Tag: yadda ake

  • Amfanin Yin Bincike A Rubutu

    Amfanin Yin Bincike A Rubutu

    1) Kai kanka a matsayinka na marubuci za ka ƙaru da ilimin da ba ka sani ba.

    2) Gamsar da mai karatu ta hanyar bayar da hujja a ilimance, ba wai kawai ra’ayi ko iya fahimta ba.

    3) Za ka koyi kallon al’amura ta fuskoki daban-daban.

    4)Duk lokacin da wani ya karanta littafinka, zai ji kamar labarin ba ƙirƙirarre ba ne. Tun da ka kawo wasu abubuwa na gaske.

    5) Littafin zai zama kamar reference book.

    6) Ba a cika saurin manta labari mai ɗauke da bincike ba.

    HANYOYIN TATTARA BAYANAI

    Babu wata tartibiyar hanya guda ɗaya da za ace dole sai ta nan ake tattara bayanai. Ya danganta daga marubuci zuwa marubuci. Kuma ya danganta da saƙon da labarin ya ƙunsa.
    Wani labarin ya fi wani zurfin bincike.

    1) TSARA YADDA ZA KA YI BINCIKE

    Ya bambanta daga mutum zuwa mutum.

    Misali wanda ya karanci ɓangaren lafiya, idan zai yi rubutu kan abinda ya shafi lafiya; ba zai ɓata dogon lokaci wajen yin bincike ba, kan wanda ba wannan fannin ya karanta ba.
    Abin nufi wanda yake expert a fage ya bambanta da yadda ba expert ba zai gudanar da nasa binciken. Wanda ba a fagen yake ba dole sai ya yi bincike mai zurfi.

    2) ABIN DA KA SANI

    Za ka fara rubuta abinda ka sani game da matsalar da ka ke so ka yi rubutu akai kafin ka nemi shawarar kowa. Misali littafin Rai da motsi na Maryam Muhammad Sani. Ta yi dogon bayani kan cutar ‘Down syndrome.’ Ta san yanayin ciwon sosai tun da tana da alaƙa mai ƙarfi da mai cutar.

    Kamar yadda Hauwa Shehu ta yi bayani kan Cyber Crime a littafinta na Harin Gajimare, tun da har certificate ta yi kan Cyber security. Zama za ka yi ka fara rubuta abinda kai ka sani ko da ɗan kaɗan ne kan abinda ka ke so ka yi bincike akai.

    Ko kina son yin rubutu kan yadda wayar hannu ke jawo matsala tsakanin ma’aurata. Sai ki fara tuna duk wani labari da ki ka taɓa ji kan yadda waya ta taɓa jawo matsala. Idan ke ma abin ya taɓa shafar ki kaitsaye, to kin ga kina da experience. A matsayinki na marubuciya experience na da matuƙar muhimmanci kan abinda ki ke son yin rubutu akai.

    3) TAMBAYA

    Ka ɗauki takarda ka jera tambayoyi kan abinda ka ke so ka yi bincike akai. Misali ina so na yi rubutu kan matsalar mantau ta ‘amnesia.’ Duk da cewa na sha karantawa a novels kuma na sha ganin yadda lalurar ta ke a films, amma ina buƙatar na rubuta tambayoyi kamar haka;

    Mece ce amnesia? Me ke jawo ta? Ya rabe rabenta yake? Ta wacce hanya matsalar ke sauya halin mutum? Ta wacce hanya ake bi a warke? Shin me matsalar zai iya tunawa da abinda ya aikata lokacin da yake cikin matsalar? Ya bayanin matsalar take a likitance?
    Ina kyautata zaton Sanah Matazu ta yi irin waɗannan tambayoyin kafin ta rubuta littafin Fitsarin fako. Jera waɗannan tambayoyin za su taimaka ƙwarai wajen saƙa zaren labarin yadda ya kamata.

    4) INTERNET

    Sheik Google zai iya zama malaminka na farko da za ka fara tuntuɓa. Sai dai ka da ka dogara da sakamako guda ɗaya kawai. Kana buƙatar bibiyar shafukan da aka yarda da su ta fuskar bincike na ilimi. Za ka sami bayanai da dama da za su ƙara maka ideas kan abinda ka ke nema.

    5) HOTUNA

    Akwai hotunan da za su taimaka maka wajen rubutu. Akwai hoto mai magana wanda ganinsa kaɗai zai iya ƙara maka idea a matsayinka na marubuci. Ruƙayya Ibrahim ta fara samun idea rubuta littafin Wata duniya ta hanyar kallon wani hoto da ke jikin foodflask ɗin wani yaro. Ta ga hoton ɗan sama jannati. Daga haka ta fara saƙa zaren labarin.
    Idan kana googling kan wani abu, to ka ke kula da hotuna. Wani hoton zai taimake ka fiye da yadda ba ka zato.

    6) MASANA

    Internet ba kodayaushe zai wadatar da kai ba. Kana buƙatar tattaunawa da masana.
    Kana buƙatar ka yi tambaya a ba ka amsa. Kana buƙatar a ba ka labari a zahiri idan ta kama a nuna maka misali. Lokacin da Maimuna Beli za ta rubuta littafin Gwanin na iya, har gidan yari ta je ta yi bincike.

    Lokacin da Bala Anas zai rubuta littafi mai suna Zinaru. Labari ne kan ‘yan Kano to Jidda. Sai da ya tattauna da ‘yan Kano to Jidda da dama baya ga waya da ya yi da wasu da ke zaune a can. Sai dai akwai abinda ya dace mu kula da shi.

    Duk lokacin da za ka tattauna da expert a wani fage, to kada ka je ba tare da ka tsara tambayoyi ba. Kuma ka yi ƙoƙari ka san wani abu a fagen. Hakan zai sa masanin ya yi maka bayani. Kwanan nan wata marubuciya ta ba ni labarin ta haɗu da wata masaniya a wani fage. Amma sai ta rasa tambayar da za ta yi mata, saboda ba ta tsara tambayoyi ba.
    Idan kika kuskura kika ƙara irin wannan shirmen sai na ambaci sunanki.

    Don karanta babban kundi danna nan

    7) ZAMA CIKIN SHIRI

    Ba ka san takamaimai lokacin da idea za ta faɗo maka ba a matsayinka na marubuci. Wataƙila kana cikin wanka abin zai zo maka, kamar yadda ya taɓa faruwa da wani masanin Physics Archimedes yana banɗaki yana wanka wata idea ta faɗo masa wacce ya daɗe yana nema. Tsirara ya fito daga banɗaki ya fita waje yana tsalle cike da murna. Sanadiyyar haka aka samu ‘Law of floatations’

    Haka marubuciyar Ƙaddarar rayuwa, Wato Bilkisu Garkuwa; jin Muryar mata daga wajen wani mai adaidaita sahu ya ƙara mata idear da ta yi rubutun da ya zo na ɗaya a gasar Gusau ta shekarar 2022.

    Ana buƙatar marubuci kodayaushe ya zama cikin shirin yin jotting ɗin idea.
    Wani sa’in wani ɓangare na labari zai iya faɗowa ƙwaƙwalwarka a wani irin yanayi. Idan ba ka rubuta ba sai ka manta.

    8) KARATU

    Akwai falsafar da ke cewa kamar yadda idan mutum ya sha ruwa mai yawa, to zai yi fitsari da yawa. Haka ma karatu da rubutu. Idan mutum yana yin karatu da yawa, to abu ne mai wahala ya rasa abin rubutawa. Ko da ka rasa yadda za ka yi a wani waje, sannu a hankali idea za ta faɗo maka wacce za ta taimaka maka wajen ɗaure zaren labarinka yadda ya kamata.

    Akwai mamaki samun marubuci amma kuma wanda ba ya yin karatu. Na taɓa saurarar hira da wani marubuci Robert Greene, duk da dai shi ba Novel yake rubutawa ba, amma yace kafin ya rubuta littafi ɗaya, a ƙalla yana karanta littafi 250 zuwa 300. Ke littafi nawa ki ke karantawa kafin ki rubuta guda ɗaya?

    9) MUƘALA

    Karanta journals za su taimaka maka sosai musamman idan labarinka ya shafi wani fanni na daban (profession). Lokacin da zan rubuta littafin Ciwon rai, sai da na karanta journals kan abnormal psychology na samu bayani sosai kan cutar Alzheimer disease. Wannan ya taimaka min sosai wajen ƙulla zaren labarin ta yadda na iya bayyana alamun ciwon sosai kan Nuraini mijin Falmata.

    10) SAURARO

    Wani sa’in kana buƙatar sauraron wasu bayanan ta audio don ƙara fahimtar abinda kake bincike. A binciken da Ruƙayya Ibrahim ta yi wajen rubuta Wata duniya, ta saurari wata lakca da Abou Uthymin ya yi kan astronomy. Wannan ya taimaka mata wajen saƙa zaren labarinta wanda ya zo a mataki na biyu na gasar Gusau a shekarar 2023.

    11) TAFIYA

    Idan da hali ana buƙatar marubuci ya ziyarci wuraren da ya yi bayaninsu a cikin littafinsa. Sydney Sheldon yace duk wani waje ko da wajen cin abinci ne da ya kwatanta a littafinsa sai da ya je wajen. Ta sanadiyyar haka sai da ya je ƙasashe fiye da 100.

    Lokacin da Bala Anas zai rubuta littafin Sara da sassaƙa. Kasancewar labarin ya faru ne a ƙasar South Africa. Sai da ya nemi map ɗin ƙasar. Duk wani tudu da kwari da sunan ƙoramu da daji na gaske ya yi amfani da shi.

    Haka lokacin da zai rubuta littafin Zinaru, sai da ya yi waya aka kwatanta masa tun daga airport har zuwa tituna da kantina duk sunayen na gaske ne. Hakan ne ya sa wasu da suka karanta littafin a can, suka yi tsammanin cewa ya taɓa zuwa Saudiyya alhali bai taɓa zuwa ba.

    11) TSAYAR DA RANA

    Tun daga lokacin da za ka fara bincike har zuwa lokacin da za ka kammala, ana so ka sa rana. Don marubuta da yawa sun sha kasa ƙarasa aikin bincike saboda rashin sa ranar dakatawa.
    “Ban kammala binciken ba…” Da haka idan ba a yi wasa ba sai mutum ya shiririce.

    12) FARA RUBUTU

    Da zarar ka kammala haɗa bayanai, abu na gaba shi ne; ka fara rubuta abinda ake cewa first draft. Ba lallai a rubutun farko za ka shigar da komai ba, sai a second draft, wani ma sai a third draft.

    Danna nan domin karanta hanyoyin bincike a rubutu

    Edita; Rumasa’u M’ Kallamu

  • Al’adun Hausawa Na Jiya Da Na Yau

    Al’adun Hausawa Na Jiya Da Na Yau

    Shi dai Malam Bahaushe a bisa tarihin da ya shuɗe, mutum ne baƙi sosai, mara tsawo, mai shafaffen hanci da faffaɗan baki. Amma dai wannan siffantawar ta Bahaushe a kan iya cewa tana daf da a kira ta tarihi, bisa ga yadda aka samun auratayya sosai tsakanin ƙabilar Hausawa da sauran ƙabilu daban-daban.

    Al’ummar Hausawa mutane ne da suka shahara a kan riko ga ɗabi’u da al’adunsu na gargajiya. Sai dai canji da suka samu na addini wanda a fari suka wanzu cikin addinin gargajiya da aka fi sani da Maguzanci, sannan daga bisani suka rungumi addininin Islama. Ga Malam Bahaushe, babu wani abu da ya ɗara addininsa martaba da kima.

    Hausawa sun bambanta da sauran ƙabilun Najeriya, ta hanyar tsananin ruƙonsu ga al’adun tufafin sa wa da abinci da gine-gine da sauransu. Ɗaukacin Hausawa za ka same su rungume da al’adunsu. Ba ma iya Bahaushen ƙasarmu Najeriya ba, har da sauran Hausawan wasu ƙasashen daban.

    A JIYA, Malam Bahaushe ba ya iya cin abincinsa na dare shi kaɗai a gida. Sai dai ya ci abincin tare da sauran maƙwabtansa. Kowa zai fiddo da abincinsa, yawanci tuwo da miyar kuka su zauna cikin da’ira, suna ci kwano bayan kwano cikin annashuwa, har kowa ya koshi.

    Idan kuma an samu saura bayan sun ƙoshi sukan tattara su bai wa almajirai waɗanda akasari suke rabewa a wajen domin ko sa ɗan samu saura, su ma su kashe yunwar cikinsu. Wannan al’adar ita ake yi wa laƙabi da ‘Ciyayya’ ma’ana dai cin abinci tare da abokan arziƙi. Idan kuma cikin rashin sa’a akwai wani da ranar Allah bai yassare masa ƙarfin iya fiddo da tuwon ba, hakan ba zai hana shi zuwa a ci tare da shi ba.

    Wannan ma shi zai sanya abokan nasa su fuskanci yanayin rashi ko matsi da ke fuskantarsa. Idan ma ya jima cikin halin matsin rayuwa, to sauran mutanen da suke taren za su tallafa masa da ‘yan kayayyakin abinci da na masarufi. Kuma idan wani ne daga cikinsu ya ɗauki ‘yan kwanaki biyu bai samu halartar ciyayyar ta su ba, to sauran fa ba za su yi ƙasa-a-gwuiwa ba wajen tuntuɓa a game da shi ba.

    Wasu har ma ba za su samu nutsuwa ba sai sun aika gidansa ko wajen mai-ɗakinsa. Idan ba shi da lafiya ne ko kuma wata matsala ta rayuwa ce ke damunsa, to za su yi yunƙurin ba shi tallafi da addu’o’i ɗaya bayan ɗaya ko kuma a ƙungiyance.

    A JIYA, budurci na ‘yan mata yana da matuƙar martaba. Kusan duka ‘yan matan Hausawa suna riƙe ɗiyancinsu har a yi musu aure. Rasa ɗiyancin ‘ya mace budurwa tamkar rasa rai ne. Wannan ita ce babbar fitina ga rayuwar yarinya kafin a yi mata aure. Ana gudanar da wani bincike na al’ada domin tabbatar da budurcin ‘ya mace kafin a kai ta ɗakin aure.

    Idan kuma aka samu yarinyar ba ta kai budurcinta ba, to za ta rasa rayuwarta nan take. Idan kuma wasu dalilai suka sanya ba a yi binciken ba har amaryar ta kwana a ɗakin mijinta, kuma daga bisani angon ya gano cewar ba ta tsira da budurcinta ba, to wannan sabon auren dai za a warwareshi. Kafin warwarewar auren, ‘yan uwan angon mata sukan ziyarci ɗakin amarcin washegarin tarewar amarya, domin tabbatar da shin surukarsu ta tsira da budurcinta kafin auren?

    Sukan nutsu su saka ido domin nazarin wata alama duk ƙanƙantarta da ka iya tabbatar musu da amaryar nan kamammiya ce. Misali a ce sun ga wani fasasshen faranti, ko wata ƙwarya, wadda angon ya fasa domin ya tabbatar da budurcin amaryarsa ga duk wani baƙo da ka iya zuwa domin nazarin amaryar sa.

    Idan kuma baƙon ya gaza ganin wata alama, yakan yi wa amaryar wata ‘yar hikima ta hanyar sanya ta ta kawo masa ruwa. Wanda a galibi a ƙwarya suke kawo ruwan. Idan suka amshi ruwan sannan suka yi nasarar ganin tsaga ko ‘yar ƙaramar ƙofa a jikin ƙwaryar, to kuma duk wani kokwanto ya kau. Amaryar ta tsira da budurcinta.

    Domin karanta zuwan ilimi ƙasar Hausa danna nan

    A JIYA, yawancin Hausawa ba su san soyayya kafin aure ba. Amma galibi auraren da ake dacen samun wanzuwar soyayya kafin su, to tattaunawa tsakanin saurayin da budurwar tana wakana da dare. Saurayin wanda yake samun rakiyar babban abokinsa sukan tura yaro ƙarami gidan su budurwar domin ya kira musu ita su yi hira.

    Wannan wata al’ada ce da ake gudanarwa da dare. Kuma Hausawa suna yi mata laƙabi da ‘zance’. ‘Ta na zuwa’ yawanci ɗan aiken yake sanar da su bayan ya sanar da ita zuwansu. Shi kuma gogan nata yakan bai wa yaron tukwuicin ‘yan kwabbai, domin nuna yabawa da kan-gadon ɗan aikensa. Cikin farin ciki yaron zai amsa daga bisani ya ruga gida baki har kunne.

    Zancensu kacokan suna aiwatar da shi cikin tsananin kunya da kamun kai. Suna zama can nesa da juna, sannan yarinyar takan gaza iya furta komai ga saurayinta, domin tsananin kunya. Sai dai ta riƙa gyaɗa kai, ko girgiza kai, a yayin da fuskarta ke fuskantar ƙasa tana kallon ƙasan.

    Bahaushiyar da sam ba ta iya amsar kuɗin zance ba. Ma’ana ’yar kyautar kuɗin da saurayin zai ba ta lokacin da ya zo zance. Zai yi iya yinsa domin ta amsa, amma sam ba ta iya karba. Wannan ba komai ba ne face tsananin kamun kai da kunya da ke cikin al’adun Hausawa. Ƙarshe dai ba yadda zai yi sai dai ya aje ’yan kuɗin a gefenta. Ita ko ba za ta iya ɗauka ba sai bayan saurayin da abokinsa sun shuri takalmansu sun tafi.

    Auren haɗi ko na ɗan dangi yawanci shi ne auren da Hausawan suka fi yi. Cikin ikon Allah kuma suna zamowa aure mai inganci cike da zaman lafiya. Ana ɗaukar lokaci mai tsawo ba ka ji wata husuma ta ɓullo a tsakanin ma’auratan ba.

    Halayyar auratayyar Hausawa da riƙon aure a zamanin da, da kuma ƙauna da son juna da sauran su, za a iya kamanta ta da karin maganar Hausawa da take cewa ‘Naka naka ne ko ya ci namanka ba zai tauna ƙashin ba’

    Hausawa kenan a wancan zamanin. Amma a wannan zamanin, mukan iya cewa labarin ya sauya salo mutuƙa gaya. Kamannin da aka san su da Malam Bahaushe su ma mukan iya cewa sun sauya. Kamar siffa da kyawunsu, duk da dai an ce shi kyau yana daga cikin idon mai hangensa.

    Wannan sauyin kuma ba komai ba ne ya kawo shi face auratayya da ta shiga tsakanin Hausawa da sauran ƙabilu, kamar Fulani da Nufawa da Barebari da sauransu. Amma auratayyarsu da Fulani ta fi kowacce tasiri da ƙarfi da har ta kai yanzu ‘yan jarida suke kiransu da sunan ‘Hausa-Fulani.’

    A yanzu muna iya cewa al’adar ciyayya ta yi ɓatan-dabo a cikin al’dun Hausawa. Wasu daga cikin ‘yan-matan Hausawa marasa aure sun fara sakin turbar da aka san su da bi. Abin takaici, wasu ana yaudararsu da kuɗi ko ƙyale-ƙyalen duniya domin a kawar da budurcinsu kafin aurensu.

    A YAU Hausawa sun ɗauki ɗabi’ar sakin matansu a kan ‘yan matsalolin cikin aure da za a iya kawar da kai gare su, ko kuma a samo masalaha cikin ruwan sanyi. Daga bisani kuma ya bar ‘ya’yan ita wadda ya saka ɗin a hannun kishiyoyi. Yin hakan kuma ba komai ya ke haifarwa ba face jefa rayuwar yaran a matsanancin ƙunci, domin gallazawar da yaran suke sha a hannun matan mahaifinsu yawancin lokuta.

    Wasu kuma matasan abin mamaki sai ka ga sun share shekaru da dama cikin tsananin soyayya, amma sai su gaza kamanta irin shekarun nan da suka yi na soyayya a cikin rayuwar aurensu. Cikin lokaci ƙalilan sai ka ji igiyar auren ta katse.

    A YAU, shagulgula kamar liyafa, yanka kek da bidiri iri-iri domin gudanar da bikin aure su ne abin da Hausawa suka fi lale da shi. Ba da jimawa ba muka samu labarin wani ango da ya mula ya maƙawa amaryar tasa saki a ranar ɗaurin aurensu.

    ‘Yan mintuna kaɗan da a kai masa amaryar ɗakin amarcinsu. Ba kuma komai ya jawo sakin ba face labarin da ya same shi na gudanar da wata liyafa da amaryar take yi, wanda wani tsohon saurayinta ya ɗauki nauyin haɗa mata. Kuma tun fil-azal angon ya nuna ƙin amincewa da hakan.

    A YAU, matasan Hausawa sun ari al’adar saɓule wando (ass down), ko saka tsukakken wando (pensil), ko askin iskanci irin na shahararren ɗan ƙwallon nan mai laƙabin Balatoli da dai sauran ƙyale-ƙyalen zamani. Wani yayi ma da bai jima sosai da shuɗewa ba, shi ne wata sabuwar rawa da ake yi mata laƙabi da ‘Dab,’ wadda wani mawaƙi ya shigo da ita ƙasar nan mai suna Olamide.

    Ita dai rawar Dab an soma ta kusan shekara shida baya ko kuma kwatankwacin hakan. Kamar dai yadda mawaƙin gambaran nan na ƙasar Amurka wato Bow Bow ya faɗi, ita rawar Dab ta samo asali ne daga al’ummar Kannabis. Wannan shi ne sabon salon yayi ga matasan Hausawa.

    A YAU, wasu Hausawan sun ɗauki halayyar nuna raini ga ‘yan-uwansu da ke karantar harshen Hausa a jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare. Idan kuma ka ce su rubuta sakin-layi guda ɗaya da harshen Hausa, da yawansu ba za su iya rubutawa daidai ba. Turawa da Larabawa da dai sauransu, duk suna karantar harsunansu cikin alfahari da tunƙaho!

    Shahararrun mutane kamar Malami-uban-malamai, Farfesa Ɗandatti Abdulkadir da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da Farfesa M.K. Galadanci da Farfesa Abdulkadir Ɗangambo, Farfesa Abdalla Uba Adamu da sauransu za a iya rubuta su a jikin zinare a matsayin shahararrun masana, kuma jigogi a fannin ilmi da nazarin harshen Hausa a ƙasarmu Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ƙarshe dai an san cewa taɓarɓarewa da wancakali da al’adu masu kyau na gargajiya ba a iya ƙabilar Hausawa ya tsaya ba. Sauran ƙabilun ƙasar nan su ma suna fama da irin wannan matsalolin, ko ma fiye da hakan. A taƙaice dai za mu iya cewa wannan matsala ce da ta shafi duk wani sashi na duniya, sakomakon sauyin zamani.

    Hausawa ma ba su fiye wancakali da al’amuran al’adu masu kyau ba kamar wasu ƙabilun. Za mu iya cewa ƙabilar Hausa tana ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙabilu a Najeriya da ma Afirka gaba ɗaya! Idan ka dubi Hausawan zamani, za ka amince da karin maganar Hausawan da ta ke cewa ‘Bahaushe mai ban Haushi.’ Amma dai Bahausahe ya yi gaskiya da ya ce: KOWA YA BAR GIDA: GIDA YA BAR SHI

    Danna nan don karanta rabe-raben auren Hausawa

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Muhimmacin Tausayi

    Muhimmacin Tausayi

    Tausayi da jin ƙai su ne kyawawan ɗabi’u da suke taimakawa wajen kyautata zamantakewa a tsakanin mutane da al’umma baki ɗaya. Suna da matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan Adam, duba da tasirin su wajen samar da fahimta, zaman lafiya, da haɗin kai. Ga wasu daga cikin muhimmancin tausayi da jin ƙai:

    1. Tallafa wa mabuƙata

    Tausayi yana sa mutum ya dinga taimaka wa waɗanda suke cikin buƙata, kamar talakawa, marayu, da marasa lafiya. Wannan yana taimakawa wajen rage wa mutane raɗaɗin damuwa da ƙunci.

    2. Ƙarfafa zumunci da haɗin kai

    Mutumin da yake da tausayi yana da sauƙin samun ƙauna da girmamawa daga mutane. Wannan yana taimakawa wajen gina dangantaka mai kyau a tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki.

    3. Samar da zaman lafiya

    Lokacin da mutane suka kasance masu tausayi da jin ƙai, suna gujewa zage-zage, husuma, da rashin tausayi wanda zai iya janyo tashin hankali. Wannan yana haifar da zaman lafiya a gida, unguwa, da al’umma gaba ɗaya.

    4. Nuna godiya ga Allah (SWT)

    Tausayi yana nuna cewa mutum yana godewa Allah kan ni’imomin da ya ba shi ta hanyar taimaka wa wasu. Allah yana ƙara wa masu tausayi albarka kuma yana sa su cikin rahama.

    5. Inganta ɗabi’u

    Tausayi yana sa mutum ya kasance mai kyakkyawar zuciya da kyautatawa ga kowa ba tare da nuna bambanci ba. Wannan ɗabi’a tana sa mutum ya zama abin koyi a cikin al’umma.

    6. Samun Rahama da lada a lahira.

    Allah (SWT) yana ƙarfafa mutane su kasance masu tausayi da jin ƙai. Wannan yana da tasiri sosai kan samun lada a lahira, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce:

    “Allah zai yi rahama ga wanda yake tausayi ga mutane.” (Hadisi)

    7. Yin aikin alheri yana ƙara farin ciki

    Taimaka wa wasu yana kawo nutsuwa da farin ciki a zuciyar mutum. Tausayi yana sa mutum ya ji cewa ya taka rawa wajen kyautata rayuwar wani.

    A ƙarshe, tausayi da jin ƙai su ne ginshiƙai na kyawawan ɗabi’u waɗanda ke ɗaukaka mutum da al’umma baki ɗaya. Duk wanda ya rayu da waɗannan halaye zai ji daɗin zaman duniya da makoma a lahira.

    Domin karanta lokacin sanyi danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Muhimmacin Zumunta

    Muhimmacin Zumunta

    Muhimmancin zumunta yana da matuƙar tasiri a rayuwar mutane da al’umma gaba ɗaya. Ga wasu daga cikin muhimmancin ta:

    1. Haɗin Kai Da Fahimtar Juna.

    Zumunta tana ƙarfafa haɗin kai tsakanin dangi da abokai. Tana haifar da yanayi mai kyau inda ake mutunta juna da kuma jin daɗin rayuwa a cikin al’umma.

    2. Taimako A Lokacin Buƙata.

    A lokacin da mutum ya shiga wata matsala, zumunta tana ba da dama ga taimako daga dangi, abokai, ko maƙwabci. Wannan na iya zama taimakon kuɗi, shawara, ko goyon baya ta ruhaniya.

    3. Kula da Jin Daɗi Da Walwala.

    Zumunta tana rage kaɗaici da damuwa, tana kuma ƙara jin daɗi da farin ciki. Dangantaka mai kyau tana taimaka wa mutum wajen samun kwanciyar hankali.

    4. Ci gaban Al’umma

    Ta hanyar zumunta, ana iya haɗa kai don yin abubuwan da za su taimaka wajen ci gaban al’umma, kamar haɗin gwuiwa wajen gina makarantu, asibitoci, ko ayyukan ci gaba.

    5. Karɓar Shawara da Hikima.

    Taimakon zumunta yana ba da dama don karɓar shawarwari masu amfani daga mutane masu hikima da gogewa, musamman daga dattawa cikin dangi.

    6. Tallafawa Marasa Galihu.

    Ta hanyar zumunta, ana taimakon marasa galihu da marasa ƙarfi cikin sauƙi, wanda yake hana su fadawa cikin ƙunci ko talauci mai tsanani.

    7. Gadawar Al’adu da Darajoji

    Zumunta tana taimakawa wajen wanzar da al’adu da kyawawan ɗabi’u a tsakanin mutane, kamar girmama manya, taimakon maƙwabta, da haɗin kai a lokutan bukukuwa ko bala’i.

    8. Ƙarfafa Imanin Addini

    A wasu lokuta, zumunta tana inganta ruhaniya, inda ake yin addu’o’i tare da goyon bayan juna cikin ɓangaren addini.

    Kula da zumunta yana da matuƙar muhimmanci, domin rashin kula da ita na iya kawo rashin fahimtar juna, rarrabuwar kai, ko ma ƙiyayya.

    Domin karanta amfanin folic acid ga mata danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Manufar Rayuwar Duniya

    Manufar Rayuwar Duniya

    Babban abinda Ɗan Adam ya kamata ya fahimta a cikin wannan rayuwa ta duniya shi ne, dukkanin samun nasarar mutum duniyarsa da lahirarsa, ya dogara ne akan fahimtarsa da abubuwan guda shida(6) idan ya fahimce su kuma ya yi aiki da su yadda ya dace, haƙiƙa ya yi nasara, kuma ya samu dukkanin arziƙin duniya da lahira baki ɗaya.Waɗannan abubuwa guda shida(6) su ne uku na ɓangaren ubangijinsa, mahalicci sauran ukun kuma sun shafi ɓangaren Iblis wato Sheɗan, maƙiyinsa.

    1. Ɓangaren ubangijinka mahalicci su ne, ka yi iyakar ƙoƙarinka ka san Allah ubangijinka, ka ba shi matsayinsa na ubangiji maɗaukaki, ka sani ba shi da abokin tarayya, ya fi kowa ƙarfi, ya fi kowa sanin ka, ya fi kowa sonka, ya fi kowa ƙaunarka, kuma ya fi kowa sanin halin da kake ciki, kuma babu abinda yake gagarar sa. Kada ka shiga cikin waɗanda ba su ƙaddara ubangiji gwargwadon matsayinsa ba.

    2. Ka nemi sanin yadda ya tsara yake so ka tafi  a cikin rayuwarka domin ka bi wannan hanyar, domin ita wannan hanyar ita ce za ka bi ka samu ribar wannan rayuwa ta duniya da kuma samun tukwuici na shiga gidan aljanna ranar gobe alƙiyama.

    3. Ka nemi sanin abubuwan alkhairi da arziki wanda ya tanada a cikin aljanna domin waɗanda suka bi shi,  suka yi masa biyayya suka bi umarninsa a nan duniya. Haƙiƙa duk wanda Allah ya taimake shi ya fahimci waɗannan abubuwa, kuma ya yi imani, da aiki da su, to haƙiƙa ya sami dukkan nasara ta rayuwar duniya da lahira, ya kuma samu haƙiƙanin Imani da Allah ubangiji mahalicci.

    Waɗannan da su ne ake samun dukkan nasara a nan duniya da kuma babban rabo a ranar gobe alƙiyama.

    Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane da Iblis Wato Sheɗan
    1. Ka san waye Sheɗan Iblis, ka san menene matsayinsa a wurinka, menene matsayinka a wurinsa.

    2. Ka san waɗanne hanyoyi ne Sheɗan Iblis ya tsara waɗanda zai bi domin ya halakar da kai domin ya sa ka bijirewa Allah ubangijinka mahalicci domin ya haɗa ka da shi a cikin wutar jahannama ranar alƙiyama.

    3. Ka san wace irin azaba da uƙuba Allah ya tanada ga Sheɗan Iblis da waɗanda suka bi shi a nan duniya. Duk yawan karatun da ka yi a duniya, waɗannan abubuwa guda shida(6) kawai ake so ka fahimta, komai tarin karatunka waɗannan su ne abubuwan da ake so ka sani domin saduwa da Allah lafiya, da kuma samun rahamarsa.

    Duk wanda Allah ya taimake shi ya gane waɗannan abubuwa guda shida, kuma ya rayu a kansu, tabbas ya gama arziƙin duniya da lahira. Alhamdulillah.

    Za Mu Ɗora A Mako Mai Zuwa, Insha Allah.

    Danna nan don karanta nauye-nauyen rayuwar aure

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Tarihin Associate Professor Mu’azu Sa’adu Muhammad Kudan

    Tarihin Associate Professor Mu’azu Sa’adu Muhammad Kudan

    An haifi Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad a ranar 13/3/1964 a unguwar Tsauni garin Kudan, Ƙaramar hukumar Kudan Jihar Kaduna. Mahaifinsa Malam Adamu Muhammad (Andiyo) mahaifiyarsa Zainab (Tadabai) Bashir Kudan.Ya zauna a Kano ƙofar Nasarawa wajen wani kakansa Alhaji Aliyu Gwarzo, ya yi karatun allo daga shekara 1969 – 1972, ya dawo Kudan 1972, ya shiga firamare 1973-1979, ya wuce Sakandiren Gwamnati ta Kagoro a ranar Alhamis 24/11/1979-15/09/1981, sai Sakandaren Gwamnati ta Maƙarfi 18/09/1981-01/06/1984. (G.C.E).

    Ya wuce kwalejin zurfafa ilimi (C.A.S) Zariya 15/01/1985- 10/08/1987 (I.J.M.B), sai ya kama aiki da hukumar ba da tallafin karatu ta Jihar Kaduna (Kaduna State Scholarship Board) a sashen kuɗi (Account Section) 09/02/1988 -15/02/1995. Ya wuce ƙaro karatu digirin farko a Jami’ar Usman ɗan Fodiyo Sakkwato 30/7/1994 -31/05/1998. (B.A Hausa).

    Ya koma ma’aikatar ilimi ta Jihar Kaduna (Ministry of Education) a sashen mulki (Admin. Section)15/02/1995-2003, ya koma Jami’ar Sakkwato yin digiri na biyu (M.A Hausa) 2/09/2003 -07/09/2007. Ya koma Kwalejin Tunawa da Sardauna Kaduna 18/12/2003 a matsayin malami.

    Ya yi ritaya a 31/1/2010 yana da shekaru 22 a aikin gwamnati. Ya yi sana’ar tela shekara 30, 1977-2007. Ya koma Jami’ar Sakkwato 12/04/2011-07/11/2015 Yin digiri na uku Ph.D Hausa. Ya yi aure ranar 11/3/1990 yana da ‘ya’ya goma (10).

    Sunayen matan 5 

    1. Asma’u.

    2. Ummukhulsum

    3. Zainab

    4. Hafsat

    5. Fatima

    Sunayen mazan 5

    1.Muhammad Bashir

    2. Abubakar Sadik

    3. Umar Faruk

    4. Suleman

    5. Muhammad Irfan

    Ya yi aikace- aikacen wucin-gadi na koyarwa a:-

    Sashen remidial (KASU) Jami’ar Jihar Kaduna 2007-2008

    2. Kwalejin Adeyemo (Adeyemo College) Kaduna 2009 zuwa 2010.

    3. Kwalejin Shabab (Shabab College of Arabic and Islamic Studies) U/Dosa Kaduna 2006-2010

    4. Kwalejin Albidaya (Albidaya College) Kaduna 2013- 2014.

    5. Ya zama malami Jami’ar Sule Lamido Kafin Hausa Jihar Jigawa 2014-Zuwa yau. A yanzu haka, shi ne shugaban sashin harsunan Najeriya na jami’ar Sule Lamiɗo da ke kafin Hausa ta jihar Jigawa.

    Sunayen maƙalolin sa

    1. Muhammad M.S.(2019); Juga Nabiso. . Takardar da ya gabatar da ita a international Conference da ke jami’ar jihar Kaduna.

    2. Muhammad M.S.(2017); Tashe Majigin Bahaushe. Takardar da ya gabatar da ita a taron shekara-shekara karo na (4th Annual International Conference) a jami’ar jihar Kaduna.

    3. Muhammad M.S.(2017); Muhammadu Ashiru Sarkin Kudan. Takardar da ya gabatar da ita a taron shekara-shekara karo na uku (3rd Annual International Conference) da ke jami’ar jihar Kaduna.

    4.Muhammad M.S.(2019); Kasuwa A Kai Miki Dole: A University Research sponsored by the Sule Lamido University Kafin Hausa.

    5. Muhammad M.S; Sakin Na Hannu. Hausa Prose-Fiction Reader Project. Association of Nigerian Authors, Kano State Branch.

    6.Muhammad M.S; Dabbobi A Tunanin Bahaushe (Ph.D Thesis 2016).

    7. Muhammad M.S; Effect Of Football (P.G.D.E Project 2010).

    8. Muhammad M.S; Hauka A Idon Bahaushe (M.A Disertation 2007).

    9. Muhammad M.S; Zumuncin Bahaushe (B.A Project 1997).

    10. Muhammad M.S; Ire-Iren Abincin Hausawa (I.J.M.B Project 1987).

    11. Muhammad M.S; Kasuwa A Kai maki dole(SLU University Research 2018)

    12. Muhammad M.S; Jirwayen Maguzanci A Rayuwar Mu Ta Yau.

    13. Muhammad M.S; Bauta Da Cinikin Bayi

    14. Muhammad M.S; Kagaggen Zumunci.

    15. Muhammad M.S; Wace Ce Mace ?

    16. Riga-kafi Ya fi Magani

    17. Muhammad M.S; Jibadau Kayan Nauyi (Wanda Yace Babu Yi Masa Aka Yi)

    18. Muhammad M.S; Ballagazar Uwa

    19. Muhammad M.S; Baƙin Bature (Baƙin Mutum Da Kan Banasare)

    20. Saɓalikita Mijin Hajiya (Sunɓulallen Uba)

    21. Ƙawalliya Romon Jaɓa.

    22. Ilimi Farkonka Maɗaci ƙarshenka Zuma.

    23. Maraya da Maraici A Yau – 2014.

    24. Rowa. (Hali, Wayau, Ko Ciwo?).

    25. Kyauta. (Ɗabi’a Ko Baiwa Ko Wauta?).

    26. Ɗa, Na Kowa Ne.

    27. Me Ka Fi, Me Ya Fi Ka, Me Kuke Dai-dai ?

    28. Dokin Zuciya, Ba A Hawanka Sai An Yi Nadama.

    29. Halayen Dabbobi A Bakin Narambaɗa.

    Sunayen Litittafansa 

    1. Bahaushiyar Al’ada.

    2. Tsufa Rigar ƙaya.

    3. Maraya da Maraici.

    4. Mace Babbar Halitta.

    5. Maza Gumbar Dutse.

    6. Haƙƙoki Abin Kulawa.

    7. Ƙuruciya A Al’adar Bahaushe.

    8. Sana’a Sa’a

    9. Tarihin Garin Kudan.

    10. Ziyara A Musulunci.

    11. Zuciya Sarauniya ce.

    Lambobin yabo

    1. Ƙungiyar ɗalibai na jihar Kaduna wanda suke karatu a Jami’ar Usman ɗanfodio a 1997.

    2. Ƙungiyar ɗalibai ta Hausa na Jami’ar Usman Ɗanfodio sokoto a 1997.

    3. Darul tahfizul ƙur’anil kareem Islamiyya Unguwar Dosa Kaduna a 2006.

    4.Markazul Alh Adamu Liddarasatul Islamiyya Unguwar Dosa Kaduna a 2007.

    5. Age Mate association Kafin Hausa a 2019.

    6. Arewa Writers Association of Nigeria (AWAN).

    Sannan kuma, a yanzu halin da ake ciki yana da mataye guda biyu, wato ya ƙara aure. Sannan kuma ya zama mataimakin Farfesa (Associate Professor).

    (Mun samu waɗannan jawaban ne daga Dr. Mu`azu Sa’adu Muhammad Kudan ta hanyar rubutawa da ya yi, ya turo min ta imail ɗi na a ranar Alhamis 02/07/2020).

    Domin karanta rayuwar ‘ya mace a ƙasashen turai da kuma a musulunci danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Dalilan Da Suke Sa A Yi amfani Da Ka-fi Sugar

    Dalilan Da Suke Sa A Yi amfani Da Ka-fi Sugar

    Dalilan sun haɗa da:

    • Sinadarin sugar wacce muka sani (sucrose) yana maƙalewa a haƙori kuma ya haddasa lalacewar haƙorin saboda ƙwayoyin bacteria suke cin sugar a matsayin abinci. Amma shan ka-fi sugar ba ya haifar da wannan matsalar.
    • Shan sugar wacce muka sani (sucrose) ba shi ba ne yake haifar da cutar diabetes. Sai dai idan mutum ya kamu da cutar diabetes ɗin, kuma ya zamo yana shan sugar ɗin, to, cutar diabetes ɗinsa za ta ta’azzara. Amma shan ka-fi sugar ba ya haifar da wannan matsalar.
    • Sayen sugar wacce muka sani (sucrose), akwai kashe kuɗi sosai yanzu. Amma sayen ka-fi sugar ba shi da wannan matsalar ta kashe kuɗi mai yawa.
    • Shan sugar wacce muka sani (sucrose) fiye da kima yana haifar da yin teɓa (obesity), amma shan ka-fi sugar ba ya haifar da wannan matsalar.

     ABINDA YASA SINADARIN KA-FI SUGAR YAKE DA ƊACI-ƊACI BAYAN MUTUM YA GAMA SHANSA

    Ɗacin da mutum yakan ji a bakinsa bayan ya gama cin ko shan abinda aka sanya sinadarin ka-fi sugar a cikinsa yana faruwa ne saboda sinadaran chemical waɗanda ake haɗa su da shi. Chemicals suna da ɗanɗanon ɗaci, ko tsami, ko gishiri, ko bauri ne. Don haka idan mutum ya gama cin ko shan abubuwa masu ɗauke da sinadarin ka-fi sugar, to, babu mamaki idan ya ji ɗaci bayan zaƙin, musamman idan an zuba sinadarin da yawa a ciki. Tsananin jin ɗacin ya danganta ne da yanayin halittar bakin mutum wajen tasirantuwa da ɗanɗano. Ma’ana, wani zai iya jin ɗacin sosai, wani kuwa zai ji kaɗan ne. Amma babban abin lura shi ne ɗacin ba ya cutarwa. Sa’annan ya kamata mutum ya sha sinadarin ka-fi sugar matsakaicin sha.

    MATSAYI NA AKAN SHAN SINADARIN KA-FI SUGAR

    Na yi wannan rubutun ne bisa amana ta ilimi. Ma’ana, domin in faɗi abinda masana suka gano game da sinadarin ka-fi sugar. Amma dai ni ba na yin amfani da shi, saboda zaƙinsa yana yi min yawa, kuma ba na jin daɗinsa a baki. Amma ba ni da wata hujja ta kimiyya wacce za ta sanya in ce yana da matsala ga lafiyar mutum.

    Kuma a fahimta ta, duk mutumin da ya sha sinadarin ka-fi sugar, kuma ya sami matsala, to, hakan zai kasance ne kawai don jikinsa yana bijire ma sinadarin, ko kuma ƙwayoyin cuta sun shiga cikinsa sun gurɓata shi.

  • Nasiha

    Nasiha

    BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

    ALKAWARIN ALLAH GASKIYA NE:

    Allah Maɗaukaki Ya ce:

                                                               “أَيْنَمَا تَكُونُوا يُدْرِككُّمُ الْمَوْتُ”
    سورة النساء: 78

    “Duk a in da kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku…”

    Ibnu Katheer ya ce:

    Duk in da kuka kasance mutuwa za ta zo ta riske ku, saboda haka ku kasance a kan ɗa’a ma Allah kuma kamar yadda Allah ya umarce ku, domin shi ne alkhairi a gare ku, saboda ita dai mutuwa dole ce kuma babu halin guduwa mata, sa’annan zuwa ga Allah ne makoma take, duk wanda ya kasance mai biyayya ne gare Shi sai Ya saka masa da mafificin sakamako, Ya ba shi mafi cikan lada…

    Allah ya sa mu dace. Allah ya sa mu cika da kyau da imani Bijahi Rasulillahi (S.A.W)

    Danna nan don karanta nauye-nauyen rayuwar aure

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Tarihin Garin Rigasa Da Ke Jihar Kaduna

    Tarihin Garin Rigasa Da Ke Jihar Kaduna

    Rigasa ƙauyen birni ne da ke karamar hukumar Igabi a yankin Kaduna ta tsakiya a cikin jihar Kaduna, Nigeria. Na kira yankin ne da KAUYEN BIRNI saboda wasu ƴan dalilai wanda zan bayyana su a nan gaba.

    Garin RIGASA yana ɗaya daga cikin yanki mafi girma da yawan jama’a a Najeriya, tare da ƙiyasin kimanin mutane miliyan uku ne suke rayuwa a cikin sa. Yana ɗauke da yankuna kamar su, Ɗanmani, Nariya, Maƙera, Mashi, Hayin Malam Bello, Sabon-garin Rigasa, Kwate, Mai-giginya, da sauransu.

    Yana da faɗin kusan kilomita 14 zuwa 8. Rigasa yana ɗaya daga cikin unguwanni 255 na jihar Kaduna. Garin Rigasa yana da manyan makarantun firamare da sakandare kama daga na gwamnati da masu zaman kansu masu tarin yawa, yana da makarantun islamiyyu su ma masu yawan gaske duk a cikin garin Rigasar.

    Haka kuma yanzu haka akwai tashar jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja wanda wannan tashar tana cikin garin Rigasar ne. An yi imanin cewa Rigasa na karɓar baƙuncin manyan baƙi irin su Shugabanin siyasa, sarakuna, Air Vice Marshal Maisaka (marigayi), Shugaban Karamar Hukumar Igabi, ba tare da ambaton wasu Farfesa da Likitoci da dama da ke zaune a cikin garin ba.

    A yanzu haka Rigasa tana da mahaddata Alkur’ani masu yawan gaske, manyan likitoci, manyan ƴan siyasa, malamai, ‘yan jarida da dukkan wani nau’i na masu ilimin kimiyya da fasaha.

    Kafin rikicin addini na 2000 a jihar Kaduna, akwai ƙabilu da yaruka masu yawa a cikin Rigasar wanda a halin yanzu an yi ittifaƙin Hausawa ne mafiya yawa a cikin garin kuma al’adar Hausa ita ce al’adar wannan yanki. Kashi 90% na al’ummar wannan yanki musulmai ne.

    Danna nan don karanta dokar Najeriya

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Sinadarin Ka-Fi Sugar (Artificial Sweetners)

    Sinadarin Ka-Fi Sugar (Artificial Sweetners)

    Sinadarin ka-fi-sugar shi ne ake kira “artificial sweeteners” a turance. A likitance kuwa ana kiransa “non-nutritive sweeteners” ko “non-caloric sweeteners”. Sinadarin ka-fi sugar yana samar da ɗanɗano mai matuƙar zaƙi a baki, wanda ya fi na sugar wacce muka sani (sucrose), don haka ne ma ake yin amfani da shi a maimakon sugar. Ita sugar ta asali tana ƙunshe da sinadarin kuzari wanda ake kira “calorie”.

    Ana samun calorie ne a cikin rukunnan abinci ko abin sha daban-daban, kamar abinci mai samar da kuzari (carbohydrates), abinci mai sanya girman jiki (proteins), abinci mai tara kitse a cikin jiki (fats). Idan mutum ya ci abinci mai ɗauke da calories, to, jikinsa zai sarrafa calories ɗin domin samar da kuzarin yin ayyukan yau-da-kullum (energy). Kuma calories ɗin ne suke taruwa su zamo taiba (obesity) a jikin mutum, musamman idan ba ya yin ayyukan motsa jiki (physical exercise).

    Amma shi sinadarin ka-fi sugar ba ya ƙunshe da calorie ko ɗaya a cikinsa. Sinadaren zaƙi da suke cikinsa ana samunsu ne daga ruwan sinadaren kimiyya (chemicals) waɗanda ake sarrafawa a cikin ɗakin binciken kimiyya (laboratory), ko kuma tsirrai (plants) amma waɗanda aka sarrafa a ɗakin kimiyya.

    Danna nan don karanta yadda ake haɗa sinadarin bleach

    NAU’O’IN SINADARIN KA-FI SUGAR 

    Akwai nau’o’in sinadarin ka-fi sugar waɗanda ake yin amfani da su a ƙasashen duniya daban-daban, ko dai a gidaje, ko kuma a kamfanonin sarrafa abinci da abin sha. Kaɗan daga cikinsu su ne:

    . Allulose: ana tatso shi ne daga cikin ɓaure (fig), alkama (wheat), da zabibi (raisins). Yana da zaƙi fiye da sugar wacce muka sani (sucrose) da kaso 70%. Duk da zaƙinsa, allulose ba ya haifar da taruwar kitse a cikin jiki, domin ba ya narkewa ya bi jiki. Ma’ana, mutum zai fitsarar da shi ne ko kuma ya yi kashinsa yadda ya sha shi.

    . Acesulfame potassium: wanda ake kira da suna “Ace-K”, ana samun sa ne daga sinadarin potassium wanda aka sarrafa a ɗakin kimiyya na laboratory. Yana da zaƙi fiye da sugar wacce muka sani (sucrose) da kaso 200%. Duk da zaƙinsa, acesulfame potassium ba ya haifar da taruwar kitse a cikin jiki, kuma hukomomin kula da ingancin magunguna da abinci na duniya sun amince da a yi amfani da shi a cikin abinci.

    . Aspartame: ana samun sa ne daga sinadaran amino acids guda biyu masu suna “aspartic acid” da “phenylalanine” wanɗanda aka sarrafa a ɗakin kimiyya na laboratory. Yana da zaƙi fiye da sugar wacce muka sani (sucrose) da kaso 200%.

    Duk da zaƙinsa, aspartame ba ya haifar da taruwar kitse a cikin jiki, kuma hukomomin kula da ingancin magunguna da abinci na America (Food and Drug Administration – FDA) da na ƙasashen turai (European Food Safety Authority – EFSA) da Nigeria (National Agency for Foods and Drugs Administration and Control – NAFDAC) sun amince da a yi amfani da shi a cikin abinci. Sai dai, mutanen da ba su da sinadarin phenylalanine hydroxylase (PAH) a cikin jikinsu wanda yake taimakon hanta wajen narkar da abinci, bai kamata su yi amfani da shi ba, saboda rashin sinadarin zai sanya hanta ta kasa yin aikinta na narkar da abinci.

    . Cyclamate: ana samunsa ne daga haɗakar sinadaran “cyclohexylamine” da “sodium” da “calcium” wanɗanda aka sarrafa a ɗakin kimiyya na laboratory. Yana da zaƙi fiye da sugar wacce muka sani (sucrose) da kaso 30% zuwa 50%. Duk da zaƙinsa, cyclamate ba ya haifar da taruwar kitse a cikin jiki, kuma hukomomin kula da ingancin magunguna da abinci na ƙasashen turai sun amince da yin amfani da shi.

    Amma America ba ta amince da shi ba saboda zargin da aka yi a shekarar 1969 cewa cyclamate yana da hatsarin haddasa cutar cancer ta mafitsara (bladder cancer). Tun daga wannan lokacin, masana sun yi bincike daban-daban domin tabbatar da zargin. Sakamakon wasu daga cikin binciken ya karyata zargin, sa’annan sakamakon wasu bincikin ya tabbatar da zargin. Don haka har yanzu hukumar FDA ba ta ɗauki matsayi ba akan yin amfani da shi.

    . Mogrosides: ana samunsa ne daga itaciyar “monk fruit” wacce ake samun ta a ƙasar China da Thailand, kuma suna kiransa “Luo Han Guo”, Yana da zaƙi fiye da sugar wacce muka sani (sucrose) da kaso 150% zuwa 250%. Duk da zaƙinsa, mogrosides baya haifar da taruwar kitse a cikin jiki, domin baya narkewa ya bi jiki. A shekarar 2017, wani kamfanin Chinese ya nemi EFSA da ta yi bincike a kansa, kuma daga nan aka tabbatar da ingancinsa a America da Australia.

    . Saccharin: ana samunsa ne daga sinadarin “toluene” wanda ake samunsa daga gurɓataccen man petroleum kuma aka sarrafa a ɗakin kimiyya na laboratory. Yana da zaƙi fiye da sugar wacce muka sani (sucrose) da kaso 200% zuwa 700%. Duk da zaƙinsa, saccharin ba ya haifar da taruwar kitse a cikin jiki, domin ba ya narkewa ya bi jiki.

    An yi muhawara mai zafi a kan ingancin yin amfani da shi a cikin abinci a ƙasar America a shekarar 1970 saboda zargin da aka yi na cewa saccharin yana da hatsarin haddasa cutar cancer ta mafitsara. Amma duk binciken kimiyya da aka yi bayan wannan lokacin ba su tabbatar da zargin ba don haka, hukumomin kula da magunguna da abinci na duniya suka amince da yin amfani da shi.

    . Steviol glycosides: ana samunsa ne daga itaciyar “Stevia rebaudiana” wanda ake samunta a ƙasar South America da Japan. Yana da zaƙi fiye da sugar wacce muka sani (sucrose) da kaso 200% zuwa 400%. Duk da zaƙinsa, steviol rebaudiana ba ya haifar da taruwar kitse a cikin jiki, domin ba ya narkewa ya bi jiki.

    A shekarar 1987, hukumar FDA ta America ta hana yin amfani da shi saboda zargin cewa yana haddasa cutar cancer ta mafitsara. Amma bayan yin nazari mai zurfi daga masana, FDA ta amince da yin amfani da shi a watan December na 2008.

    . Sucralose: ana samunsa ne daga sinadarin “sucrose” na sugar wacce muka sani wanda aka sarrafa a ɗakin kimiyya na laboratory. Yana da zaƙi fiye da sugar wacce muka sani (sucrose) da kaso 400% zuwa 700%. Duk da zaƙinsa, sucralose ba ya haifar da taruwar kitse a cikin jiki, domin ba ya narkewa ya bi jiki.

    A shekarar 2005, ƙungiyar kamfanoni masu yin sugar a America sun yi ƙoƙarin ɓata wa sucralose suna da zargin cewa yana da hatsari ga lafiyar mutum. Amma daga baya kotuna sun sanya an yi bincike an tabbatar da rashin gaskiyar wannan zargin, don haka hukumomin duniya suka amince da yin amfani da shi.

    . Sugar alcohols: ana kiransa polyols, ana samunsa ne daga sinadaran ’ya’yan itatuwa. Sinadaran su ne:

    (a) Xylitol wanda ake samu a cikin  berries, plums, da corn husks 

    (b) Erythritol wanda ake samu a cikin grapes, melons, da pears 

    (c) Sorbitol wanda ake samu a cikin apple, pears, peaches, cherries, carrots, sweet potatoes 

    (d) Mannitol wanda ake samu a cikin seaweed, mushrooms, watermelons, pineapples 

    (e) Maltitol wanda ake samu a cikin wheat, corn, potatoes 

    (f) Isomalt wanda ake samu a cikin sucrose.

    Domin karanta muhimman abubuwan da suke inganta lafiya danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu