Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Small Dove - A turance tana nufin kurciya.
Misali; Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa.
HAU; Kurciya (Tana nufin ƙaramar tsuntsuwa)
Small hide container - A turance tana nufin kuratandu.
Misali; Inna Hajjo ta kawo wa mai jego kyautar kurantandu cike da farin kwalli.
HAU: Kuratandu (Tana nufin mazubin kwalli wato mazubin da ake adana kwalli a ciki)
Small Hole - A turance tana nufin kafa.
Misali; Ko yaya ɓeran ya samu kafa guduwa zai yi.
HAU; Kafa (Tana nufin ƙaramar hanya)
Small one stringed bowed musical instrument - A turance tana nufin kukuma.
Misali; Makaɗan kukuma suna da baiwa ta musamman.
HAU; Kukuma (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kaɗe-kaɗe na gargajiya)
Small one-stringed plucked musical instrument - A turance tana nufin kuntigi.
Misali; Na jiyo kiɗan kuntigi a ƙofar gidan maigari.
HAU; Kuntigi (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa)
Small patch or plot of land given to a young boy to farm on - A turance tana nufin gayauna.
Misali; An ba wa Ɗahiru gayauna saboda ya samu kuɗin hidimar bikin kalankuwa.
HAU; Gayauna (Tana nufin wani sashi na gona da ake ba wa matasa don su noma)
Small poisonous green snake - A turance tana nufin damatsiri.
Misali; Akwai damatsiri a gonar shinkafar da ke bayan gari.
HAU; Damatsiri (Tana nufin ƙaramin koren maciji mai dafi)
Small Round Gourd - A turance tana nufin kurtu.
Misali; Maharazu ya zuba tawada a cikin kurtu.
HAU; Kurtu (Tana nufin ƙaramin mazubi na duma)
Smoke - A turance tana nufin hayaƙi.
Misali; Hayaƙi yana tashi saboda itacen ɗanye ne.
HAU; Hayaƙi (Tana nufin abin da yake fitowa daga wuta idan an kunna, yana cutar da huhu musamman idan ana shaƙar sa da yawa)
So Angry - A turance tana nufin fusata.
Misali; Ya fusata sosai har kyarma yake.
HAU; Fusata (Tana nufin tsananin fushi)