Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ɓari - Tana nufin zubar da abu ba da gangan ba. Misali; Kande ta yi ɓari ɗazu, duka garin tuwon ta zubar. ENG;Dropping Something (A turance tana nufin ɓari)
Ɓari - Tana nufin karkarwa saboda jin sanyi. Misali; Gambo sai ɓari yake saboda zafin zazzaɓi. ENG; Shivering (A turance tana nufin ɓari)
Ɓarna - Tana nufin lalata abu. Misali; An yi iska mai ƙarfi jiya kuma ta yi ɓarna sosai ENG; Damage (A turance tana nufin ɓarna)
Ɓarza - Tana nufin niƙa tishi ɗaya ko biyu, ma'ana ba mai laushi ba. Misali; Na kai wa Inna ɓarza, za ta yi dambu da yamma. ENG; Grind Coarsely (A turance tana nufin ɓarza)
Ɓata - Tana nufin a nemi abu a rasa. Misali; Ina tunanin takalmin ya ɓata, don na duba ko ina ban ganshi ba. ENG; Lost (A turance tana nufin ɓata)
Ɓauna - Tana nufin wata dabbar daji mai kama da saniya. Misali; A gidan ajiyar namun daji akwai ɓauna da sauran manyan dabbobi. ENG; Bush-cow (A turance tana nufin ɓauna)
Ɓaɓatu - Tana nufin magana ba ƙaƙƙautawa. Misali; Mun baro su suna ta ɓaɓatu a ɗakin taron. ENG; Noisy (A turance tana nufin ɓaɓatu)
Ɓaɓe - Tana nufin samun saɓanin da zai kai ga kowa ya kama gabansa. Misali; Talle ya ɓaɓe da budurwarsa jiya. ENG; Break Off relationship (A turance tana nufin ɓaɓe)
Ɓaɓɓake - Tana nufin jijjige abu daga tushensa. Misali; Ya ɓaɓɓake bishiyar daga ƙofar gidansa. ENG; Uproot (A turance tana nufin ɓaɓɓake)
Ɓingire - Tana nufin kwanciya ba tare da tsammani ba.  Misali; Ta ɓingire da bacci ana karatu. ENG; Topple Over (A turance tana nufin ɓingire)
1 295 296 297 298 299 300