Tag: ilimi

  • Yadda Illolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya Suke

    Yadda Illolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya Suke

    Abu ne mai kyau  mu zayyana kaɗan daga wasu kayan kwalliya na tufafi da shafawa da sauransu, waɗanda za su iya zama illa ga mace don necsancesu.

    Saboda ta yi amfani da nau’in  kayan kwalliya da zasu biya mata buƙatarta ta ado ba ta kauce  ƙa’idojin Muhaliccinta ba , kuma ba tare da ta cuci kanta-da-kanta ba.

    • Matsatsatsun Kaya:
      Sanya matsatstsun kaya ga wasu mata ya zama rowan-dare gama duniya. Irin waɗannan mata sukan fifita kayan da za su matse jikin tamau! Yadda za a iya ganin ƙirar jiki
    Mafi yawa daga bayanan kiwon lafiya da suka zo a wannan Babi, an tsamo su ne daga wani littafi mai saua “Zinatul Mar’a Bainal Dibbi Washshar’i” Na Muhammad Abul-Aziz  Al-Musuid, wanda gidan bugu littattafi na Sarki Fahad dake Saudi Arabia ya buga, a Watan Sha’aban, 1416 A.H.
    Sosai, masana da yawa sun yi tsokaci akan irin waɗannan kaya, ta fuskokin ilimi daban- daban.
          A ɓangaren kiwon lafiya, a na ganin irin waɗannan ɗamammaun kaya suna tsananta matse jikin mace,  haka kuma yana azabtar da ita sosai, ta hanyar takurata, da rashin samun walwala, saboda haka yawan sanya irin waɗannan kayan zai sanya mace yanwan jin damuwa a ranta.
                Haka kuma matsewar da tufafi ke wa jiki zai takurawa tsarin zagayawar jini a jijiyoyinta, wannan kuma zai iya sabbaba mata cutar hauhawan jinni.
    A wani faɗin ma, wasu masana cewa su ka yi;yawaita sanya matsatstsun kaya zai iya hanawa mace haihuwa, ko kuma yayi  sanadin samun tangarɗar haihuwar.
    (2) Tufafi masu Bayyana Fatar jiki:
             Koƙari kwaikwayon kangararrun Turawa, ya sa wasu matan Musulumi, su na sanya  tufafi  masu bayyana wasu sassa na jiknsu, yadda za a iya ganinsa ƙarara, kamargadon baya ko faɗin ƙirji ko sha-raba, da dai sauransu.
                 Sakamakon bincike ya tabbatar da bambanci tsakanin yanayin fatar maza da ta mata, a yiyin da mafiya yawan maza su ke ayyukan a waje kuma wasu sana’o’ insu sai sun kwaɓe kayansu  cikin  zafin rana , ko ruwan damina ko hunturun sanyi, amma su wanye lafiya, ikon Allah!Saboda namiji dama ɗan gaganiya ne da hada-hadar faratutowa iyali abin  masarufi,
    amma mace wadda tafi kyau da killatuwa guri guda cikin aminci da mutunci, idan ta cika bayyanar da fatar jikinta ga zafin rana ko haskanta da sauran nau’o’ in yanayi mai tsanani, nan da na za ta gamu da illolin fata da na ƙashi baki ɗaya, sannan kuma yana ragewa mace ƙyallin ƙuruciya, sannan ya sanyata  ta yi saurin  tsufa.
    (3) Takalmin Coge:
     Wani dogon takalmi ne mai tsinin dunduniya, ko mai faɗinta. Da yawan mata suna sanya shi don a ga tsawon su.Saya iri wannan takalmi ya na da haɗari ga laifyar mace, idan an lura za a ga takalmin yana da doguwar dunduniya sosai, sannan kuma goshinsa ya kifa ƙasa idan matce ta sanya shi, itama haka za ta kifa, don haka tafiya a gunta ba ƙararamin aiki ta ke zama ba.
    Sau da yawa maza sukan zame su faɗi sakamakon sanya takalmin, kuma yawan sanya shi yana sanadin sanrewar jijiyoyin ƙafarta, daga bisani sai a sami ƙafar matce ta yi tsauri kamar dutse.
            Haka nan wannan takalmin ya na gadarwa da ciwon baya, kamar yadda takalmin yana mayar da waɗanda suka sanya shi maƙaryata, domin wadda ta sa shi kamar tana cewa ni mai tsaho ce ko kuma ni doguwa ce, amma da zarar ta sauka daga takalman sai ungulu ta koma gidanta na tsamiya! Wani mashahurin masani a ƙasar Masar Al-Ustaz Anis Mansoor, ya faɗa  a cikin littafinsa mai sun “Fi Salunil Akkad Kanatlana Ayyam” cewa wani Kamfani dake sana’anta coge a Italiya yayi bayanin sirrin da yasa suke ƙera shi a irin siffar da ita.
    Cewa idan mace ta hau kan coge to za ta kifa gaba kaɗan, to idan ta yi takun tafiya, sai ta danga ƙaƙarin, dawo da jikinta bayan a wannan lokacin ko’ina a jikinta sai ya dinga kaɗawa yaddaza ta fi jawo hankalin mazaje!
    • Tiyatar kwalliya:
    Larura da rashin lafiya ke sanya mutane su kwanta a yi masu aiki a Asibiti, amma wasu matan tsananin son kwalliya ne yake kai su ayimusu aikin tiyata don ƙara musu kyau (a zaton su!).
    Irin wannana aikin tiyata a kan yiwa mata ne (ko maza ma a wasu lokuta) ta hanyar rage wani abu ko ƙarashi a jikinsu, akan yi aiki a rage mata faɗin ƙirji, a rage mata girman nono, ko a jeme mata fatar jiki, ko a tsaga mata wuahhirya, duka irin waɗannan ayyauka su na da haɗari ga lafiya da rayuwar mutan.
    , yana da kyau a dubi irin wahalar da mashahurin hatsabibin mawaƙin nan ɗan ƙasa Amurka Michel jackso yake sha sakamakon irin waɗannan ayyuka da ka yi masa, baya ga ɓarnar dukiya da ya ke yi saboda tarairayar wannan jone-jone da aka yi a halittarsa ta asali.
          Haka kuma kowa ya san irin wannan aiki ne ya yi sanadin halakar mata Shugaban Ƙasar Nijeriya Stella Obasanjo Wadda  ta mutu a hannun ‘yan kwalliya dake wani Asibiti a Ƙasar Spain, a ƙoƙarinta na jeme fatarta ta koma kamar yarinya ‘yar bana-bakwai.
          Haka kuma irin wannan aiki na kwalliya, ya na da haɗari ga aƙidar Imani da Allah, domin a cikinsa akwai ƙoƙari canja halittar Allah, abin da ya ke haramun ne a Mu
    (5) Kayan Shafe-Shafe:
    Da a kwai kayan shafe-shafe iri-iri wanɗanda galibi su ke fatan, ta hanyar hana bushewa,da kuma ƙara mata taushi, da kyau, sannan a kwai wasu maye-mayen waɗanda musamman a na shafa su ne domin canjawa mace launin  fatar ta ɗungurungum, daga baƙa zuwa jawur.
    2 Babu lafiya ga aikin d aaka yi saboda larura, kamar gaɓar roba ko haƙorin Asibiti.
     To,irin waɗannan kayan shafawa masu sanya launi, su ne suka fi haɗari da cutarwa ga lafiyar mutum, sannan kuma su na nuna halin rashin godiyar Allah. Kamar mace baƙa mai yin amfani da shi ta na nuna rashin gumsuwar ta da irin halittar da Allaha Ya yi mata, wananan kuwa rashin ladabi ne ga Ubangiji Maigirma da Daukaka.
        Haka kuma kayayyakin da a ke haɗa mayuka masu sauya launin, fata abubuwa ne na ƙyama da rashin imani, saboda haka ne man ya ke da ƙarni marar daɗi, kuma yawan shafa shi ya na jeme fatar mutum yadda (abin Allah ya kiyaya)idan wata larura ta samu wadda sai an yi ɗinki a gurin, to ɗinkin zai yi wahalar yiwuwa.
      (6)  Jan-Baki:
    Jan-baki shi ne wani abu mai kamar alƙalmi wanda mata suke shafawa a leɓensu, sai yayi ja-jajir, ko shuɗi ko wani launin daban.
           Kasancewar jan-baki abu ne da a ke damɓara shi a leɓe, don haka yana hanawa fatar leɓe cikakkiyar iska. Saboda haka bayanwani lokaci sai leɓan ya danga yin ƙaiƙayi, da saɓa,da ɗaɗewa.
           Koda ya ke jan-baki ba shi da matsananciyar hatsari, amma ya fi kyau a rage shafa shi, kuma kada mace ta dinga sanya shi lokacin da za ta fita waje ko za ta gamu da mazajen da basu halatta ta bayyana adonta a gaban su ba , domin ya na matuƙar ƙawata ta, zama abin sha’awa ga maza.
    • Jan-Farce/Faratun Roba:
      Jan-Farace wani ruwa ne mai kama da fenti,wanda  a ke lafta shi a kan farce, don ya sanya masa kayau da birgewa. Yawanci launinsa ja ne, amma a na samun launukansa iri-iri.
           Shi  kuma farcen-roba, farce ne ɗan-kanti akan sanya shi don adoda kwalliya, ya kan zamo mai tsaho ne zaƙo-zaƙo a yatsun wanda ya sanya shi.
          Dukkannin su (jan-farce da farcen roba) suna da ill, shi dai jan-farce yana tarewa farce samun iska, ya kan sabbaba kakkaryewar farce da gautsinsa, kuma ya na hana ruwan alwala saduwa da farcen mutmu.
           Shi kuma farcen roba irin matsalarsa ɗaya da ta jan-farce, kuma ga shi ya kan cutar da wanda a ke maƙa masa abu, ko a ke karɓa daga shi ta hanyar kartarsa da dogwayan farautan su ke yi.
    • Kona Gashi:
    Duk da ya ke wasu malamai sun yi rangwame a kan gyaran gashi na zamani, amma ya na da kyau a lura da wasu matsalolinsa, kamar haka:
    • Ya kan zamewa mace laura, ya zama dole a ci gaba da yinsa yadda in a ka daina sai ya jawo zubewar gashi.
    • Ya kan zama fitina, domin idan matce ta yi ƙunan gashi ya yi kyau, sai a dinga ƙoƙarin yadda za a yi ta fito da shi waje don a gani. Saboda haka, ya kamata Musulma ta keɓe maigidanta da wannan gyaran gashin. Kuma ta auna ta gani, shin ba zai cutar da ita ba?
    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin “Sutura Da Kwalliyar Mata” Domin karanta cikakken littafin ko daukoshi  Danna nan
  • Yadda Za Mu Yi Koyi Da Annabi (S.A.W) A Dukkanin Tsare-tsaren Rayuwa

    Yadda Za Mu Yi Koyi Da Annabi (S.A.W) A Dukkanin Tsare-tsaren Rayuwa

    Duk wanda ya ce shi musulmi ne, to lallai ne abin koyinsa ya zamo Manzon Allah (S.A.W), a dukkanin tsare-tsare na rayuwarsa.

    Misali: Tsarin Ilmi, tsarin zamantakewa, tsarin tattalin arziƙi, tsarin siyasa (shugabanci) da tsarin shari’ah. Abin nufi a nan shi ne, duk waɗannan tsare-tsare na rayuwa, su zamo a kan tsarin Alƙur’ani da sunnah, bisa fahimtar magabata na ƙwarai.

    Kada mutum ya zama sai a sallah, Azumi, aikin Hajji kaɗai, yake Musulmi. Watau ya zama yana bin tsarin da ya saɓa wa na Allah. Allah (SWT) Yana cewa:

     “Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku shiga Musulunci gaba ɗaya (watau ku miƙa wuya gaba ɗaya). Kada ku bi takun sheɗan, ba na Allah ba). Shi abokin gaba ne a gare ku, bayyananne” (suratul Baƙarah, Aya ta: 208).

    Abin takaici shi ne, a halin da muke ciki a yanzu, za mu ga cewa a dukkanin tsare-tsare nan na rayuwa babu wanda muke tafiyar da shi a kan tsarin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo da shi.

    Misali: Tsarin Ilminmu ba ya  koya mana tauhid da tsoron Allah da ranar lahira da Tarbiyyar Musulunci. A tsarin zamantakewa.

    Idan muka ɗauki zamantakewarmu ta aure da zaman iyali, ba a kan Alƙur’ani da sunnah take ba. Tsarin Tattalin arzikinmu cike yake da cin hanci da rashawa, cin riba, gululu, (Watau satar dukiyar jama’a) da sauransu.

    Tsarin siyasarmu (shugabanci) tsari ne na Damakwaraɗiiyya, wanda babu Allah a  cikinsa.

    Shi kuwa tsarinmu na shari’ah kowa ya san dokokin ‘yan Adam muke fifitawa a kan dokokin Allah (SWT). Abin nufi a nan shi ne, son Annabinmu  na baka ne kawai. Ba a aikace yake ba. Gashi kuwa Allah (SWT) yana cewa:

    Gaya musu, idan ku kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah ya so ku, ya gafarta muku zunubanku. Allah mai gafara ne, mai rahama” (Suratu Ali Imrana, Aya ta:31)
    Allah (SWT) yana cewa: Ka ce musu Idan iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan’uwanku  da matanku, da danginku da dukiyoyinku da kuka nema da hanyar samunku da kuke gudun kada ta yi tasgaro da gidajen da kuke jin daɗinsu, su suka fi soyuwa a  gare ku, maimakon Allah da Manzonsa, da  ƙoƙarin tabbatar da tsarinsa, to ku zauna, har sai Allah ya zo da lamarinsa (Mutuwa ko halakarwa). Allah ba ya shiryar da mutane fasiƙai”
    (suratul Taubah, Aya ta:24).

    Wannan duka yana nuna cewa ba za mu zama musulmi ba, sai mun gudanar da kowane ɓangare na rayuwarmu bisa tsarin Allah.

    Wannan kuma ba zai samu ba, sai ta hanyar koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), watau ta hanyar riƙo da Alƙur’ani da Sunnah. Annabi(S.A.W) ya ce:

    “Na bar muku nauyaya guda biyu, ba za ku ɓata ba, matuƙar kun yi riƙo da su: Littafin Allah da sunnata”

    Domin sanin yadda sahabbai suke koyi da manzan Allah danna koren rubutun nan.

  • Maganin Damuwa

    Maganin Damuwa

    MAGANIN DAMUWA
    Wani bincike da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar a farkon wannan shekarar 2020, ya tabbatar da cewa kimanin mutane miliyan 264 a duniya suna fama da cutar damuwa. Kuma kusan mutane dubu 800 ne suke mutuwa ko su kashe kansu a kowace shekara saboda damuwa.
    Damuwa cuta ce ta ƙwaƙwalwa, wacce take haifar da matsanancin baƙin ciki da ɓacin rai da fargaba da rashin jin daɗin rayuwa da amincewa kowa.
    Wanda ya kamu da wannan cuta sai ya rasa abin da zai yi, ya ji daɗin rayuwarsa, wannan ne ya sa wasu suke kashe kansu wai don su huta.
    Babban abin da yake haifar da damuwa shi ne, baƙin ciki kan abin da ya wuce da wanda ake ciki da kuma fargaba da tsoron abin da ake zaton zai faru nan gaba. Wato In mutum ya tara wa kansa ɓacin ran jiya ya haɗa da na yau, ga kuma tunanin gobe ma haka za a tashi, to dukkanin rukunan cutar damuwa sun tabbata ga mutum.
    A Musulunci babu wata cuta da ba ta magani, sai mutuwa. Kuma maganin Musulumci kan kowane irin ciwo shi ne kat kuma kaifiyya.
    Musulunci zai ba ka riga-kafi,ya bayyana maka dalilan da suke jawo ciwo da maganinsa da kuma yadda za a yi amfani da shi a warke da iznin Allah.
    Ga waɗansu taƙaitattun bayanai da za su taimaka wajen magance damuwa da ɓacin rai Insha Allahu.
    DALILAN DAMUWA DA MAGANINTA
    1.RASHIN GODIYAR ALLAH TA’ALA DA WADATAR ZUCI
    Sau da yawa In mutum ya rasa wani abu da yake da shi, ko kuma bai samu abin da yake so ba, sai ya mance da duk wata ni’ima da Allah ya yi masa, ya rinka jin shi rayuwarsa ba ta wani amfani. Wani ma abin da yake so ɗin ba ya cikin lalurar rayuwa, kuma babu rufin asirin da bai samu ba, amma duk da haka, sai ya damu kansa da ƙunci saboda bai samu yadda ransa yake so ba.
    Maganin wannan shi ne, mutum ya gode wa Allah bisa ni’imomin da ya yi masa waɗanda ba za su ƙirgu ba, ya rinka duban na ƙasa da shi, kada ya rinƙa hangen na sama da shi.
    Wannan zai haifar wa mutum wadatar zuci da samun gamsuwa da yanayin da ake ciki
    .
    2.RASHIN YARDA DA HUKUNCIN ALLAH TA’ALA
    Allah Ta’ala shi ne mai iko a kan komai, shi ne mai yin yadda ya so, a lokacin da ya so ga wanda ya so,ta yadda ya so. Rashin yarda da haka yakan jefa mutum cikin damuwa marar iyaka.
    Maganin wannan shi ne cikakkiyar yarda da amincewa da dukkanin hukuncin da Allah ya ƙaddara kanka ko ga waninka koda kuwa ba haka kai kake so ba, saboda shi Allah Taala ba a sa shi, ba a hana shi, ba a ce masa ga yadda zai yi, kuma ba a tashin hukuncinsa.
    3.KANGAREWA KA’IDOJIN RAYUWA
    Allah Ta’ala ya tsara rayuwar duniya kan waɗansu dokoki da tsare-tsare waɗanda a kansu take tafiya.
    Duk wanda ya bi wadannan dokoki zai zauna lafiya ya ji daɗin rayuwarsa, wanda kuwa ya ƙi bin su, zai gamu da damuwa da tsaki a rayuwarsa.

    Misalin waɗannan ka’idoji sun haɗa:

    _Allah ba ya kawo canji sai mutum/mutane sun canja salon rayuwarsu.
    _Duk abin da ka aikata sakamakonsa zai dawo maka.
    _Wanda ya dage ya yi ƙoƙari, shi ne zai samu nasara.
    _Zalunci sama da ƙasa shi ne yake ruguza al’umma.
    _Allah bai yi mutane iri ɗaya ba, kowa da halinsa da yanayinsa, sai kowa ya tsaya iya matsayinsa.
    _Kowane wuri akwai hanyar shigarsa.
    Rashin fahimtar waɗannan ka’idoji da aiki da su, yana haifar da matsananciyar damuwa da ci baya a rayuwa.
    4.SABON ALLAH TA’ALA
    Sabo ko zunubi shi ne karya dokokin Allah Ta’ala wanda ya haɗa da shiga haƙƙoƙin Allah da na bayinsa.
    Ƙin bin umarnin Allah da bauta masa kamar yadda ya yi umarni, da aikata abubuwan da ya hana ,da zaluntar mutane da tauye musu hakkokinsu, shi ne babban abin da yake haifar da ɓacin rai da damuwa. Saboda duk wanda ya hana wani barci, tabbas shi ma ba zai yi barci ba, ko ya yi sai dai da ido ɗaya.
    Saboda bin Allah Ta’ala da bai wa kowa haƙƙinsa shi ne babban maganin damuwa.
    5.CIN HARAM DA ALMUBAZZARANCI
    Bin hanyoyin ya ki  halal ya ki haram, da son tara abin duniya ta kowane hali, da shirme da almubazzaranci da dukiya koda ta halal ce, shi ne musabbabin faɗawar mutane da dama cikin damuwa da baƙin ciki da ɓacin rai.
    Maganin wannan shi ne mutum ya zage damtse ya nemi halal kuma a yi amfani da abinda aka samu ta hanyar da dace ba kauro ba ɓarna.
    6.FIDDA RAI
    Fidda rai daga samun sauƙi da canji daga Allah Ta’ala, babban zunubi ne kuma yana jawo matsananciyar damuwa da ɓacin rai.
    Ya wajaba ga duk wanda yake cikin wani hali na damuwa, ya cika zuciyarsa da kyakkyawan fata da zaton samun sauƙi da yayewar duk wani ƙunci da tashin hankali. Kuma mutum ya rabu da tsoro da fargabar abin da bai zo ba, saboda mai tsoron rashin lafiya ya fi kamuwa da ita, haka mai tsoron talauci yakan zama abokin kut da kut ga talauci.
    7.CAMFI
    Canji yana jefa mutane cikin damuwa. Misali camfa wata sana’a ko mace ko wurin zama wannan zunubi ne babba, kuma yana jawo damuwa da.gurɓata rayuwa.
    In dai mutum yana son zaman lafiya da kwanciyar hankali, to lallai ne ya dogara ga Allah Ta’ala ya yi fatali da camfe-camfe da shashanci.
    8.SHA’AWAR HARAM
    Sha’awar lalata ta maza ko mata tana jefa mai yinta cikin damuwa, musamman idan bai samu damar cimma burinsa ba, In kuma ya samu, ba zai taɓa gamsuwa ba, saboda jini ba ya maganin ƙishirwa, haka dai za a yi ta rayuwa cikin damuwa da ɓacin rai.
    maganin wannan shi ne jin tsoron Allah da kaucewa duk wani kallo da tunani da abota da ƙawance na haram.
    9.TSANANIN SON ABIN DUNIYA DA DOGON BURI
    Wannan ma yana haifar da damuwa da sanya a bi kowacce hanya domin samun wannan ba kuma lallai ne a samu ba.
    Maganin wannan shi ne taƙaita buri da baya-baya da duniya.
    10.HASSADA
    Hassada ciwo ne babba kuma zunubi ne mai girma, wanda yake hana mai yinta sakat a rayuwa.
    Maganin wannan shi ne a guji hassada a wanke zuciya.
    11.ZALUNCI
    Mutum ya yi zalunci, ko a zalunce shi yana haifar da damuwa.
    Maganin wannan adalci da hakuri.
    12.TALAUCI
    Yana jawo babbar damuwa, kamar yadda kowa ya sani.
    babban maganin sa shi ne haƙuri da dagewa wajen neman halal da wadatar zuci.
    Insha Allahu a rubutu na gaba zan kawo hanyoyin samun sauƙin musibu.
    Allah Ta’ala ya yaye mana dukkan damuwar duniya da lahira. AMEEN
  • Dimokiraɗiyya Da Jamhuriya ta huɗu (1999 – Zuwa Yanzu)

    Dimokiraɗiyya Da Jamhuriya ta huɗu (1999 – Zuwa Yanzu)

    A ranar 29 ga Mayu, 1999, Abdussalam Abubakar ya miƙa mulki ga wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa na 1999, tsohon shugaban mulkin soji Janar Olusegun Obasanjo a matsayin zaɓaɓɓen shugaban farar hula na biyu na Nijeriya, wanda ke ba da sanarwar farkon Jamhuriyar Nijeriya ta Hudu. Wannan ya kawo ƙarshen kusan shekaru 33 na mulkin soja daga 1966 har zuwa 1999, ban da jamhuriya ta biyu da ba ta daɗe ba (tsakanin 1979 da 1983) ta hannun masu mulkin kama-karya na soja waɗanda suka karɓi mulki a juyin mulki da kuma yin tawaye lokacin juyin mulkin soja na Nijeriya daga 1966 zuwa 1979. da 1983–1999.
    Duk da cewa an yi Allah wadai da zaɓukan da suka kawo Obasanjo kan mulki, a zaben shugaban ƙasa na 1999 da kuma wa’adi na biyu a zaben shugaban ƙasa na 2003 a matsayin maras adalci da rashin adalci, amma Nijeriya ta nuna ingantaccen ci gaba a ƙoƙarin magance cin hanci da rashawa na gwamnati da kuma hanzarta ci gaba. Rikicin ƙabilanci don mallakar yankin Neja Delta dake haƙo mai da kuma tayar da ƙayar baya a Arewa-maso-Gabas wasu matsaloli ne da kasar ke fuskanta.
    Umaru Yar’Adua na People’s Democratic Party(PDP) ya hau karagar mulki ne a babban zaben 2007. Kasashen duniya da suka sa ido a zabukan NIjeriya don Ƙarfafa tsari na gaskiya da adalci, sun la’anci wannan zaɓe da cewa yana da nakasu sosai. Shugaban ƙasa na wancan lokacin, Olusegun Obasanjo, ya yarda da maguɗi da sauran “laps” amma ya ce sakamakon ya nuna yadda ake gudanar da zabe. A wani jawabin da ya yi a gidan talabijin na ƙasa a 2007, ya ƙara da cewa idan ‘yan Nijeriya ba su son nasarar magajin nasa da ya zaɓa, to za su sami damar sake zabe a cikin shekaru hudu. Yar’adua ya mutu a ranar 5 ga Mayu 2010.
    An rantsar da GOODLUCK JONATHAN a matsayin na ‘Yar’adua, ya zama Shugaban ƙasa na 14. Goodluck Jonathan ya yi aiki a matsayin muƙaddashin shugaban Nijeriya har zuwa 16 ga Afrilun 2011, lokacin da aka gudanar da sabon zaben shugaban ƙasa a Nijeriya. Ya ci gaba da lashe zaɓuɓɓukan, yayin da kafafen yaɗa labarai na duniya suka ruwaito cewa zaɓen ya gudana lami lafiya, ba tare da wani tashin hankali ba, ko magudin masu zabe, sabanin zabukan da suka gabata.
    Gabanin babban zaben shekarar 2015, haɗewar manyan jam’iyyun adawa guda uku – Action Congress of Nigeria (ACN), Congress for Progressive Change (CPC), All Nigeria Peoples Party (ANPP), wani ɓangare na All Progressives Grand Alliance (APGA) da sabuwar PDP (nPDP), wani ɓangare ne na gwamnonin dake riƙe da madafun iko na Jam’iyyar Democratic Party mai mulki a lokacin – suka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
    A zaben shugaban ƙasa na 2015, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Janar MUHAMMADU BUHARI, shugaban jam’iyyar CPC na APC – wanda ya taɓa tsayawa takara a zaben shugaban ƙasa na 2003, 2007, da 2011 a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ya kayar da Shugaba mai ci Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP ta mutane da kuri’u sama da miliyan biyu, wanda ya kawo ƙarshen mulkin jam’iyyar na shekaru goma sha shida a ƙasar, kuma wannan shi ne karon farko a tarihin Nijeriya da wani shugaban ƙasa mai ci ya kayar da ɗan takarar adawa. Gaba ɗaya ‘yan kallo sun yaba da zaben da cewa an yi adalci. haka zalika, an yaba wa Jonathan saboda yarda da shan kaye da kuma taƙaita barazanar tashin hankali.
    A zaben shugaban ƙasa na 2019, an sake zaben Muhammadu Buhari a karo na biyu a ofis inda ya kayar da abokin takararsa Atiku Abubakar.
  • Mulkin Farar Hula Da Jamhuriya Ta Biyu

    Mulkin Farar Hula Da Jamhuriya Ta Biyu

    A shekara ta 1977, an zaɓi majalisun dokoki don tsara sabon kundin tsarin mulki, wanda aka buga a ranar 21 ga Satumba, 1978, lokacin da aka ɗage dokar hana yin siyasa. A shekarar 1979, jam’iyyun siyasa guda biyar sun fafata a jerin zaɓuka inda aka zabi ALHAJI SHEHU SHAGARI na jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN).
    Obasanjo cikin aminci, ya miƙa mulki zuwa Shagari, ya zama shugaban ƙasa na farko a Tarihin Najeriya da son ransa ya sauka. Dukkanin jam’iyyun guda biyar sun sami wakilci a Majalisar Kasar. A watan Agusta 1983 aka dawo da Shagari da NPN kan madafan iko yayin gagarumar nasara, tare da mafi yawan kujerun Majalisar Wakilai da kuma ikon gwamnatocin jihohi 12.
    Amma tashin hankalin da rikice-rikice da zargin maguɗi da maguɗin zaɓe ya haifar da taƙaddama kan doka a kan sakamakon. A babban zaɓen da aka sanya a shekarar 1979, an zaɓi Alhaji Shehu Shagari kan dandamali na NPN.
    Tun daga 1979, ‘yan Najeriya suka shiga cikin komawar dimokradiyya lokacin da Olusegun Obasanjo ya miƙa mulki ga farar hula na mulkin Shehu Shagari. A ranar 1 ga Oktoba, 1979, aka rantsar da Shehu Shagari a matsayin Shugaba na farko da Babban Kwamandan Rundunar Sojin Tarayyar Najeriya.
    Sojojin sun yi shirin dawo da mulkin farar hula, suna ta aiwatar da matakan tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa suna da cikakken goyon baya fiye da yadda aka shaida a lokacin Jamhuriyyar farko. Gwamnatin Shagari ta zama kamar cin hanci da rashawa ta kusan dukkan sassan al’umman Nijeriya. A shekara ta 1983 masu binciken kwastomomin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) sun fara lura da “jinkirin da guba ya yiwa ruwan ƙasar nan”. Amma akwai rashin tabbas, irin su jamhuriya ta farko, shugabannin siyasa za su iya yin shugabanci yadda ya kamata wanda zai sake kawo sabbin shugabannin mulkin soja.
  • Mulkin Soja Da Yaƙin Basasa A Nijeriya (1966-1979)

    Mulkin Soja Da Yaƙin Basasa A Nijeriya (1966-1979)

    Mulkin Soja Da Yakin Basasa (1966-1979)
    Rashin jituwa da rikice-rikice na zaɓe da tsarin siyasa ya faru, a cikin 1966, ƙungiyoyin soja na baya-baya. Juyin mulkin farko ya kasance a cikin watan Janairun 1966, kuma yawancin sojojin Igbo ne ke jagorantar su, ƙarƙashin Majors EMMANUEL IFEAJUNA da CHUKWUMA KADUNA NZEOGWU. Masu shirya juyin mulkin sun yi nasarar kashe SIR. AHMADU BELLO da ABUBAKAR TAFAWA ƁALEWA tare da manyan shugabannin yankin Arewa da kuma Primier SAMA’ILA AKINTOLA na Yammacin Yamma, amma waɗanda suka yi juyin mulkin sun yi ƙoƙarin kafa gwamnatin haɗaka. Shugaban Majalisar Dattawa NWAFOR ORIZU ya miƙa ragamar mulki ga Sojoji, sannan a ƙarƙashin umarnin wani jami’in Igbo, Janar JOHNSON AGUIYI-IRONSI.
    Daga baya, juyin mulkin da aka yi a shekarar 1966, wanda ya samu goyon baya daga hannun jami’an soji na Arewacin ƙasar, ya kawo sauyin YAKUBU GOWON a matsayin shugaban mulkin soja. Tashin hankali ya tashi tsakanin Arewa da Kudu; Sannan Igbo a biranen Arewacin na fama da zalunci kuma yawancinsu sun gudu zuwa yankin Gabashi
    A watan Mayun shekarar 1967, Gwamnan Yankin Gabashin Laftanar Kanar EMEKA OJUKWU ya ayyana yankin a  mai ‘yanci, a matsayin wata ƙasa da ake kira Jamhuriyar BIAFRA, a ƙarƙashin jagorancinsa. Wannan shelar ta haifar da yaƙin basasa na Nijeriya, wanda ya fara a yayin da ɓangaren gwamnatin Nijeriya ke yakar Biafra a ranar 6 ga Yulin 1967 a Garkem. Yaƙin na watanni 30, tare da tsawan dogon yaƙi na Biafra da keɓewa daga kasuwanci da kayayyaki, ya ƙare a cikin Janairu 1970.
    Adadin waɗanda suka mutu a tsohuwar Yankin Gabas yayin yaƙin basasa na watanni 30 ya kai daga miliyan ɗaya zuwa uku. Faransa, Misira, Tarayyar Soviet, Burtaniya, Isra’ila, da sauransu sun shiga cikin yaƙin basasa a bayan al’amuran. Burtaniya da Tarayyar Soviet su ne manyan masu goyon bayan gwamnatin Nijeriya; tare da Nijeriya ta yi amfani da tallafin iska daga matukan jirgin saman Masar wanda Gamal Abdel Nasser ya bayar, yayin da Faransa da Isra’ila suka tallafa wa Biafra. Gwamnatin Kongo, a karkashin Shugaba Joseph-Désiré Mobutu, ta yi tsayin daka kan matakin kafa kasar Biafra, tana mai bayyana cikakken goyon baya ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, tare da tura dubunnan dakaru don yin yaƙi da masu ɓallewa.
    Bayan yaƙin, Nijeriya ta ji daɗin hauhawar mai a shekarun 1970, a lokacin ne ƙasar ta shiga OPEC da karɓar kuɗin mai mai yawa. Duk da waɗannan kuɗaɗen shiga, gwamnatin soja ta yi kaɗan ta inganta daidaiton rayuwar mazauna, taimaka wa ƙananan kamfanoni da matsakaita, ko saka jari a harkar. Yayin da kuɗaɗen shiga na man fetur ke ƙara hauhawa,hauhawar tallafin tarayya zuwa jihohi, gwamnatin tarayya ta zama cibiyar gwagwarmayar siyasa da kuma kusan karfin iko a kasar. Yayin da samar da mai da kuma kuɗaɗen shiga ya ƙaru, gwamnatin Nijeriya ta zama mai dogaro da kuɗaɗen shiga na mai da kasuwancin kayayyakin masarufi na kasa da kasa, saboda damuwa game da kasafin kuɗi da tattalin arziki. Juyin mulkin a watan Yulin 1975, ƙarƙashin jagorancin Janar SHEHU MUSA YAR’ADUA da JOSEPH GARBA suka hamɓarar da Gowon, waɗanda suka gudu zuwa Biritaniya.Waɗanda suka yi juyin mulkin suna son maye gurbin mulkin Gowon ne da wasu janar-janar uku waɗanda Kwamitin Sojoji zai iya bijiro da hukuncin. A saboda wannan nasarar, sun shawo kan Janar MURTALA MUHAMMAD ya zama shugaban mulkin soja, tare da Janar OLUSEGUN OBASANJO a matsayin janar na biyu, da Janar THEOPHILUS ƊANJUMA a matsayin na uku. Tare da haɗin gwuiwa, sun gabatar da matakan tallafi na daƙile hauhawar farashin kaya, da kafa Ofishin Bincike na Yankin Cin Hanci, da maye gurbin duk gwamnonin soja da sabbin jami’ai, tare da ɓullo da “Operation Deadwood” ta hanyar da suka kori jami’ai 11,000 daga aikin farar hula.
    Kanar BUKA SUKA DIMKA ya ƙaddamar da juyin mulkin a watan Fabrairun 1976 a kan Gwamnatin Nijeriya, lokacin da aka kashe Janar Murtala Mohammed. Dimka ya rasa cikakken goyon baya a tsakanin sojoji da juyin mulkin da ya yi, kuma hakan ya tilasta shi tserewa. Bayan yunƙurin juyin mulki, an naɗa Janar Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban mulkin soja. A matsayinsa na shugaban ƙasa, Obasanjo ya yi alƙawarin ci gaba da manufofin Murtala. Sanin hatsarin dake tattare da raba kawunan ‘yan Arewacin Nijeriya, Obasanjo ya kawo Janar Shehu Yar’Adua a matsayin wanda zai maye gurbinsa da kuma muƙami na biyu a matsayin shugaban Ma’aikata, Babban hedikwatar da ta kammala aikin soja, tare da Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa, da Janar Theophilus Ɗanjuma a matsayin Babban Ma’aikatan Soja, ukun sun ci gaba da ƙoƙarin sake ƙwace iko da tsarin mulkin soja da tsara yadda za a sauya tsarin mulkin soja: jihohi da ƙirƙirar ƙasa, sake fasalin ƙananan hukumomi da kwamitin tsara kundin tsarin mulkin Jamhuriyyar Nijeriyar
  • ‘Yancin Kai Da Jamhuriya Ta Farko A Nijeriya (1960-1966)

    ‘Yancin Kai Da Jamhuriya Ta Farko A Nijeriya (1960-1966)

    Nijeriya ta samu ‘yanci daga ƙasar Ingila a ranar 1 ga Oktoba 1960, a matsayin Tarayyar Nijeriya, yayin da ta rike sarautar Ingila, Elizabeth ta II, a matsayin shugabar ƙasa mai martaba da Sarauniyar Nijeriya.
    Gwamnatin ƙasa Najeriya mai zaman kanta haɗin gwuiwar jam’iyyun ne masu ra’ayin mazan jiya: Kungiyar Hadin Kan Arewa (NPC) ƙarƙashin jagorancin SIR AHMADU BELLO, wata jam’iyya ce dake da rinjaye da Musulman Arewa, kuma Igbo da Kiristocin dake ƙarƙashin majalisar wakilan Nijeriya da Kamaraons (NCNC) ƙarƙashin jagorancin Nnamdi Azikiwe.
    Azikiwe ya maye gurbin janar-janar kan mulkin mallaka a watan Nuwamba 1960. ‘Yan adawar sun haɗa da wata kungiya mai sassaucin ra’ayi, wacce aka fi sani da Yarbawa da kuma Obafemi Awolowo. A lokacin ‘yancin kai, bambance-bambancen al’adu da siyasa sun ƙaru sosai a tsakanin ƙabilun dake da rinjaye a Nijeriya: Hausa-Fulani (Baƙi), Igbo (Baƙi’) da Yarbawa (‘Yammacin Turai).
    An ƙirƙiro rashin daidaituwa a cikin tsarin, sakamakon fatawar 1961. Kudancin Kamaru (tun daga masu raba gari da sunan Ambazonia) ya zaɓi shiga Jamhuriyar Kamaru, yayin da Kamarawan Arewa, suka zaɓi ci gaba da zama a Najeriya. Yankin Arewacin kasar sannan ya zama ya yi girma fiye da yankin Kudu.
    A shekarar 1963, Nijeriya ta zama Jumhuriya, tare da Azikiwe a zaman shugabanta na farko. Lokacin da aka gudanar da zaɓe a shekarar 1965, Jam’iyyar National Democratic Party ta hau karagar mulki a Yankin Yammacin Nijeriya.
  • Yadda Ake Gyara Farcen Turaren Wuta

    Yadda Ake Gyara Farcen Turaren Wuta

    YADDA AKE GYARA FARCEN TURAREN WUTA

    Farce ɗaya ne daga cikin kayan haɗi ne da ake amfani da shi wajen haɗa turaren wuta da humra da sauran nau’ikan turare.
    Dabbace a cikin ruwa ake samu, kuma sai an masa gyara sosai inba haka ba sai ya ɓata ma turare ba, zai ƙamshi mai daɗi ba.

    YADDA AKE WANKE FARCEN TURARE

    1. Za a zuba farce a tukunya a zuba masa ruwa da omo a ɗora a wuta, sai a bar shi ya tafasa .
    Sai a sakko da shi ya huce sarai .
    2- Za ka sa hannu a dinga wanke shi za ka ji wani abu a jikinsa kamar nama, har sai ya fice fes.
    3- Sai a zubar da ruwan, a zuba sabon ruwa a ci gaba da wankewa. In yai datti a ƙara sake ruwan har sai an ga yai fes.
    4- Sai a baza shi a tire(faranti) har ya kwana domin ya bushe sarai.

    YADDA AKE SOYA FARCEN TURARE

    Za ki samu ƙasa, ki zuba ta a cikin kasko. Ki juye busasshen farcen da kika wanke shi fes.
    Ki ɗora a kan wuta ki yi ta soyawa kamar dai suyar gyaɗa.
    Idan na turaren wuta ne, in ya yi ja sosai sai ki kwashe shi. In kuma na baƙar humra ce in ya yi ba ki sai ki sauke shi .
  • Zamanin Mulkin Mallaka (1500-1800) Tarihin Nijeriya kashi Na Biyu(2)

    Zamanin Mulkin Mallaka (1500-1800) Tarihin Nijeriya kashi Na Biyu(2)

    Tarihin Nijeriya (1500-1818)
    A cikin ƙarni na 16, masu binciken Ƙasar Portugal su ne mutanen farko na Turawa da suka fara kasuwanci kai tsaye, tare da mutanen Kudancin Nijeriya, a tashar jiragen ruwa da suka sanyawa suna Legas da kuma a Calabar ta yankin Slave Coast. Turawa sun yi ciniki tare da mutane a bakin tekun; Kasuwancin bakin teku tare da Turawa har ila yau, alama ce ta farkon kasuwancin bayi na Atlantika.
    Tashar  jiragen ruwa ta Calabar, a kan tarihin Bida na Biafra (wanda yanzu ana kiranta da Bight of Bonny) ya zama ɗayan manyan kasuwancin bayi a Yammacin Afirka, a zamanin cinikin bayi. Sauran manyan tashoshin jiragen ruwa a Nijeriya sun kasance ne a Badagry, Legas a kan Bight of Benin da kuma a tsibirin Bonny a kan Bight of Biafra.
    Mafi yawan waɗanda aka bautar da su zuwa wannan mashigan jirgin an kama su a cikin hare-hare da yaƙe-yaƙe. Yawancin lokaci ana mayar da fursunoni zuwa yankin masu nasara a matsayin tilasta masu aiki; bayan lokaci, a wasu lokuta ana tattara su, kuma su shiga cikin jama’ar masu nasara. An samar da hanyoyi da yawa na bayi a cikin Nijeriya waɗanda ke haɗa wuraren dake bakin teku da manyan tashoshin teku.
    Wasu daga cikin mafi muhimmancin masarautun kasuwanci, waɗanda suka shiga cikin kasuwancin bayi, sun kasance suna da alaƙa da Daular Edo ta Benin a Kudu, Masarautar Oyo a Kudu maso Yamma, da kuma  Conferaeracy a Kudu maso Gabas. Beninarfin Benin ya ƙare tsakanin ƙarni na 15 zuwa na 19.
    Nasarar mulkinsu ya kai har zuwa garin Eko (wani sunan Edo daga baya ya canza ta zuwa Legas daga Fotigal) da ƙari. Oyo, a iyakar yankinta a karshen karni na 17 zuwa farkon ƙarni na 18, ya faɗaɗa tasirinsa daga yammacin Nijeriya zuwa Togo. Masarautar Edo ta Benin tana cikin Kudu maso Yammacin Nijeriya.
    A Arewaci, gwagwarmaya tsakanin jihohin Hausawa da ragowar Daular Bornu ya haifar da ƙungiyar Fulani ta shiga cikin yankin. Har zuwa wannan lokaci, Fulani wata ƙabila ce mai kiwo, da farko sun bi yankin Sahelian na hamada, dake Arewacin Sudan, da satar shanu da kauce wa ciniki da kuma yin shisshigi tare da mutanen Sudan, A farkon ƙarni na 19, Usman Ɗan Fodio ya jagoranci gwagwarmaya da nasara a kan masarautun Hausa, waɗanda aka kafa cibiyar Sakkwatocin Sakkwato (wanda kuma ake kira Daular Masarautar Fulani).
    Daular tare da Larabci a matsayin harshenta, na haɓaka cikin sauri a ƙarƙashin mulkinsa da na zuriyarsa, waɗanda ke aika mayaƙa ta kowane ɓangare. Manyan daulolin da suka mamaye yankin sun haɗa Gabas da yankin Yammacin Sudan sannan suka sanya Kudu zuwa wasu yankunan Daular Oyo ,suka kuma wuce zuwa yankin Yarbawa na Ibadan, tare da burin isa tekun Atlantika.
    Iyakokin da masarautar ta ƙunsa ya ƙunshi yawancin Arewacin yau a tsakiyar Nijeriya. Sarkin Musulmi ya aike da sarakuna don kafa madawwamiyar iko a kan yankuna da aka ci da yaƙi da kuma bunƙasa wayewar Musulunci, bi da bi kuma sarakunan sun sami wadata da ƙarfi duk da cewa kasuwanci da bautar. Ya zuwa shekara ta 1890, mafi yawan bayi a duniya, kusan miliyan biyu, an mai da hankali ne ga yankuna na Sakkwato. Yin amfani da bautar bayi ya yawaita, musamman a aikin gona. Har ya zuwa lokacin da ta wargaje a cikin shekarar 1903 zuwa ga masarautun Turai daban-daban, Masarautar Sakkwato ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka da suka yi mulkin mallaka a baya.
  • Tarihin Nijeriya Kashi Na Ɗaya(1)

    Tarihin Nijeriya Kashi Na Ɗaya(1)

    Tarayyar Nijeriya, ƙasa ce mai ‘yanci, wacce take a Yammacin Afirka dake iyaka da Nijar a arewa, Chadi a arewa maso gabas, Kamaru a gabas, da Benin a yamma. Bakin tekunta ta kudu suna kan tekun Guinea ne a tekun Atlantika. Nijeriya babbar jamhuriyya ce ta tarayya, wacce take da jihohi 36 da kuma Babban birnin tarayya, inda babban birnin tarayya a Abuja yake.
    Nijeriya ta kasance gida ga tsoffin gwamnatocin ƙasashe da suka yi mulkin mallaka da masarauta tun shekaru aru-aru. Harshen zamani ya samo asali ne daga mulkin mallakar Turawan Ingila tun daga karni na 19, sannan ya ɗauki yankinsa na yanzu tare da haɗewa da Kudancin Nijeriya na kariya da Arewacin Nijeriya kariya a shekara ta 1914(amalgamation) daga hannun FRED FREDRICK LUGARD.
    Birtaniya ta kafa tsarin gudanarwa da na doka, yayin aiwatar da mulkin kai tsaye ta hanyar manyan hanyoyin gargajiya; Nijeriya ta zama ƙungiya mai zaman kanta a ranar 1 ga Oktoba, 1960. Ta samu yaƙin basasa daga 1967 zuwa 1970.Bayan haka ta sauya tsakanin gwamnatocin farar hula da aka zaɓa da mulkin soja har sai ta samu ingantacciyar demokraɗiyya a shekarar 1999.
    Nijeriya tana da ƙabilu sama da 250 waɗanda ke da yarika sama da 500 waɗanda suke da al’adu iri-iri. Ƙabilu mafiya girma, mafi shahara guda uku ne a Nijeriya waɗanda suka haɗa da: HAUSA–FULANI a AREWA YARBAWA a YAMMA, da IGBO a GABAS; ya ƙunshi sama da 60% na yawan jama’a. Harshen hukuma shi ne Ingilishi. An zabi Ingilishi ne don sauƙaƙe haɗin harshe a matakin ƙasa. Nijeriya ta kasu kusan rabi tsakanin Kirista, wadanda galibi suke zaune a Kudancin kasar, da kuma Musulmai, galibi suna zaune a Arewa.
    Ƙasar ta Nijeriya tana da yawan musulmai, kuma tana cikin na biyar a duniya da suke da musulmi da kuma yawan mabiya addinin Kirista na shida a duniya, tare da tsarin mulki wanda ke tabbatar da ‘yancin addini. Tsiraru daga cikinsu na yawan gudanar da addinai na asalin Nijeriya, kamar waɗanda ke asalin ƙabilar Igbo da Yarbawa.
    Nijeriya ita ce ƙasa mafi yawan jama’a a Afirka, kuma na bakwai mafi yawan al’umma a duniya, wanda ke da kimanin 206 miliyan mazaunan har zuwa ƙarshen 2019.
    Jamhuriyar Njeriya tana da yawan matasa na uku a duniya, bayan India da China, tare da sama da miliyan 90 na yawan jama’arta ‘yan ƙasa da shekaru goma sha takwas.
    Tarayyar ta Nijeriya na da mafi ƙarfin tattalin arziki a Afirka, kuma ita ce ƙasa ta 24 mafi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya bisa ga lissafin da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ta bayar a harsashenta na (kimanta 2020), da darajan sama da Dala biliyan 500 da $ 1 tiriliyan dangane da GDP na maras muhimmanci, a bi da bi. A Matsakaicin bashi zuwa GDP na 2013 ya kasance kashi 11 bisa ɗari yayin da na 2019 ya tashi zuwa kimanin kashi 16 cikin ɗari.
    Nijeriya wata ƙasa ce mai matsakaiciyar ƙasa, wacce ke da kudin shigar kowace kasa a tsakanin dala 1,026 zuwa $ 3,986. Ana kiran Nijeriya da suna “Giant of Africa”, saboda yawan jama’a da tattalin arziƙinta, Haka nan ana ganin kasuwa ce dake fitowa daga Bankin Duniya; an gano shi a matsayin ikon yanki a kan yankin Afirka, wani yanki na tsakiya a cikin harkokin ƙasa da ƙasa, kuma har ila, yau an gano shi a zaman mai ƙarfi na duniya. Asalin cigaban ɗan Adam ya zama na 158 a duniya.
    Nijeriya memba ce a cikin kungiyar MINT ta kasashe, wadanda ake ganinsu a matsayin kasashen dake gaba, na tattalin arziki “BRIC-like” na gaba. Haka nan an lissafa shi daga cikin “tattalin arziki na gaba” na gaba “wanda zai zama na daga cikin manya-manya a duniya. Nijeriya memba ce ta Ƙungiyar Tarayyar Afirka, kuma memba ce a wasu ƙungiyoyi daban-daban na duniya, waɗanda suka haɗa da Majalisar Ɗinkin Duniya, Tarayyar Afirka, ECOWAS, da OPEC
    Sunan Nijeriya ta samo asali ne daga Kogin Neja, wanda yake gudana a cikin ƙasar. Wannan sunan an sanya shi ne ranar 8 ga Janairu, 1897, daga marubuciyar jaridar Birtaniyar, Flora Shaw, wanda daga baya ta auri LORD LUGARD, wani shugaba mai mulkin mallaka na Burtaniya. Asalin sunan Nijar, wanda ya samo asalinsa da tsakiyar kogin Neja, ba shi da tabbas. Wataƙila kalmar tana iya canza sunan Tuareg egerew n-igerewen da mazaunan suke amfani da shi, a tsakiyar kogin da ke kusa da Timbuktu kafin fara mulkin mallaka na ƙarni na 19.

    Domin ci gaba da karatu danna nan.