Tag: yadda ake

  • Haifo Jarirai Cikin Rigar Sac

    Haifo Jarirai Cikin Rigar Sac

    Haƙiƙa akan haifo wasu yaran cikin amniotic sac ba tare da ta yage iya yaran sun fito ba. Yana da kyau mu fahimta faruwar hakan ba wani matsala ba ne, a cikin cikin ita wannan sac ko in ce jakar haɗe take da jikin mahaifa ita ce ke samar wa da jariri iska sanda yake cikin mahaifa (placenta).

    Amma a yayin da haihuwa ta zo ita sac ɗin kan yage ta yadda hakan ke ba wa huhun jariri (lungs) damar fara ɗaukar iska da kansa, maimakon sac ɗin da da take ba shi.

    Hatta a asibiti wasu ba ta yagewa jami’an lafiya ne ke farka ta da hannunsu ba tare da kowa ma ya sani ba sai dai ku ga jaririn kurum.

    Don haka haifo su cikin sac ba matsala ba ne. Allah yasa mu gama haife-haife lafiya.

    Danna nan domin karanta yadda ake yi wa jarirai huɗubar haihuwa

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Gwargwadon Shayarwa Gwargwadon Kariyarki

    Gwargwadon Shayarwa Gwargwadon Kariyarki

    Matan da kan shayar na da ƙarancin yiwuwar haɗuwa da cutar sankarar nono wato ‘breast cancer’ da ƙarancin haɗuwa da kansar kwanson ƙwayayen halitta wato ‘ovarian cancer’, ƙarancin haɗuwa da ciwon zuciya, cutar shanyewar ɓarin jiki, haɗuwa da ciwon sugar tare da samun kariya daga cutar damuwa da kan shafi wasu matan bayan haihuwa.

    Gwargwadon tsayin lokacin da kika ɗauka kina shayarwa gwargwadon kariyar da za ki samu daga waɗancan cuttukan, wacce ta shayar da yaro iya wata 12 kacal ba za ta sami kariya kamar na wacce ta shayar tsawon watanni 18, shekara 2 ko 3 ba.

    Haka gwargwadon tsayin lokacin da kika ɗauka kina shayarwa gwargwadon lafiyar yaro ko yarinyar ki, duk me son lafiyayyar zuri’a to ya shayar na ɗan lokaci me tsawo. 

    An yi abin ne don a shayar ba domin a yi ado kurum ba.

    Danna nan don karanta sankarar nono

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Abdullahi Mustaspha Mai Hoto Kudan

    Tarihin Abdullahi Mustaspha Mai Hoto Kudan

    An haifi Abdullahi Mustapha a 1985 a unguwar tsauni Kudan. Ya yi karatu Islamiyya a Madarasatul Hayatul Islam bakin kasuwa Kudan daga 1990/1997. Ya yi Firamare daga 1990/1996. Ya yi karatun gaba da Firamare daga 1997/2014.

    Ya sake komawa makaranta, wanda ya yi karatu a National Teachers Institude Kaduna (NTI), amma a ɓangaran karatun nesa (Distanca learning Studies) a reshen su da ke Hunƙuyi, wanda a nan ne ya samu shaidar malanta (NCE).

    Bayan haka, ya yi gwagwarmaya a gidan mai (Petroleum station) gidan man na mahaifinsa, tun a shekara ta 1995-1998 inda daga nan Allah ya amshi rayuwar mahaifinsa marigayi Alh. Zakari Haladu Kudan, Allah ya ji ƙansa da rahama.

    Bayan wasu shekaru ya fara tunanin ya fara aiki a studio wato shagon ɗaukan hoto, sannan ya nemi izinin babban mai ɗaukar hoto na wannan lokaci wato marigayi Hassan haske Allah ya ji ƙansa da rahama, inda a wurinsa ya samu ƙwarewa na tsawon shekaru biyar (wanda shi wancan bawan Allah yana ɗaya daga cikin mutanan da suke zuwa Kudan ɗaukar hoto a duk ranar Juma’a) kuma sun rabu da shi lafiya cikin girmamawa da ladabi.

    Bayan haka, wani lokaci Alhaji Sabi’u Ibrahim kansila a lokacin yana da studio, shi ma ya ɗauke shi aiki a shagonsa, a matsayin shugaban shagon ƙarƙashin kulawar Aliyu Wada (mai Talata) na tsawon wani lokaci. A wannan studio, ya yi aiki tare da ma’aikata uku, wato  Usman Isah (Ameer hoto) da Jamilu Zakari da Sani Umar.

    Dukkanin su ya koya musu aiki ta yanda kowannen su ya samu ƙwarewa, biyu daga cikinsu ma sun samu damar mallakar studio nasu, wato Usman Isah (Ameer hoto) da kuma Jamilu Zakari. A yanzu haka yana da babban  studio, wanda mallakarsa ne, wanda yake printing/photocopy da su. Yana yin  noma da kasuwanci, yana da  aure da ‘ya’ya, Allah ya ƙarama rayuwa albarka amin summa amin.

    Ya yi karatu a Nigerian communication commission (NCC) Zaria a reshensu da ke GSS Kudan, a inda a nan ne ya samu takardar diploma a computer,  a networking/computer engineering daga 2013/2014.

    (Mun samu wannan jawabin ne daga bakin sa, wanda ya rubuta ya turo min da WhatsApp a ranar 12/02/2021 da misalin ƙarfe 7:33 na safe).

    Danna nan karanta tarihin Hajiya Halima Jumare Kudan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Amfanin Ilimin Kwamfuta

    Amfanin Ilimin Kwamfuta

    Abu ne mai matuƙar mahimmanci akan kowane mutum ya iya sarrafa tasarrafin ragamar kwamfuta (na’ura mai ƙwaƙwalwa) ta hanyoyi da dama, domin yin ninƙaya a cikin ko ina a duniya ta hanyar karatu ko kasuwanci ko sadarwa. Haka kuma kwamfuta ana iya amfani da ita wajen  ganin yadda ran mutum yake fita da sauran su.

    Kwamfuta na da amfani da yawa tun daga yara ƙanana har  zuwa manya. Kowace masana’anta na buƙatar kwamfuta, don gudanar da ayyukanta cikin sauƙi. Yin amfani da kwamfuta mai inganci zai haifar da ci gaban duniya  baki ɗaya. Kwamfuta na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da mutum ya ƙirƙira.

    Sannan kuma ba zai  yiwu ba ga mutum ya  yi hasashen yanayi ba tare da amfani da kwamfuta ba. Na’urorin kwamfutoci suna sauƙaƙa ayyuka da dama, saboda suna iya sarrafa bayanai da yin wasu ƙididdiga waɗanda za su ba da sakamakon abin da ake buƙata.

    Kwamfuta tana amfani ta ɓangaren sadarwa ko shigar da bayanai ta ɓangarorin daban-daban, tana ba da manya da ƙanana harkar  kasuwanci tare da kayan aikin da ake buƙata, don dai-daita mahimman ayyuka kamar ajiyar kuɗi da ƙirƙirar takardu. Har ila yau, su ne maɓalli a cikin masana’antar tallace-tallace, inda suke taimakawa wajen sarrafa kaya daga shigarwa zuwa fitar su.

    Don karanta me ake yi da kwamfuta danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Mecece Kwamfuta?

    Mecece Kwamfuta?

    Kwamfuta ita ce na’urar da take amfani da wutar lantarki, wacce ke sarrafa tasarrafin ragamar bayanan da aka shigar mata, don sarrafa su zuwa wani abu mai ma’ana ko fa’ida, ta hanyar shigarwa da karɓarwa gami da adanawa tare da fitar da bayanan abin da aka shigar mata.

    Na’urar kwamfuta wata aba ce wacce take taimakawa mutane wajen gudanar da ayyukan su cikin sauƙi gami da adana musu bayanan su tare da binciko abin da suke buƙata cikin sauƙi.

    Kwamfuta ita ce take mayar da abu mai wahala zuwa sauƙi da kuma kiyaye ingancin wani abu ta hanyar shigar da shi cikinta, wanda tsawon shekarun da zai kwashe a cikinta yana nan, kuma ingancinsa yana nan. Misali littafin da aka ajiye shi a cikin  kwamfuta da kuma wanda aka ajiye shi a cikin ɗakin karatu sama da shekaru hamsin, wanne ne daga cikin su zai kasance mai inganci sosai daga cikin su?

    Kwamfuta ita ce take karɓar ɗanyen saƙo (data), sai ta sarrafa shi zuwa abu mai ma’ana wanda kuma zai bayar da bayanai masu inganci. Misali mutane sun yarda shinkafa da masara abinci ne, amma idan mutum ya siyo shinkafa a kasuwa ko a shago, ba zai iya ɗauka a matsayin abinci kai tsaye ba, har sai ya dafa ta, ta hanyar yin amfani da shinkafa, tukunya, mai, magi, gishiri, ruwa, kayan miya da sauran su. Sannan idan sun gama dahuwa a tukunya ɗaya, sai mu ɗauka a matsayin abinci. To haka ita ma kwamfuta take wajen sarrafa bayanai.

    Domin karanta menene data informationn danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Rt. Hon. Isa Muhammad Ashir Kudan

    Tarihin Rt. Hon. Isa Muhammad Ashir Kudan

    An haifi mai girma Isa Muhammad Ashir a garin Kudan a ranar 23rd ga watan October, 1962, a cikin ƙaramar hukumar Kudan, jihar Kaduna. Ya yi karatu a Model Primary School Kudan daga 1968-1974, ya yi karatu a makarantar Kufena wacce take a Wusasa Zaria a 1976-1980.

    Ya yi karatu a Polytecnic Katsina a 1982-1985, wanda ya samu shaidar Diploma a ɓangaren harkan kasuwanci (Business administrative), ya kuma halarci makarantar Polytechnic Kaduna, wanda ya yi karatun gaba da Diploma wato HND a 1987-1989.

    Haka kuma a 1990 ne ya halacci wajen horas da manyan ɗalibai, wato NYSC Corps a Barno (BD/KD/89/4217). Sannan kuma a 1999 ne, ya yi Post-graduate a ɓangaren  cinikayya (marketing management). Bugu da ƙari kuma ya yi Master’s degree a public policy and administration a 2000-2001 a jami’ar Bayero Kano (B.U.K).

    Har ila yau, ya tsunduma harkar siyasa a 1996 a Jam’iyyar Zero party (ZP), wanda ya tsaya takarar shugaban ƙaramar hukuma (Chairman), amma bai samu nasara ba, ya kuma sake tsayawa a jam’iyyar Social democratic party (SDP) a 1997, sannan kuma ya zama member a KSHA ƙarƙashin jam’iyyar DPW a 1999-2000. A inda  aka zaɓe shi a matsayin ɗan-majalisar jihar Kaduna (House of Assembly) mai wakiltar Kudan-Maƙarfi zuwa 2000-2003.

    Haka kuma, an sake zaɓansa a matsayin ɗan-majalisar jihar Kaduna daga 2003-2007. Sannan kuma an sake zaɓansa a 2007-2011 a matsayin ɗan-majalisa na tarayya mai wakiltar Kudan-Maƙarfi a jam’iyyar People Democratic Party (PDP). Haka kuma, ya sake zama ɗan-majalisa na Tarayya a karo na biyu daga 2011-2015.

    Haka kuma a 2014 ne ya koma jam’iyyar All progress congress (A.P.C), wanda ya yi takarar Gwamna na zaɓen cikin gida, amma bai samu nasara ba, a 2019 ne kuma ya sake tsayawa takarar Gwamna a jam’iyyar PDP bayan ya koma cikin Jam’iyyar, wanda kuma bayan an yi zaɓen gama-gari nan ma bai samu nasara ba. Haka kuma ya yi aure yana da mata guda ɗaya da kuma ‘ya’ya guda bakwai.

    Bugu da ƙari kuma, ya sake tsayawa takarar Gwamna a kakan zaɓe ta 2023, a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, wanda a nan ma bai samu nasara ba, tun da mutane suna ganin cewa an yi maguɗin zaɓe sosai.

    Sannan kuma, ya samu damar samun sarautar Sarkin bai Zazzau, wanda masarautar Zazzau ta naɗa shi, duba da irin tulin ayyuka na ci gaba, wanda ya samar da su a lokacin da yake kan mulkin. Haka kuma an samu ‘yan majalisun jiha da na Tarayya a ƙaramar hukumar Kudan-Maƙarfi, amma kuma ba a samu wani wanda ya kai shi aiki ba, saboda a lokacin da ya riƙe waɗannan mukamai ya samar da ayyuka kamar haka;

    1.Ya gina babban Asibiti a garin Kudan kusa da masallacin Idi na garin Kudan.

    2. Ya gina makarantar horas da ‘yan sanda a garin Kudan hanyar Sundu ko hanyar Barmo.

    3. Ya gina Masallacin Juma’a a garin Kudan, wanda yake ƙofar gidan hakimi.

    4. Ya gina makarantar koyan sana’a, wanda take kan hanyar zuwa Doka daga Kudan.

    5. Ya gina makarantar Firamare a ƙofar Arewa a garin Kudan.

    6.Ya gina ɗakin koyan sarrafa na’ura mai kwakwalwa a garin Kudan da Hunƙuyi (E-library).

    7. Ya gina wajen zaman ‘yan Sanda (Headquater) a garin Kudan kan hanyar zuwa Doka daga Kudan.

    8. Ya gina wajen koyon wasan ƙwallon ƙafa a garin Kudan wanda yake kan hanyar zuwa Garu.

    9. Ya gina ɗakin taro a garin Kudan wanda yake kan hanyar zuwa Garu.

    10. A samar da fitilloli masu samar da haske ta hanyar amfani da hasken rana (electry-Solar) a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya.

    11. Ya samar da famfo wanda yake amfani da hasken rana (Water-solar) a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya.

    12. Ya tura mutane ashirin zuwa ƙasar wajen domin yin karatun digiri na farko.

    13. Ya samar da tituna a cikin garurruwan da suke a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya.

    14. Ya  sabunta da faɗaɗa  ginin Dam, wanda yake Kudan kan hanyar zuwa Doka ko Sundu daga Kudan.

    Guraren da ya yi aiki

    1. Ya yi aiki a ma’aikatar kuɗi (Ministry of finance) a 1980-1982.

    2. Ya yi aiki a ma’aikatar samar da kuɗin cikin gida (Internal Revenue) a 1985-1992.

    3. Ya yi aiki a ma’aikatar kasuwanci da wajen shakatawa (ministry of commercial Industry and Tourism) a 1992-1993.

    Danna nan don karanta tarihin Adamu Yero Hunƙuyi

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Dangantakar Annabi Muhammad Da Rasuwar Mahaifinsa

    Dangantakar Annabi Muhammad Da Rasuwar Mahaifinsa

    1.Mahaifinsa: Shi ne Abdullahi ɗan Hashim ɗan Abdulmanaf ɗan Ƙusayyun ɗan Kilab.

    2.Mahaifiyarsa:- Ita ce Aminatu ‘yar wahabu ‘yar Abdulmanaf ‘yar Zuhra ‘yar Kilabu.

    3.Mahaifiyarsa da Mahaifinsa;- Sun haɗu a kakansa na biyar (5), shi ne Kilabu.

    4.Haƙiƙa Baffansa ya rasu, yana ɗan shekara goma sha Takwas (18), an rufe shi a garin Madinah, bai bar masa komai ba na daga dukiya.

    Sharhi:

    A lamba ta ɗaya (1), ya ce Mahaifinsa shi ne Abdullahi (shi ne wanda ake masa inkiya da Abu-alƙamata), shi ne wanda ya auri Aminatu ‘yar Wahab, Azzuhriyyatu Baƙuraishiya, sai Abdulmuɗalib, wanda ya auri Fatimatu ‘yar Amiru Almakazumiya (Abdulmuɗalib yana ɗaya daga cikin manyan mutane Ƙuraishawa, wanda Ƙuraishawa, suke haɗuwa akan ra’ayinsa, sannan suna gabatar da shi a wajen Mu’amalarsu).

    Sai Hashimu shi ne wanda ake kira da Abu-Haris Za’im Baƙuraishe a lokacin Jahilya, sannan yana ɗaya daga  cikin manya-manya labarawa. Ya kasance yana shayar da masu aikin Hajji ruwan Zam-zam. Sannan shi ne wanda ya auri Salma ‘yar Amru Alnajariyatul Khazrajyya.

    Sai Abdulmanaf yana ɗaya daga cikin Kakannin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam), an ce sunansa Mugira Abdulmanaf, laƙabinsa ne, shi ne wanda ya auri Aitika ‘yar Murra Assalamiyatu (ɗaya daga cikin ƙabilar Ƙaisun-ilani bin Madhar).

    Sai Ƙusayyun (Shi ne shugaban Ƙuraishawa, sannan kuma shi ne wanda aka yake kula da ɗakin Harami) shi ne wanda ya auri Hubayyu ‘yar Hulilu Alku Za’iyatu (Alkhuza’atu Bin Iliyasu Bin Madhar) sai Kilabu (ana yi masa laƙabi da Kilab ne, saboda ya kasance yana yawaita yawan farauta da Kare.

    Amma sunansa Hakimu ko Uwarta), Shi ne wanda ya auri Fatimatu yar Sa’adu, sai Murrata shi ne wanda ya auri Hindu ‘yar Sariru daga ƙabilar Banu Fahra Bin Malik (Shi ne Abu-Husaisu) Shi ne ya auri Mahaifiyar Ka’abu Mariyatu ‘yar Shaibana daga ƙabilar Fahra. Sai Lu’ayyi shi ne wanda ya Mahaifiyar Ka’abu Mariyatu ‘yar Ka’abu daga ƙabilar Kadha’ata.

    Sai Ghalib shi ne ya auri mahaifiyar Lu’ayu Salma ‘yar Amaru Alkhuza’i l, sai Fahra (shi ne wanda ƙuraishawa suke yi masa laƙabi da Ahlul Ashira), shi ne wanda ya auri mahaifiyar Ghalib, Laila ‘yar Sa’adu daga Haulin. Sai Malik shi ne wanda ya auri Jundilatu ‘yar Haris daga ƙabilar Jurhum).

    Sai Nadhir ya auri Atika ‘yar Adwana daga ƙabilar ƙaisun I’ilani, sai kinanatu shi ne wanda ya auri Burratu ‘yar Murra Addi, sai Mudrakata, amma sunansa Amru) shi ne ya auri Salma ‘yar Aslama daga Kabilar Kudha’atu,  sai Nazar shi ne wanda ya auri Saudatu ‘yar Akka sai Ma’adu.

    Danna nan don karanta jikokin annabi

    Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu

     

  • Tarihin Adamu Yero Hunƙuyi

    Tarihin Adamu Yero Hunƙuyi

    An haifi Adamu Yero a garin Hunƙuyi a cikin ƙaramar hukumar Kudan, jihar Kaduna a ranar 12/02/1960 ya yi karatu a makarantu kamar haka;

    1. LGEA Firamare School Hunƙuyi 1972-1978

    2 UPE teacher collage Zaria 1978-1983 Grade 11

    3. Collage of Education Kafanchan 1984-1987 NCE

    4. ABU Zaria 1987-1990 BA (Hausa)

    5. KDS Poly Zaria 1997-1998 ADPA

    6. ABU Zaria 2012-2015 MA (Hausa)

    7. Rauda School Al’aƙsa center for education and vocational training Zaria June 2008

    8. KD state civic servant commission (exam)  June 2003 statement of research

    9. Teacher Registration Council(TRC)  of Nigeria April 2005 Certificate of Registration

    Ayyukansa da ƙwarewarsa

    1. Ya yi aiki a Gaskiya Firamare School Zaria  a 1982 T/ Practice .

    2. Ya yi aiki a Ƙofar Gayan Firamare School  Zaria a 1983 T/Practice .

    3. Ya yi aiki a Domoso Firamare School Hunƙuyi a 1983-1984  V/teacher .

    4. Ya yi aiki a Government Secondary School Maƙarfi a 1985- T/Practice .

    5. Ya yi aiki a Government Secondary School Maƙarfi a 1987 T/Practice .

    6. Ya yi aiki a KWSCOE Illorin a 1991-1993 Asst lecturer.

    7.Ya yi aiki a LGEA MIGA Maƙarfi a 1993-2002 HOD/PM.

    8. Ya yi aiki a Kudan Hunƙuyi a 2002-2006 HOD /PM.

    9. Ya yi aiki a LGEA GIGA Giwa a 2006-2007 HOD/PM.

    10. Ya yi aiki a LGEA Kudan Hunƙuyi 2007-2015 a matsayin shugaban ilimi na ƙaramar hukuma (E. S).

    11. Ya yi aiki a Maƙarfi zonal officer (SUBEB)  2015

    12. A yanzu kuma yana aiki a Quality Assurance and Evaluation (QAE)

    Rubuce-rubucensa

    1. Yero Adamu: Harshen Hausa da batun harshen ƙasa, wanda aka wallafa a Gaskiya ta fi kwabo a watan mayu a 1991.

    2. Yero Adamu : Matsayin rubutaccen wasan kwaikwayo a rubutaccen adabin Hausa (ABU Zaria) a watan juni a 1990.

    3. Yero Adamu : Koyo da koyar da Hausa a matsayin harshe na biyu a COE Illorin a 1993.

    4. Yero Adamu : Tashen machukule a matsayin wasan kwaikwayo na musamman a ƙasar Zazzau ( MA Thesic, ABU Zaria)Dec 2014.

    Lambobin yabo da aikin sa-kai

    1. Hunƙuyi District Development Forum a matsayin Sec. Gen a 2007/2009.

    2. National Association of Educational Secretary of Nigeria Kaduna Branch (NAESN) a matsayin Sec. Gen 2008/2015.

    3. National Association of Education Secretary of Nigeria 2012/2015.

    4. Award of excellence as the outstanding Educational Secretary in KDS. Honored by AOPSHON June 2011.

    5. Award of excellence as the outstanding Educational Secretary in Northern Kaduna. Honored by Media monitors Kaduna state may 2012.

    (Mun samu wannan jawabi  ne daga bakinsa a ranar Asabar 12/12/2020 da misalin ƙarfe 10:03 na safe wanda ya turo min da  kansa ta  WhatsApp ɗina).

    Domin karanta cinikin bayi a tarihin Afrika danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Larabci Da Yanda Ya Shigo Ƙasar Hausa

    Larabci Da Yanda Ya Shigo Ƙasar Hausa

    Da yake addinin Musulunci yana tafiya ne ɗanɗan da yaren Larabci ta yadda duk in da aka ga ɗaya to ba shakka ɗayan ma ya na nan in aka yi duba na tsanaki, duk da kuwa cewa shi Larabci bai cika neman rakiyar Musulunci ba in yai aniyar shiga wani lardi. Akwai zantuka mabambanta dangane da shigowar waɗannan tagwaye ƙasashen yammacin Afirka.

    Ustaz Sa’id Galadanci a littafinsa mai suna (حركة اللغة العربية وآدابها في نيجيريا) ya ambaci wasu hanyoyi da masana suka bayyana cewa ta su ne addinin Musulunci da yaren Larabci suka samu shigowa wannan yanki namu na ƙasar Hausan waccen lokacin. Idan muka ajiye batun shigowar Sahabin Annabi (saw) Wasil bin Aɗa(ra) wanda aka ce shi ne ya kawo Musulunci Afirka ta wannan lokacin, ko in ce aka ce da’awarsa ta dangane da wani yanki na lardin, kamar yanda wasu suka ce Libiya ce ƙasar da ya dakata, amma bayan wafatinsa da’awa ta cigaba har ta mamaye yankin gaba ɗaya.

    Duk da cewa ba maganar shigowar addinin Musulunci wannan yanki nake ba, amma babu laifi da na ɗan ci ramaniya na wuce. Ba kamar sauran yankuna da addinin Musulunci ya je musu ta ƙarfi ba, wannan kuma har yankin labarawan mu nan ba a kashe ko daki ko mutum ɗaya da sunan ya yi imani ba, waɗanda suka zo da’awa suka yi ba jahadi ba.

    Mu koma ga batun shigowar larabcin da na faro. Maganar da ta tabbata cikin littattafan tarihin zuwan Larabawa wannan yanki ta nuna cewa lalle Larabci shi ya fara zuwa ƙasar Hausa kafin addinin Musulunci ya shigo, domin kuwa a tarihi akwai waɗanda aka kira da “TUJJARU” da kuma “DU’ATU”.

    Tujjaru waɗansu mutane ne da suka shigo ƙasar Hausa domin kasuwanci, waɗanda su ne baƙuwar Al’umma ta farko da bahaushen wannan yanki ya fara mu’amala da su daga ƙabilun da ke nesa sosai da ƙasar Hausa. Lokacin da waɗannan rukuni suka shigo ƙasar Hausa sun iske al’ummar da ba ta jin yarenta haka su ma ba sa jin nata yaren.

    Manyan abubuwan da waɗannan ‘ƴan kasuwa suke siyarwa su ne dabino da kuma makamai, irinsu masu, takubba da sauransu. An ce lokacin da waɗancan Larabawa suka fara tallata dabinon da suka zo da shi sun fuskanci matsalar saɓanin harshe, wanda kuma shi ne ya ba su haske tun farko kan cewa lalle suna da buƙatar sanin harshen waɗannan al’umma da suka tarar domin sauƙaƙa harkar siye da siyarwa.

    Bahaushen wancan lokacin bai san kalar dabino irin na ƙasashen larabawa ba sai a wannan karo dan haka yana da buƙatar farko ya san menene ma tukunna sannan ya siya idan yana da buƙata. Da larabawa suka fahimci Hausawa suna yi wa wannan haja tasu kallon ko meye wannan?

    Sai suke amfani da kalmar “KUL” wacce a yarensu ta ke nufin “CI” ma’ana dai ya kai wannan da ya ke kallon wannan abu wanda kallon ke nuna kamar bai san menene ba, “CI” ka ji yanda yake, sai aka yi rashin sa’a domin kuwa kalmar “Kul” a yaren Hausa tana nufin “BARI” ko “KAUCE” ma’ana dai kalma ce da take nuni da hani, a can kuma tana nufin umarni, don haka duk mutumin da ya zo zai sayi dabino sai Balarabe ya ce masa “KUL” sai mutum ya kauce ya ba su guri abinsa, wannan shi ne abin da ya fara haɗa waɗannan yaruka mu’amala.

    Su kuma DU’ATU sun shigo ne domin yaɗa addinin Musulunci duk da kuwa an ce waɗancan ‘ƴan kasuwar sun yi abin da suka yi wajen yaɗa Musulunci su ma, musamman yanda waɗanda suka sauke su da waɗanda suka ɗauka yara a kasuwancin da suke suka karɓi Musulunci, amma dai ba kamar yanda DU’ATU suka yi ba, a nan za mu iya cewa DU’ATU su ne kamar missionaries da suka shigo don yaɗa addinin masihiyanci.

    Da yake zan yi magana ne a kan alaƙa ba tarihi ba kai tsaye, amma babu lefi idan na tsagaita haka na kuma tunkari abin da zai fisshe ni na bayyana wannan daɗaɗɗiyar alaƙa ta fuskar yare da al’adu.

    Kamar yanda yake a bayyane cewa Larabci da larabawa sun samu tagomashin girmamawa da soyayya ne kasancewarsu wasu kayan aiki ko alamomi manya da ke nuni kai tsaye ga samuwar addinin Musulunci a duk bigiren da aka ji ko aka gansu. Wannan tasa yaruka da dama kan saki al’adu wani lokacin ma da shi kansa yaren nasu su rungumi Larabci da al’adun Larabawa a tsammaninsu da ƙoƙarinsu na zama yanda Musulunci yake son su zama.

    Misali mu ɗauki yaren Hausa da al’adun Malam Bahaushe, ba na jin a tarihi an taɓa samun wata ba’ajamiyar al’umma da take ganin mutuncin Larabci da Larabawa kamar Hausawa, na san da cewa wasu ma barin yarensu suka yi suka rungumi Larabcin wanda ta kai ga yau babu ɗuriya bare labarinsa. Duk da mu ma ana cewa kaso 60 cikin ɗari na kalmominmu Larabci ne (duk da akwai waɗanda suke ganin adadin bai kai haka ba, kuma sahihin bincike ya gaskata su) wanda hakan ta faru ne sakamakon kasancewarsa harshen ƙetare na farko da Bahaushe ya fara mu’amala da shi.

    Daga cikin tagomashin da Larabci ya samu akwai karɓuwar wasu kalmominsa zuwa yaren Hausa kamar yanda na bayyana da farko wanda mai karatu zai so ya san dalilin da yasa ake ganin kalmomin ba na Hausa ba ne asalaninsu, da kuma yanda ake bi a gano.

    Ga masu karantar kimiyyar harshe akwai hanyoyi da dama da ake iya gane asalin inda kalma ta tsiro, shigowa ta yi ko ‘ƴarsalai ce, daga cikin hanyoyin da ake bi a gano asalin kalmar Larabci a yaren Hausa akwai la’akari da harufan “AL” (ma’arifa) a farkon kalma, ma’ana kusan duk kalmar Hausa da ta fara da “AL” to ana kyautata zaton balarabiyar Kalma ce asalinta, misalinsu su ne:

    1-Alkama – Al-ƙamha
    2-Alkaki – Al-ka’aka’a
    3- Allo – Al-lauhu
    4- Almakashi – Al-miƙsu
    5- Albasa -Albaslu.

    Amma kuma in muka yi duba ya zuwa irin waɗannan kalmomi za mu ga daman yawancinsu kalmomi ne da suke nufin abubuwan da larabawan ne suka fara shigo mana da shi. Don haka bahaushe yake amfani da sigar da ya ji mai su “Balarabe” yana kiransu shi ma yake kiransu da shi.

    Alhamdlilah gwara kalmomi ma daman ana yi domin shi ma larabcin ya aro da dama daga Farisanci, ga wanda yake karantar kimiyyar harshe na Larabci ya san da wannan ƙadiyar. Kuma dama aro ba kashi ba ne ga yare, bilhasli ma duk yaren da ba ya aro to akwai yiwuwar ya mutu.

    Danna nan don karanta zuwan ilimi ƙasar Hausa

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Dakta Ado Zakari Kudan

    Tarihin Dakta Ado Zakari Kudan

    An haifi Dr. Ado Zakari a garin a Kudan a gidan Makaɗa a ranar 30 September 1962 a ƙaramar hukumar Kudan jihar Kaduna.

    Dr. Ado Zakari yana ɗaya daga cikin mutanen da suke bayar da gudunmawar su a cikin jihar Kaduna da kuma ƙasa baki ɗaya, duba da yadda harkar kula da lafiya take da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan-Adam ya sa Dr. Ado Zakari yake zuwa mahaifar sa a duk ranar Asabar, domin duba marasa lafiya kyauta tare da rubuta musu magungunan da za su yi amfani da su domin samun lafiya.

    Karatun sa

    1. Ya yi karatu a Model PrimarySchool 1971-197.

    2. Ya yi karatu a GSS Maiduguri 1977-1982.

    3. Ya yi karatu a school of basic studies ABU Zaria 1982-1983

    4. Ya yi jami’ar Ahmad Bello (ABU) 1983-1989.

    5. Ya yi karatu a ABU teaching hospital 2005-2010.

    Aikin sa

    Yana aiki da ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna, wanda ya riƙe muƙamai da dama a cikin jihar Kaduna kamar haka;

    1. Ya riƙe Medical Officer II 1991-1995.

    2. Ya riƙe Medical officer I 1995-1998.

    3. Ya riƙe Senior Medical Officer II 1998-2001.

    3. Ya riƙe Senior Medical Officer I 2001-2003.

    4. Ya riƙe Principal Medical Officer II 2003-2007.

    5. Ya riƙe Principal Medical Officer 1 2007-2010.

    6. Ya riƙe Chief Medical Officer 2010-yau.

    7. Ya zama Consultant Public Health Physicians 2016- yau.

    (Mun samu wannan bayanin ne daga bakinsa, wanda ya rubuta ya turo min ta WhatsApp a ranar 20/01/2021) .
    Danna nan don Karanta tarihin Malam Mammada Kudan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu