Tag: yadda ake

  • Waƙar Baƙar Rama (Ta Haruna Uji)

    Waƙar Baƙar Rama (Ta Haruna Uji)

    Wanda ya yi ma masoyiyar Khadija, wacce aka fi sani da suna “Dije. A inda ya kamanta ta da suna “baƙar rama”. Saboda ita rama, tana da farin jini sosai a wajen Bahaushe. Ga baitin waƙar nan kamar haka;

    Ibrahim Sheme
    Home Columns Online Musings
    Waƙar ‘Baƙar Rama’ ta Haruna Uji
    By IBRAHIM SHEME July 24, 2018

    Haruna Uji ya na kaɗa gurmin sa
    Na rubuta wannan waƙar daga wani faifai na Alhaji Haruna Uji a ranar 21 ga Mayu, 2015. A lura da cewar da yake Uji ya rera wannan waƙar a lokuta daban-daban, mai yiwuwa ne ka ji wani samfur na waƙar wanda ya bambanta da wannan da na rubuto.

    Waƙar “Baƙar Rama” dai Haruna Uji ya yi wa matar sa Tasalla ne, don nuna shauƙin soyayya da ke tsakanin su. Bismilla:

    Ruwa isa gayya, Baƙar Rama,
    Ruwa isa gayya, ya ki!
    Allah Sarki, Baƙar Rama,
    Ke ‘yar masara mai yawan zani,
    Sannu da rana, Tasalla!

    Na kaɗa gangar Baƙar Rama
    Wa’yansu mutane suna faɗi: “Baƙar Rama ko ba mutum ba ce?!”
    Na ce musu, “A’a, ku bar faɗi, Bakar Rama amma mutum ta ke.”

    Ai sai suka ce min: “Haru Uji, Baƙar Rama in dai mutum ta ke,
    Ka yi mana taɗin Baƙar Rama.”
    Sai na ce “Na yarda!”

    Sai ku matso zan gaya muku,
    Na farko zancen Baƙar Rama,
    Mai son ‘yar nan Baƙar Rama,
    In gan shi ga kogo kamar guza kamar gansheƙa, ya ja ciki,
    Ta ce ba ta so, ba za ta ba.

    Ina mai son ki?
    In kai shi ga kogi,
    Iy yi nutso ya ɗebo yashi,
    Sai ya ƙirge yashi,
    Baƙar Rama ta ce ba ta so, ba za ta ba!

    In ya haɗa wannan,
    In kai shiga rairai ya tandara,
    Ta ce ba ta so!
    Ya hau kan rimi,
    Sai ya kere rimi, ya faɗi da ƙirji,
    Baƙar Rama ta ce ba ta so, ba za ta ba!

    Mai son ‘yar nan Baƙar Rama,
    Ya zabura sosai,
    Ya je dawa ya samu giginya,
    Ya hau giginya da baya,
    Baƙar Rama ta ce ba ta so!

    In ya haɗa wannan,
    Ya zauna ya yi mata kukan wata bakwai da kwana hamsin,
    Sai ta ce ba ta so, ba za ta ba. Allah Sarki, Baƙar Rama!

    Danna nan don karanta waƙar ban mutu ba ta Fati Niger

    Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu

  • Tsafi (Metaphysics)

    Tsafi (Metaphysics)

    Tsafi shi ne haɗa waɗansu ‘yan dabaru (siddabaru), domin cutar da wani mutum ko dabba ta haramtacciyar hanya. Karatun tsafi yana ɓangaren “Metaphysics” a Falsafa. Ya wuce ilimin kimiyya (Science), domin shi yana karatun bayan ɗabi’a ne (Beyond the nature), sannan ita kuma kimiyya na karantar halaye ne (nature). Saboda haka, ilimin kimiyya zai gaya maka ilimin halaye, sai shi kuma “Metaphysics”ya gaya maka dalilin da yasa ake iya haɗa siddabaru (tsafi).

    Ita kuma kimiyya za ta gaya maka daga Baba sai Mama, amma shi “Metaphysics” yana binciken meye dalilin da yasa daga Baba sai Mama. Don haka kimiyya ba za ta iya karantar da tsafi ba, don haka ta gindaya shi a cikin “Pseudoscience”, domin tabbatar da ilimin tsafi sai a “Philosophy”.

    Har ila yau, shi ilimin tsafi, daɗaɗɗen ilimi ne, wanda a tarihin Ɗan-dam da ya samu ci gaba a shekaru dubbai da suka wuce. Mutanen Syria, Egypt, Babylons, Nabataens da Chaldaens su ne suka samu ci gaba a ɓangaren wannan sana’a. Bayan zuwan musulunci an samu waɗansu daga malamai da suka karanci sihiri da tsafi, don su san haƙiƙarsa ta fannin kariya, don  sanin sharri ba don a aikata sharri ba.

    Jabir bn Hayyan, wanda babba ne a cikin masana kimiyya (Alchemy), ya karanci tsafi har sai da aka riƙa kiransa da “Chief sorcerer of Islam”. Sannan a Spain an samu irinsu Maslama bn Ahmad Almajiristi da har littafi ya rubuta akan tsafi mai suna “Ghayah” wanda yake tattare da abubuwan mamaki ƙwarai da gaske!

    Aikata tsafi haramun ne a addinin musulunci, saboda cutarwar da yake wa mutane kuma ilimi ne da ya  dogara ga wanin Allah a zahiri. Matsafa suna fara iya tasarrufi da ruhinsu kafin su aikata duk abin da suke so. Wanda zai yi tsafi, yana buƙatar ya zama mai iya juya ruhinsa (soul) ta yadda jikinsa ba zai yi tasiri ba a lokacin da yake aikata tsafin.

    Tamkar mutumin da yake hawa dogayen gida ne (skyscrapers), idan yana so ya yi gudu ya tsallaka daga wannan gidan zuwa wancan mai tsawon gaske, to dole sai ya cire tsoron da yake ransa kafin ya tsallaka. Rashin haka zai iya sanyawa ya yi karkarwa ya faɗo. Kamar wanda yake tafiya a tsaye akan igiyar da aka ɗaure tsakanin dogayen gini biyu.

    Idan mutum ya ji tsoro a lokacin da yake tafiya akan igiyar, to shi kenan sai ya yi karkarwa ya faɗo, amma idan bai ji tsoro ba, to zai iya tasarrufi da jikinsa ya ci gaba da tafiya bai faɗo ba. Irin wannan hanyar ita take sanyawa matsafa suna iya tasarrufi da jikinsu ta hanyar sarrafa ruhinsu gurin faruwar waɗansu abubuwan na ban mamaki. Idan mutum ya ƙware wajen iya tasarrufi da ruhinsa, to a nan zai iya tasarrufi da abubuwa da yawa a cikin halaye.

    Masu aikata “sorcery” ba su fiye amfani da wani abu wajen yin tsafinsu ba. Ga wanda ya kalli film ɗin “Marlin” wanda yake iya tasarrufi da idonsa wajen tsafi, to wannan shi ne “sorcery”. Masu “witchcraft” su ne bokaye da suke amfani da waɗansu abubuwan na itatuwa ko dabbobi da suke ganin alaƙarsu wajen aikata wani lamari da ruhinsu a lokacin da suke tsafin.

    Irin waɗannan su ne masu cewa a kawo itace kaza ko farar tsuntsuwa wajen aikata wani lamari. Akwai wani littafi, wanda wani mai tsafi, mai ban tsoro da ya ce a jiƙa gawar mutum da man riɗi har tsawon kwana 40 a riƙa yagar naman da ya ragargaje ana ci a lokacin da ake tasarrufi da ruhi, to ta nan mai tsafin duk abin da ya faɗa ya ce zai faru to a kaso 100 za a samu 80 ya faru! Irin waɗannan matsafan malaman musulunci suka ce a kashe su. Saboda hakan ya saɓa da shari’ar musulunci.

    Bambancin mai tsafi da mai mu’ujiza ko karama shi ne, shi mai mu’ujiza ko mai karama an san shi da kyawawan halaye (ethics), kuma har lokacin da yake aikata mu’ujizar ko karamar bai daina aikata kyawawan halayen ba. Shi kuma mai tsafi an san shi da munanan ayyuka da kuma aikata waɗansu abubuwan da ake ganin nutsattsen mutum ba zai aikata ba, domin har kisa suna yi akan hanyar tsafinsu.

    Abinda yasa waɗansu daga masana tsafi suke yarda da Annabawa shi ne gane cewar hanyar tsafi daban da ta Annabta. Wannan shi ne yasa matsafa suka yarda da Annabi Musa, saboda sun gane cewa hanyarsa daban da tasu. Abin da yasa ingantattun mu’ujizozin Annabi Muhammad (S.A.W) ba su zamo tsafi ba saboda larabawa sun riga sun san shi da kyawawan halaye har suka riƙa kiransa da sunan  “Amintacce”.

    Domin karanta yunƙurin Hausantar da kimiyya danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Marigayi Alaramma Suraj Yunus Kudan

    Tarihin Marigayi Alaramma Suraj Yunus Kudan

    An haifi  Alaramma Surajo Yunusa a ranar 07/03/1966 a garin Kudan, cikin ƙaramar Hukumar Kudan, Jihar Kaduna, Nigeria. Sunan Mahifiyarsa Maimuna, sunan mahaifinsa Liman Yunusa. Ya rasu a ranar Alhmamis 06/04/2017 dai-dai da 9/7/1438 A.H.

    Kuma ya bar mata biyu, ya bar ‘ya’ya’ guda goma sha biyu (12), Maza bakwai (7) da Mata biyar (5). Allah Ubangiji ya amince masa ilimai, musamman wajen warware sarƙaƙiya ta ɓangaren rabon gado, wanda har sai da ya yi shura tun daga ƙaramar hukumar Kudan har zuwa Zaria akan wannan fannin da sauransu.

    Karatun Addinin / Litattafai

    A ranar Litinin 06/02/1984 dai-dai 5/5/1404 ya fara rubutun Alƙur’ani. Ranar Laraba 9/09/1984 dai-dai 24/12/1404 ya kammala rubuta Alƙur’ani. Ranar 11/12/1986 ya kai Alƙur’ani gida, Kudan. Ranar Litinin 19/09/1984 dai-dai 24/12/1404 ya fara karatu wajen Malam Musa Ƙofar Nasarawa jihar Kano.

    A ranar Laraba 24/4/1991 dai-dai 11/10/1411 ya fara karatu da Malam Lawal Jinjin. Ranar 06/05/1991 dai-dai 23/10/141, ya fara karatu da Malam Mammada gidan malamai Kudan. Ranar 12/08/1991 dai-dai 2/2/1412 aka ɗauke shi aikin koyarwa a Model Primary School, Kudan. Ya tafi aikin Hajji a ranar Lahadi 15/11/2009 dai-dai 27/11/1430.

    Ya dawo ranar Alhamis 10/8/2012. Ya jagoranci sallar juma’a na riƙo na tsawon sati shida a rayuwarsa. Ya fara a ranar 10/08/2012. Sannan kuma ranar litinin aka ba shi muƙamin (S.A.S) a ƙaramar hukumar Kudan, wato Senior Arabic Supervisor (Shugaban Malaman Arabiya Na ƙaramar Hukumar Kudan).

    Karatun Zamani

    Ya halarci makarantu kamar haka;

    1. Model Primary School Kudan, Kaduna (Sep, 1973 – June, 1978).

    2. School For Arabic Studies, Kano (S.A.S) (1983 – 1989).

    3. Institute of Education, Ahmadu Bello University Zaria, Nigeria (1985 -1989).

    4. Jama’atu Institute of Arabic & Islamic Education, Zaria (2000 – 2002).

    5. Institute of Education, Ahmadu Bello University Zaria, Nigeria (2000/2002 Session). Allah Ya amshi rayuwarsa a ranar Alhamis 06/04/2017 = 9/7/1438 A.H, Allah Ya gafarta masa zunubansa, Amin.

    Don karanta al’adar Bahaushe danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Marigayiya Hajiya Gude Mai Magani

    Tarihin Marigayiya Hajiya Gude Mai Magani

    An haifi hajiya Gude mai magani a Ƙofar Arewa gidan malam Tanko, ta yi aure a gidan malam Tanko, wanda aka yi haɗin zumunci da Yusha’u (wakili), hajiya Gude ta shahara wajen bayar da magani kowace cuta, wanda sai mutum ya tafi asibiti sun kasa sai a turo mutum wajen ta wanda da yardar Allah kuma sai ka ga an samu nasara.

    Hajiya Gude tana aiki ne da aljanu wajen warkar da mutane cutar da take damunsu, wanda hakan kuma ya faru ne  bayan an ɗaura mata aure, wata rana tana daka da rana, sai kawai aka ga ta tsaya ƙyam tana  lallauyewa,  tana yin ƙasa, tana faɗuwa ƙasa sai kawai aka ga ta kasa tafiya, to tun daga ranar ƙafar ta ba ta sake miƙewa dai-dai ba har sai da ta rasu.

