Tag: yadda ake

  • Sunayen Kakannin Annabi Mazaje Da Mataye

    Sunayen Kakannin Annabi Mazaje Da Mataye

    Sunayen kakanin Annabi maza

    1. Abdulmuɗalib.

    2. Hashim.

    3. Abdulmanaf.

    4. Ƙusayyu.

    5. Kilab.

    6. Murrata.

    7. Ka’abu.

    8. Lu’ayyu.

    9. Ghalib.

    10.Fahra.

    11.Malik.

    12.Nadhir.

    13.Kinanata.

    14.Khuzaimata.

    15. Mudhir.

    16. Nazir.

    17. Mu’adu.

    18. Adnan.

    Domin Karanta Koyi Da Annabi SAW Danna nan

    Sunayen kakanin Annabi mata

    1.Fatima ‘yar Amru Almakhazumi.

    2. Salma ‘yar Amru Alnajariyatu khajraz.

    3. Atika ‘yar Murrata.

    4. Hubayyu ‘yar Hulilu Alkhuza`i.

    5. Fatima ‘yar Sa’adu.

    6. Hindatu ‘yar Sariru.

    7. Wahshiyatu ‘yar Shaibana.

    8. Mariyatu ‘yar Ka’abu.

    9. Salma ‘yar Amru alkhuza`i..

    10. Laila ‘yar Sa’adu alkhuza’i.

    11. Jundilatu ‘yar Haris Aljurhum.

    12. Atika ‘yar Adwana Alƙaisul-ilani.

    13. Burratu ‘yar Murra.

    14. Awanatu ‘yar Sa’adu Alƙaisul-ilani.

    15. Salam ‘yar Aslama Alkhudha’atu.

    16. Khundifa.

    17. Rubabi ‘yar jundatu.

    18. Saudatu ‘yar Akka.

    19. Muzanatu ‘yar Jaushimil-aljurhum.

    Danna nan don karanta sunayen jikokin annabi Muhammad SAW

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Sunayen Jikokin Annabi

    Sunayen Jikokin Annabi

    1. Ummul-khulsum daga Nana Fatima.

    2. Alhassan ɗan sayyadina Aliyu daga Nana Fatima.

    3. Alhussain ɗan sayyadina Aliyu daga Nana Fatima.

    4. Abdullahi ɗan sayyadina Usman daga Nana Zainab.

    5. Aliyu ɗan Abul-As ɗan Riba daga Nana Zainab.

    Danna nan don karanta sunayen annabi Muhammad SAW

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

     

  • Menene Motsin Rai?

    Menene Motsin Rai?

    Motsin rai shi ne sanin yanayin da kake ciki ko yanayin da wasu suke ciki (farin ciki ko baƙin ciki) da sanin yanda suke faruwa da iya sarrafa wannan yanayi sannan ka iya mu’amala da mutane, har ma ka iya jan ra’ayin mutane.

    Motsin rai ya kasu kashi hudu, wanda ya haɗa da:

    1. Sanin yanayin kai (na farin ciki ko na baƙin ciki)
    2. Iya sarrafa kai
    3. Sanin yanayin wasu
    4. Iya mu’amala da mutane (a duk yanayin da suke ciki)

    Bayani

    1. Sanin yanayin kai: shi ne sanin yanayin da kake ciki (na farin ciki ko baƙin ciki) da kuma sanin yanda suke faruwa da kuma me ke kawo su.

    Abubuwan da suka haɗa sanin yanayin kai:

    1. Gane yanayin kai: sanin yanayin ka/ki da sanin menene zai iya faruwa idan kana/kina a cikin wannan yanayin.
    2. Auna kanka/ki  a mizani: sanin me zaka/ki iya da iyakokin ka/ki.
    3. Amincewa da kai: sanin darajar kanka da abubuwan da suke dai-dai da kai.

    Muhimmancin mutum ya san yanayin kansa:

    1. Iya zartarwa da kai hukunci a cikin kwanciyar hankali.
    2. Amincewa da kai.
    3. Iya mu’amala da mutane.
    4. Iya riƙe kansu.

    Hanyoyin da za ka bi don iya gane yanayinka

    1. Yawan lura da abubuwan da kake aiwatarwa da kuma yanayin da kake/kike ciki a yayin aiwatarwa.
    2. Yawan kallon kanka idan za ka aiwatar da wani abu.
    3. Tambayi mutane kan yanda ɗabi’unka suke a duk yanayin da kake ciki.
    1. Iya sarrafa kai: shi ne iya amfani da sanin yanayin kai gurin sarrafa yanayin da kake ciki da kuma karkatar da ɗabi’unka a lokacin da ya dace.

    Abubuwan da za ka yi dan iya sarrafa kai

    1. Daina yawan tunanin da bai dace ba.
    • Ka/ki dena haɗe kowa ka soke su da wani abu.
    • Ka/ki dena faɗan abubuwan da ba su kamata ba akan mutane
    • Cire girman kai
    • Yi kokari ka/ki sa mutane nishadi
    • Karkatar da fushinka
    • Sanin yanayin wasu: shi ne kintatar dai-dai irin yanayin da mutane suke ciki (farin ciki ko baƙin ciki), sannan ka san me ke faruwa da su.

    Abubuwan da suke da alaƙa da sanin yanayin wasu:

    1. Zurfafa tunani
    2. Tausayi
    3. Girmama mutane
    4. Yadda da bambancin da ke tsakanin mutane
    1. Iya mu’amala da mutane: shi ne amfani da sanin yanayin kanka da na wasu dan ka riƙe mu’amala da ke tsakaninku ta cigaba.

    Abubuwan da suke da haɗi da iya mu`amala da mutane

    1. Jan ra’ayi
    2. Jagoranci
    3. Sadarwa
    4. Gina mu’amala
    5. Aiki tare
    6. Haɗin gwuiwa
    7. Warware matsaltsalu

    Amfanin ilimin sanin motsin rai mai kyau

    1. Masu ilimin motsin rai mai kyau sun fi samun farin ciki, lafiya da kuma samun nasara a mu’amalarsu da waɗansu.
    2. Masu ilimin motsin rai mai kyau sun fi iya haɗe tsakanin yanayinsu da kuma dalilan faruwarsu.
    3. Masu ilimin motsin rai mai kyau suna sane da irin yanayin da suke ciki a kodayaushe.
    4. Masu ilimin motsin rai mai kyau suna da tausayawa waɗansu.
    5. Masu ilimin motsin rai mai kyau suna da kamun kai.

    Matsalolin da rashin ilimin motsin rai yake haifarwa

    1. Ɗabi’a mara kyau
    2. Rashin iya mu’amala
    3. Rashin ƙwarewa a aiki
    4. Tunani mara kyau. Da dai sauransu

    Yadda ake Sarrafa yanayi na sauran mutane

    1. Yi amfani da salon mu’amala mai ma’ana
    2. Ba da amsa maimakon mayar da martani ga rikici
    3. Yi amfani da basira wurin sauraro
    4. Ɗauki suka ko zagi da sauƙi
    5. Ka tausayawa mutane
    6. Kasance mai kusanci da zamantakewa

    Ilimin motsin rai abu ne mai ƙarfi wanda zai iya haɓaka rayuwarmu ta sirri da ta sana’a sosai. Ta hanyar fahimta da sarrafa motsin zuciyarmu, da kuma ganewa da kuma rinjayar motsin zuciyar wasu, za mu iya gina dangantaka mai ƙarfi, warware rikice-rikice yadda ya kamata, da yanke shawara mafi kyau.

    Danna nan don karanta yanayin duniya kafin aiko da manzon Allah SAW

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Abubuwan Da Suke Haifar Da Mura Wacce Ba Ta Warkewa (Causes Of Chronic Rhinitis)

    Abubuwan Da Suke Haifar Da Mura Wacce Ba Ta Warkewa (Causes Of Chronic Rhinitis)

    Mura ita ake kira “cold” a turance. Ƙwayoyin cutar virus su ne suke haddasa mura. Amma yana da kyau mu fahimci cewa akwai ƙwayoyin cutar virus daban-daban waɗanda suke haddasa mura, wasu suna sanya mura maras tsanani, wasu kuma suna haifar da mura mai tsanani. 

    Misali ƙwayoyin cutar mura su ne: rhinoviruses mai haifar da mura ta yau-da-kullum, corona viruses mai haifar da mura mai tsanani da sarƙewar numfashi, respiratory syncytial virus (RSV) mai haifar da mura ga ƙananan yara, adeno viruses mai haifar da sarƙewar numfashi da ciwon ciki da ciwon ido, entero viruses mai haifar da zazzaɓi, human parainfluenza viruses (HPIV) mai haddasa tsananin zazzaɓi ga yara ƙanana, metapneumo virus mai kama yara ƙanana da manya da kuma haifar da sarƙewar numfashi tare da zazzaɓi.

    Yawanci cututtukan da ƙwayoyin virus suke haddasawa ba su da magani na kai-tsaye. Ma’ana, babu maganin da mutum zai sha domin magance su na din-din-din (complete and permanent cure), sai dai a shawo kansu su lafa ƙwarai ta yadda ba za su iya yin tasirin haifar da rashin lafiya a cikin jikin mutum ba.

    Misali, idan mutum yana da cutar HIV/AIDS, har yanzu ba a gano maganin cutar na din-din-din ba, sai dai a ɗora shi akan magungunan da za su kashe kaifin ƙwayar cutar har ta zamo ba ta da tasirin cutar da shi ko abokan zamansa (antiretroviral therapy).

    Haka nan ƙwayar cutar hanta (hepatitis virus), ba ta fita daga cikin jikin mutum gaba-ɗaya, sai dai ta yi sauƙin da ba za ta iya haifar masa da matsala ba ko kuma abokan zamansa, matuƙar an yi masa allurar riga-kafinta kafin ta kama shi, ko kuma maganinta bayan ta kama shi.

    Ita ma cutar mura haka take, lafawa yake yi, ma’ana magungunan mura ba su kashe ƙwayar cutar mura kwata-kwata. Abinda suke yi shi ne su magance alamomin da mura take zuwa da su (symptomatic treatment or supportive care). A nan ina nufin abubuwan da magungunan mura suke warkarwa su ne ciwon kai, toshewar hanci, zazzaɓi, tari, ciwon ido, da sauransu.

    Amma ba ƙwayar cutar virus ta mura suke magancewa ba. Kuma ƙwayoyin cutar virus na mura sun fi hayayyafa a lokacin da mutum yake yin zirga-zirga, amma da zarar ya kwanta wuri daya, to, za su rage hayayyafa. Wannan shi ne babban dalilin da yasa yawanci magungunan mura suke ƙunshe da sinadaran kashe jiki ne (sedative agents), kamar diphenhydramine ko chlorpheniramine.

    Sa’annan, abin lura shi ne, a lokacin da mutum ya kasance yana fama da mura na tsawon lokaci ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, to, abubuwan da za su iya haddasa hakan su ne:

    1. Kamuwa da ciwon mura mai tsanani (chronic rhinitis) ko kuma cututtukan bututun hanci (nasal passages issues).

    2. Kamuwa da cutar asma (asthmatic attack) ko bijirewar hanci sakamakon yin mu’amala da wasu abubuwa da suke jawo mura akai-akai (allergies), kamar mu’amala da ruwan sanyi, ko ƙanƙara, ko iska, ko ƙura, ko hayaƙi, ko turare, ko yaji, da sauransu.

    3. Matsalar raunin garkuwar jiki (weak immune system) sakamakon kamuwa da wasu cututtuka na daban, wanda hakan yake sanya garkuwar jiki ta kasa dakushe kaifin ƙwayar cutar mura.

    Saboda haka, idan mutum ya ga yana fama da cutar mura, kuma ya ga duk maganin da ya sha ba ya warkewa na dogon lokaci sai murar ta dawo, to, sai ya lura da abubuwan da yake yin mu’amala da su yau-da-kullum. Idan ya gane abinda yake haddasa masa murar, to, sai ya daina yin mu’amalar da su. Kenan mutum ba ya buƙatar yin amfani da wani magani.

    Idan kuwa bai gane ba, to, yana da kyau ya je asibiti domin ganin ƙwararren likitan kunne da hanci da makogoro (Otolaryngologist), saboda ya yi masa gwaje-gwaje ya tabbatar da abinda yake faruwa da shi.

    Danna nan don karanta Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction)

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Marigayi Malam Mammada Kudan

    Tarihin Marigayi Malam Mammada Kudan

    Marigayi malam Mammada (wato Muhammad wanda aka fi sani da malam Mammada) an haife shi a garin Kudan a watan Azimi. Sunan mahaifinsa shi ne Malam Abdulhamid, mahaifiyar sa kuma Habiba (‘Yar gero), ya haifi ‘ya’ya goma sha shida a duniya, guda shida sun rasu kafin ya rasu.

    Ya auri mataye guda biyu daga cikin ‘ya’yan sa akwai Muhammad da Suleman da Ɗayyabu da Hafsat da dai sauran su. Ya yi karatun allo a garin Kudan da kuma Zaria gidan malam na Iya. Ya kuma tafi Kano ya yi karatu a wajen malamai da dama, ya kuma tafi Azare ta jihar Bauchi, ya yi karatu a can ma.

    Malam Mammada mutum ne wanda yake sana’ar siyar da garwa daga Kudan zuwa Kano, domin samun abin sa wa a baka wai ya fi a rataya in ji masu iya magana. Saboda haka malam Mammada ya samu ilimi mai zurfi a ɓangaren ilimi addinin musulunci, wanda har Alaramma malam Surajo Yunusa Kudan, wanda ya rubuta littafi akan rabon gado a wajensa ya yi  karatu.

    Haka kuma shi ne kusan babban ɗalibin sa, saboda duk inda zai tafi wajen koyar da karatu ko rabon gado, to da malam Surajo Yunusa Kudan yake tafiya. Haka kuma a lokacin da yake raye malam Mammada har sai ta kai matakin da dukkanin  littafin da mutum ya buɗe, to malam Mammada yana kishingiɗe zai biya maka littafin ba tare da ya tambaye ka sunan littafin ba.

    Haka kuma, idan mutum ya yi kuskure wajen karantowa, to sai dai ka ji kawai ya gyara ma yadda wajen yake, haka kuma Malam Shitu Bashir Kudan ya tabbatar mana da cewa idan mutum kullum zai dinga zuwa wajen malam Mammada karatu har tsawon  rayuwar sa, to ba zai iya ƙure ilimin da Allah ya ba shi ba, sannann kuma shi ne wanda yake fassara alkur’ani a masallacin juma’a na garin Kudan a lokacin da yake raye, haka kuma ya rasu a watan Azimi a ranar 16/09/1440 hijira=2018

    (Mun samu waɗannan jawaban ne ta hannun ɗan sa wato Suleman Muhammad wanda ya kira a waya ranar litinin 17/03/1442 hijira=02/11/2020 da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe a lokacin ina gidan Musa Gauda shi kuma yana Kaduna).

    Domin karanta cinikin bayi a tarihin Afrika  danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa 2

    Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa 2

    Aure wani zama ne halastacce tsakanin mace da namiji bisa ga matsayin miji da mata, wanda al’adar Bahaushe da kuma addinin musulunci suka amince da shi. Babban dalilin da yasa ake yin aure shi ne, don samun yaɗuwar jinsi a doron ƙasa gami da wanzuwar al’umma. Aure ba ya inganta sai da waliyyi (mace waliyyi, namiji kuma wakili), siga, sadaki da kuma shaidu.

    Abubuwan da suke da alaƙa da aure a ƙasar Hausa

    1. Samartaka (Zance ko hira).

    2. Sallama/ nuna kai.

    3. Toshi.

    4. Baiko / sa rana.

    5. Sa lalle/ rufi.

    6. Ɗaurin aure.

    7. Wankan amarya.

    8. Biki (gidan su amarya da ango).

    9. Biɗar kai/ buɗan kai.

    10. Sayen baki.

    11. Kai Gara.

    12. Gai-da surukai.

    13. ‘Yar zaman ɗaki/ ƙanwar rana.

    Danna nan don karanta rabe-raben auren Hausawa

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Hajiya Halima Jumare Kudan

    Tarihin Hajiya Halima Jumare Kudan

    An haifi Hajiya Halima Jumare a garin Kudan, ƙaramar hukumar Kudan, jihar Kaduna a ranar 11th Afrilu a shekara ta 1964, ta yi karatu a Girls’ Boarding Firamare School, Zaria a shekara ta 1976, ta yi karatu a Women Teachers’ College, Kaduna (GR.II) a shekara ta 1981, ta yi a karatu a College of Education, Kafanchan (NCE) a shekara ta 1985, ta yi karatu a Ahmadu Bello University, Zaria (B.ED) a shekara ta 1990, ta yi karatu a Ahmadu Bello University, Zaria (PGDM) a shekara ta 2001, ta yi karatu a Ahmadu Bello University, Zaria (MBA) a shekara ta 2005.

    Guraren Da Ta Yi Aiki

    1. 1985-1990 ta yi aiki a Government Science Secondary School, Ikara a matsayin malamar aji (Class room teacher), a ƙaramar hukumar Ikara, jihar Kaduna.

    2. 1991-1993 ta yi aiki a GGSS Maraban Kubau, a matsayin mataimakiyar shubaga (Vice Principal), ƙaramar hukumar Kubau, Jihar Kaduna.

    3. 1993-1997 ta riƙe Senior Education Officer, ƙaramar hukumar Maƙarfi, Jihar Kaduna.

    4. 1997-2007 ta riƙe Education Secretary, ƙaramar hukumar Kudan, Jihar Kaduna.

    5. 2007-2008 ta riƙe Assistant Director, School Services, SUBEB, Jihar Kaduna.

    6. 2008-2015 ta riƙe Deputy Director, School Services, SUBEB, Jihar Kaduna.

    7. 2015-2018 ta riƙe Director, School Services, SUBEB, Jihar Kaduna.

    8. 2018- Yau tana riƙe da Quality Assurance Evaluation (KAE) ta Jihar Kaduna.

    Lambobin Yabo

    Ta samu lambobin yabo a gurare da dama, sakamakon yanayin ƙwazon aikin ta, wajen hidimtawa mutane a gurare daban-daban kamar haka;

    1. 1997/1998 ta samu takardar karramawa daga ma’aikatar ilimi da kuma ci gaban matasa (Ministry of Education and Youth Development) ta Jihar Kaduna.

    2. 1997/1998 – ta samu takardar karramawa daga LGEA UNICEF Assisted Model Primary School, Kudan, ƙaramar hukumar Kudan.

    3. 1999 ta samu takardar karramawa daga Jihar Kaduna Firamare Education Board on the judicious utilization of funds, Schools Development and Improvement, effective management of staff.

    4. 1999 ta samu takardar karramawa daga ƙaramar hukumar Kudan.

    5. 1999 ta samu takardar karramawa daga Kudan Development Association, Kaduna Chapter.

    6. 2000 ta samu takardar karramawa daga Farin Wata Youth and Drama Organization T/Wada, jihar Kaduna.

    7. 2001 ta samu takardar karramawa a matsayin jajirtacciyar magatakardar ilimi ta ƙaramar hukuma ta uku (3rd Best Education Secretary) daga ma’aikatar ilimin farkon na Jihar Kaduna.

    8. 2001 ta samu takardar karramawa daga NYSC Area Inspector, Kudan Local Government.

    9. 2004 ta samu takardar karramawa daga ma’aikatar ilimi da LGEA Firamare School, Sabon Garin Hunƙuyi, ƙaramar hukumar Kudan.

    10. 2004 ta samu takardar karramawa daga LGEA Firamare School, Nasarawan Kudan, ƙaramar hukumar Kudan.

    11. 2004 ta samu takardar karramawa daga LGEA Central Firamare School, Likoro, ƙaramar hukumar Kudan.

    12. 2004 ta samu takardar karramawa daga LGEA Firamare School, Yakubu ƙaramar hukumar Kudan .

    13. 2004 ta samu takardar karramawa daga Hunƙuyi Education Development Committee, ƙaramar hukumar Kudan.

    14. 2007 ta samu takardar karramawa daga Kaduna COPHON Award for Education Secretaries.

    15. 2009 ta samu takardar karramawa daga ƙungiyar ɗalibai ta Ikara Students Association, Bayero University, Kano.

    Danna nan don karanta ƙa’idoji goma sha ɗaya na samun nasara a rayuwa.

    16. ta samu takardar karramawa daga LGEA Firamare School, Hunquyi, ƙaramar hukumar Kudan.

    17. Ta samu takardar karramawa daga Ashiru Memorial Qur’anic Recitation Competition, ƙaramar hukumar Kudan.

    18. 2018 ta samu takardar karramawa daga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i for our involvement in the development of the education sector in Jahar Kaduna.

    19. 2018 ta samu takardar karramawa daga Taskira Newspaper for the most outstanding service to humanity.

    20. 2018 ta samu takardar karramawa daga UK AID (Teacher Development Programme) in recognition for an outstanding performance in implementing the in-service Reforms in Jihar Kaduna.

    21. 2019 ta samu takardar karramawa daga Model Primary School Hunƙuyi in recognition of an outstanding contribution towards the development of the school.

    Tarurrukan da ta halarta

    1.Ta halarci taron ƙarawa juna sani na shekara-shekara (Annual Conference) na ƙaramar hukuma wanda Education Secretaries of Nigeria suke shiryawa a 1998 zuwa 2007.

    2. Ta halarci taron ƙarawa juna sani akan Effective Management of Firamare Schools a jihar Kaduna wanda Firamare Education Board suka shirya a 19th-20th December, 1994.

    3. Ta halarci taron ƙarawa juna sani akan ” Enhancing Productivity and School Personnel for the Success of UBE Programme” organized by Guidance and Counseling with Educational Administration and Planning Sector Department of Education, ABU, Zaria. 20th October, 2000.

    4. Ta halarci taron ƙarawa juna sani na tsakiyar shekara(Biennial Conference) na ƙungiyar National Association of local government Education Secretaries of Nigeria wanda aka yi a jami’ar Jos, jihar Plateau a 20th-25th December 2000.

    5. Ta halarci taron ƙarawa juna sani na ƙungiyar National Association of Educational Planners and Managers (NAEPM) Congress Conference on Planning and Management of Education in Nigeria; A key success to sustainable development: takardar da aka gabatar da ita akan “Management of Universal Basic Education Programme Towards Effective Goals Management” wanda aka yi a tsakanin 12th-14th October, 2004 a jami’ar ABU, Zaria.

    6. Ta halarci taron ƙarawa juna sani, wanda aka yi akan “Capacity building training on Effective School Management”, Classroom Assessment in 2011.

    7. Ta halarci taron ƙarawa juna sani, wanda aka yi akan “Due Process of Financial and Administrative Management of SUBEB and LGEA’s” wanda a Hamdala hotal da ke jihar Kaduna a tsakanin 27th-28th April, 2006.

    8. Ta halarci taron ƙarawa juna sani, wanda aka yi akan “Planning and Management of Basic Education” wanda aka yi a Jahar Kaduna ƙarƙashin ƙungiyar “State Education Sector Project (SESP)” an Intervention by the department for International Development (DFID) United Kingdom in 2000-2011.

    9. Ta halarci taron “Joint Consultative Committee on Education (JCCE)” wanda aka yi a Lokoja, jahar Kogi a 2011.

    10. Ta halarci taron ƙarawa juna sani na sati uku (three week) wanda aka yi akan “Strategic Management for Senior Managers” an yi taron ne a Cape Town, a cikin kudancin Africa, 14th March zuwa 1st April 2011. Ƙarƙashin “Ministry of Education”da kuma kulawar “State Sector Education Programme [SESP]”.

    11. Ta halarci taron ƙarawa juna sani, wanda aka yi akan “New Methods Mathematics, Nigerian Firamare English, Basic Science and Basic Social Studies” wanda ƙungiyar Learn Africa PLC ta shirya, an yi taron ne a Multi-purpose hall da ke Kaduna a ranar 12th June, 2012.

    12. Ta halarci taron ƙarawa juna sani akan ”Planning and Management of Basic Education in Kaduna”ƙarƙashin “Education State Sector Project in Nigeria (ESSPIN)” tare da ƙungiyar “United Kingdom, department for International Development (DFID)”.

    13.Ta halarci taron “Heart of Europe Schools Debate Competition” wanda aka yi a Olumouc, a cikin ƙasar Czech a June, 2016.

    14. Ta halarci taron “Management Development Services Ltd” wanda aka yi akan “Result –Driven Total Project Management, an yi taron ne a tsakanin Monday 5th to Friday, 9th December, 2016.

    15. Ta halarci taron “Executive Leadership and Management of Senior Civil Servants working in Girls Education Programming in Northern GPE” ƙarƙashin ƙungiyar “National Institute of Policy and Strategic Studies, Kuru (NIPSS)”a tsakanin 19th – 21st December, 2016.

    16. Ta halarci taron ƙarawa juna sani na ɗalibai maza da mata yara akan “Child Education Programmes”wanda aka yi a Tafawa Ɓalewa hotal a cikin ɗaki na goma sha bakwai, a jihar Kaduna a ranar 10th 11th March, 2017.

    17. Ta halarci taron ƙarawa juna sani akan “Tsangaya Education Programme” wanda aka yi a ranar 24th – 25th March, 2017 wanda aka yi a Tafawa Ɓalewa hotal a cikin ɗaki na goma sha bakwai, a jihar Kaduna .

    18. Ta halarci taron “Stakeholders Meeting on Recruitment and Deployment of Effective Teachers in the Firamare Schools”wanda aka yi a ranar 5th-6th of April, 2017 a Tahir Guest Palace, Kano.

    19. Ta halarci taron “training of the trainer (TOT) capacity building workshop on implementation of professional standards for Nigerian Teachers” na ƙungiyar “Teachers’ Registration Council of Nigeria” daga 12th-15th June, 2017 a U.l Conference Centre; a cikin U.l Hotel, lbadan, jihar Oyo.

    20. Ta halarci taron “Heart of Europe International Debating Tournament” wanda aka yi a July, 2017 a Olomouc, a ƙasar Czech, an yi taron ne a ranar 12th-19th July, 2017.

    22. Ta halarci taron ƙarawa juna sani na shekara-shekara “National Council on Education (NCE)” a July, 2017.

    23. Ta halarci taron “Training on Result-Driven Monitoring and Evaluation for optional Performance of Educational Projects” wanda aka yi a Silver Sand hotel, Katuru Road, Kaduna 7th-11thAugust, 2017.

    24.Ta halarci taron “Teaching of Literacy and Numeracy, Leadership Skills to Head teachers in Jihar Kaduna” wanda ƙungiyar ESSPIN and TDP suka shirya daga 2012-2018.

    25. Ta halarci taron “Computer Training on Human Resource Approval at Federal Polytechnic, Kaduna” ƙarƙashin kulawar gwamnatin Jihar Kaduna.

    26. Ta halarci taron “Trainings on the Teaching of Jolly Phonics to Firamare School Teachers”.

    Ayyuka na musamman 

    1. Ta zama Member – Committee on Teacher Competency Test for Kaduna State teachers;

    2. Ta zama Member – Committee on Teacher Competency Test In Kaduna L.G.A;

    3. Ta zama Member – Teacher Development Programme (ESSPIN/TDP)

    4. Ta zama Member -Teacher Registration Council (TRCN)

    5.Ta zama Component Lead -Teacher Professional Development (TPD) under the Grand Partnership in Education/Nigeria partnership in Education Programme (GPE/NIPEP). STRENGTH:Prudent management of resources, Commitment to the service for good result and respect for constituted authority.

    (Mun samu waɗannan jawabai ne daga bakin Hajiya Halima Jumare wanda ta turo min ranar bakwai ga watan yuni 2020 ta imel ɗi na).

    Domin Karanta tarihin hakimin Kudan danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

     

  • Rabe-Raben Zawarawa

    Rabe-Raben Zawarawa

    Bisa ga al’adar Bahaushe, ya yi duba na tsanaki gami da dogon nazari, don rarrabe ire-iren zawarawa, kamar haka;

    1. Bazawara (Tsohon hannu).

    2. Ta-ƙi zama.

    3. Sakin wawa.

    4. Shirinya raɓi ki kashe.

    5. Zari-wuya.

    6. Ƙafar wala.

    7. Goɗiya ta siddi.

    Don karanta rabe-raben gara danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Rabe-Raben Auren Hausawa

    Rabe-Raben Auren Hausawa

    Auren Hausawa ya rabu gida-gida kamar haka:

    1. Auren kuɗi.

    2. Auren sadaka.

    3. Auren zumunci.

    4. Auren dole.

    5. Auren ɗauki sandar ko takalmin ka.

    6. Auren jeka da kwarinka.

    7. Auren ɗaukar buta.

    8. Auren kashe wuta.

    9. Auren huce takaici.

    10. Auren ɓuyan wata.

    11. Auren kangara.

    12. Auren Jari.

    Don karanta matsalolin mace-macen aure danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Ma’anar Gara Da Rabe-Rabenta

    Ma’anar Gara Da Rabe-Rabenta

    Wata kyauta ce, wacce iyayen amarya ko mai jego suke kai wa ‘yarsu, don amfanin yau da kullum. Wato wasu kayayyaki ne, wanda iyaye mata suke kai wa ‘yarsu bayan an watse daga biki, ko kuma idan mace ta haihu, sai a kai mata kayan da za ta sanyawa jariri kafin ranar suna, shi ne ake kira “kayan agwaja”, idan kuma bayan suna ne, to ana kiransu da suna “kayan gara ne”.

    Rabe-raben Gara 

    Bisa ga al’adar Bahaushe, yana da gara iri bakwai, kuma kowacce da dalilin yin ta. Misalin;

    1. Garar amarya:   Dalilin yin aure.

    2. Uwa ta waiga:   Bayan an kai garar farko ta aure.

    3. Garar kayan salla: Dalilin bikin salla.

    4. Garar haihuwa: Dalilin haihuwar mace (ita kuma wannan ta kasu gida biyu, akwai wacce ake kai ta kafin a yi suna da kuma wacce ake kai ta bayan an yi kwanaki arba’in da haihuwa).

    5. Garar yaye: Dalilin yaye abin da aka haifa.

    6. Garar Kaciya: Dalilin yi wa yaro kaciya, wanda mafi yawanci kakanni suke yankawa ɗan-kaciya kaji, don rage masa raɗaɗin kaciya.

    7. Ka-fi-mai-kora: Dalilin yi wa mace kishiya.

    Danna nan don karanta Aure a ƙasar Hausa

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu