Nauye-nauyen Rayuwar Aure

0
34

A musulunce, rayuwar aure ba ta kyautatuwa ta zama nagartacciya har sai idan an aiwatar da ita ta salon da Musulunci ya tsara, ta hanyar ɗorawa ma’aurata wasu nauye-nauye da ake buƙatarsu da su sauke su kamar haka:

1. Haƙƙoƙin mace a kan mijinta. 

  1. Haƙƙoƙin miji a kan matarsa. 
  2. Haƙƙoƙin da miji da mata suke tarayya a kansu. 
  3. Haƙƙin wanda mutuwa ta raba shi da abokin zamansa daga cikin ma’aurata. 

HAƘƘOƘIN MACE A KAN MIJINTA

(a) Sadaki: Wanda bayaninsa ya riga ya gabata. 

(b) Ɗora iyali a kan bin Allah tare da rainonta da kyawawan ɗabi’u. Shi wannan haƙƙi na biyu da samuwarsa da kuma ɗorewarsa ne mace za ta kyautata tsakaninta da ubangijinta, da kuma tsakaninta da bayinsa. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Da farko Allah Mai girma da Buwaya yace: 

“ ka ambaci (labarin) Isma’il cikin wannan littafi (Alƙur’ani), haƙiƙa shi mai cika alƙawari ne, kuma Annabi ne Manzo. Ya zamanto yana umartar iyalinsa da (tsaida sallah da kuma ba da zakka, sannan kuma shi yardajje ne a wajen ubangijinsa ). 

Abin nufi a nan, Annabi Isma’il yardajjen Allah, a zamansa da iyalinsa yana umartarsu ne da su riƙa tsayar da sallah, kuma su riƙa bayar da zakka, domin alaƙarsu da Ubangiji ta kyautata. 

Sannan kuma mun ji cewa shi mutum ne mai cika alƙawari, sanin kowa ne kuma duk wanda yake haka za ka tarar yana ƙoƙarin rainon iyalinsa da yin haka. 

Sannan kuma Allah ya ce da Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi): 

“ka umarci iyalinka da tsai da Sallah kai ma kuma ka yi haƙurin dawwama akan tsai da ita, ba zamu tambaye ka dukiya ba, mune ma zamu azurta ka, kuma kyakkyawan ƙarshe (duniya da lahira ) ga masu tsoron Allah yake”.

Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya aiwatar da wannan umarni da Allah ya yi masa kamar yadda Imamut- Tirmizi ya rawaito hadisi cewa, an karɓo daga Ummu- salama Allah ya yarda da ita tace: “ Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya kasance idan watan Ramadan ya rage kwana goma ya ƙare, ba ya barin ko da mutum ɗaya daga cikin mutanen gidansa matuƙar dai zai iya yin sallar dare face sai ya tashe shi (domin ya yi)”. 

To, ‘yan uwa, idan Annabi bai bar sallar nafila ta wuce mutanen gidansa ba; ina kuma ga sallar farilla. 

Sannan kuma Allah Maɗaukaki yace: “yaku waɗanda kuka ba da gaskiya, ku tserar da kanku da kuma iyalanku (daga shiga ) wuta (wadda ) mutane da duwatsu ne makamashinta, kuma akwai wasu ƙarfafan mala’iku masu kauri da suke tsaron ta, waɗanda ba sa saɓawa Allah abin da ya umarcesu da shi, kuma suna aikata duk abin da aka umarce su da shi”. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

A wannan ayar kuma kiran muminai gaba ɗaya Allah ya yi, sannan ya umarce su da su dage su bi irin turbar da Annabawa suka bi, wajen ɗora kansu da iyalansu a kan hanyar bin Allah da nisantar saɓa masa, domin su gudu tare su kuma tsira tare. 

Har wa yau, Bukhari ya rawaito hadisi da aka karɓo shi daga Malik ɗan Huwairis Allah ya yarda da shi yace: Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace da (ayarin) jama’ar Abdul- Kais da suka zo wajen “su kiyaye imaninsu da kuma ilimin da ya sanar da su shi, sannan kuma yace da su, “ku koma wajen iyalanku ku sanar da su”. 

Saboda waɗannan dalilan da muka ji ya zama lallai a kan miji ya sanar da matarsa ilimin yadda za ta bautawa ubangijinta, ko kuma ya turata inda za ta je ta koya, kamar yadda matan sahabbai suke zuwa wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) su koyo addini. 

Bayan haka, an karɓo daga Amru ɗan Ahwas Allah ya yarda da shi yace, ya ji Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) a hajjinsa ta bankwana yana cewa: “ku saurara, ku yi wa mata wasici da alheri”. ( Tirmizi ne ya rawaito shi ). 

Haka kuma an karɓo daga Aisha (Allah ya yarda ita ) ta ce: “ (wata rana ) Yahudawa sun zo wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) sai suka ce dashi: “Assamu alaikum” wato halaka ta tabbata a kanku, a maimakon su ce:

“Assalamu alaikum” wato amincin ya tabbata a gare ku, jin haka, sai Aisha ta ce: Halaka a kanku, Allah kuma ya tsine muku; ya yi fushi da ku. 

Sai Annabi yace da ita: ‘A a Aisha, yi a hankali, ina umartarki da yin sauƙi, kuma ki kiyayi kausasawa da munanan maganganu. Sai kuwa tace da Annabi ba ka ji abin da sukace ba ne? Annabi yace: To ke ba ki ji abin da na ce da su ba? Ai na mayar musu da martani da cewa a kansu dai. Sai Allah ya amsa mini addu’ar da na yi musu, su kuma ba zai amsa musu wadda suka yi mini ba. (Bukhari ya rawaito shi). 

A nan idan muka lura da kyau, za mu fahimci cewa, waɗannan hadisai suna ɗora magidanta ne a kan hanyar da ya kamata su ɗora matansu a kai, ta nusar da su yadda ya kamata su zauna da mutane a cuɗanyarsu da su. Allah dai ya ba mu ikon kulawa da kuma aiki da wannan koyarwar ta Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi), amin. 

(c) Samawa Mace Mazauni (Gida ko ɗaki): 

Shi kuma wannan nauyi ya hau kan miji ne a sakamakon faɗar Allah Madaukaki daya ce: “ku zaunar da su (mata) a inda kuke zaune dai-dai halinku, kada ku cuce su don ku ƙuntata musu”. 

Domin Karanta Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe Danna Nan

Da kuma faɗar Allah Maɗaukaki cewa: “ ku ji tsoron Allah Ubangijinku kada ku fitar da su daga ɗakunansu, su ma kada su fita, sai dai idan sun zo da mummunan aiki mabayyani, waɗancan iyakokin Allah ne, to haƙiƙa ya cuci kansa”. 

Saboda haka, haramun ne mai gida yace da matarsa ta fice ta bar masa gidansa, ko ɗakinta don ya saketa, matuƙar dai ba ta gama idda ba. Haka kuma ita ma mace bai halatta ta bar gidan mijinta ba don ya sake ta har sai bayan ta gama idda. Wannan sai ya tabbatar mana da cewa alhakin miji ne ya tanadar wa matarsa mazauni. 

(d) Ciyarwa da Tufatarwa: 

Haka ma ciyarwa da tufatarwa, hakki ne da mace take da shi a kan mijinta. Saboda faɗar Allah Maɗaukaki yace: 

“ ciyar da mata da tufatar da su gwargwadon iko, wajibi ne a kan wanda aka haifawa da, ba a ɗorawa (kowanne) rai sai gwargwadon ikonsa”. A wata ayar kuma Allah Maɗaukaki yace:

“ Mai yalwa ya ciyar daga yalwarsa, wanda kuma aka ƙuntata arzikinsa, (wato talaka), to, ya ciyar daga ɗan abinda Allah ya ba shi, Allah ba ya ɗorawa kowacce rai sai abinda ya bata, da sannu Allah zai sanya sauƙi bayan matsi (tsanani)”. 

A hadisance kuwa, an karɓo daga Hakim ɗan Mu’awiya daga babansa (Allah ya yarda da shi) yace: “ Na tambayi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) cewa, menene haƙƙin matar kowannenmu a kansa? Sai yace: “ Ka ciyar da ita idan ka ci, ka kuma tufatar da ita idan ka tufata…”. ( Ahmad da Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi). 

Sannan kuma sahabin Annabi Amru ɗan Ahwas ( Allah ya yarda da shi ) yace: Haƙiƙa ya ji Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) a hajjinsa ta bankwana yana cewa: “ ku saurara, hakika matanku na da haƙƙi a kanku, haƙƙinsu a kanku ku kyautata tufatar da su, da ciyar da su”.( Tirmizi ne ya rawaito). 

Bisa dogaro da waɗannan dalilai, ya zama tilas a kan miji ya ciyar da matarsa, ya tufatar ita gwargwadon irin halin da yake da shi. 

Sannan kuma amana ce a wuyan miji ya ciyar da matarsa da halal ba da haram ba.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceRanar Haɗuwar Ango Da Amarya
Labarin na GabaHaɗarin Ƙuntatawa Iyali Wajen Ciyarwa