    Idan an kai mace asibiti ɓangaran haihuwa, sai likitoci suka yi iya bakin ƙoƙarin su, amma kuma ba a samu nasara ba, sai a turo mace wajen ta, to da zarar ta dafa kan mace,  ta yi waɗansu addu’o’i haɗi da ba mace rubutu, sai kawai can sai a ga mace ta haihu lafiya. Haka kuma, idan mace ma tana da ciki suna zuwa wajenta domin karɓan magani.

    Don karanta tarihin ranar demokraɗiyya a Najeriya danna nan

    Bugu da ƙari kuma, akwai wani aljani wanda yake zuwa kanta wanda ake kiransa da suna “Ɗan malam”, wanda shi ne yake zuwa kanta duk ranar Laraba, wanda mutane da dama suna jin daɗin aikin ta, sannan  kuma idan mutum kayansa ya ɓace ko yana yin sata  ko dai wani abu mara kyau, to da zarar an kai mutum wajenta akan samu mafita.

    Har ila yau, idan ta gama aikin, to kuɗin da ta samu a wannan ranar takan ɗauka ta raba wa yara, haka kuma akwai wani mutum ana kiransa da suna Magaji yana ɗaya daga cikin mutanen da suke yi mata rubutun sha, wanda take ɗebowa ta ba mara sa lafiya idan ta yi musu aiki.

    Hajiya Gude mai magani ta shahara wajen bayar da magun-gunan gargajiya wajen warkar da marasa lafiya akan cututtaka daban-daban kamar su cutar Aljanu da cutar jiki (Ciwon kai, ciwon ciki, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon ƙirji, rashin haihuwa da kuma maganin naƙuda), ta rasu a shekara ta 2012 ta bar ‘ya’ya guda huɗu daga ciknsu akwai Maryam (Dogara) da Abdullahi da Mustapha (muɗɗafa) da kuma Balaraba.

    Danna nan don karanta maganin damuwa

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Hassana Abdullahi Hunƙuyi

    Tarihin Hassana Abdullahi Hunƙuyi

    An haifi Hassana Abdullahi a garin Hunƙuyi a shekarar 1980. Tana zaune da maigidanta da yaransu a garin Hunƙuyi, Ƙaramar hukumar Kudan, jihar kaduna.

    Ta yi karatun firamare, a central firamare school Hunƙuyi, daga nan sai ta wuce makarantar kwana ta ‘yammata da ke Kaduna (G.G.S.S KAWO KADUNA). Tana da takardar shaidar malanta ta (NCE). Inda take aiki da sashin ilimi na ƙaramar hukumar Kudan. Tana riƙe da muƙamin (Head mistress) shugabar malamai.

    Haka kuma ɗaliba ce a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Inda take karatun digiri ɗinta a fannin library and information science. Sannan kuma, ita ce mataimakiyar Ameerah ta biyu(2) a ƙungiyar Muslims students’ society of Nigeria a Kaduna Area Unit, Maƙarfi /Kudan Area council. Haka kuma, ita ce mataimakiyar magatakardar ƙungiyar marubutan Arewa ta ƙasa Nijeriya (Arewa Writers Association of Nigeria).

    Har wa yau, ta yi aiki tare da wata ƙungiya da ke tallafawa ‘ya’ya mata, don ci gaban karatunsu, wato adolescent girls iniative Center for Girls Education. Ta taɓa cin Gasar Rubuta ƙagaggun ƙananun labarai, wanda makarantar malam banbadiya tare da haɗin gwuiwar pleasant library and book club, Katsina suka shirya, inda ta zo ta biyu a labarinta mai taken “A SASANTA”

    Ita marubuciyar littattafan Hausa ce, ta rubuta littattafai kusan ashirin, ga kaɗan daga cikin su:

    1. Makircin Zuciya.

    2. GSM Kururuwar Iblis.

    3. Kinfin Kishiya.

    4. Hangen Nesa.

    5. Komai da Lokacinsa.

    6. Mummunar ƙaddara.

    7. Illar Kwaɗayi.

    8. Tsananin Kiyayya.

    9. Rashin Jituwa.

    10. Dogon Buri.

    11. Dubu Ta Cika.

    12. Kin Yi Bajinta.

    13. Ya Fi Dare Duhu.

    14. Akwai Babbar Matsala.

    15. Mizanin Hankali.

    16. Ragayar Dutse .

    Da sauran su.

    (Mun samu waɗannan jawaban ne daga bakin Hassana Abdullahi Hunƙuyi ta hanyar rubutawa da ta yi ta turo min ta imel ɗina a ranar Lahadi 12/07/2020).

    Don karanta larabci da yanda ya shigo ƙasar Hausa  danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Mawaƙi Salahuddeen Sani Kudan

    Tarihin Mawaƙi Salahuddeen Sani Kudan

    An haifi Salahuddin Sani a gidan limamin juma’a na garin Kudan, wanda ke ƙofar Arewa Kudan a cikin ƙaramar hukumar Kudan a ranar 01/01/1989, ya yi karatu a Model Primary school take Kudan a shekara ta 1995-2000. Ya yi karatu G.G.S.S Kudan a 2000-2006, ya yi karatu a makaranatar gaba da sakandire ta Maƙarfi wato Shehu Idris Collage of Health a 2014-2017. Ya yi aikin asibitin kuɗi da ke Kaduna Tudun Wada mai suna AITAM.

    Yanzu kuma yana aiki a asibitin Gwamnati wanda ke garin Kudan a cikin ƙaramar hukumar Kudan, jihar Kaduna. Sannan kuma ya fara karatun addininsa ne a makarantar Hayatul Islam ƙofa, wacce take bakin kasuwa Kudan, amma kuma ya yi saukarsa ne a makarantar Irshadul Aulad wacce take ƙofar Arewa Kudan, haka kuma ya fara bege ne a Irshadul Aulad a 2003 waƙar da ya fara yi ita ce “Mubar cuta”, sannan kuma ya yi karatun fiƙihu a wajen marigayi malam Suraj Yunusa Kudan, ya yi karatun allo a wajen Alaramma malam Iliya na tsawon shekara biyu kafin ya kuma zuwa islamiyyah.

    Shaharar sa

    Shi ne wanda ya assasa ƙungiyar sha’irai a garin Kudan mai suna Raudatul shu’ara’ul Islam Kudan a shekara ta 2015, wanda a yanzu tana da mutane guda ashirin. Bugu da ƙari kuma, ya iya sana’ar kafinta wanda ya koya a wajen ‘ya’yansa wato Ahmad Gaddafi, ya kuma iya sana’ar nona da kiwo, sannan kuma shi ne wanda ya buɗe makarantar Taufiƙil Islam, wanda take Furoja a garin Kudan, jihar Kaduna.

    Ya kuma rubuta ƙasidu da dama , ga kaɗan daga cikin kamar haka;

    1. Raddi.

    2.Shu’ara’u ‘yan Kudan.

    3. Raudatul Shu’ara’ul Islam.

    4. Ta’aziyyya (Rabi’u).

    5. Ƙololuwar matsayi.

    6. Ranar murna.

    7. Maulidin muke yi.

    1. (Mun samu wannan jawabin ne daga bakin Salahuddin Sani wanda ya rubuta ya turo min da shi ta waya (Message) a ranar Asabar 25/12/2020) da misalim ƙarfe 7;30 na safe).

    Domin karanta tarihin Salmanu Faris Adam danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Tarihin Salmanu Faris Adamu

    Tarihin Salmanu Faris Adamu

    An haifi Salmanu Faris A. Shu`aibu a garin Kudan a ƙofar Arewa Gidan Malam Tanko, a Ƙaramar hukumar Kudan wacce take jihar kaduna, sunan mahaifinsa shi ne Alhaji Adamu Shu`aibu Kudan ya rasu a ranar talata 05/08/2008 dai-dai da 1439 bayan hijra da misalin ƙarfe 05:30 na yamma.

    Haka kuma sunan mahaifiyarsa ita ce Fatima Mahmud Kudan ‘ya ce ga Maryam sarki Yakubu (wacce aka fi sani da ɗango), sannan kuma su goma sha ɗaya ne a cikin ɗakin su, akwai yayyan sa guda huɗu su ne Rahinatu da Murtala da Umar da Bilkisu, sai kuma ƙannan sa guda shida su ne Saratu da Hamisu da Hajara da Mahmud da Zahariyya da kuma Zulaihat, sai kuma waɗanda suka haɗa mahaifi ɗaya daga cikin su akwai Talatuwa da Labaran da Isah da kuma Lawan.

    Karatunsa Da Rayuwarsa

    Ya fara karatun allo a hannun Alaramma Malam marigayi Aliyu Labaran Kudan (Damo sarkin haƙuri) a shekara ta 1998 har zuwa Shekara ta 2008, a inda ya samu damar sauke Alƙur’ani mai girma na farko, sannan kuma ya cigaba da sauka ta biyu, ya yi karatun littattafai na addini a hannun malamai da dama kamar su Marigayi Alaramma Malam Surajo Yunusa Kudan da Malam Shitu Bashir Kudan da marigayi Malam Adamu Azare Panshekara da Alaramma Malam Misbahu Tsaure Panshekara da Malam Nura Yahaya Panshekara da kuma Sheikh Umar Sani Fagge Kano.

    Sannan kuma ya fara karatun zamani (boko) ne a makarantar Model Primary School Kudan a Shekara ta 2001-2007, sai ya wuce makarantar gaba da Firamare ƙarama ta garin Kudan wato J.S.S Kudan a Shekara ta 2007-2010, sai ya tsallaka zuwa Unity School ƙaraye, amma kuma ya kamala karatun sa ne G.S.S ƙayi Panshekara a Shekara ta 2013.

    Sai ya wuce makarantar koyar da Ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer), wato Troubleshooting and Information Technology (T.I.T) Kano, a inda ya samu damar karanta Data and Information Technology (Professional Diploma) da News Reporting and Photographic (Professional Diploma) da Networking and Maintenance (Higher  Professional Diploma) da Web Designing (Higher  Professional Diploma).

    Sai kuma ya tsallaka zuwa jami’ar Bayero, a inda ya samu shaidar shiga (Admission) a Shekara ta 2015 wanda ya karanci Ilimin nazarin halittu  {Bsc  (Ed)  Biology}. Bugu da ƙari kuma, ya yi karatu a ɓangaran kiwon dabbobi (Poultry farming) a  makarantar Directorate Youth Development  & Economic Empowerment Kano state  2016.

    A lokacin da yake ƙarami har zuwa tasowarsa ya ɗan yi sana’o’i daban-daban kamar su tallan attarugu da albasa da ƙosai da Tibani da Youghout a ranakun da babu makaranta ko kafin ya tafi makaranta ko kuma bayan an taso daga wata makaranta, domin samun abun sawa a baka.

    Haka kuma, a lokacin da yake J.S.S yana zuwa daji ,domin yin ƙwadugo ko kwandilo (bushashshan kashin shanu) ko Tushiya (bushashshiyar tushen dawa) ko ciyawa a lokacin da babu karatu, domin biyan kuɗin  makaranta da samun abin sa wa a baka wai  ya  fi a rataya, saboda a lokacin mahaifinsa ya rasu.

    Har ila yau, a lokacin da yake S.S.S Two (2) Yana zuwa aikin kwana masana’anta, sannan kuma da safe sai ya wuce makarantar boko da yamma kuma sai ya ɗan yi karatun allo da na Fiƙihu kafin dare ya yi, sai ya tafi wajen aikin sa, ga kaɗan daga cikin guraren da ya yi aiki kamar haka;

    1. Ya yi aikin matsen man gyaɗa a kamfanin matsan gyaɗa na Alhaji Gambo wanda yake Zuwaciki (2010-2013).

    2. Ya yi aiki a kamfanin samar da lemu na kwalba (coka-cola 2013-2014).

    3. Ya yi aiki a Wreca Staff School Challawa (2015- 2019).

    3.Ya yi aiki a Vital Academy bayan janare a Zuwaciki (2019- 2021).

    4. Ya yi aiki a Madrasatun Nuruddin Islamiyya wa tahfizul ƙur’an Panshekara a matsayin mataimakin shugaban makaranta (2015-2019).

    5. Ya yi aiki a Madrasatun Imamu Malik Bin Anas Islamiyya Panshekara a matsayin ma`ajin kuɗi (Treasure 2015-2017).

    6. Ya yi aiki a Madrasatun Darussunnah Firamare School Islamiyya Panshekara a matsayin shugaban musabaƙa (2014-2015).

    7. Ya yi aiki a Madrasatul Irshadul Aulad Islamiyya Panshekara (2013-2024).

    8. Ya yi aikin ƙwarewa(IT) na gidan rediyon Kano (Kano Radio 89.3 FM) na tsawon watanni  uku.

    9. Ya yi aikin sakai (Voluntary) a  Express Rado 90.3 FM Kano daga 2019-2022.

    10.Ya samar da ƙungiyar marubutar Arewa ta ƙasa Nijeriya (AWAN) a 2019.

    11. Ya zama shugaban ƙungiyar marubutan Arewa, wato “AREWA WRITERS ASSOCIATION of NIGERIA(AWAN)” na ƙasa daga 2019-Yau.

    13. Ya yi aiki da makarantar Cradle to Career Academy (C2C) Zuwaciki, Kano daga 2021-yau.

    14. Ya zama mataimakin shugaban tashar “Use Your talent Tv” daga 2022 – yau.

    Ya yi waɗancan karatu na na’ura mai Ƙwaƙwalwa (Computer) ya kuma shiga jami’ar Bayero Kano da ‘yan sana’o’isa na hannu.

    Fara Rubutunsa

    Ya fara rubutu ne a Shekara 1435 bayan hijira dai-dai da 2013, a lokacin yana karatu a Unity School Ƙaraye, bisa dalilin ganin irin matsalolin mace-macen aure da ya gani haɗi da gori da waɗansu mutane musulmi suke yi wa waɗanda suka musulunta ko kuma suke aikata wani abu mara kyau, sai kuma daga baya suka tuba suka koma ga Allah (Subhanahu Wata’ala). Sai ya rubuta wani littafi mai suna “KAMBUN MA’AURATA” da kuma “NASIHA GA MUSULMI AKAN SON ZUCIYA”. Daga cikin littattafan da ya rubuta su ne kamar haka:-

    1.Kambun Ma’aurata 1&5.

    2.Nasiha ga musulmi akan son Zuciya 1&4.

    3. Ramadan Mubarak.

    4. Khulasatu Siratun Nabiyyi.

    5.Ɗarikul Hudah.

    6. Ina Ma’aurata.

    7. Babban Kundi (Alƙur’ani mai girma).

    8. Righteous path to Islamic education 1.

    9. Salmanu da Salma.

    10.Kambun masoya.

    11.Mace ikon Allah.

    12.Kyauta ko Rance.

    13.Abincinka maganinka.

    14.Miskilar mace.

    15.Yar islamiyya

    16.Gwarazan Kudan (ya koma tsani).

    17. Tarkon ƙauna.

    18.Hausa ba dabo ba 1&2.

    19.Muguwar ƙaya 1.

    20.Shugabanci ko mulki ?

    21. Na duƙe tsohon ciniki (Agriculture).

    22. Mata hasken rayuwa.

    23. Duniyarka A Hannunka (Computer)

    Da Dai sauran su.

    Muƙalolin sa

    1.Influence of student’s learning difficulties in Biology on Academic achievement in Gwale local government area of Kano state (Bsc{Ed} Project 2019).

    2. Aure tushen arziki.

    3. Alƙu’ani jigon rayuwa.

    4. Sanadiyar soyayya.

    5. Matsalolin mutuwar aure.

    6. Alamomin shigar so.

    7. Magani a gonar yaro.

    8. Falalar da Allah ya yi wa mace.

    9. Amfanin shayar da jariri nono zalla.

    10. Dokin tsira.

    11. Wacece mace.

    12. Hukuncin jinin haila.

    13. Illar rubutu/karantun batsa ga marubuta da makaranta; Takardar da aka gabatar da ita a majalisar marubuta ta jahar Yobe 07/01/2021.

    14. Rayuwar Manzon Allah (S.W.A) ita ce abin koyi: Takardar da aka gabatar da ita Madrasatul Darul Haƙ Islamiyya Zawaciki Panshekara, ƙaramar hukumar Kumbotso, jihar Kano.

    15. Wacece mace ta gari.

    16. Hikimar yin zance (soyayya).

    17. Lokutan da soyayya ta fi daɗi.

    18. Illolin yin tsafi ga al’umma.

    19. Amfanin taimako.

    Lambar Yabo

    Ya samu lambobin girmamawa daga wurare daban- daban kamar su;

    1.Kainuwa Authors Kano, wanda suka koma Kainuwa Authors Forum a yanzu 2020  (2019).

    2.Darussunnah Firamare Islamiyya School Panshekara   (2016).

    3.Irshadul Aulad Islamiyya Panshekara (2016).

    4.Nuruddin Litahfizul ƙur’an Islamiyya Panshekara (2015).

    5.Imamu Malik bin Anas Islamiyya Panshekara (2015).

    6.Wreca Staff School Challawa Panshekara  (2016).

    7.Nigeria Universities Education Students Association (NUESA) Bayero University, Kano Chapter (2019).

    8.Yobe Writers Association (YOWA) a (2020).

    9. Majalisar Marubuta 2021 (akan illar rubutu da karantun batsa).

    10. Arewa Writers Association of Nigeria (AWAN).

    11. Cradle to Career Academy (C2C) Zawaciki, Kano (The most active extra-curricular activities and the effective student learning support teacher).

    12. Hadiza Ibrahim Aliyu School of Festival (HIASFEST) a matsayin wanda ya lashe gasar kimiyyar halittu (Biology) zuwa ga harshen Hausa (Hausa science book/biology) na shekara ta 2023.

    14. Hadiza Ibrahim Aliyu School of Festival (HIASFEST) a matsayin wanda ya zo na biyu a gasar kimiyyar kwamfuta (Computer) zuwa ga harshen Hausa (Hausa science book/computer) na shekara ta 2024.

    Danna nan don karanta tarihin Dakta Ado Zakari Kudan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Hanyoyin Bincike A Rubutu

    Hanyoyin Bincike A Rubutu

    Kusan duk rubutun da marubuci zai yi, ƙirƙirarre (fiction) ko wanda ba ƙirƙirarre ba (non-fiction) abu na farko da ake sa ran mutum zai yi shi ne; bincike. Bincike hanya ce ta fito da abinda ke ɓoye zuwa sarari. Hanya ce da ake bi don ganin an amsa wasu tambayoyi game da wani al’amari.

    Ta hanyar bincike ake tattaro bayanai da killace su tare da sarrafa su ta yadda za a iya samun wani sabon ilimi, ko tabbatar da wani abu da ake zargi ko ake da tantama a kai. Kusan duk wani cigaba da ake samu a duniya to bincike ne ke haifar da shi.

    Kamar yadda idan aka tsinci gawa, za a ɗauke ta a je a yi forensic investigation har a gano dalilin mutuwar mamaci, haka ake sa rai idan marubuci ya samu jigo, zai soma gudanar da bincike kafin ma ya fara rubuta komai.

    Bincike na nufin karantar wasu abubuwa ko hanyoyi, don gano haƙiƙanin gaskiyar da zai iya zama wata hujja ko madogara kan abinda ka ke son bayyanawa. Wani marubuci mai suna Robert Mekee na cewa; “Idan ka gudanar da wadataccen bincike, to za ka ga tamkar labarin ya kammala rubuta kan sa, tun ma kafin ka fara rubutawa.”

    Bincike ba abu ne mai sauƙi ba, wasu marubutan ba su san ta yadda za su fara yi ba. Sai ka ga mutum ya tattara bayanai har sun yi masa yawa. Ya kasa gane ta hanyar da zai sanya bayani a cikin labari. Garin a rubuta labari mai cike da nishadantarwa, sai rubutun ya zama mai gundura. A maimakon ya rubuta novel sai ka ga ya ɓuge da rubuta textbook ba tare da ya kula ba.

    DALILAI BIYU NA YIN BINCIKE

    1) Wataƙila kana da cikakken ilimi kan abinda ka ke son yin rubutu a kai, to amma duk da haka kana buƙatar ƙarin bayani ta wata mahangar. Hakan zai taimaka wajen gamsar da mai karatu har ya gamsu cewa wannan ba kawai zallar ra’ayinka ba ne.

    2) Wataƙila ba ka san komai game da saƙon da ka ke son bayyanawa ba ta fuskar ilimi. To amma kana buƙatar sani don ka wayar wa da mutane kai.

    KAFIN FARAWA

    Kafin ka fara bincike akwai abubuwa guda uku da ya dace ka halarto zuwa allon majigin zuciyarka.

    1) Wanne saƙo kake son ka isar (message)

    2) Su wane ne za su karanta saƙon (target audience)

    3) Sai ka yi wa kan ka tambaya kamar haka; “Wacce irin hujja zan ba wa mai karatu ya gamsu da bayanin nan nawa?”

    Sai dai kada ka damu da lallai sai ka gamsar da mai karatu. Duk abinda ka yi ba za ka iya gamsar da kowa ba. Kawai ka yi iyakar bakin ƙoƙarinka.

    Danna nan don karanta babban kundi

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Haihuwarsa Da Shayar Da Annabi S.A.W

    Haihuwarsa Da Shayar Da Annabi S.A.W

    1. An haifi Mazon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) a garin Makkah ranar litinin, sha biyu ga watan rabiyul-auwal (12) Shekarar Giwaye.

    2. An ambaci shekarar haihuwarsa Giwaye, Saboda sarkin Habasha, ya aika sojoji a shekarar haihuwarsa zuwa garin Makkah, domin su rushe Ka’aba, ya kasance a cikinsa akwai Giwa mai mai girma, sai Allah (Subhanahu wata’ala) ya hallaka rundunar (sojojin), domin (saboda) girmama shekarar haihuwar annabi (Sallallahu alaihi wasallam).

    3. Suwaibatul-Assalamiyya ta shayar da shi, bayan mahaifiyarsa, wacce take yi ma babansa hidima Abu-Lahabi, sannan sai Halimatu-Sa’adiyya, har sai da ya kai shekaru huɗu (4) na daga rayuwarsa.

    Sharhi;

    An haifi manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ne a ranar litinin sha biyu (12) ga watan rabbiyul-Auwal, ko da yake wasu ruwayoyin sun ce ranar sha bakwai ne (17) ga watan rabbiyul-Auwal, a garin Makka, a shekarar da ake kira da shekarar Giwaye . Dalilin da ya sa ake kiran wannan shekara shi ne wani gwamnan sarkin Habasha mai suna Abrahata ya shigo Makka da runduna mai yawa, bisa kan giwaye (bayan ya kame garin Yaman) da nufin rusa ɗakin Ka’aba da sauya alƙiblar mutane zuwa San’a (domin a wancan lokacin mutane sukan kawo ziyarar bauta a Ka’aba).

    Inda dama tuni ya gina wani guri don wannan ziyara. Amma daga baya lokacin da Abrahata ya iso Makka da wannan runduna tasa, sai Allah Ya aiko da wasu irin tsuntsaye ɗauke da tsakuwoyi a bakunansu, inda suka rinƙa jefo waɗannan tsakuwoyi a kan waɗannan runduna, nan take suka kashe sojojin da giwayen. Ta haka ne Allah ya yi maganin wannan azzalumi da mutanensa.

    Mahaifinsa dai shi ne Abdullah ɗan Abdul-Muɗallib ɗan Hashim; Mahaifiyarsa kuwa ita ce Amina ‘yar Wahbu, Kakansa kuwa shi ne Abdul-muɗallibi, wanda ya kasance yana da ‘ya’yaye da yawa, amma Abdullahi (mahaifin Annabi) da Abu-ɗalib (mahaifin Imam Ali) mahaifiyarsu guda ne. Don haka ya fito ne daga cikin tsatson Banu-Hashim, su kuma daga ƙabilar ƙuraishawa, waɗanda ke da dangantaka da annabi Isma’il (A.S) ɗan annabi Ibrahim (A.S).

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) dai ya tashi ne a matsayin maraya, saboda kasancewar mahaifinsa ya rasu yayin da ya kai ziyara Yathrib (Madina) watanni uku kafin haihuwar manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam). Tattare da baƙin cikin rasuwar Abdullah, amma haihuwarsa ta sanya iyalansa, Amina da Abdul-Muɗallib, cikin farin ciki da ba shi da iyaka.

    Sun shirya gagarumar walima ga ‘yan uwa da maƙwabta, inda aka yi yanka don murnar wannan haihuwa. A sakamakon haka duk Makka ta ɗauki murna, inda mutane suka yi ta zuwa gidan Abdul-Muɗallib don miƙa saƙon taya murna gare shi.

    A bisa al’adar mutanen makka, sukan kai ‘ya’yayensu shayarwa ƙauye, saboda samun kyawawan halaye da kuma yanayi mai kyau da dai sauransu, don haka an aika da Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) wajen da Halima ‘yar Abi-zu’aib a ƙauye, don shayar da shi. Haƙiƙa Halima ta sadu da alhairai masu yawa daga abin shayarwarta Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam).

    Har ila yau, al’adace ta Labarawa idan sun haihu, sai su nemi mace wacce za ta shayar masu da ‘ya’yansu a cikin ƙauyukan garin, saboda ‘ya’yansu su taso da hikima da dabaru iri-iri na harkar rayuwa, sannan kuma da Juriya na wahal-halun duniya daban-daban, saboda mutane da suka saba da jin daɗin rayuwar birni, za ka iya samun su  da lalaci  haɗi da rashin hikima na yau da kullum.

    Domin karanta sunayen baffanni ƙwarori da gwaggonnin Annabi SAW  danna nan

    Amma mutumin da ya saba da shan  wahala da jin daɗi na rayuwa, to za ka same shi da hikimomi haɗi da kaifin basira da jajircewa akan ayyuka na yau da kullum, sannan ba ya raina sana’a ko ɗan yaya take. Saboda haka, an san ƙabilar Banu-Sa’ad sukan fito neman yaran da za su shayar da su, sai Halimatu ‘yar Abi-zu’aibin ‘yar ƙabilar Banu-Sa’ad ta ɗauke shi za ta shayar da shi (sallallahu alaihi wasallam).

    Sannan suka yi wa Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) laƙabi da suna ɗan kabshata, a lokacin da yake yi masu wa’azi akan su bar bautar gumaka, su dawo bautar Allah (Subhanahu wata’ala), sai suke cewa ka ji ɗan Kabasha! Yana cewa wai “yana da wanin abin bauta, ana yi masa magana daga Sama!, wato Allah yanayi masa wahayi, ba irin  Allolin da muke bautawa ba, sannan kuma Allah (Subhanahu wata’ala) Na sama ba a ganinsa” da dai sauransu.

    Halima Sadiya ta shayar da Shi tsawon shekaru huɗu (4), wanda yake a lokacin da take shayar da shi akwai abubuwa da yawa waɗanda suka faru, kaɗan daga cikin akwai: magana da zaki a lokacin da annabi da wasu mutane suka fita waje lokacin yana ƙarami sai ga wani karkeci (zaki) babba, sai sauran mutanen suka fita da gudu, sai annabi ya tsaya ya yi magana da zakin har zuwa ƙarshen labarin.

    Sannan mala’iku guda biyu (2) sun zo wajen sa da siffar tsuntsu suka tsaga ƙirjinsa shi ma har zuwa ƙarshen labarin. Sannan kuma akwai wani lokaci da annabi ya tashi cikin dare zai yi fitsari, ga shi Halimatu tana bacci a ƙofar ɗakin, sai ya ji tsoro wucewa ta gabanta, saboda kadda ta farka daga bacci, ta hana shi fita waje, saboda wancan abin da ya faru na mala’ikun can, sai annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ɗauki taska ya yi fitsarin a cikinta, sannan ya koma ya kwanta bacci, can sai Halimatu ta tashi daga baccci tana jin ƙishir ruwa, sai ta ga wancan taska, ta ɗauka ruwa ne sai  ta shanye ba ki ɗaya.

    Bayan gari yawaye, sai annabi yana neman wancan taskar zai zubar da abin da yake cikinta, sai ya duba inda ya ajiye ta, amma bai ganta ba, sai ya tambayi Halimatu, tace ai na ɗauka ruwa ne har ma na shanye, sai annabi yace da ita tun da kin sha wannan, to  zai yi miki maganin cututtuka da yawa sosai a jikin ki.

    Sannan ya yi wa tsuntsaye addu’o’i a lokacin da Halimatu za ta dawo da shi gida, da dai sauransu. Lokacin da annabi ya cika shekaru shida da haihuwa sai Halima ta dawo da shi zuwa Makka, yayin da ya sami kakansa Abdul-muɗallibi a matsayin mafi alherin mai raino gare shi; domin ya kasance yana ba shi duk abin da yake buƙata na tausayi da ƙauna irin ta iyaye masu lura. Ya kasance yana ba shi matsanancin kulawa fiye da duk iyalansa.

    A shekara ta shida da haihuwarsa, sai mahaifiyarsa ta tafi da shi ziyarar danginsa na nono, wato Banu-Uɗayyu bin Najjar a Yasrib (Madina), a tare da su akwai Ummu Aiman. Sai suka saura a can har na tsawon wata ɗaya, sannan sai suka juyo suka kama hanyar dawowa Makka. A hanya ne ajali ya samu mahaifyarsa Amina, aka binne ta a Abwa’i, wanda wani gari ne da ke tsakanin Makka da Yathrib (Madina).

    Sai Ummu Aiman ta dawo da shi wajen kakansa, yayin da ita kuma ta ɗauki nauyin aikin uwa, kamar yadda kakansa Abdul-muɗallibi ya ɗauki aikin uba. Wannan kulawa dai ba ta jima sosai ba don shi ma wannan kakan nasa Allah Ya ɗauki ransa a lokacin Annabi  na ɗan shekara takwas da haihuwa. Daga nan sai kulawarsa ta koma hannun Baffansa Abu-ɗalib, wanda ya yi mu’amala da shi da ƙauna, sassauci da lura irin ta iyaye, ta yadda babu wani daga ‘ya’yansa da ya samu irin hakan.

    Ya kasance yana bacci a shimfiɗar Baffansa, yana zama gefen sa, yana cin abinci tare da shi, yana fita tare da shi duk lokacin da ya fita daga gidansa; da wasun waɗannan na daga nau’o’in lura da so waɗanda irin su ke da wuyan samu.

    Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana girma a hannun Baffansa da halayensa na girma tare da shi, ta yadda har sai da ya keɓantu da wasu siffofi na nagarta a tsakaninsa da mutanensa da suka haɗa da gaskiya, riƙon amana, waɗannan siffofi dai sun keɓanta da shi ne ban da waninsa; har ma ta kai ma mutanen suna kiransa da “mai gaskiya da riƙon amana”.

    Ganin cewa dai ya fara girma kuma don kada ya zauna haka, sai annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya fara aiki a lokacin yana matashi. Aikin da ya fara yi shi ne kiwon tumaki/awaki (dabbobi). Sannan sai ya bi Baffansa Abu-ɗalib zuwa Sham don kasuwanci. A wannan lokaci ma dai manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya nuna fasaha, ƙwazo, gaskiya da kuma riƙon amana a wannan fage.

    Lamarin da ya jawo hankalin wata hamshaƙiyar attijira mai suna Khadijah ‘yar Khuwailid zuwa gare shi. Don haka sai ta neme shi da ya kula mata da wani sashi na kasuwancinta, ta ba shi wasu dukiya mai yawan gaske don gudanar da kasuwanci, wanda daga ƙarshe ta samu riba mai girman gaske da ba ta taba samu ba a baya.

    A shekarar da aka haifi Annabi Muhammad  (Sallallahu alaihi wasallam), an ga abububuwa iri-iri waɗanda suka faru. Kaɗan daga cikinsu su ne: Mutuwar wutar Kisra, wacce mutanen gari suke bautawa wadda ta ɗauki shekara da yawa ba ta mutuwa, sannan sama ta yi haske, gari ya yi tsit ba hayaniya, da dai sauransu.

    Haka kuma dalilin da yasa aka ambaci shekarar haihuwarsa da shekarr giwaye shi ne, a wannnan shekara ne sarkin Habasha ya tura giwaye da yawa sosai, domin su zo rushe ɗakin Ka’abah, wanda yake a wannan lokacin akwai gumaka guda ɗari uku da sittin (360) wanda ake bautawa, bayan gumaka na Ugunwanni da na kasuwanni haɗi da na gidaje.

    Danna nan don karanta sunayen annabi SAW

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Alaƙar Ɗaukakar Yaren Larabci Da Kasantuwarsa Yaren Addinin Musulunci

    Alaƙar Ɗaukakar Yaren Larabci Da Kasantuwarsa Yaren Addinin Musulunci

    Allah bisa hikimarsa kan yi duk abin da ya so ya ɗaukaka yasasshe ya sakko da wanda al’amarinsa ke bisa. Wanda kuma wannan na cikin abubuwan da Allah maɗaukaki ya keɓanta da su da yake nuna buwaya da iko akan komai.

    Kafin yaren Larabci ya sami ɗaukakar samun kansa a matsayin yaren addinin musulunci wasu yaruka da dama sun samu wannan ɗaukaka wanda yake nuna cewa ba kansa farau ba, kuma ba kansa za a ga wasan sallah ba.

    Ba ina maganar su sauran yarukan sai sun zama sun taɓa zama yaren da musulunci ya yi amfani da su ba ne a a, magana ake ta wannan yaren ya taɓa zama na addini? Addinan nan kuwa ko da na gargajiya ne, domin aikin da addinai ke yi wa yare kusan duk iri ɗaya ne da ba ya gaza taimakawa wajen wanzar da shi ta hanyar sanya shi a ayyukan ibada da rubuce-rubuce da shi domin koya ko koyar da wannan addini.

    Balarabe ya yi amfani da damarsa ya tallata yarensa da wasu daga cikin al’adunsa ta hanyar musulunci a inda ya shiga ya fita har sai da ya girmama yaren nasa a idon mabiya addinin musulunci ta nuna cewa kamar shi da yarensa wasu abubuwa ne da suke da matsayi daban a gurin Allah ta’ala da ba kowanne yare da al’ummarsa ne suke da wannan matsayi ba, wannan zai bayyana ƙarara ne ga wanda yake da masaniyar abubuwan da suka faru a daulolin da larabawa suka kafa da sunan daulolin Musulunci bayan lokacin Habibi (saw) da sahabbansa ya wuce.

    Ala sabilil misali ka ɗauko tsari da yanda aka bi aka mulki mutane a lokacin mulkin Banu Umayyah. Duk wanda yake nazartar tarihin waɗannan dauloli ba ta ɓangaren addini ba kawai ya san yanda Banu Umayyah suka dawo da wasu daga cikin ɗabi’un jahiliyya na fifita duk balarabe akan waninsa wannan kuwa ko da sahabi ne, tuna da tsarin MAWALI da suke da shi mana, bayan kuma Larabawa sun san cewa Habibi (saw) ya faɗa cewa “Babu banbanci tsakanin Balarabe da waninsa sai wanda ya fi wani tsoron Allah” Ka san abin da ya faru har shugaba (saw) ya faɗi wannan hadisi?

    Balarabe ya ɗauka ɗaukar yarensa a yi amfani da shi a matsayin yaren addini kamar wani abu ne da babu yanda aka iya dole sai haka ya faru, musamman yanda yake ganin cewa wai yarensa na cike da abubuwa gagararru da da yawa ko ma dukka sauran yaruka ba su da su, ya manta da cewa Allah ta’ala ba shi da yare, domin addinin dai da suka ƙi a farko dole ta sa suka ƙarɓa daga baya, yanzu kuma suka ɗauka gadon gidansu ne shi ne ya bai wa yaren nasu wannan girma da ɗaukaka.

    Sun manta da cewa da Allah ya ga dama sai ya ƙaddara Shugaba (saw) ya fito Bahabashe kamar yadda wasu Annabawa suka kasance, ko Banufe ko kuma ma Bahaushe wanda zai sa a sauƙar da Littafi maɗaukaki da Nufanci ko da Inyamuranci, yanda kuma kake ganin Larabci da girma yanzu haka shi ma yarenka da kake rainawa zai zama haka a wajenka da Allah ya ƙaddara hakan.

    Daga cikin abubuwan da Balarabe ya yi har da samar da hadisan da da yawan malamai suka ra’afanta shi da ke nuna falalar Balarabe da Larabci, ban ce dukansu ƙirƙirarru ba ne kamar yanda masana ba su faɗa ba amma kusan da yawansu akwai lauje cikin naɗi a yanda suka fito. Domin wasu daga cikinsu babu abin da suke nuni sai wariyar launi da fifita wasu bisa wasu ba kuma da tsoron Allah da Al-qur’ani yace shi ne ma’aunin fifiko ba, a a bari kawai dai dan sun kasance Larabawa.

    Balarabe musamman na yau a rashin wayo da gidadancinsa ya ɗauka musulunci ma shi ne ya masa rana, ka kula mana ka ga yanda ya ɗauka musulunci gado ne ya yi da dole ya zama shi ne shugaba ko abin koyi in dai a abin da ya shafi addinin ne, ka gwada yin mu’amala da Balarabe na yanzu ka ga yanda abin zai kasance.

    Abin da nake son na faɗa shi ne Larabci ya cancanci girmamawa tabbas ko dan wani hadisi da ban san tabbacin sahihancinsa ba (Domin ni ba ɗalibin hadisi ba ne) da yake cewa Habibi (saw) ya ce ina son Larabci domin abu uku, kasancewa ta Balarabe, yaren ‘ƴan Aljanna Larabci ne kuma Al-qur’ani ma balarabe ne.

    Amma tabbas addini ne ya bai wa Larabci dukkan matsayi, duk da kuwa masu yaren na ganin akasin haka, wanda mu a ƙasar Hausa shaida ne cewa saboda ganin Musulunci da muke wa Larabci har baƙaƙensa ba ma bari su ke yawo a ƙasa, balle kuma wasu kalmomin cikinsa ko jimloli, kamar yanda zaurukan ɗaukar karatunmu ake koyar da abubuwan da tunda da larabci aka rubuta su sunansu ilimi amma da da wani yaren ne to sunansu shisshigi da taimakawa ɓarna ta ci gaba.

    Domin karanta larabci da yanda ya shigo ƙasar Hausa danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu