Abubuwan dake sawa mutum ya sami tsira (a dunƙule) guda huɗu ne, kamar haka:
- Imani:
- Aiki nagari;
- Umarni da kykkyawan aiki da hana mummunan aiki;
- Koya wa juna haƙuri da juriya.
Wato ya kamata ya zama mai kintsa kai da shiryar da shi, tare da shiriyar da sauran mutane da nuna musu duk abin da zai amfana musu duniya da lahirarsu.
Ɗabi’ar Dabba
Dabban, kalma ce ta Larabci, wadda take nufin halittar dake taka ƙasa, wato halittu masu rai kenan. Amma galibi idan aka ce (dabba) to, ana nufin sauran halittu marasa hankali, kamar jaki da kare da doki da dai sauransu.
Babban abin da aka san dabboin da shi; shi ne rashin hankali irin na mutane, kuma da rashin iya sarrafa al’amura bisa cikakkan zaɓi na Turanci da ilimi, duk da yake ana samu wasu dabbobi masu baiwa ta hazaƙa a wasu fannonin rayuwa ire- ire, amma duk da haka matsayinsu ƙasa yake da na mutane saboda cikakken hankali da Allah ya ba su, tare da wahayi ta hanyar Manzanni, abin da ya iya jagorantarsu su bi tafarkin shiriya tsantsa.
Dabbobi ba su da wata manufa ta musamman da suke iya zaɓa wa kansu a rayuwa, mafi muhimmancin abin dake gabansu shi ne ci da sha da Barbara.
Lallai ne mutum ya ɗinga faɗakar da al’amuransa na yau da gobe, domin ya tabbata yana tafiyar da su a kan tafarkin imani da kuma aiki da hankali, domin idan ya sake ya zama shima ba shi da manufa sai dai ci da sha da sauransu. To sai ya fi dabboi lalacewa. Allah Ya kiyeye mu, ameen.