Tag: ilimi

  • Fara Jinin Haila Da Bayanin Siffofinsa

    Fara Jinin Haila Da Bayanin Siffofinsa

    Yaushe mata suka fara jinin haila?

    Farkon fara jinin haila ya kasance ne a kan Hauwa’u matar Annabi Adamu, amincin Allah ya tabbata a gare su;

    Bayan an sauko da su daga Aljanna zuwa duniya. Sannan Allah ya hukunta shi a kan ‘ya’yan Annabi Adamu mata.

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa ya ce, “Haƙiƙa, wannan wani al’amari ne da Allah ya hukunta shi a kan ‘ya’yan Annabi Adamu mata” .

    Mece ce sifar jinin Haila?

    Jinin haila baƙi ne, mai wari, kuma ƙazanta ce. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa ya ce, “Haƙiƙa, shi jinin baƙi ne kuma yana da ƙarni, kuma Allah tsarkakakke maɗaukaki ya ce:

    “Kuma suna tambayar ka game da jinin haila, ka ce da su ƙazanta ne…”. Kuma shi wannan jinin yakan zo ja ko fatsi-fatsi, mai baƙi kuma a ƙarshensa, yakan canja ruwan ƙasa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ambaton Abin Da Ake Sanin Zuwan Jinin Al’ada Da Shi Da Yankewar sa danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Yadda Za Ki Gyara Kanki danna nan.

  • Jinin Haila Da Jinin Biƙi

    Jinin Haila Da Jinin Biƙi

    Darasi Na Farko Game Da Jinin Da Yake Fita Daga Mace

    Game Da Jinin Da Yake Fita Daga Mace, Jini Nawa Ne Yake Fita Daga Mace? 

    Jini Uku Ne Yake Fita Daga Mace, su ne: Jinin Haila, Jinin Biki da Jinin Cuta.

    Mece ce Haila?

    Haila ita ce jinin da yake fita daga mahaifar mace idan ta balaga, a wasu kwanaki sanannu. 

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa ya ce da Hannatu ‘yar Jahshi.

    Ki yi hailarki kwana shida, ko kwana bakwai. Hakan sai ya zama shi ne galibin kwanakin jinin haila, kuma yana iya ƙasa da haka ko ya ƙaru.

    Mene ne Jinin Biƙi?

    Jinin biƙi shi ne jinin da yake fita daga gaban mace saboda haihuwa ko da abin da aka Haifa ɓari ne.

    Mene ne Jinin cuta?

    Jinin cuta shi ne, ci gaban fitar jini daga gaban mace saboda rashin lafiya, ba a lokacin jinin haila. kuma ba a lokacin jinin biƙi ba.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mene Ne Hukuncin Yi Wa Mace Kaciya? danna koren rubutun nan.

  • Alamomin Tsufa.

    Alamomin Tsufa.

    Da zarar tsufa ya cimma mutum, alamominsa za su bayyana a tare da shi, kamar:

    a. Yanƙwanewar fata da tattarewa.
    b. Tsanantar cututtukan gado kamar hawan jini, ciwon shuga, olsa mai riƙe baya da ƙirji (basir).
    c. Raunin ƙwayoyin dake ba wa jiki garkuwa.
    d. Ciwon gaɓoɓi. Da dai sauransu.

    Saboda haka, babu wanda zai tsufa wani mai ba da magani ko likita ya ba shi maganin da zai tafiyar masa da tsufansa ko gajiyawar da ya yi.

    Bayan haka, an karɓo Hadisi daga Abu Hurairi Allah ya yarda da shi ya ce: “Haƙiƙa ya ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa “Tabbas a habbatus sauda (baƙin algaru) akwai waraka daga kowane ciwo sai dai mutuwa.” Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
    Wato babu wani magani da yake hana mutuwar bawa idan lokacin mutuwarsa ya yi, kuma yadda tsufa ba shi da magani, to haka ma mutuwa ba ta da  magani.
    Bayan haka, malaman Hadisi suna fuskantar da maganar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ta cewa akwai waraka daga kowane ciwo a tattare da habbatus-sauda cewa, wannan bayani ba Manzon Allah ya shafi cututtukan da sanyi yake sabbabawa ne, ba kowane irin ciwo ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Amfanin Kaho danna nan.

    Wannan bayanin an ciro Shi ne daga littafin Akula Da Lafiya Wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Mene Ne Kishi

    Mene Ne Kishi

    Kishi shi ne, sosuwar zuciya da ɓacin ran da suke jawo fushi, a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani, a kana bin da wanin ya keɓanta da son sa, ko mallakar sa.

    Mene ne Asalin kishi

    Asalin kishi shi ne ƙyama da ƙiyayyar munanan abubuwa.

    Mene ne Abin da Yake Jawao Kishi

    So da ƙaunar wanda aka yi kishi domin sa shi ne ke jawo kishi.

    Mene ne Matsayin Kishi

    Kishi wata maɗaukakiyar halayya ce, kuma wata kyakkyawar sifa ce da ta dace da a siffatu da ita.

    Gaske ne kishi na da Fage-fage?

    Na’am, gaske ne, kishi yana da fage-fage, da ake yin sa da aiwatar da shi a cikinsu, ga jerinsu kamar haka:
    1. Kishi a fagen tsare addinin Allah da dokokinsa. An karɓo hadisi daga Aisha (Radiyallahu An ha) ta ce: “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai taɓa dukan wani abu ko wata mata ko wni hadimi da hannunsa ba, sai dai a yaƙi saboda Allah, don ɗaukaka addinin Allah, kuma ba a taɓa munana masa bay a ɗau fansa; sai dai fa in an keta hurumin wata dokar Allah ne, sai ya ɗau fansa saboda Allah Maɗaukaki” .
    2. Kishi a fagen tsare mutuncin kai
    3. Kishi a fagen tsare darajar iyalai kamar mai gida ya sa tsaron da iyalansa ba za su samu damar yin shiga ta rashin mutunci ba, ko kuma yin barkwanci da maza ba.

    Domin karanta cikakken bayani akan Kishi Iri Nawa Ne danna nan.

    Wannan bayani anciro shine daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafi danna nan.

  • Mu Ɗin Su Wanene?

    Mu Ɗin Su Wanene?

    Mu halitta ce ta jinsin mutane, kuma muna daga cikin waɗanda Allah bai halicce su domin komai ba, sai domin su bauta masa kawai. Saboda haka, Ya ba mu hankali domin mu yi ilmi, da shi ne za mu san dai-dai kuma mu san abin da ba dai-dai ba, mu bambance tsakanin gaskiya da ƙarya, mu gane bambanci shiriya da ɓata. Da haka za mu iya yin aiki nagari, mu kuma nesanci miyagun ayyuka.

    Mutum cikakke shi ne wanda ya yi imani da Allah da Manzo Sa, kuma ba ya rabuwa da yin managarcin aiki, idan a ka samu saɓani, ya yi tuntuɓe, ya aikata kuskure, sai ya yi sauri ya tuba ya koma ga Allah Mahalicci , saboda shi mai imani ne da Allah, kuma mai yin koyi da Manzon Allah (S.A.W).

    Wannan ita ce siffa ta cikikken mutum, a mahangar Musulunci. Ba kawai kasancewar sa mai ɗauke da kai da ƙafa da iya magana, da dariya ba, ya zama tilas sai ya haɗa waɗannan siffofi sannan zai amsa sunansa Ɗan’Adam. Daga nan ne idan an yi tambaya: “Mu Ɗin Su Wane Ne?” Za mu cancanci bayar da amsar: “Mu mutane ne”.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ɗan’Adam Kamar Yadda Allah Yake Son Sa wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa domin karanta cikekken littafin nan DANNA KOREN RUBUTUN NAN

  • Matakan Kula Da Tarbiyya Guda 100

    Matakan Kula Da Tarbiyya Guda 100

    A wannan matashiya, za a kawo taƙaitattun bayanai a kan mataki da hanyoyn tarbiyya da ya kamata iyaye su yi, ta hanyar karanta waɗannan bayanai, su kuma haɗa kai wajen aiwatar da su, domin samun zuri’a managarciya mai amfani ga kowa, zuri’ar da za ta samu lada mai ci gaba bayan mutuwar iyaye. Allah ka sa mu dace.

    1.Tausayi da jinƙai

    Ya kamata iyaye su kasance masu tausayi da Jin ƙai da bi sannu-sannu wajen tarbiyyar ‘ya’ya. Su yi koyi da Manzon Allah (S.A.W.) yadda yake tausaya wa ƙananan yara, yake jan su a jiki.

    2. A guji zagi da tsinuwa

    Waɗansu iyayen suka ɗauka gallazawa da tsanantawa da zagi da la’anta da ɗaure fuska shi ne kaɗai zai sa ɗa ya taso da tarbiyya. A gaskiya wannan kuskure ne babba.

    3. A guji azabtarwa da yawan duka

    Wannan ma kuskure ne ta yadda za ka ga waɗansu iyaye har hana ‘ya’yansu abinci suke yi, ko su yi musu zigidir su zane su, wannan yana da mummunan tasiri a fannin tarbiyya.

    4. Koyarwa

    Ya wajaba a rinƙa koyawa ‘ya’ya abinda zai amfane su da abin da zai cutar da su. A yi wannan koyarwar mataki-mataki gwargwadon shekaru da fahimtar yaro.

    5.Wasiyyar Lukman (A.S)

    Ya kamata a ɗora tarbiyyar ‘ya’ya kan wasiyyar Lukman (A.S) ga ɗansa wacce Allah Ta ala ya kawo ta a suratu
    Lukman aya ta 12 19. Domin ta ƙunshi gaba ɗayan turakun tarbiyya. Yi ƙoƙari ku karanta waɗannan ayoyi tare da sanin ma’anoninsu.

    6. Koyar da ladabi

    Ladabi shi ne gishirin zaman duniya, wanda ba shi da ladabi komai ilminsa komai kuɗinsa komai mulkinsa ya yi asara. Lallai ne a koya wa ‘ya’ya ladabin zama da kowane irin rukuni na mutane, ladabi ga Allah da Manzonsa da Alƙur’ani da sauransu.

    7. Tsoron Allah Ta’ala

    A cusa wa yaro aƙidar tsoron Allah Ta’ala da yarda da cewa duk inda mutum yake Allah yana jin sa yana ganinsa yana sane da duk abinda yake aikatawa, babu abin da yake ɓuya a gare shi.

    8. Imani da Alƙiyama

    A dasa masa wannan a zuciyarsa, ya yarda cewa a wannan rana. Allah zai yi sakamako ga kowa kan abin da ya aikata na alheri da Aljanna ko na sharri da Wuta.

    9. Ladabi ga Manzon Allah (S.A.W.)

    A koya wa ‘ya’ya ladabi ga Manzon Allah (S.A.W.) ta yadda za su yi cikakken imani da shi, su rinƙa girmama shi, kada su yi masa kishiyoyi, su sallama masa, su ƙanƙame sunnarsa su tsani bidi’a, su guji munana ladabi a gare shi.

    10. Ƙaunarsa da sahabbansa da iyalansa

    A dasa ƙaunar Manzon Allah (S.A.W.) da sahabbansa da iyalansa (R.A) a zukatan ‘ya’ya ta yadda za su rinƙa koyi da su. Su guji aƙidar ƙin sahabbai da zagin su da allanta iyalan Annabi (S.A.W.)

    11. Ladabi ga Al-ƙur’ani

    Su yi imani da shi, su rinƙa ƙaunarsu., su haddace shi su san ma’anarsa, su rinƙa aiki da shi a kowanne ɓangare na rayuwarsu. Su ringa girmama shi ya zama shi ne jagoransu a rayuwa.

    12. Bin lyaye

    Lallai a koya musu biyayya ga iyayensu, musamman Uwa. Su ringa girmama su, su rinƙa yi musu godiya, da tausaya musu da taimakon su da kaucewa saɓa musu.

    Yana daga ladabi ga iyaye sakaya sunayensu, Kada ɗa ya Jawo musu zagi, kada ya ɗaga muryarsa sama da ta su, ya yi magana da su cikin tausasawa da ganin girma.

    14. Babu biyayya Cikin saɓon Allah.

    A sanar da ‘ya’ya cewa babu wani mahaluƙi kowane ne shi da za a yi masa biyayya in ya yi umarni da saɓon Allah Ta’ala ko Manzonsa (S.A.W.).

    15. A kyautata musu koda sun kauce hanya

    Ƙin bin iyaye a kan saɓa wa Allah Ta’ala ba ya nufin a daina kyautata musu, a’a, a ci gaba da kyautata musu amma kada a yi musu biyayya a kan saɓon Allah Ta’ala. A koyar da ‘ya’ya wannan.

    16. Koyi da Annabawa da Salihan bayi.

    A nuna wa ‘ya’ya cewa a faɗin duniyar nan, babu waɗanda suka cancanci a yi koyi da su sai Annabwa da Sahabbansu da sauran bayin Allah nagari. Su guji kwaikwayon maƙiya Allah; maƙiya addinin Allah da Manzonsa.

    17. Girmama Malamai

    A koya musu girmama malamai da martaba su, kada su rinƙa kiransu da sunayensu, ballantana da sunan banza. Kada a rinƙa kushe malami a gabansu, a nuna musu cewa malami uba ne.

    18. Umarni da Sallah

    A tilasta su, su rinƙa yin sallah daga shekara bakwai, in sun shekara goma suka ƙi yin salla a doke su. Kafin su shekara bakwai a rinƙa lallaɓa su da kwaɗaitar da su a kan salla.

    19. Alamomin Balaga

    Tun kafin su balaga, ya wajaba iyaye da malamai su sanar da su alamomin balaga da sanar da su cewa, da zarar sun ga waɗannan alamomi, to, fa dokokin Allah sun hau kansu, kada su yi ta ɓarna ko su yi ta wasa da ihu suna jin cewa wai su yara ne.

    20. Umarmi da kyakkyawa da hana mummunan aiki.

    A sanar da ‘ya’ya kyawawan ayyuka da kishiyoyinsu, a koya musu hanyoyi umarni da kyawawan ayyuka a hana munana, bisa koyarwar Ƙur’ani da sunna da bin salon magabata na Ƙwarai.

    21. Girmama manya da tausaya wa ƙanana

    Iyaye su koya wa ‘ya’yansu su rinƙa yiwa duk wanda ya girme su kallon uba ko uwa, na ƙasa da su kuma, su ɗauke su a matsayin ƙanne. Su girmama manya su tausaya wa ƙanana, su yi kyakkyawar mu’amala da sa’o’insu a matsayin abokai.

    22. Kula da kyawawan halaye

    lyaye su ɗora ‘ya’yansu a kan halaye na haƙuri, juriya, wadatar zuci, nutsuwa, da mutunci su nisanta da munanan halaye, kamar girman kai, alfahari, wulaƙanci da sauransu.

    23. Wasiyyar Manzon Allah (S.A.W.) ga Ibn Abbas

    Lallai ne iyaye su tarbiyanci ‘ya’yansu a kan abubuwan da wasiyyar Manzon Allah (S.A.W.) ga Ibn Abbas ta ƙunsa.
    Waɗannan abubuwa su ne: Bin dokokin Allah a kowanne hali, roƙon Allah da neman taimakonsa shi kaɗai, dogaro gare shi da rataya zuciya gare shi, shi kaɗai, sai ƙarfin hali da jajircewa da kyakkyawan fata a rayuwa.
    Wannan hadisi shi ne hadisi na 26,669 a Musnad na Imam Ahmad na 2516 a Timizi na 19 a Arba’ una Hadis.

    24. Wasiyyar ƙarfafa gwuiwa

    Haka nan ya kamata a ɗora yara a kan wannan wasiyyar ta Manzon Allah (S.A.W.) wacce yake cewa: “Mumini mai ƙarfi ya fi alhairi, kuma Allah ya fi son sa fiye da mumini mara ƙarfi. Amma kowanne yana da alhairi. Ka dage kan abinda zai amfane ka, ka nemi taimakon Allah. Kada ka gaza, idan wani abu ya same ka, kada ka ce da na yi kaza da kaza ne zai faru. Kawai ka ce haka Allah ya ƙaddara, kuma abinda ya ƙaddara shi ne yake kasancewa, saboda irin waɗannan maganganu suna buɗe kofar shaiɗan.

    25. Su guji kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe

    A yi wa ‘ya’ya tarbiyyar nisantar kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe saboda suna kashe zukata, suna koya ɓarna suna buɗe ƙofofin sha’awa da fitintinu iri-iri.

    26. Nisantar hotuna da gumaka

    Asalin bautar gumaka ta faru ne daga kakkafa da liƙa hotunan bayın Allah, daga nan sai aka sassaka gumakansu, sai aka kama bauta musu. A yanzu abin jiya ya fara dawowa saboda haka a yi hattara. Hoto in dai ba na lalura ba ne, kada a yi sai dai hotunan abubuwa marasa rai ko waɗanda za a rinƙa tattaka su ana wulaƙanta su amma ba girmamawa ba.

    27. Nisantar kafirci da danginsa

    A dora ‘ya’ya a kan nisantar da ƙyamar kafirci da danginsa wato aiki na shirka da saɓo irinsu zage-zage da shaye-shaye, maganganun batsa, caca, karance-karancen batsa da soyayya, tsafi da camfe-camfe da sauransu.

    28. Yaba wa yaro in ya yi abin kirki.

    Yana daga hanyoyin tarbiyya, a yaba wa yaro in ya yı abin kirki, a yi masa addu’a, amma kuma kada a yi masa yabon da zai sa masa girman kai, ko kuma duk lokacin da ya yi kirki ya saurari yabo, ta yadda kuma zai koma yin abu ba don Allah ba, sai don a yaba masa.

    29. Salla da addu’ar Istihara

    Tun da wurwuri a koya wa yara yadda ake yin istihara don su kaucewa istihara ta bidi’a da bokanci. Saboda Manzon Allah (S.A. W.) yana koyar da istihara kamar yadda yake koyar da karatun Ƙur’ani.

    30. Ba da kyauta

    Ba da kyauta ko wata shaida ta yabo kan kula da sallah ko ƙoƙari a makaranta da sauransu abu ne mai kyau a fannin tarbiyya. ldan wani ya yi ƙoƙari an ba shi kyauta to shi kuma wanda bai yi ƙoƙarin ba, sai a dubi wani ɓangaren da ya yi koƙari a kansa kamar tsafta ko kula da salla a yi masa kyauta a kan wannan.

    31. Yin faɗa da nasiha a ɓoye

    Idan yaro ya yi laifi, kada a yi masa faɗa ko nasiha a gaban ‘yan uwansa, a’a ya kamata a yi masa a keɓance musamman in abin da ya yi ba halinsa ba ne, ko kuma ya yi ne a ɓoye.

    32. Ya san dalilin horo

    Hanyoyin horo suna da yawa sun haɗa da: ɗaure fuska, ƙin yi masa magana, hana shi abin wasa, ko yin wasan, ba shi hadda ko wani rubutu da sauransu, ba duka ne kawai hanyar horo ba. Kuma ya san dalilin da ya sa aka yi masa horon.

    34. Horo da duka

    Ba a yin horo da duka, sai bayan an yi gargaɗi, an bi dukkannin hanyoyin da suka gabata, ba su yi amfani ba. Kuma ya san dalilin dukan, kada kuma a yi duka a fuska da maƙarfafa, kada a haɗa da zagi ko wani abu na wulaƙanci, kuma dukan ya kasance sama-sama.

    35. Adadin bulala

    Ba a dukan yaro a kan barin haƙƙin Allah Ta’ala, sai ya kai shekara goma, kuma ba a wuce bulala goma tare da sharaɗan da suka gabata.

    36. Ku kasance abin koyi ga ‘ya’yanku

    Mai dokar barci bai kamata ya yi gyangyaɗi ba. Saboda haka ya wajaba iyaye da malamai da dukkanin manya, su kasance managarta domin yara da su suke koyi. Kada a rinƙa faɗa ba aiki, ko aiki ya rinƙa saɓawa magana.

    37. Haɗin Kai

    Ya kamata uwa da uba bakinsu ya zo ɗaya a kan tarbiyya, kada su raba hankalin ɗa wannan ya ce yi, wannan ta ce kada ka yi, wannan yana da hatsari babba.

    38. Lallai ne uwa da uba su ɓoye duk wani saɓani da yake a tsakaninsu, ta yadda ‘ya’yansu ba za su fahimci me ake yi ba. Kada su yi ko da musu a gabansu ballantana dambe da zage-zage.
    39. Sai fa an haɗa da naci

    Tarbiyya a wannan zamanı tana bukatar naci da haƙuri da yawan maimaitawa da bibiya, saboda yawaitar masu rusa tarbiyya da matsanancin naci da maimaita ɓarna da suke yi ba dare ba rana da hanyoyi da salo daban-daban.

    40. Yanayi mai kyau

    Ya kamata a samar da yanayi mai kyau na tarbiyya, wannan yanayi ya haɗa da auren mace/miji managarci/managarciya da samun maƙota da abokai da malamai managarta. In waɗannan suka haɗu, tabbas za a samu tarbiyya insha Allah.

    41. Abokai da malamai nagari

    Ya kamata iyaye su taimaka wa ‘ya’yansu wajen zaɓa musu abokai da ƙawaye da malamai nagari. Saboda zama tare yana da tasiri ƙwarai da gaske wurin kwaikwayo da nason hali.

    42. A raba su da muggan abokai da ƙawaye

    Ya wajaba su hana ‘ya’yansu yin abota da lalatattun abokai da ƙawaye cikin hikima da dabara, ba tare da nuna musu cewa su tsarkakakku ba ne. Waɗancan kuma wasu najasa ne.

    43. Kada ku yi nesa da ‘ya’yanku

    Ya kamata duk inda ‘ya’ya za su je, ya kasance da sanin iyayensu. lyaye mata su rinƙa zama da ‘ya’ya mata, su kuma maza ya kamata su rinƙa tafiya da ‘ya’ya maza wurin ayyukan alhairi, Saboda su saba, kuma su rinƙa koyar kyawawan halayensu.

    44. Siffofin malamai

    A nutsu sosai wurin zaɓar malaman da za su koyar da ‘ya’yan, su kasance masu mutumci da hankali da ladabi da ilhami, da riƙo da addini da hikima da tsafta da tausasawa.

    45. Malamai su haɗa kansu
    Malamai a matsayinsu na ginshiƙi a fagen tarbiyya, ya kamata su haɗa kansu, kada wani yana tufka wani yana warwarewa. Kada malamin wani fannin ya raina na wani fannin.
    46. Son ya zo na ɗaya a kowane fanni

    Ya kamata malamai da iyaye su dasa wa ‘ya’ya son da ƙaunar gasa da juna wajen zama na ɗaya a kowane fanni na rayuwa. Kada su taso da aƙidar “da ƙyar na sha, ya fi da ƙyar aka kama ni” a’a kada ma a ce an biyo ka da gudun tuni ka yi gaba shi ya fi.

    47. Karatu a gida

    Lallai ne duk runtsi da kujiba-kujiba a ware lokaci a gida da za a rinƙa karatu na gaba ɗaya, a maida hankali wajen karatun hadisin kwaɗaitarwa da tsoratarwa da fiƙhu da tafsiri da sira da Arabiyya.

    48. Ɗabi’ar Karatu

    Ya kamata iyaye su koya wa ‘ya’yansu ɗabi’ar yawan karance-karance da son karatu da tara littattafai, kada a bar su, su yi wa komfuta matsanancin sabon da za ta sa su ƙauracewa karatu da littafi.

    49. A samar da laburare

    Samar da daƙin karatu in da hali a gida, ko yin wasu ‘yan kantoci da jera littattafai a cikinsu da ake karantawa, zai taimaka wajen cusawa ‘ya’ya ɗabi’ar son karance-karance.

    50. Kwana a gidan ‘yan uwa

    Ba da dama ga ‘ya’ya su rinƙa ziyartar gidajen danginka, kai har ma su kwana in ta kama, wannan abu ne da yake koya wa ‘ya’ya zama da mutane da mu’amala da su da sabo da rashin abin da aka saba da shi

    51. Shiga Cikin Jama’a

    Kada a ƙuntata wa yaro a cukwikwiye shi a gida, ba ya zuwa ko’ina, ba ya hulɗa da kowa daga makaranta sai gida, a rinƙa ba shi damar shiga cikin jama’a da halartar sabgogi da suka dace da shari’a da shekarunsa, a bisa kulawa da sa idon iyaye da ‘yan uwa.

    52. Yin raha da yara

    Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai sakin fuska yakan yi raha da kakaci, har da ƙananan yara. Saboda haka lokaci zuwa lokaci iyaye su rinƙa yin raha da ‘yan wasanni da ‘ya’yansu waɗanda suka dace da shekarun kowannensu.

    53. A Koya musu siye da siyarwa

    Ya kamata iyaye su koya wa ‘ya’yansu wayewar saye da sayarwa, gwargwadon shekarunsu. Kada a bari har su girma ko ƙirga ba su iya ba, ko ma ba sa iya bambamcewa tsakanin takardun kudi, ballantana saye da sayarwa.

    54. Riƙe sirrin gida.

    A koya wa ‘ya’ya riƙe sirrin gidansu da sauran abubuwan da suka shafi iyali, kada a bari yawan surutunsu ya kai matsayin da har zai je waje yana yaɗa sirrin gidansu.

    55. Kada ya rinƙa faɗar matsalolinsa

    A sanar da ‘ya’ya cewa bai kamata su rinƙa fadar matsalolin da suke ciki ba, sai ga wanda yake ganin zai iya ba shi mafitar warware wannan matsalar, kamar iyaye da malamai.

    56. Daidaita kishi da gasa

    Dukkan ɗan Adam yana da ɗabi’ar ƙananan yara, wannan ne yasa yaya yake kishi da ƙanınsa. Jariri shi ma yana son a rinƙa ɗaukarsa da sauran kulawa kamar a da, to a nan iyaye su saita wanan ɗabi’a cikin hikima, kamar a ɗauke hankalinsa da wani abin wasa. A juyar da ɗabi’ar gasa wurin karatu da sauran ayyukan alhairi.

    57. Addu’a

    Kada iyaye su gaza ko su ƙosa wajen yi wa ‘ya’ya addu’ar neman shiriya da nagarta. A rinƙa bibiyar lokutan amsa addu’a, a rinƙa yawaita sadaka da kyautata wa malamai da mabuƙata a kan wannan manufa.

    58. Ban da baƙar Addu’a

    Duk ɓacin ran da iyaye za su shiga, su iya bakinsu, kada su kuskura su yi wa ‘ya’yansu baƙar addu’a ko baki. Wannan abu ne mai hatsarin gaske a kan dukkan al’umma.

    59. Bayar da tsaro

    Ya wajaba iyaye su kula sosai da tsaron lafiya da hankali da mutumcin ‘ya’yansu. Su daina sakinsu kamar dabbobi, musamman farkon dare lokacin da shaiɗanu suke fara dabdalarsu.

    60. Hana kwanciyar rub da ciki

    Manzon Allah (S.A.W.) ya ga wani ya kwanta rub-da-ciki sai ya ce: “Wannan kwanciyar Allah ba ya son ta (Abu Dawud, Timuizi, Ahmad). Kuma likitoci sun tabbatar da cewa wannan kwanciyar cike take da illoli da jawo cututtuka.

    61. Nisantar da motsa sha’awa

    A kula da abubuwa masu motsa sha’awa a rinƙa nesanta yara daga gare su, kamar kwanciyarsu a mayafi guda, cuɗanyar maza da mata, bayyana tsiraici, kalle-kalle da karance-karancen soyayya da batsa.

    62. Kau da kai daga kallon tsiraici

    A tarbiyyar yara a kan runtse idanu kan kallon mata da tsiraici ta hanayar karantawa da nisantar na’urori masu yaɗa hotuna da fina-finan batsa.

    63. Koya wa mata suratun Nur

    Suratun Nur ta ƙunshi hukunce-hukuncen hijabi da neman izini da sauransu, saboda haka Sayyadina Umar yake ba da umarni ga wakilansa su rinƙa koya wa mata wannan sura tare da bayanin ma’anoninta.

    64. Su nisanci lalata.

    Tun da wuri a sanar da yara haramcin zina luwaɗi da Maɗigo ta hanyar da ta dace da fahimtarsu da shekarunsu.

    65. Kare mutunci da matsayi

    A cusa wa yara kishin kare mutuncinsu da matsayinsu. A koya musu cewa duk abinda ba ka so a yi maka, to kada ka yi wa wani. Ka tsare mutuncin mutane, sai a tsare maka naka.

    66. Kunya

    Kunya tana daga cikin imani, a koya wa yara ɗabi’ar jin kunya, bayyana tsiraici da sanya matsattsun kaya masu bayyana tsiraici da jin kunyar saɓa wa Allah, da shiga haƙƙin mutane.

    67. Daga shekara Bakwai

    Tarbiyyar suturce jiki da sanya cikakken hijabi ga mata ya kamata ya fara tun daga shekara bakwai na rayuwar ‘ya’ya.

    68. Idan ta balaga 

    A yayin da yarinya ta balaga ta hanyar fara al’ada ya wajaba ta rinƙa rufe gaba ɗayan jikinta kafin ta fita, ko a lokacin da take tare da wanda ba muharraminta ba.

    69.Kowa ya sanya kaya irin nasa

    Lallai ne iyaye su kula da suturun ‘ya’yansu, maza su sa kayan maza, mata su sa kayan mata.

    70. Ban da kwaikwayon kafirai da fajirai

    Kada iyaye su ƙyale ‘ya’yansu suna kwaikwayon suturu da ɗabi’u na kafirai da watsattsun mutane irin waɗanda ake ganinsu a kafafen sadarwa da sauransu.

    71. Auren Wuri

    Ya kamata iyaye su taimaka wa ‘ya’yansu maza su yi aure da wuri, muddin sun samu sana’a da nutsuwa da ilmi, daidai gwargwado, Kada a ƙyale su har su ƙosa ba aure, saboda babu abinda zai magance yawaitar lalata sai aure.

    72. Daƙile aƙidar tsarin iyali

    Tsarin iyali wani abu ne da yanzu yake nema ya zama kamar wani abin yayi. Wannan tsarin yana da illoli masu yawa na kusa da na nesa. A koyar da matasa masu aure da masu shirin yin aure illolin tsarin iyali. A koyar da su hanyoyin faɗaɗa sana’o’i da inganta su da kuma tarbiyyar wadatar zuci.

    73. Tarbiyyar sha’awa

    Addinin Musulunci ya koya yadda ɗan Adam zai sarrafa sha’awarsa ya bayyana halal da haram da hanyoyin riga kafin aikata laifuffukan jinsi, ya wajaba ‘ya’ya su san wannan tsarin da hukunce-hukuncen tun kafin balagarsu.

    74. A rinƙa yin kinaya

    Dukkan bayanar da koyarwa da suka shafi alaƙar mace da namiji da maganar Jinsi ya wajaba su kasance cikin tsafta da amfani da kalmomi masu tsafta ban da gatsal-gatsal don gudun gyaran gangar Auzunawa.

    75. Neman lzini

    A koya wa ‘ya’ya hukunce-hukuncen neman izini da sallama kafin shiga gida ko ɗaki. Wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da amfani.

    76. Hulɗa da mutane

    Ya kamata a koyar da ‘ya’ya yadda ake hulɗa da kowane jinsi na mutane misali malamai iyaye, maƙota, shugabanni, ‘yan uwa, tsofaffi, masu buƙata ta musamman da sauransu.

    77. Shawara da su

    Yin shawara da ‘ya’ya musamman a kan abin da ya shafe su, da kuma harkar gida a lokacin da ya dace, abu ne mai kyau ƙwarai da gaske a fannin tarbiyya.

    78. Tashen balaga

    Wannan lokaci ne mai muhimmanci da rikice-rikice a rayuwar ‘ya’ya. Yana farawa daga shekaru goma sha uku zuwa shekaru goma sha takwas. Ya wajaba iyaye su fahimci haƙiƙanin yadda wannan mataki yake da buƙatun yara a wannan lokaci da yadda ya kamata a ɓullowa matsalolin lokaci.

    79. Hira da ‘ya’ya

    Ya wajaba iyaye su rinƙa zama suna yin hira da ‘ya’yansu, a irin waɗanan lokuta ne, za su rinƙa koya musu ladaban hira da tattaunawa, da ma ilmin zaman duniya.

    80. Yawan Tambayoyi

    Kada iyaye su nuna ƙosawa ga yawan tambayoyi na ‘ya’yansu, kada su rinƙa kwaɓar su a kan irin waɗannan tambayoyin. A ba su amsa gwargwadon hankalınsu. In tambayar ta fi ƙarfinka sai ka waske ta hanyar dabara.

    81. Sauraron ‘ya’ya

    ldan yaro ya zo maka da matsala, ko ya kawo maka ƙara ka tsaya ka saurare shi komai rashin muhimmancın matsalar, shi a wajensa muhimmiya ce. da haka zai saba har ya rinƙa kawo maka muhimman matsalolin. kuma ya koyi ɗabi’ar sauraron mutane da taimakonsu.

    82. Girmama yara

    Kada a rinƙa walaƙanta yara da nuna musu su kamar su ba mutane ba ne. wasu iyayen har ɗa ya yi furfura yana nan a matsayin yaro a wurinsu. Wannan babban kuskure ne.

    83. Adalci

    Ya wajaba iyaye su yi adalci tsakanin ‘ya’yansu maza da mata, manya da ƙanana. ‘ya’yan uwargida da ‘ya’yan amarya. Wannan yana taimakawa sosai a fannin tarbiyya.

    84. Ciyarwa Ibada ce

    Ya kamata iyaye su sani cewa, ciyar da iyali da kula da ɗawainiyarsu ta lafiyarsu ilminsu da sauransu ibada ce. Saboda haka su saki ransu su yi farin ciki, ban da yi wa ‘ya’ya gori ko gaya musu maganganu da suke nuna ƙosawa ko jin haushin ɗawainiyar da yake yi.

    85. Banda shagwaɓawa

    Kada iyaye su shagwaɓa ‘ya’yansu, a ƙarshe sai su zo su fi ƙarfinsu, su gagari kowa.

    86. Kwanciyar hankali

    Duk wani abin da zai firgita yaro, ya tayar masa da hankali ya kamata a nisanta razana, yana da mummunan tasiri a kan tarbiyyar ‘ya’ ya.

    87. Tarbiyar ‘ya’yan fari

    Lallai iyaye su kula sosai da tarbiyyar ‘ya’yansu na fari. Kada ɗoki da soyayya ta sa a bar su su sangarce. ldan na farkon suka gyara, to haka ‘yan gidan za su taso, in kuwa suka karkace, to haka abin zai ta tafiya. Wannan kuma ba ya nufin daga kun manyanta a dakata ba, a’a, a ci gaba harkan ɗan auta.

    88. Tarbiyyar ‘ya’ya mata

    A kula sosai da tarbiyyar ‘ya’ya mata, saboda su ne masu raino da kula da ‘ya’ya fiye da iyaye maza. In mata suka samu tarbiyya, duk al’umma za ta gyaru.

    89. A kula da marayu

    Lallai ne al’umma su kula da marayu a ba su ingantacciyar tarbiyya saboda maraici zai iya samun ‘ya’yan kowa kuma ba a san irin amfanin da marayun nan za su yi ba ga al’umma in sun sami tarbiyya mai kyau.

    90. Kalmar farko

    A yi ƙoƙari kalmar farko da yaro zai buɗi baki da ita ta kansance Laa ilaha illallahu.

    91. Girmama baƙi

    A koya wa ‘ya’ya girmama baƙi da yi musu hidima. Kada kuma su zauna, su zura idanu su buɗe kunnuwa suna jin hirar da ake yi.

    92. Haƙƙokin hanya

    Hanya tana da haƙƙokin waɗanda suka haɗa da tafiya cikin nutsuwa, da bin dokokin tuƙi tsaftace hanya, kada a ci wani abu a wurgar, da leda ko ɓawo a kan hanya. A kawar da abu mai cutarwa, kada a yi fitsarı ko kashi a kan hanya da sauransu. A koya wa yaro waɗannan ladabai.

    93. Lokacin Hutu

    A yi amfani da lokutan hutun ‘ya’ya wajen shirya musu abubuwa masu amfanı kamar tafiye-tafiye da wasanni masu ma’ana da koyon sana’o’i da karatuttuka na musamman.

    94. Wakilci

    Idan yaro ya ɗan data, a rinka wakilta shi a kan waɗansu abubuwa da suka dace don ya taso da tarbiyyar hulɗa da mutane.

    95. Cika alƙawari da gaskiya

    Kada ka yi wa ɗanka alƙawarin da ka san ba za ka iya ba. Duk abin da za ka faɗa wa ‘ya’yanka ka tabbatar gaskiya ne. kada ka rinƙa shara ta, sai girmanka ya faɗi, kuma su ma su zama maƙaryata.

    96. Rarraba ayyuka

    Ka raba wa ‘ya’yanka ayyuka, kowa ka dubi abin da ya fi dacewa da shi saboda gida kamar masarauta ce, akwai buƙatar sarki, waziri, fadawa (masu ba da tsaro) da sauransu.

    97. Neman afuwa

    Ku koya wa ‘ya’yanku ɗabi’ar yarda da amsa kuskure in sun yi da kuma neman afuwa. Su ga misali daga gare ku.

    98. Fasaha

    A lokacin da yaro ya yi wani kuskure na magana, ko ya yi shirme, ka gyara masa don ya taso da hikima da fasaha.

    99. Kowa da irin baiwarsa

    Ya kamata iyaye su kula da bambance-bambancen da suke a tsakanin ‘ya’yansu da irin baiwar da Allah ya yi wa kowane ɗaya daga cikinsu. Sai a sarrafa wannan baiwar da Allah ya yi wa Kowane ɗaya daga cikinsu ta yadda za amfani kansa da al’umarsa.

    100. Tsoron Allah

    Babban al’amari mafi muhimmanci a komai, shi ne tsoron Allah a fili da ɓoye da neman ilimi da aiki da shi, Ya Allah ka ba mu zuri’a managarciya.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Mansur Dala ya wallafa shi, domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.

  • Siffofin Da Suka Bambanta Mutum Da Dabba

    Siffofin Da Suka Bambanta Mutum Da Dabba

    Abubuwan dake sawa mutum ya sami tsira (a dunƙule) guda huɗu ne, kamar haka:

    • Imani:
    • Aiki nagari;
    • Umarni da kykkyawan aiki da hana mummunan aiki;
    • Koya wa juna haƙuri da juriya.

    Wato ya kamata ya zama mai kintsa kai da shiryar da shi, tare da shiriyar da sauran mutane da nuna musu duk abin da zai amfana musu duniya da lahirarsu.

    Ɗabi’ar Dabba

    Dabban, kalma ce ta Larabci, wadda take nufin halittar dake taka ƙasa, wato halittu masu rai kenan. Amma galibi idan aka ce (dabba) to, ana  nufin sauran halittu marasa hankali, kamar jaki da kare da doki da dai sauransu.

    Babban abin da aka san dabboin da shi; shi ne rashin hankali irin na mutane, kuma da rashin iya sarrafa al’amura bisa cikakkan zaɓi na Turanci da ilimi, duk da yake ana samu wasu dabbobi masu baiwa ta hazaƙa a wasu fannonin rayuwa ire- ire, amma duk da haka matsayinsu ƙasa yake da na mutane saboda cikakken hankali da Allah ya ba su, tare da wahayi ta hanyar Manzanni, abin da ya iya jagorantarsu su bi tafarkin shiriya tsantsa.

    Dabbobi ba su da wata manufa ta musamman da suke iya zaɓa wa kansu a rayuwa, mafi muhimmancin abin dake gabansu shi ne ci da sha da Barbara.

    Lallai ne mutum ya ɗinga faɗakar  da al’amuransa na yau da gobe, domin ya tabbata yana tafiyar da su a kan tafarkin imani da kuma aiki da hankali, domin idan ya sake ya  zama shima ba shi da manufa sai dai ci da sha da sauransu. To sai ya fi dabboi lalacewa. Allah Ya kiyeye mu, ameen.

     

  • Yadda Za A Gabatar Da Aiki Mafi Muhimmanci

    Yadda Za A Gabatar Da Aiki Mafi Muhimmanci

    Ma’anar wannan shi ne  jera ayyuka cikin rayuwa ko burikanmu daki-daki. Ɗaya bayan ɗaya, gwargwadon muhimmancin kowannensu. Ta yadda aikin nafila ba zai jawo kuɓucewar farilla ba.

    misali, wannan shi ne mutumin da ya yi sallolin ƙiyamul laili a cikin dare, amman bai iya yin sallar asubahi a lokacinta ba, ko barcin ya kwashe shi, har jam’i ya wuce shi.Kasancewar lokaci a rayuwarmu, wata ƙaddara ce mai daraja kuma yana gudu cikin gaggawa.
    Saurinsa na awoyi 24hrs a rana, ko awoyi 168hrs a sati. Ko awoyi 1720hrs a wata, za ka ga akwai bukatar, mu san yadda za mu kasafta su, kamar yadda mahauci ke feɗe dabba ya kasafta ya ware kayan ciki da tsoka.
    ya fitar da fata da kai da ƙafa. Dole kuma mu ririta lokacinmu na rayuwa, kamar yadda matafiyi ke taka-tsantsan wajen taɓa guzurinsa, ta yadda ba zai shantake a zango yana kwasar dabge da taba-ka-lashe ba, alhali akwai dogon tagi a gabansa, ga kuma guzirin kaɗan.
    Za mu iya auna ayyukan da muke yi da muhimmancinsa a bisa waɗannan ma’aunai:
    •   Aiki mai matuƙar muhimmanci, kuma mai buƙatar a gaggauta shi: Irin Wannan nau’i, ba a jinkirta shi, kuma ba a gabatar da wani aiki a kansa. Misali ayyukan ibada ko salloli biyar ko ɗaukar ɗanka da ya yanke, kuma jini ya ƙi tsayawa zuwa asibiti, ko shan magani a lokacinsa. Rashin bin wannan ƙa’idar zai iya jawo mummunan sakamako.
    • Aiki na larura mai buƙatar gaggawa, ƙarƙashin wannan nau’i akwai dukkan ayyukan da ba su kai darajar nau’in farko ba.
      Misalin wannan shi ne, kai yara makaranta, saurararen baƙo ko karɓarsa idan ya zo.
    •  Aikin da ba larura ba ne, amma yana buƙatar gaggawa: Ƙarƙashin wannan nau’i, akwai dukkan wani aiki da za a iya jinkirta shi, ba tare da an cutu ba. misali tsaftace haƙora da safe, shirya tafiya yawon buɗe ido, halartar wata lacca da dai sauransu.
    •  Aikin da ba larura ba ne, amma yana buƙatar gaggawa. Dukkan aikin dake jawo asarar lokaci, kuma ba shi da alaƙa da cimma manyan burikanmu da manufofinmu a rayuwa a matsayinmu na musulmi.
    •  Misali a nan shi ne, ka shirya za ka je duba mara lafiya asibiti, sai kallon wani fim a talabijin ya ɗauke hankalinka, har lokacin ya ƙure ka fasa.
        Ko tsawaita hira ta talfon(waya) ko ma a kan taɗin kwallo, ko kakaci a kan siyasa ko sinima har ka kai tsakar dare. Abin mamaki irin waɗannan ayyuka kan cinye wani kaso mai yawa a rayuwarmu ba mu sani ba. Aikin da ba larura ba, kuma ba ya buƙatar gaggawa:
         Misalan wannan nau’in su ne mafi  muni, misali cinye awoyi a gaban talabijin don kallon  fina-finai, karta ko ludo, karatun mujalla da jaridu na tsawon sa’o’i.
    •  ɗaukar lokaci ana yawo a yanar-gizo (internet browsing) yawan barci, zama a kulob, zaman bencina a bakin titi, ko cikin lokuna ana hira.
    Mai karatu shin ka taɓa tsara ayyukanka gwargwadon mahimmancin wanensu? Sau nawa ka taɓa gabatar da aikin da ba larura ba, bisa aiki mai matukar mahimmanci kuma na lalura?
             domin samun karanta cikkakken littafin danna koren rubutu
  • Yadda Halittar Lokaci Da ƙarewarsa Yake

    Yadda Halittar Lokaci Da ƙarewarsa Yake

    Ƙudurar Ubangiji  kadai itace wanzanjjiya. Domin kuwa tun farko babu jiya babu yau, ba nan ba can , babu gaba  ba baya.

    Ba a san nisa da kusanci ba, balantana kuma ko banbanci, kamshi ko wari babu su, dare da rana babu zuriyarsu, lissafi da kwatance ba mai tunani su.

    Domin babu sama, ba ƙasa, ba  halitta. Sai ALLAH ya halicci sarari da lokaci sannan ya samar da halittu da rayuwa da mutuwa da ma’auni Ayoyi masu zuwa na ƙarfafa wannan ma’ana:

    Sannan ya daidaita zuwa ga sama alhali kuwa ita (a lokacin) hayaƙi ce,sai ya ce mata, ita da ƙasa ku zo bisa ga yarda ko akan tilas “suka ce muzo, muna Da’a
    Sura fussilat-Aya 11

    Wannan Aya na nuna farko halittar sarari (space) tun a farkon al’amari. Daganan kuma halittu suka bigire da matsuguni. Kamar yadda Ubangiji maɗaukaki  ke faɗa dangane da farkon halittar  Annabi Adamu a lokaci yana cikin aljanna da matarsa Hauwa’u:

    Kuma kuna da matabbaci da ɗan jin daɗi izuwa wani lokaci a bayan ƙasa (doron duniya)’’. Sura Bakara Aya 36

    Rayuwa ɗan-Adam a doron ƙasa ba zata yiwu ba, ba don Ubangiji yahore tagare shi ba. Ubangiji na cewa:

    kuma yahore muku rana da wata dawwamammu da kuma dare kuma ya baku dukkan abinda kuka roƙe shi. Da zaku ƙirga ni’imomin Allah (Maɗaukaki) ba za ku iya ƙididige su ba

    sura-Ibrahim:33-34

    Ubangiji Maɗaukaki na cewa:

    shi ne wanda ya sanya rana mai haske wata kuma mai haskawa. Ya gwargwaje shi a masauki don ku san ƙididdigar shekaru da lissafi. Allah (MAɗaukaki) bai halicci wannan ba  sai don gaskiya yana rarrabe ayoyi ga mutane masu sani.
    “Yunus-Aya 5

    Saboda kimar lokaci kuwa ubangiji maɗaukaki ya yi rantsuwa da shi a wurare da yawa cikin Alqurani:

    • (Ina) rantsuwa da lokaci (zamani)…………………..
    • A wani gurin yace (Ina) rantsuwa da alfijir…………………………….
    • Wata ya yar kuma (Ina) rantsuwa dada lokacin walaha……………….
    • (Ina) rantsuwa dada Dare……………………………

    Malam tafsir na cewa idan Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da wani abu to akwai ishara izuwa ga irin girman wannan al’amari da tasirinsa da amfaninsa. Lokaci na shuɗewa ne ta yadda mutum ba zai  Ankara ba har sai ya zagayo, wata ya wuce shekara ta zo ta tafi.

    Wani mai hikima na cewa.
    • Ɗaya ta wuce biyu ta biyo ta:
    • Uku na nufin cin didigenta
    • Hudu ko kamar na rarako ta:
    • Zancen ya shekara ba wuya
    • Ka san da ranar haihuwarka:
    • Yau ga shi ka zama ɗan gidanka:
    • Domin gudu nata duniya

    Ka lura da kyau daga ƙuruciyarka zuwa yau din nan, zaka ga kamar sati ne ya wuce. Babban misali a nan shine: ɗaukar ciki da haife shi. Yaye  da shayi Gama karatun firamare da sakandare. kammala ilimin jami’a. Ga shi yau har ka yi aure ka zama magidanci. Ashe dai lokaci gudu yake yi amma ba mai gani sai mai idanuwan zuciya da lura.

    LOKACIN RAYUWA KAMAR ZAREN KASET NE

    Lokaci rayuwa ga kowannemu ya danganta da irin yadda Ubangiji Maɗaukaki ya ɗeba masa. Manzon Allah (SAW) na cewa rayuwarmu shekaru sittin ko saba’in kadan ne ke wuce wannan.

    Mu ɗauka wasu za su kai shekaru casa’in wasu ɗari. Wasu kuwa talatin wasu arba’in ko hamsin da sauransu. To ka ga kuwa rayuwarmu tamkar kaset ne mai 60 ko 70 ko 90 ko 100 ko 30 ko 40 ko 50 gwargwadon yawan shekarun da aka qaddara mana ba daɗai ba ragi.

    Da zarar an haifi jariri sai  kaset ɗin rayuwarsa ya fara naɗe bayanan motsinsa da ayyukansa masu kyau da munana. Hatta minshari da kakaki da ihu  da ashariya da ibada, kaset ɗin zai cigaba da juyawa cikin zaren lokaci ba tsayawa. Ruwan mutum ya kama tasbihi ko karatun Alƙur’ani ko barci ko ya shiga kakaci da batsa, kaset ba zai tsaya ba. Kuma ba zai dena naɗa ba har sai ya je ƙarshe.

    Da yaje ƙarshe kuwa mutum zai bar duniya ko da shiri ko ba shiri. Jama’a mu lura a kowanne lokaci zaren rayuwarmu ƙarewa yakeyi kullum cikin daƙiƙa. Mu ribaci lokutanmu don in ya tafi ba zai dawo ba. Ubangiji Maɗaukaki Na cewa:

    Lallai ajalin Ubangiji Maɗaukaki in ya zo ba a jinkirta shi. Da kun sani (hakan)”. Sura munafiƙun-Aya-11

    Game da gaggauta ayyuka na gari kuwa Ubangiji Maɗaukaki na cewa:

    “Ku ciyar daga abinda muka azurta ku tun kafin mutuwa ta zo wa dayanku. Sannan ya ce Ubangijina ina ma ka jinkirta min izuwa ɗan lokaci na zamo cikin nagartattu.”

    Allah (maɗaukaki) baya taɓa jinkirtawa wata rai idan ajalinta ya zo. Kuma Allah (maɗaukaki) Mai bada labari ne game da abinda kuke aikatawa”-Sura Munafiƙun: Aya 10

    KIMAR LOKACI A RAYUWAR ƊAN ADAM

    Manzon Allah (SAW) ya ce: Ka ribaci abubuwa biyar kafin abubuwa biyar (suzo)

    1. Quruciyarka/kafin tsufanka
    2. Lafiyarka kafin rashin lafiyarka
    3. Wadatarka kafin talaucinka
    4. Faragarka kafin shagaltuwarka
    5. Rayuwarka kafin mutuwarka

    Bugu da Ƙari Manzon Allah (SAW) yace:” Ƙafafun Ɗan adam ba za su gushe ba a ranar alƘiyama har sai an tambaye shi game da abubuwa huɗu:

    • Rayuwarsa ta yaya ya ƙarar da ita?
    • Quruciyarsa ta yaya ya ƙarar da ita?
    • Dukiyarsa ta ina ya same ta, kuma ta yaya ya kashe
    • Iliminsa ya yayi da shi?

    Akwai hadisi da Bukhari ya ruwaito Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ni’imomi biyu ana yiwa mutane da yawa kumunga a cikinsu”. Ma’ana suna tozarta su cikin abinda ba zai bayar da amfani ba. Lafiya da samun dama”.

    domin samun cikkekken littafin danna koren rubutu

  • Yadda Musulmi Zai Ribaci Lokutansa Na Rayuwa

    Yadda Musulmi Zai Ribaci Lokutansa Na Rayuwa

    Kwaikwayon Manzon Allah (S.A.W) A dukkan fuskokin rayuwa.  Kasancewar Manzon Allah (S.A.W) shi ne mafi cikar mutane wajen kamala da tsoron Allah Maɗaukaki, kuma ya fi kowa sanin lokaci da yadda za a ribace shi.

    Sai rayuwarsa ta zamo cike da abubuwa masu amfani, kuma masu kusata mutum ya zuwa Ubangiji Maɗaukaki. Babu wani motsi ko minti a rayuwar Manzon Allah (S.A.W) wanda bai yi wa dabaibayi da ayyuka nagari ba.
    Tun  daga wayewar gari har zuwa kwanciya, akwai nau’o’in zikiri da nafiloli da ayyuka nagari da yake yi. Cin abincinsa, sanya tufafinsa, ƙailulansa da barcinsa duk ibada ne, domin yanayinsu bisa yadda Ubangiji Maɗaukaki yake so a yi. Zikirin safiya da maraice duka ɓangare ne na rayuwar Manzon Allah (S.A.W). Mai ƙoƙarin bin koyawar Annabi (S.A.W) da ɗabbaƙa su cikin awoyi 24hr a kowace rana babu shakka, zai fi kowa ribatar lokacinsa.
        “Tirmizi ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi bn Umar cewa: Akan ƙidaya (istigfarin Annabi (S.A.W) a zamansa guda (tsakanin sahabbansa) kafin ya tashi sama da sau 100 yana cewa:
    “YA Ubangiji ka gafafrta min, ka karɓi tubana, domin kai ne mai yawan karɓar tuba kuma yawan gafara”.
    Duk motsin da Annabi (S.A.W) zai yi, akwai nau’in zikirin da yake yi idan ya farka  daga barci, ko zai sanya tufafi ko zai fita daga gida ko zai shiga.
    A halin tafiya, yayin hawa ko gangara. In ya sha. Idan iska ta taso, ko ruwa ya sauka ko an yi tsawa ko sabon wata ya kama. A yayin da wasu al’amura suka wuyata ko kuma yayin haɗuwa da abokan gaba ko magabta. Da zikirin shiga kasuwa ko hawa ko sauka a wani gari.
    Don neman ƙarin haske game da irin addu’o’i da zikiran Annabi (S.A.W)  cikin awoyinsa 24hr, sai a nemi littafin Hisnil Muslim ko a duba Zadul Ma’ad na Ibnul Ƙayyim ko kuma Alkali Muddayyib na Shehul Islam ibn Taimiya.
    Game da sauran ayyukan ibada kuwa, Manzon Allah (S.A.W) ya ce wanda ya yi sallah raka’a goma sha biyu  ta nafila, to za a gina masa gida a Aljannah da su. Kuma ya yi wa Abu Huraira wasiya da kada ya bar azumtar kwanaki uku na kowanne wata, da yin sallar walaha da kuma wuturi.
    Wanda duk ya bar kwaikwayon rayuwar Annabi (S.A.W) ya saki  reshe ya kama ganye. Domin rayuwarsa ba za ta cika da ayyukan ba.
    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan