Tag: ilimi

  • Yadda Ake Yin Kabbarar Harama

    Yadda Ake Yin Kabbarar Harama

    Bayan gama iƙama a sallar jam’i ko sallar mutum shi kaɗai; mace ce ko namiji, sai ya yi kabbarar harama wacce ita ce mabuɗin sallah.

    Yadda ake yin ta shi ne, furta kalmar (Allahu Akbar) tare da ɗaga hannuwa biyu daidai kafaɗu biyu; ko kuma daidai kunnuwa biyu; ko kuma saman ‘yan yatsun, su kawo daidai kunnuwa.

    Shi kuma mahaɗar tafin hannu da tsintsiyar hannu ya zo daidai kafaɗu; wannan kabbarar haramar ita ce da zarar mai sallah ya furta ta, ta haramta masa duk wani aiki da ba shi da alaƙa da sallar; kamar yin magana, ko waiwaiye, ko cin wani abu, ko tauna, ko dariya, ko sauraren wani abu can daban, da bai shafi karatun liman ba.

    Sai ɗan abin da yin sa babu laifi, kamar yin kuka saboda jin abin da Ƙur’ani yake faɗa; na rahama, ko azaba, ko daɗin karatun ko sosa jiki, ko yin ɗan motsi kaɗan, ko gyaran murya. Yin wannan kabbara ta harama, wajibi ne a sallah ga bin jam’i ko yin sallah; shi kaɗai mace ce ko namiji ne, mamu ne ko limami ne, wanda duk bai yi ta ba, ba shi da sallah, saboda da ita ce ake fara buɗe sallar, kamar yadda bayani ya gabata.

    Ana so mai sallar ya yi (du’aa’ul istiftah) wato addu’ar buɗe karatun sallah wacce yin ta (mustahabi) ne; ma’ana abin da aikata shi lada ne, rashin aikata shi kuma ba laifi ba ne; a taƙaice dai an ba ka zaɓi na idan kana so ka yi; idan ba ka so kuma ka bari.

    Ga yadda ake furta wannan addu’ar:

    (Allahumma baa’id baini wa baina kaɗayaya kama ba adta bainal mashriqi wal magribi, Allahummag silni bil ma’i wal salji wal bardi wa nakkini minaz zunubi wal kaɗayaya kama yunaƙƙal saubul abyad minal danas).

    Fasarar wannan addu’a shi ne; Allah ka nisanta tsakanina da zunubaina kamar yadda ka nisanta tsakanin mahudar rana da mafaɗar ta; Allah ka wanke ni da ruwa da kankara da ruwan sanyi, ka wanke ni daga zunubaina da kurakuraina; kamar yadda ake wanke fararen tufafi daga cikin datti.

    Bayanin da Ibnu taimayyah ya yi a kan wannan addu’ar a lokacin da ɗalibinsa; Ibnul Ƙayyim ya tambaye shi ma’anar wannan addu’a ga mai yin sallah, shi ne ya ce; “Idan mutum yana aikata saɓo zuciyarshi bushewa take yi, har ta kai matakin da za ta yi tauri, yadda hasken imani ba zai iya shiga ba, sai ya wayi gari imaninsa ba ya ƙaruwa.

    Idan ya aikata wani babban saɓon, sai zuciyarsa ta kama da wuta tana cinye ragowar imanin da ke zuciyar. Ga shi kuma babu abin da ke kashe wuta sai ruwa, shi Kuma ruwan sanyi shi ne zai ƙarasa murkushe ragowar ɓurɓushin wutar, bayan an kashe asalin wutar da ruwa, ita kuma ƙanƙara ita ce za ta mayar da zuciyar ta koma mai laushi, kamar yadda take kafin ta aikata manyan saɓo. Wannan shi ne dalilin da yasa ake so mumini ya dinga yin wannan addu’ar.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani da Bismillah A Cikin Sallah Danna nan

  • Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da Bismillah A Cikin Sallah

    Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da Bismillah A Cikin Sallah

    Mai yin sallah zai buɗe karatun Alƙur’ani da Bismillah a ɓoye, ba tare da mamu sun ji karatun Bismillah ba, shi ne limami kuma sallah ce da ake bayyana karatu.

    A mazhabin Malikiyya kuma zai bayyana karatun Bismillah ne a fili, zai karanta Fatiha sannan ya sake yin wata Bismillah kafin ya karanta surar gaba.

    Zai tsaya ne ya ɗora hannunsa na dama a kan hannunsa na hagu; a kan ƙirjinsa ko ƙasan ƙirjinsa saman cibiyarsa; ya ɗora idanunsa biyu a daidai inda yake sujuda, kuma ya bar idanunsa a buɗe, ba tare da lumshe su ko rufe su ba; domin rage yawan tunani da zancen zuci a cikin sallah.

    Sannan zai karanta surah ko wani yanki na surah ko wasu ayoyi; gwargwadon abin da Allah ya sanar da shi na Alƙur’ani yana tsaye; yana iya fasa karanta surah ko ya canza surah idan ya ji ya kakare; ko kuma ta ɗauke a cikin ƙwaƙwalwarsa ko ya rasa mai tuna masa ko bai rasa ba, 

    Yana iya karanta aya ɗaya koda ba mai tsayi ba ce, wajan karatu ya kula da haƙƙin mamu; kar ya tsawwala musu wajen karanta surori masu tsayi ko yawa idan yana limanci; idan shi kaɗai ne ya tsawaita yadda ya so.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Alwala danna nan

  • Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

    Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

    A yadda mayuka da kayayyakin gyaran jiki suka yi yawa a kasuwa; zaɓar abubuwan da za su taimaka wa fatar jikinki yana iya zama abu mai matuƙar wahala. Amma idan kin san yanayin fatarki, sai ki zaɓi abubuwan da za ki yi wajen kula da fatarki a kullum.

    Ga misalan yadda za ki kula da fatarki:

    1. Goge Kwalliya Kafin Bacci

    Idan ya kasance an miki kwalliya mai yawa ta zamani, to yana da kyau ki samu abin da za ki goge ta tas, kafin ki kwanta barci. Koda wacce ta yi miki kwalliyar ta taya ki gogewa, amma idanuwa da laɓɓa suna buƙatar kula ta musamman, saboda haka; sai ki samu abin goge kwalliya (wiper) jiƙaƙƙiya, ki sake gogewa a hankali.

    2. Wanke Fuska

    Yana da kyau mace ta dinga wanke fuskarta sau biyu a rana. Da safe kafin ki yi kwalliya, sai kuma da dare kafin ki kwanta. Ana wanke fuska da ruwan ɗumi, ba mai zafi ba; sannan kuma a sake shafa sabulu a murza a hankali lungu da kwarmin fuska, sannan a sake ɗaurayewa.

    3. Amfani Da Toner

    Bayan an wanke fuska, ana so a shafa toner. A samu wani ɗan soso mai laushi a matsata kaɗan, sai ana shafawa a hankali ban da gurin ido sannan ba a wankewa.

    4. Amfani Da Moisturizer

    Bayan toner ta bushe a kan fuskarki, yana da kyau a yi amfani da moisturizer a kan fuska, hadda tafin hannu ma idan kin so. Idan kuma kina fama da baƙin zagaye ko kumburi ko tattarewar ido, sai ki samu wani mai na musamman.

    5. Yin Murza (Scrubbing)

    Ana iyayin murza ta, musamman sau ɗaya ko sau biyu a sati, za ki samu sinadarin AHA ko BHA ko Kuma wani sabulun ruwa, sai kina dangwala da hannunki, kina murzawa a hankali a kan fuskarki.Bayan wasu mintoci sai a wanke da ruwan ɗumi.

    6. Yin Amfani Da (Sunscreen)

    Yawan shiga rana kan iya jawo tattarewar fuska, ko kuma nuna alamun girma. Yana da kyau duk lokacin da za ku fita rana, ku shafa sinadarin da yake hana hasken rana illa a kan fatarku. Ana shafa wannan sinadarin ne bayan amfani da toner da moisturizer.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman danna nan

    Domin karanta bayani akan Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau danna nan

  • Hukunce-Hukuncen Jinin Cuta

    Hukunce-Hukuncen Jinin Cuta

    Shin ko kun san mene ne hukuncin jinin cuta?

    Jinin cuta ba ya hana wani abu daga abubuwan da jinin haila da na biƙi suke hanawa; kuma haƙiƙa mai jinin cutar hukuncin ta ɗaya da mace mai tsarki, tana salla, kuma tana azumi; kuma tana ittikafi a cikin masallaci, kuma ana iya saduwa da ita.

    Fadima ‘yar Abi Hubaish, Allah ya yarda da ita ta ce:

    “Ya Manzon Allah, ni ina jini ba na tsarkaka, shin zan bar salla ne?

    Sai Manzon Allah ya ce: “A’a, … idan hailar ta zo, to ki bar salla, idan kuma ta kau, to ki wanke jinin ki yi salla”.

    Sai dai mai jinin cuta tana yin alwala lokacin shigar kowace sallah.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Hana Mace Bin Miji danna nan.

  • Hukunce-hukuncen Jinin Haila Da Na Biƙi

    Hukunce-hukuncen Jinin Haila Da Na Biƙi

    Mene ne yake haramta saboda jinin haila da na biƙi?

    Salla tana haramta saboda jinin haila da na jinin biƙi da Azumi da Ɗawafi da saduwa da saki; a bisa haɗuwar Malamai.

    Kuma maganganun malamai sun saɓa game da zama a masallaci da taɓa Alƙur’ani da karanta shi; sai wasu daga cikinsu suka halatta haka, wasu kuma suka hana.

    Ko za ka ambata mana dalilan haramcin abubuwan da suka gabata?

    Amma haramcin salla, saboda jinin haila dana biƙi. Saboda faɗar Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa, ga Faɗima ‘yar Abi Hubaish. Idan haila ta zo, to ki bar sallah.

    Amma haramcin yin Azumi, saboda jinin haila da na biƙi; saboda faɗar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa; shi ashe ba idan ɗayarku tana jinin haila ba ta Azumi ba ta salla ba? Suka ce haka abin yake.

    Dalilin haramcin yin Ɗawafi, saboda jinin haila da biƙi faɗar Manzon Allah; tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi;

    Ga A’isha lokacin da ta yi jinin haila tana mai harama da aikin Hajji; ki aikata duk abin da mai aikin Allah, har sai kin samu tsarki;

    Haramun ne saduwa da mai jini haila da na biƙi.

    Saboda faɗar Allah Maɗaukaki: “To ku ƙaurace wa mata a kwanakin jinin haila; kuma kada ku kusance su har sai sun samu tsarki”.

    Kuma saboda faɗar Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa, lokacin da ayar ta sauka; “Ku aikata komai da matanku, in ban da saduwar aure”.

    Abin da ake nufi da haka a sake su lokacin tsarkin da ba a sadu da su ba.

    Faɗakarwa:

    Jinin biƙi yana bambanta da na haila ne; da kasancewar idda ba ta afkuwa da shi; saboda iddar mai ciki tana ƙarewa ne da haifar ciki.

    Allah Maɗaukaki ya ce: “Mata masu ciki iddarsu shi ne su haife cikinsu”.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Tukunyar Mace Ta Musamman danna nan.

  • Maimaituwar Jinin Haila A Wata Ɗaya

    Maimaituwar Jinin Haila A Wata Ɗaya

    Shin jinin haila yana maimaituwa a wata ɗaya?

    Ko mai ciki tana jinin haila?

    Galibin mace tana jinin haila a kowane wata haila ɗaya, saura kwanakin watan kuma suna zama tsarki; sai dai ana samun wacce take jinin haila a wata sau biyu.

    Mai ciki tana jinin haila kuwa?

    Malamai sun yi saɓani game da jinin da wasu daga cikin mata suke gani a tsaka da lokacin ciki. Sai wasu daga cikinsu suka ce, “Haƙiƙa shi jinin ne da hujjar afkuwar sa a sifar jinin haila ga wasu daga cikin mata kuma wasu daga cikinsu suka ce:

    “Haƙiƙa shi ba jinin haila ba ne, a’a, shi jinin cuta ne, domin shi jinin haila rushewar shirin mahaifa ne game da ɗaukar ciki, idan ciki ya samu sai a rasa jinin haila. Kuma saboda Hadisin da Imam Ahmad ya rawaito daga salim daga babansa cewa;

    Haƙiƙa ya saki matarsa, alhali tana jinin haila, sai Umar ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa, game da haka. Sai Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa, ya ce:

    “Ka umarce shi da ya mayar da ita, sannan ya sake ta tana mai tsarki ko tana mai ciki”. Sai ya sanya ciki ya zama alama a kan rashin jinin haila, kamar yadda ya sanya tsarki ya zama alama a kan rashin sa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Fassarar Littafin Fikhul Muyassar Na Biyu wanda Rukayya Dalha ta wallafa shi; Domin karanta cikakken littaffin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Darasi Na Biyar Game Da Bayanin Mafi Yawancin Kwanakin Jinin Biƙi danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Wannan Ita Ce Mace Tagari danna nan

  • Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

    Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

    An haifi Sa’idu Muhammad Gusau a ranar 24 ga watan Maris 1952 a shiyyar Madawaki, bakin Masallacin Juma’a; unguwar Bube Attajiri da ke garin Gusau, Jihar Zamfara.

    Farfesa Gusau ya fara karatun allon a gaban Mahaifinsa Malam Muhammadu Ɗankullum da Malam Husaini Kanoma da Malam Labbo Haruna Gummi da sauransu; inda har Allah ya sanya ya sauƙe Alƙur’ani mai tsarki tun yana da shekaru goma sha huɗu (14) a duniya.

    Dagan aka sanya shi a makarantar Nizamiyya Islamiyya; a ƙofar gidan Ɗangaladiman Waziri Malam Attahiru daga 1965 zuwa Disamba 1969.

    Ya zarce zuwa Kwalejin Sarkin Musulmi Abubakar, Sashen Koyar da Larabci da Addinin Musulunci (H.M.S) Sakkwato daga Janairu; 1970 zuwa Yuni, 1973.

    A watan Oktoba na shekarar 1974 ya sami gurbin karatun Difloma a fannin Hausa da Larabci da Addinin Musulunci a Kwalejin Abdullahi Bayero Kano, kuma ya kammala a watan Yuni shekarar 1977.

    Sannan ya ci gaba da karatun digirin farko (B.A Combined Honors) a Jami’ar Bayero Kano, daga Oktoba, 1977 zuwa Yuni 1980.

    Bayan nan, sai ya sake komawa karatun digiri na biyu (M.A) a fannin Hausa daga Oktoba, 1982 zuwa Oktoba, 1983; A watan Mayu na shekarar 1989 ce ya kammala karatun digirinnsa na uku (Ph.D) a fannin Hausa; a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.

    Farfesa Gusau:

    Ya koyar a Makarantar Firamare ta cikin garin Talatar Mafara, wato Township daga Satumba 1973 zuwa Satumba, 1974. Ya koyar a Makarantar Horon Malamai ta U.P.E Wasugu, a shekarar 1977.

    Sannan ya yi karantarwa a Kwalejin Larabci (S.A.S) daga Agusta, 1980 zuwa Yuli, 1981.
    Farfesa Gusau ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban Makarantar Horon Malamai (G.T.C) Zuru daga 1981 zuwa Satumba, 1982. Ya taɓa zama Shugaban Sashen Hausa (H.O.D Hausa) a Babbar Kwalejin Horon Malamai (A.T.C), Maru daga 1984 zuwa Satumba, 1985.

    Daga watan Yuni na shekarar 1990 ya juya aikinsa na koyarwa zuwa Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami’ar Bayero Kano, a matsayin Malami mai daraja ta ɗaya.

    A shekarar 1991, ya zama Babban Malamin Jami’a, sai a shekarar 1995 aka ɗaga shi gaba ya zama Mataimakin Farfesa. A ranar ɗaya ga watan Oktoba, 2000 ya zama Farfesa.

    Farfesa Gusau ya yi rubuce-rubuce da dama a cikin muƙalu da rubuta littattafai da dama waɗanda suka shafi Hausa da kuma na Addinin Musulunci. Ya kuma halarci tarukan ƙara wa juna sani da dama, kuma ya gabatar da muƙalu da dama a tarukan.

    Yanzu haka yana zaune a Kano tare da iyalansa (matansa da ‘ya’yansa da jikokinsa) (Gusau, 2020:91-92).

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi: Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Yabo danna nan

  • Yadda Ma’anar Roƙo Take

    Yadda Ma’anar Roƙo Take

    Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya (2006:374), ta bayyana roƙo da cewa; “Sana’ar maroƙa ta yi wa mutane kirari ko yabo don a yi musu kyauta” Ko kuwa, “Neman kyauta daga wani”.

    Kenan roƙo, wata dabara ce ta neman abu a hannun wani ta hanyar zuga shi da yi masa kirari da yabon kyawawan halayensa; a wani lokacin ma da ƙoƙarin ƙarin gishiri kan halin da ba nasa ba.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Wayon Roƙo a Adabin Baka; Nazarin Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa danna nan

    Domin karanta bayani akan Kasuwanci Da Fatauci A Ƙasar Hausa danna nan

  • Ma’anar Yabo

    Ma’anar Yabo

    Yabo na nufin ba da shaida mai kyau game da mutum bayan ya yi wani abin a yaba; na burgewa ko kuma ana so ya aikata abin na burgewa ko na a yaba.

    Misalin Yabo:

    Jagora: Ka ji waƙa tana fita,
    Gurin ɗan Bafillatana,
    Abu kamar harsashi,
    In na yi hushi harsashin ɗin me?
    In dai waƙa ce,
    Allah ya yarda. (Gusau, 2009:350).

    A nan, za mu fahimci yabo da cewa wasu kalmomi ne da ake amfani da su wajen bayyana zahirin yadda mutum yake, shin waɗannan kalmomin da aka ambata ƙarya ce ko kuma gaskiya ce.

    Domin akan yabi mutum ta hanyar faɗar abin da yake ba gaskiya ba ne, an dai yi ne kawai domin a faranta masa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi: Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammd Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabo A Waƙoƙin Baka danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan

  • Ma’anar Kiɗa da Makaɗi

    Ma’anar Kiɗa da Makaɗi

    Da yake aikin ya shafi kiɗa ne, ya kamata a bayyana ma’anar kiɗa da kuma makaɗi.

    Alhassan da wasu (1982:75) sun bayyana kiɗa da cewa; “Shi ne buga abubuwan da aka yi musamman don bugawa da busa abubuwan da aka yi don busawa; shi ake kira kiɗa.

    Kayan kiɗan wato na bugawa da na busawa har ma da na girgizawa suna da yawa a Hausa, sai dai a raba su aji-aji”.

    A wurin Zarruƙ da wasu (1987:1) kiɗa na nufin; “Wanzar da daddaɗan amo daga abubuwan bugawa ko na gogawa ko na busawa ko kuma na girgizawa.”

    Shi kuwa Gusau (2014:7) ya bayyana makaɗi a ma’ana ta fannu da cewa; “Makaɗi shi ne wanda yake gwama kiɗan da waƙa lokaci ɗaya, kuma yake shirya kalmomi cikin jumloli ya fitar da martani na waƙa, ya rera shi, ya sadar da shi, sannan ya lizamci yin haka har ya zama mai raya adabi.”

    Makaɗan Hausa suna amfani da kayan kiɗan mabambanta don ƙara wa waƙoƙinsu zaƙi da karsashi da jan hankalin mai sauraro.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ra’in Bincike Hausawa danna nan