce masa Read of Habees copus cewa lallai a kawo shi wannan bawa kotu, kawo shi kotu da hukuncin da shi Lord Chief Mans… ya bayar ne ya fara jawo mutane su san cewa lallai akwai azaba a harkar cinikin Bayi. Kuma abin ya samu karɓuwa, cewa a san yadda za a yi a hana wannan.

    Bayan shekara goma sha biyar ana ta wannan gwagwarmaya da mutane irin su Williams Wilberforce da wannan Grandba Shap da Thomas Clascis suka yi wata ƙungiya suka kira ta da Society for the Revolution of  Slave Trade, kuma shi Willberforce ya zama shi ne mai magana da yawun su a majalisa, har yasa dai aka yi wannann doka ta shekarar 1907.

    Amma dai sun ci gaba da yin gwagwarmaya da sauran mutane da yin wannan, inda daga baya Ingila ta ce lallai za ta hana wannan cinikin, amma dai ba wai sun hana ne don tausayi kaɗai ba,  akwai maganar tattalin arziki da maganar sun samu ci gaban masana’antu (Industrial revolution). Bayin dai buƙatar su ta ragu a ɓangaren tattalin arziki a Ingila, tunda Ingila ta ci gaba kuma suna ganin cewa, gwanda mutane a ƙyale su a Afrika su dinga yin noma don a samu wanda ake yin amfani da shi a masana’antu (Factories).

    Ingila da sojojin ta na Ruwa suka ɗauki gabaran hana wannan ciniki tunda ta fi kowa ƙarfi a ruwa, su za su yi maganin cinikin Bayin nan. Duk da haka dai abin ya ba su wahala yadda mutane suke ta ƙoƙarin su kauce mu su, sun fito da dabaru da yawa na kaucewa inda za a kama su, duk da dai an kama jirage da yawa.

    A cikin shekara 20 daga 1818-1838 an kama jirage 280 da wani abu, haka dai kullum jiragen da ake kamawa ƙaruwa suke inda a shekarar 1845 ma an kama jirage 30, amma duk da haka sun ci gaba da yin dabaru su masu ɗiban Bayin nan domin su kaucewa sojojin ruwa na Ingila, domin duk jirgin da suka kama saisu kai shi Freetown Sierra Leon a nan a ke yi masa hukunci.

    Wani lokacin ma su masu cinikin Bayin sai su ɓoye su ko su zubar da su a ruwa domin kada a kama su, sai da aka canja dokar aka ce idan an ga wasu abubuwa da suka yi kama da kayan cinikin Bayi a kama jirgin shi ma a yi masa shari’a. 

    Wasu idan an kama su an kai su Sierra Leon ɗin nan to sai a saki Bayin tun da wannan gari ana ce masa Freetown, wasu idan an sake su Mishan suna ɗaukan su su koya mu su karatu su mayar da su Kirista da sauransu. Har ma aka samu wani babban Kirista da aka taɓa yi a Najeriya ana ace masa Bishop Samuel Ajayi Crowther wanda shi ma aka sace shi aka mayar da shi Bawa a shekarar 1821. 

    Haka aka ɗauke su daga wannan hannu zuwa wannan tun da yana da rabon zai tsira aka kai shi Sierra Leon daga nan kuma dai ya samu ya kuɓuta tunda an kama jirgin da yake ɗauke su, aka mayar da shi Kirista a shekarar 1825 aka yi baptizing ɗinsa ya zama Samuel Crowther, wanda yasa aka sa masa wannan su na shi ne shugaban Cochi a nan Sierra Leon.

     Kowa ya san gwagwarmayar da ya yi wajen kawo addinin Kirista Najeriya, shi ne ɗan Afrika na farko ɗan asalin Najeriya da ya zama Bishop na Angalican kuma ya shahara, yana ɗaya daga cikin mutanen da aka kuɓutar da su daga hannun masu cinikin Bayi.

    Haka dai suka yi da aka gama cinikin Bayin nan sai ya zama cewa, Mishan sun duƙufa sosai wurin yaɗa addinin kirista, saboda su wanke laifukan su da suka yi wa mutanen Afrika su kawo mu su addinin kirista. Wannan abu ya yi tasiri da yadda su Turawan mulkin mallaka suka yi amfani da Mishan don su tabbatar da mulkin su a Afrika ta yin amfani da Mishan da cinikayya da dabaru da sauran su har suka zo suka tabbata, tun da an gama cinikin Bayi an shiga wata marhala ta danniya daban (mulkin mallaka).

    Don karanta tarihin Afrika danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Jinkirin Warkewar Nankarwa (Delayed Healing Of Strech Marks)

    Jinkirin Warkewar Nankarwa (Delayed Healing Of Strech Marks)

    Nankarwa (stretch marks) takan zamo mai tsananin ƙaiƙayi ko zafi ne, sa’annan kuma mai wahalar warkewar saboda haɗakar abubuwa guda biyu: 

    (a) Bubbuɗewa da kumburin fatar wurin da take 

    (b) Ƙoƙarin warkewar da fatar wurin take yi.

    Yadda abin yake faruwa shi ne:

    Nankarwa ta fi fitowa mace a jikinta, musamman a  damtsen hannuwa, ko jikin nonuwa, ko cinyoyi, ko duwawu, ko, kwuiɓi, ko ciki, ko baya, ko sha-raɓa, da sauransu. Babban abinda yake kawo ta shi ne yin ƙiba, ko juna biyu, ko ramewa. Ma’ana, idan mace ta yi ƙiba, sa’annan ta rame daga baya, to, akwai yiwuwar nankarwa ta fito mata.

    Haka nan, idan nonuwan mace suka yi girma sakamakon shayarwa, sa’annan, suka rage girma bayan ta daina shayarwa, to, akwai yiwuwar nankarwa ta fito mata. Haka nan yin ƙiba da yin rama a sauran sassan jiki.

    Nankarwa ta fi fitowa mace a jikinta, musamman a damtsen hannuwa, ko jikin nonuwa, ko cinyoyi, ko duwawu, ko, kwuiɓi, ko ciki, ko baya, ko sha-raɓa, da sauransu. Babban abinda yake kawo ta shi ne yin ƙiba, ko juna biyu, ko ramewa. Ma’ana, idan mace ta yi ƙiba, sa’annan ta rame daga baya, to, akwai yiwuwar nankarwa ta fito mata.

    Bubbuɗewar za ta haddasa yagewar zaren da yake haɗe tsakanin sassan fatar jiki (collagen) da kuma zaren da yake sanya fatar ta iya tattalewa (elasting). Daga nan sai waɗannan tabbai na nankarwa su fito ruɗu-ruɗu a jikin fata. Kuma tasirantuwar da fatar take yi (skin response) ne ga waɗannan abubuwan, yake haddasa kumburin da ƙaiƙayin ko jin zafi.

    Warkewa (healing process) daga yagewar fata wacce nankarwa ta haifar, shi ma yana sanya jin ƙaiƙayi da kuma wahalar magancewa, musamman idan mace tana yawan sosawa. A nan, jijiyoyin jini za su riƙa bubbuɗewa (dilation) suka aikawa ƙwaƙwalwa sakon cewa zaren collagen da elastin na wurin sun yage, kuma akwai buƙatar su warke. To, a lokacin da ƙwaƙwalwa ta bayar da umurnin warkewar wurin, kuma sababbiin  ƙwayoyin halittar cells (new skin cells) suke fitowa, wurin zai riƙa yin ƙaiƙayi.

    Bushewar fatar nankarwa (dryness of stretch marks skin), sakamakon rashin shafa mayukan samar da damshi (moisturizers) a wurin, shi ma yana haifar da jin ƙaiƙayi sosai. Sa’annan yana sanya nankarwa ta yi ruɗu-ruɗu sosai, ta yi wahalar warkewa.

    Rashin kaurin fatar nankarwa (thinning skin structure of the stretch marks) shi ma yana haddasa jin ƙaiƙayi da wahalar warkewa. Ma’ana, idan nankarwa ta fito, to, fatar wurin za ta zamo ba ta da kauri kamar yadda sauran fatar sassan jiki take, kuma hakan zai sanya jin ƙaiƙayi a wurin.

    Bayan haka, rashin kaurin fatar zai sanya ta daɗe ba ta warke ba, musamman idan mace tana sosawa, ko kuma tana sanya matsattun tufafi suna yawan gugar wurin. Nau’in kumburin da nankarwa ta haddasa (nature of the stretch marks inflammation) shi ma yana haifar da jinkirin warkewa ko kuma ƙaiƙayin. Ma’ana, wata nankarwa tana fin wata yin ruɗu-ruɗu a jiki.

    Don haka, gawargwadon tsananinta, gawargwadon yanayin ƙaiƙayinta da wahalar warkewar ta. Magungunan da ake yin amfani da su wajen magance nankarwa yawanci mayuka da sabulai ne masu samar da damshi a jikin fata. Sai kuma magungunan hana kumburi da ƙaiƙayin fata. Sa’annan yawanci magungunan suna rage tsananinta ne kawai, amma ba su gusar da ita gaba-ɗaya.

    Don karanta yadda za a kula da fata danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu