Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ɓaɓatu - Tana nufin magana ba ƙaƙƙautawa. Misali; Mun baro su suna ta ɓaɓatu a ɗakin taron. ENG; Noisy (A turance tana nufin ɓaɓatu)
Ɓaɓe - Tana nufin samun saɓanin da zai kai ga kowa ya kama gabansa. Misali; Talle ya ɓaɓe da budurwarsa jiya. ENG; Break Off relationship (A turance tana nufin ɓaɓe)
Ɓaɓɓake - Tana nufin jijjige abu daga tushensa. Misali; Ya ɓaɓɓake bishiyar daga ƙofar gidansa. ENG; Uproot (A turance tana nufin ɓaɓɓake)
Ɓingire - Tana nufin kwanciya ba tare da tsammani ba.  Misali; Ta ɓingire da bacci ana karatu. ENG; Topple Over (A turance tana nufin ɓingire)
Ɓoye - Tana nufin a ɗauke abu a kai shi inda ba za a ganshi ba. Misali; Yaran sun ɓoye kayan wasan su, mun nema mun rasa. ENG; Hide (A turance tana nufin ɓoye)
Ɓulele - Tana nufin mai ƙiba. Misali; Sabon ɗalibin da aka kawo mana ɓulele ne. ENG; Fat (A turance tana nufin ɓulele)
Ɓullo - Tana nufin fitowa. Misali; Rana ta ɓullo da wuri yau. ENG; Appear Suddenly (A turance tana nufin ɓullo)
Ɓulɓul - Tana nufin ƙiba sosai. Misali; Jamila ta yi ɓulɓul tunda ta dawo daga Ikko. ENG; Excessive Fat (A turance tana nufin ɓulɓul)
Ɓuntu - Tana nufin kwanson da shinkafa ke ciki. Misali; Shinkafar da muka siyo cike take da ɓuntu, sai an gyara ta ƙwarai. ENG; Husks of Rice (A turance tana nufin ɓuntu)
Ɓuruntu - Tana nufin ɓare-ɓare da hayaniya. Misali; Ɓera yana ta ɓuruntu a ɗakin Kaka. ENG; Looting in a noisy manner (A turance tana nufin ɓuruntu)
1 293 294 295 296 297